← Book details Tushen Mu Daya Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 39 OF 78

Sashe 39

Tushen Mu Daya Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Na tabbatar zai aikata dan yadda yake zare ido yana da,da, kawo wukar kusa dani da ba abin da zai hanashi yankar tawa

Ina ji ina gani ya kamani ya hada hannayena ya daddaureni ya hada kafafuwana da jikin gadon ya daure su

Kawai na gama saddakarwa yau shikenan ya gama dani addu,o,i kawai nake taja a zuciyata akan allah ya kawomin dauki ga waje ni kadai ba kowa

ya na gama daddaureni ya tashi yana layi ya haskeni da fitila ya haskeni yana lashe baki nan yashiga babbaka dariya yana nuna ni da hannu

Ashe dai kedin karamar mara kunya ce hhhh ina cika bakin naki na banza da kike na kinfi karfina zaki tona min asiri

Yau dai gani gaki daga ni saike babu mai kwatarki zanyi abin dana ke so dake babu mai hanani inyaso saiki fito kice ni na shigo dakinki na miki wani abu hhh kinga sai inga wanda zai yarda

Kinsan dai hajjo ba yarda zatai ba ki batamin suna dan awajenta ma nayi tafiyar dana ce mata zanyi tun shekaran jiya kinga kowa yasan bana ma gida bare ko kince nine a yarda inyi abin danake so inyi gaba

Nan ya shiga kokarin kunce belt din jikin wandon shi yana dariya yana nuna ni da wukar hannun shi

Da sauri na kauda kaina wasu zafafan hawaye na zubomin cikin tsananin kunar zuciya ina kara jan addu,o,i a zuciya ta duk da kuwa yana shirin aiwatar da mummunan kudirin shi a kaina nasan dole sai allah ya so zai aikata min abin da yayi niya

Ya allah kada ka jarrabeni da abin da bazan iya ba na rintse danuwana hawaye nata sintiri bisa kuncina

Naji saukar numfashinsa a gefen fuskata yana busamin iskar bakinshi me shegen warin kayan mayen da yasha da sauri na kauda kaina ina mai rintse ido

Kaina yayo gaba daya najishi jikina ina jinshi lokacin da yake amfani da hannunshi daya yana kokarin rabani da kayan jikina har zuwa lokacin bai rabu da wukar hannunshi ba

Taimakon allah kawai naci gaba da nema jin har ya rabani da zanin jikina ya rage min pant din dana sa a ciki
cikin sauri na kauda kaina ina mai zubda hawaye

Nasan banida wani karfi a halin yanzu koda ba wuka a hannun sa innace inyi ihu babu maijina saboda muryata gaba daya ta dashe na riga dana mika lamurana wajen ubangiji shine kawai zai cece ni

Ina cikin tunanin naji ya fara jan wandon jikina cikin son ya rabani dashi

*_Wayyo allah aminatu😭😭🤦🏻‍♀️Baiwar allah_*

*Sai kuma monday insha allah masoya aminatu 😭😭ku kawo dauki*

_*😍MAMAN DAN ALBARKA CE*_😍✍️
09/11/2022, 2:22 pm - Maman Dan Albarka Ce: *_WANNAN LITTAFIN NA KUDINE KI SIYA KIKARANTA CIKIN AMINCI AKAN FARASHI MAI SAUKI 300 KACAL TA WANNAN ACCOUNT NUMBER 2375144550 LAWALI AHMAD ZENITH BANK KITURO EVIDENCE TA WANNAN NUMBER 09138320449 INKUMA KATIN MTN NE SHIMA TA WANNAN NUMBER 09138320449_*

*_INKUMA DUKA LITTATTAFAN BIYU KIKE SO FANSAH 2022 DA KUMA TUSHEN MU DAYA ZAKI TURO 500_*

*🪴TUSHEN MU DAYA🪴*

_*😍MAMAN DAN ALBARKA CE*_

*_PAID PAGE 22_*

Kamar yadda yace da safe kafin baba ya fita yace indauko mai takardar filin na dauko na bashi cikin farin cikin da dashi ya kwana sakamakon yana ganin yasamu hanyar da zamuyi nesa da wannan gidan

Da sallama ya shiga dakin ya tarda baba a zaune akan tabarma hajjo a gefenshi

Ya tsugunna ya gaida mahaifan nashi cikin girmama suka amsa baki dayansu

Ya kalli baba baba dama maganar filin dana maka kwanaki ce to ansamu amma a area 1 jiya na je nabiya komai ga takardar mallakin filin nan in kasamu lokaci sai muje kagani

Cikin farin cikin baba ya miko hannu ya amshi takardar filin
allah ubangiji yasa albarka ya rufa asiri duniya da kiyama kace ansamu ba asamu dai na cikin garin da kace kanaso ba ?

Ba asamu ba baba

Ba komai karka damu ko a ina ne inhar waje mallakin mutum ne ai babu matsala allah yabaka ikon ginashi lafiya ya sa ashiga cikin aminci

Ya amsa da amen

Hajjo dake gefe da tsananin mamaki ya kasheta ganin wai ahmad ya siyi fili batare da shawararta ba alamar ya riga da yayi shawara da mahaifinsa kenan kafin ya siya tunda gashi maganganunsu sun nuna hakan

Jin baba na miko mata takarda yana washe baki kinga yaron ki dai ya bada himma ya sayi fili Sauran mu bishi da addu ar allah yabashi ikon ginawa gashi kisa albarka

Tayi kokari matuka wajen danne bakin ciki da bacin ranta tukun ta amshi takardar itama cikin yake a a Masha Allah kace muma mun kusa yin gidan kanmu a a abin farin ciki muma dai zamu tashi daga gidan gargajiya mu koma sabon gidanmu mu kadai abinmu kaga yan uwanshima kowa zai samu dakin kanshi insunyi aure sun huta kenan

Baba ya kalleta yana dariya a a fa wannan nashine yayi niyar ginawa iyalinshi mu sai nan gaba in allah ya hore masa ya sai mana namu a nutse tunda nan din bawai haya muke ba

Batun yan uwanshi kam ai inaga kowa na sana,ar shi kinga wannan kowa zai nemi nashi na kanshi ne ya gina rayuwarshi kina fatan ya,yanki su tattaru guri guda wajen dan uwansu komai shi zai musu zuwa yanzu ai yakamata suma sufara yiwa kansu wasu abubuwan umar da salaha ne kawai yara acikinsu kinga kenan batun filinnan mu muce zamu shiga ai bai taso ba

Ahmad da fargaba ta kamashi farkon maganar hajjo jin abin da baba yace yasa shi cikin farin ciki

Ya ce ai baba kafin ma ingama gina nawa din insha allah kuma nakun zanyi kokarin ganin na siya nima ina da burin ganin kun mallaki gidan kanku ku kadai aciki

Baba yace a a karka raba hankalinka gida biyu ka nutsu kayi gininki gini ba wasa bane maganar wani sai mana fili yanzu ma bata taso ba ahto kaje kaji da yadda zaka tsara ginin allah zai taimakeka insha allah

Hajjo ce ta hayayyako au mu sai mu zauna harsai ka kammala gini tukun zama mallaki namu aikwa wannan bata taso ba wannan filin fa bakara min fili bane wallahi ko dakuna ashirin za a iya ginawa a ciki to kaga zai dauke mu tsaf

Baba ya kalleta ke waya ce miki haka ake gini yanzu zube su da ke aikin gidaje yasan yadda yayi niyar tsara abinshi ginin yanzu ba irin wanda kika sani bane komai girman fili akwai tsarin da ake mai

Kaga ahmad tashi kaje allah ya muku albarka allah yakara taimakonka

Har ya tashi zai tafi hajjo tayi caraf kadai kawo takardar filin in aje ko inhar inada matsayin hakan

Baba ya kalleta ya girgiza kai yace ahmad bata ta aje aidai ajiye ce ko bata

Haka ya dau takardar ya mika mata yadai san duk abin da za ai basu zasu ginaba kuma baba na bayanshi inba rigimar hajjo ba daga jin ansiyi fili saiki fara kasafin ga yadda za ai haka ya taso ya dawo daki

Na tambayeshi ina takardar nan yake sanar min yabawa hajjo ta adana mai dan tafimu sanin yadda zata adana tunda su manya ne

Haka ne kam allah ya taimaka

Yace amen

Haba mero meyasa kike wa yaronnan hakane kefa kikace nike nuna masa bake kika haife shiba amma yanzu ke ke kokarin nuna masa hakan

Yanzu me kaga na nuna masa ne malam me d'a nace meka ga na nuna na banbanci da har yasaka fadar hakan duk kokarin danake akan yaronnan baka gani

Ada inka ce haka dan kana ganin ban haifa ba nima yanzu na haifa alhamdulillah to mekwa zan tsaya batawa kaina lokaci da zan nuna masa banbanci ban nuna masa tun yana karami ba sai yanzu da girman shi ni kokarina kullum kawai shine su hade kansu da,yan uwanshi susan taimakon juna tun yanzu shima yasan darajarsu

Ok in maganar nan kike fisabilillah baza kice wai filinnan shida yan uwanshi bane damu baki daya sau dadama kina aikata haka kina nunawa yarannan cewa abun dan uwansu nasune amma abin mamaki su in sun samu basu san shiba kansu suka sani kuma bakya fada musu abin da kike fada mishi kina yawan tilastawa yaronnan akan abubuwa dayawa inba da ban bantaba fada masa bake kika haifeshi ba tabbas zai zargi haka saboda banbancin a fili yake

Babu d'an dayake mana biyayyarshi kema kinsani kibi rayuwa a hankali mero

Yanzu da kika amshi ta kaddun nan me kike nufi da hakan

Hmm malam kagama cimin mutumci akan yaronka ka gwada min dan hasana ba dana bane nan ta rushe da kukan munafurci ni kullum burina shine yaron nan rayuwar shi ta inganta kafi kowa sanin nafi sonshi akan ya,yan dana tsugunna na haifa amma yau nikake fadawa magana kai tsaye kana nunamin ban isa da dukiyar ahmad ba aina gama maka wahalar na rikeshi ya girma ya zama mutum kafito kawai ka fada masa banice mahaifiyar sa ba saina san kaji dadin rikon dana masa

Malam musa da kukanta baisa yaji komai yau shi kanshi yana mamakin maganganun da yake fadawa hajjo dan abin yadade a zuciyar sa yadda take takurawa ahmad amma baisa meyasa baya iya magana ba
Haka ya tashi ya kade rigarshi ni kinga tafiyata saina dawo kuka kuma kici gaba dayi kina mai maita maganar har yarannan su shigo su tambayeki ba asi inyaso saiki nemi amsar da zaki basu takarda ce dai nace baida ce ki amsa ba amma tunda ajiye ce aigatanan allah yabamu aron rai da lafiya

Yasa kai yayi ficewarsa abinsa

Fadar irin tashin hankalin da hajjo tashiga ma bata lokacine me kenan yau ita musa ke fadawa magana kai tsaye babu shakkar komai musan da ada intayi magana ko tari baya iyawa

Duk tana me hakan take faruwa komai na neman rugujemata dole ne ma ta tashi tsaye malam musan ma datake juyawa yau yana neman juya mata baya ga ahmad wanda dama ita kanta tasan bawai asirin datake bane ke rike da biyayyar daya ke mata

Kallon mahaifiyar dayake matane yasa baya iya tsallake maganar ta muddin kwa tayi sake yasan ba itace mahaifiyarsa ba kashinta ya bushe
Chapter 39 · 0% Book details