Sashe 36
Tushen Mu Daya Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Sannu kinji nan yashiga tofa min addu,o,i ko asibiti zamuje eh ?
Na girgizamai kai
tabbas na zargi hajjo akan faduwarnan tawa tunda gashi naga ta fita kuma ina fitowa tana fita wajen cikin sauri danni harga allah tun ranar da hauwa ta zo tasamin kwalabennan a cikin pillow zuciyata takasa yarda da su har ita hajjon sai gashi yau nafara ganin alama wata irin murdawa cikina yayi
Nan da nan saiga amai ya taho min kafin ma in mike na fara kwarashi a tsakar dakin ahmad ya tallafoni yabi aman da kallo wani irin amai nayi bakikkirin sai kuma bayan nakammala jikina yayi lakwas cikin ya daina murdamin
Sannu kinji sannu me kikaci haka kike amai irin wannan dakin ci zogalen ma sainace ko shine sannu kinji
Nidai ina jinshi yayi kokari wajen ciremin rigata dan duk ta baci ya gogemin bakina ya kamani ya dan kaini bakin kofa ya zuba min ruwa ya kuskuremin bakin ya daukoni ya dawo dani daki ya kwantar dani yashiga gyaran wajen dana bata
Ahmad mutumne ne tsabta nan danan saigashi ya gyare wajen
Ya dawo kusa dani ya zauna yana min sannu
Nidai duk na kara tsorata da lamarin gidannan na bude hannuna da har yanzu a jimke yake naga naga ashe tsummane alamar kuma maganine aka kulla a cikinsa ahmad da hankalinshi gaba daya na ga cikina da yake ta faman shafarshi baima san me nake yiba
Ikon allah saiga hajjo ta dawo cikin sallama ma yanzu ta shigo
Da sauri ahmad ya dauke hannun sa daga cikina ya gyaramin rigata
Ina jin maganarta na rufe idona kamar mai barci
Ta kalleshi a a lafiya naganku a haka meya sameta ne?
Wallahi hajjo ta fita kenan zata wanke hannu naji karar faduwarta koda na fita bata iya tashi da kanta ba saida na taimaka mata tukun tace cikinta na ciwo ta dai samu tayi amai yadan lafa mata yanzu inaga tasamu barcine
Ikon allah to kota ci zogalen dana kawo?
A a bata ciba tanason cinne taje ta wanke hannu shine fa ta fadi
To indai ta tashi ka tabbatar tacinye zogalen dama nayi tunanin ta cine nazo amsar kwanon amma indai ta tashi ka tabbatar ta cinye kaji kasan masu ciki da kwadayi
Na dan bude ido na kadan saina ga harara kawai take antayamin na rufe idona nashiga jan addu,o,in neman tsari
Ahmad da bai kawo komai a ransa ba asalima murna da farin ciki ne suka cikamai zuciya ganin hajjo ta fara sakkowa sanadiyyar cikin dana samu yasa shi cemata insha allah inta tashi zansa taci ai akwaita da son zogale bakiga yadda taso ciba faduwar datayine ya hanata ci
To kadaiyi kokari tasa kai ta fice
Zuwan da ta kuma yi tabbas ya kara tabbatar min da zargina akanta tunda nake da ita bata taba shigowa dakina cikin salama da mutumci ba sai yau
Nan dai tun ina barcin karya har na gasken yayi gaba dani
Ban farka ba sai bayan la,asar na tashi da addu ar farkawa daga barci a bakina ina mai jin jikina yamin tsami kuguna na ciwo sanadiyyar buguwar dana yi na kai kallona dakin ahmad baya nan alamar ya fita kenan ko masallaci yaje ina ga
Haka na lallaba na tashi sai lokacin na tuna da tsumman dake gefena na dauke shi na yi hanyar waje da addu a ina kokarin rage marata inyi alwala inyi sallah
Har zan kara taka waje saina tuna da dazu na kurawa sumintin wajen ido tabbas kam magani aka barbada dan ga wani baki bakin abuna an barbaza a wajen
Na tuna da zogalen da takawo da sauri na koma daki na nemi leda na bude kwanon zogale ne yaji kayan hadi da ishashshen kuli ga su tumatir da albasa amma ko sha awar shi banyi ba duk sona da shi ya fita raina
Na juyeshi a ledar cikin sauri na jefa tsumman maganin ciki dan nidai da hankalina bazan ciba aikuma ta riga da tasamin zarginta a raina anyi angama nida cin abin hannunta
Da sauri na doshi kofa dashi dan banason ahmad ya dawo yace naci bansan mezance masa ba gwara inya dawo ince nacinye dan bazan iya cemasa bazanciba ayadda naji mahaifiyar sa na maimaitawa naci nasan sai ya matsamin ko kadanne yasa naci
Kafin inkara taka wajen saina nemi tsintsiya da makwashin shara na yi bismillah na share wajen tas tukun nayi addua na fita na tafi can bayan dakina inda katangar babu tsayi na jefa a ramin block na dawo na wanke hannuna
Nayi alwalar sallar la,asar na tada sallah duk abin danake jikina babu kwari sam
Ina kan abin sallar ya shigo ya zauna bayan na idar ya kalleni allah ya karba nace amen
Ya jikin naki?
Nace da sauki
Allah ya kara sauki
Nace amen
Yanzu zaki iya cin abincin ko kuma zogalen zan miko miki dan kinsan hajjo ta zo ta kara dubaki kina barci tace inkin tashi kicinye zogalen
Na kalleshi yanayin yadda yake cikin farin ciki a zuciyata nace bawan allah allah ya hadaka da muguwar uwa
Nace aina ma cinye zogalen tuni dan ina tashi da yunwa na tashi bakina kawai na wanke na cinye abincinne dai saina yi wanka tukun inci
Kice harkin cinye sannu acici nayi dariya ina tashi ina mai linke daddumar danayi sallar nace ai dan banci abinci bane kuma kaima kasanni da zogale
Cab nikam naga ranar da zan iya cin wannan abun da kuke ci ni ban iya cinsa ba sam
Zaka koya ai tunda muna tare na kare tare da yin wajen heater dan in jona ruwan wanka
Daya fahimci abin danake niyar yi sai ya taso ya rikoni kinga koma ki zauna keda bawani kwari ba bari na jona miki
Na kwa koma na zauna ya jona dan ba dadin jikinnawa nake jiba har zuwa lokacin
Bayan nayi wanka ina cikin cin abinci saiga salaha tashigo ta kalle mu tukun yau da yan mutumcin ke kanta sai ta hada mu duka ta gaisar muka amsa tace hajjo tace ta amso kwanon zogalen inna cinye
Na kalleta na nuna mata kwanon sai dai ban wanke ba kice bandade da cinyewa ba nagode
Ta amsa ta tafi
Ikon allah lallai hajjo hmm da muwar nan tata kadai ta isa inyi zargin wani abu koda kuwa banganta lokacin datake barin wajena ba amma inba haka ba mezanyi da wani kwanon silbarta data ke damun a amso mata
*************************
Yawwa kinga bani kwanon ingani nan salaha ta bata kwanon tayi gaba
Hhh ja,ira harda su sude kwano taji zogale yaji hadi tsinanniya yaudai taki ta kare dole cikin nan ya zube allah yasa ku wuce tare ina nan ina jiran jin kyakykyawan labari ta kare tare da fitowa tsakar gida tana zubawa kwanon ruwa ta wanke tas ta shimfida tabarmarta ta kunna redio rabin hankalinta naga lungun aminatu rabi tana sauraron redio
***********************
_*KANO*_
Salima wai me kike nufi da ni ne ina matsayin mahaifiyar ki ban isa na fada miki magana kiji ba kenan
Nifa gaskiya mama bazan yarda azubar da cikinnan ba ahto ina son abuna kuma haka kawai bazan je garin zubarwa ba in rasa raina wallahi gwara na haife shi da dai in mutu a banza haka fa sa,aden malam bashir garin zubar da ciki ta rasa rayuwarta
Kinga salima babu wata mutuwa da zakiyi rufamin asiri zakiyi a matsayina na mahaifiyarki ki zo muje a zubar da cikinnan kema kinsan fitar wannan maganar dai dai take da tarwatsewar rayuwarki wallahi zaiyi wuya ki samu mijin aure nan gaba kuma sannan kin riga da kin bata mana sunan gidannan
Mahaifinki mutane naganin darajarshi a ce a gidanshi aka haifi dan shege aikin kashe mu salima ga aysha kullum dama abdullahi duk da irin yadda nake masa bashi da abin yabo wajen tarbiyar yara sai ita
Ita kanta intaji labarin cikinnan aita samu abin aibatani ki taimakamin kinji salima ki yarda banason kishiya tamin dariya bare kuma mutanen waje wallahi mukayi wasa dani dake har mahaifinki fita saita gagaremu
Nifa mama cikin nan yanada ubanshi ubanshima kuma yasan da zamanshi shi kanshi da yace azubar lokacin da yasan da zaman cikin dana nuna masa inason abuna yabani goyon baya saboda son da yake min
Kawai ki share duk wasu surutan mutane in kuma baba kikeji nasan nashi mai sauki ne baya wuce ya jibgeni kuma duka baya kisa ahto dole dai ya barni in zauna agidan
Inkuma mama aysha kike ji ita ina ruwanta matar da babu ma ruwanta da sha aninmu bare har kice zata mana dariya ji kinga mama kawai kibar maganar nan ninasan abin dayasa bazan zubar ba
Salima nikike fadawa magana haka kamar wata sa arki ban isa in ceba ki yarda shi dan iskan daya miki cikin ba dole inkikace kina so ba yace yabarmki tunda ba ajikinsa masifar take ba to wallahi badani ba baki isa ki haifamin dan shege agidannan ba dan ubanki
Dan haka koki yarda azubar da cikinnan wallahi kona tsine miki albarka gwara kibi duniya da wannan abin bakin cikin da kike kunsa min ta kare fadar cikin daga murya
Mama aysha dake tsakar gida tana hada hadar abincin rana kalmar karshennan ce ta doki kunnenta
Ta taho cikin sauri tana mai daga labulen zuwa lokacin zainabu tafara kaiwa salima duka ta ko,ina tana ikirarin gwara ta kasheta da ta bari ita taga bayanta
Haba maman hajara meyayi zafi haka da kike kokarin aibatata haka yarannan nan yanzu hakuri ake dasu sai ana kai zuciya nesa kiyi hakuri
Kinga ni malama bankiraki ba bankuma sakoki cikin maganata ba saiki kara gaba yar neman gulma kawai
Salima ce ganin mama aysha tace allah yabaki hakuri tana kokarin juyawa tayi saurin cewa mama aysha cikine dani ita kuma mama ta dage saina zubar dole dole nikuma wallahi bazan yarda ba inje in mutu a banza
Mama aysha dataji kafafuwanta sunyi nauyi takasa takasu tadawo da baya ciki salima har kike fada da bakinki subhanallah
Ganin salima tariga data tona asirin yasa uwar rufeta da duka ta ko ina shegiyar yarinya tsinanniya asirinnawa ne dai bazaki taba rufamin ba saikin tona agaban kishiyata kingama dani salima