Sashe 10
Tushen Mu Daya Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Haka dai ake rayuwa gidan kakanmu yayi kokarin basu ilimin addini gwargwado sai kuma noma da wannan mazan keyi Allah yawa gidan nasu albarka inda koda baki akayi a garin to fa gidan kakanmu za asauke su
kakanmu yana da son mutane da kyauta shiyasa gidan koda yaushe cike yake da mabukata
Kwatsam wata rana fatima ta kwanta ciwo wanda anyi maganin anyi maganin amma ina anma kasa gano kan cutar tata
Inda watarana aka wayi gari rai yayi halinsa Mutuwar fatima ta girgiza malam muhammadu matuka tare da ya,yanta da yan uwanta inda tawani bangaren tazama abin farin ciki ga kishiyoyinta
Lokacin Musa nada shekara ashirin da hudu Abdullahi nada shekara ashirin sai mahaifina salisu dan shekara Goma sha bakwai
******"*****************
Bayan rasuwar Fatima sai gidan ya zama kamar dama jiran mutuwar tata kishiyoyin keyi inda Suka fito da sabon salon wulakanci ga su Musa saboda babu idanun mahaifiyar su gallazawa iri iri dan ma dai lokacin da wayon su bawani zaman gidan suka cika ba saidai insunzo amsar abinci da sauransu
Sai yazamana aliyu yaron Asabe me shekaru sha biyar ya daina zuwa gonar ma saboda daurin gindi da mahaifiyar shi tamai zasu tafi gonar tare shi kuma zai kama hanyar yawon shi
Su musa suke zuwa gonar
Kuma asabe ta musu gargadi mai tsauri insuka bari mahaifinsu yasan aliyu baya noma zasu gani dayake musa da wayonsa yasan abin data ke nufi bawai
Zata cutar dasu ta fili bane tsoronsa karta cutar mai da kanne dan haka sai yaja kannensa yace karsu sake su fada
Haka dai rayuwa taciga ba da tafiyar musu yau dadi gobe akasin haka
******""***"**************
Kwatsam malam Muhammadu shima ya kwanta jinya inda ko sati be cika ba yace ga garinku
Allah sarki alokacin Su musa sunsha kuka sunyi jimamin rashin mahaifinsu sun zama marayu
Gaba da baya
Ahaka akai sadakar uku har bayan arba,in su mahaifina suna rayuwa ne kawai amma su sunsan basu da wani gata sai allah
Bayan rasuwar malam Muhammad da Kwana arba,in da biyar ne limamin garin da sauran yan uwanshi suka yanke shawarar rabon gado
inda suka zo har gida suka tara iyalanshi suka gabatar musu da bukatarsu danneman a yanke shawarar yaushe yakamata a raba gadon da kuma yadda za atattaro kan dukiyar sa dan yabar gonaki da filaye harma da gidaje ba iya garin kawai ba harta da makotan su
Anan dai Talatu tayi zaraf gurin cewa ita gaskiya bata fita a jimamin rashin mijinta ba babu wani gado da za ataso da rabonshi yanzu ta kare maganar da rushewa da kuka
Asabe ma ganin haka sai itama tace batason rabon yanzu abari a kwana biyu dan tasan halin talatuwa tsaf ruwa baya tsami banza itama dan a tsaye take da tuni talatuwa ta kaita kasa
Haka dai taron ya watse ba asamu matsaya ba inda aka bar magabar kan insun bukaci hakan sa yiwa liman magana
***********************
Akwana a tashi akace asarar mai rai kwatsam aka wayi gari salisu ya bata sama da kasa anne meshi an rasa anyi duban anyi duban amma babu shi babu labarinsa
Hankalin su musa yayi matukar tashi karamin kaninsu ya bace
Inda suka bazama gari gari suna nemanshi Sune nan sune can duk sun fita hayyacinsu
Abin mamaki kuma su asabe ko ajikinsu amma fa idan yan jaje sunzo sunfi kowa nuna damuwar su
ta hanyar yi mishi sharrin guduwa yayi yawon duniyar sa harda kuka wai ya watsa musu kasa a ido sunkasa rike amanar malam
Haka dai tafi tafi tun ana sa ran ganin salisu har anfidda rai Tunda
kusan shekara uku kenan yanzu amma fa yana ran yan uwanshi suna da burin nemoshi duk duniyar da yashiga
Zuwa wannan lokacin asabe da talatuwa bakinsu daya sun daina fadan sun hade kai sun kara gaje gidan kuma abun mamaki ba akara tado da maganar rabon gado ba
Asannanne kuma musa ya fito da matar auran sa hasana yarinyar wajen liman nan aka yi auran ya tada daki guda yasa matar shi inda tanan abdullahi yasamu saukin wasu abubuwan tunda ga matar yayanshi.
Lokacin su asabe suka fara gallazawa amaryar ganin itama fa tana da gata insuka cigaba liman zai iya sanin halin da ake ciki
Sai suka yanke shawarar biyomata ta bayan gida
Tun ana saran zata haihu har aka fidda rai dan ko batan wata bata taba yiba tsahon shekara biyu kenan
duk da alokacin bawani damuwa aka cika ba dan kin kwana biyu baki haihuba amma haka su asabe suka sakota gaba
Wai juya musa ya auro Haka dai suka sata gaba da manakisa kala kala
***********************
Watarana Musa ya dawo daga gona yana kokarin shiga gida yaji ana kwala mai kira
Ya juyo bawani bane sai abokin sa Abashe
Abashe Dan kasuwane kina kasuwancin sa a Nigeria yake yinsa sai in ankwana biyu yake zuwa yaga gida da iyalansa ya koma
Ya tsaya yajira shi ya karaso suka shiga gaisuwa
Malam musa ya bayan saduwa?
Alhamdulillah zamu ce Malam abashe
Yace masha allah
Dama nazone in fada kasan sana ata a nigeria nake yinta to Wancan satin munkai kaya lagos Sai kawai na hadu da Salisu.......
Bai bari ya gama maganar ba yayi sauri kama kafadun shi cikin zumudin son jin labarin dan uwansa ji yake hakan da yaji kamar ma ance masa ga salisun yadawo
Ina kaganshi ?
dan allah a ina ne meyasa baku taho tare ba ?
Meka ga yanayi?
Inane lagos a Nigeria .?
Ya shiga jeromai tambayoyi batare da yabari ya karasa maganar da ya dauko ba
Malam abashe ya masa kuri cikin tausayawa yace naganshi suna Aikin lody ne Kuma nakira shi mun gaisa yake cemin ina kuke
.Nace kunanan cikin tashin hankalin rashin sa ya taimaka ya komo gida
Yana hawaye yace min shi baisan meyasa yabar gida ba yadaiji garin ya mai zafine kamar ana wura masa wuta kuma bayajin zai iya dawowa amma infada maka yana cikin koshin lafiya
Yace gaishe ku sosai naso ya tsaya ko doguwar magana muyi amma da dai yace min yana zuwa har aka gama lodyn motarmu ta tashi bankara ganin sa ba
Na tambayi mutanen wajen ko sunsan inda,yake zama sunce basu sani ba kullum indai akwai aiki yana zuwa kuma ana gama aiki
Suke neman sa su rasa
Haka dai na hakura amma tabbas yana garin lagos
Musa yayi shiru can yanisa yace tafiya Nigeria ta kamamu dole zanje nemo dan uwana yana maganar yana zubda hawaye
duk da yana cikin farin cikin jin cewa dan uwansa na raye amma hakan bai hanashi kokawa ba
Ya yi wa malam abashe godiya sosai tare da fadin zaiyi shawara insha allah su kayi sallama suka rabu
Malam musa ya kira abdullahi yamai bayanin halin da ake ciki allah sarki dan uwa mai dadi shima tuni ya rude da murna
Inda yabawa dan uwanshi shawarar su tafi Nigeria neman kaninsu
Sun tsaida maganar zasu tuntubi malam abashe lokacin komawar shi inya so sai su koma tare
************************
Bayan wasu yan kwanaki Musa da abdullahi sun yanke shawarar tafiya sunne mi malam abashe
Inda tafiyar su ta kama washe gari da asuba sun fadawa Asabe da talatuwa
suna fada musu sukace amma dai da matarka zaka tafi musa
Yace a a zaibarta nan tukun tunda neman kaninsu zasu kawai bawai zamaba kuma sannan basu san yanayin inda zasu sauka ba
Haka dai washegari suka musu sallama suka rankaya sai Nigeria kasa mai cike da albarkatu....
********************"****
Akano suka sauka ainahin inda abashe ke aikin sa inda daga baya bayan sun huta
ya musu jagora zuwa lagos sun sha wahalar neman basu sami komai kamar shi ba
Inda abashe yace ya ganshima ca sukai ko me kamarshi basu kara gani a gurinba daga ranar
Haka dai kwanan su uku a lagos suka hakura suka juyo da niyar zasu kuma dawowa daban tunda sunsan hanya ko za adace dan karsu shiga hakkin abashe
*******************"*"**
Sun dawo kano bayan sati musa da abdullahi suka kuma nikar hanya ko za adace nanma dai haka suka dawo babu labari gari irin lagos ina zasu ganshi sannan gashi ba wani suka sani ba
Bayan dawowarsu ne abashe ya basu shawarar me zai hana su dawo da kasuwanci kano madadin noma da suke acan sai sun jira damuna
Inyaso in damuna tayi sai su koma suyi noma
Daganan sai su cigaba da neman dan uwansu asannu ko zasu dace
Sunyi shawara da juna inda sunsan dole inzasuyi kasuwanci sai da kudi to su kuma basu dashi
karshe dai suka yanke shawarar sai sun koma zasu dawo inda yiyuwar hakan
*******""***************
Bayan dawowarsu sun sami liman da shawarar kuma yabasu goyon baya dari bisa dari
Musa ya tattauna da matarshi inda suka ajiye maganar akan sai yaje yafara zama inyasamu inda zai ajeta yazo ya dauketa
Sai dai matsalar kudi inda suka fadawa liman liman da sai lokacin maganar gadon su ta fadomai yace
Kuna da kadara ai in da anraba gadon amma ikon allah wajen shekara da shekaru babu wanda yakara tada zancen
Yakamata ace ansaukewa mahaifinku nauyin amma matannan shiru daga cewa zasu tuntubeni
Amma ni dole zan tada maganar saboda abawa kowa hakkin sa kwa samu
guzirin tafiya dan kukafa kasuwanci mai inganci
*************************
Ha ka kwa akayi inda liman ya samu su asabe da maganar kai tsaye da kuma kudurinsu
Inda asabe da talatuwa suka sam su basu yarda ba saboda me aidai suna zaune lafiya bawani rabon gado salon kan ya,yan su ya rabu da dai sauran maganganun su marasa kan gado
Karshe liman ya fahimcesu suna kokarin handame dukiyar marigayine saboda duk takardun filayen marigayi na wajen asabe
Liman ya tunatar dasu illar abin dasuke kokarin yi inda suka fututtuke su ba niyarsu kenan ba a karshe dai dole ya barsu ya dawo .
Yayiwa su musa bayani
Musa yace kabarsu Baba ni akwai wata takardar gidan baba dake can hayi to kafin ya rasu ya bani yace in aje masa sai kuma har allah ya mai cikawa bai ne meta ba
Dama ina da niyar in anzo rabon gado infito da ita amma yanzu me zai hana mu saida gidan inyaso
Daga baya in anzo rabon gadon sai mu fito da kudin gidan