← Book details Tushen Mu Daya Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 37 OF 78

Sashe 37

Tushen Mu Daya Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Shikenan kin kasheni ni zainabu na shiga uku ta fashe da kuka ganin irin dukan data ke kaiwa salima ta ko ina da kyar mama aysha ta amsheta a hannunta

Ta kalleta maman hajara kiji tsoron allah da kanki kike cewa ta zubar da ciki bayan kinsan hakan babban laifine ga zunubin zina ga na kashe dan haba kiyi imani da kaddara mana

Har zata cuccusawa ayshar zagi saita tuna da sharadin boka dayace muddin tayi fada da aysha tabbas zamanta a gidan ya kare saita ja bakinta tayi tsit dan bata shirya rabuwa da abdullahi ba yanzu ina

Nan mama aysha ta kama salima ta mikar ta fice da ita zuwa dakinta ta bar zainabu nan zaune abin duniya ya isheta

Dubarar kiran wayar nafesa ne yazo mata tuni ta danna mata kira kome kike nafee ina son ganin ki zuwa anjima da yamma

Daga can nafee ta hau tambayar ta lafiya ne mama?

Ki dai zo inason ganin ki

To ganinan ma yanzu innagama girki

Kamar yadda tace sai ga ta nan ta shigo ta gaida mama aysha dake tsakar gida tukun ta karasa dakin mahaifiyar ta

Ta tarda mama zainabun a firgice da sauri ta karasa lafiya mama naganki ahaka?

Dole ki ganni haka nafee yarnyar nan salima so take ta kasheni ta kunyata mu nan tashiga bata labarin abun daya faru ta kwashe komai ta fada mata

Mun shiga uku mama abin da yarinyar nan ta jawo mana kenan yanzu tana ina

Tana dakin waccan munafukar mana

aikwa dole ta fito dan ubanta muje a fitar da cikinnan wallahi bazata kunyata mu ba

Ta tashi tayi hanyar dakin mama aysha tana shiga taci karo da salimar a zaune a parlour tayi rashe rashe tana cin shinkafa da waken da mama aysha ta zuba mata ga cikinnan har ya turo

Tace to dan ubanki ko tashi ki shirya wallahi sai anzubar da cikinnan dan tsabar iskancinki da fitsara kiyi ciki kice bazaki zubar ba ana neman rufamiki asiri kina kokarin tona mana

Mama aysha dake uwar daka ce ta fito tace nafeesa harda ke amasu cewa a zubar da cikin kenan saboda rashin tsoron allah to wallahi babu wanda ya isa ya zubar da cikinnan muddin ina raye a gidannan inhar kuka ce zaku matsa kuma wallahi nime sanar da mahaifinku ne

Kun dade kuna abu a gidannan bana magana amma wannan karon badaniba ina kallo baza ayi wannan danyen aikinba

Salima dai ta riga da tayi abin da,zatai wanda nake ganin ba laifin kowa bane saina mahaifiyar ku da ta kasa saka ido akan tarbiyar yarannan mahaifinku nayi iya kokarin shi amma a banza bajin maganar shi kukeba gwara sanki a likkafa yadda kika zo ki koma da kafarki gidanki

Nafeesa kasa magana tayi ganin yadda mama aysha ta hakikance akan abin da babu ruwanta meta ke nufi kenan zata hana su rufawa kansu asiri kenan kokuwa kishin mahaifiyar su yasata farin ciki da samuwar cikin harta ke ikirarin hana zubar dashi

Ta kalli salima shegiya duk ke kika badamu kika tona mana asiri gaban makiya zakwa ki canza uwa dannima dai ki dauka nidin ba yar uwarki bace tunda kin zabi tonuwar asirinmu akan rufuwarshi

Mama aysha dake jin duk abin data ke fada inda sabo ta saba da fitsarar su tun suna kanana ta kada kanta tayi shigewarta daki cikine dai bazata bari a zubar ba kuma bari baban nasu ya dawo tasan ba dadi yaji wannan mummunan labarin amma yazama dole tasanar mai dan yasan yadda za ai in uban cikin yakamata anema anemoshi inyaso in salimar ta haihu in zai aureta ya aureta inma bazai aureta ba tabashi abin data haifa allah ya kawo mata wani mijin tayi aure mutumcin kanta ne dai tariga data zubar

Haka nafee ta koma wajen mahaifiyarta tasanar da ita komai ta shirya ta koma gidanta cikin bacin rai

***********************

Tun hajjo na zuba idon ganin ankirata aminatu ba lafiya har aka kira magriba shiru har zuwa dare bataji ance komai ba sai hankalinta ya tashi kardai maganin baiyi aikiba amma ai boka ya tabbatar mata muddin taci maganin shikenan kuma yace inhar

Wani baiganta ba lokacin data ke zubawar maganin zai ci to kodai anganta ne? kai ina ai lokacin da aminatun ta fito ta gama zubawar kuma yace sai anganta tana zubawa to me kenan yazama dole tasake sabon shiri gaskiya da alama ansamu kuskure

Tun daga lokacin da abin ya faru na kara ja baya da hajjo tsoronta yakara karuwa a raina tunda abin nata ya wuce ido biyu harda ta bayan gida ta fara biyomin haka naci gaba da renon cikina cikin kulawar da mijna ke bamu har cikina ya shiga wata shida a lokacinne kuma na fara zuwa awo

Har zuwa lokacin hajjo bata daina aikomin da kayan kwadayi ba in da,tana kawowa nake amsa in faki ido injuye a leda inkai in jefa a raminnan saina wanke kwanon inkaimata da kaina inhada da godiya

Duk da har zuwa lokacin
Bawai muna shiri bane da ita din dan acewarta ko abin datake bani saboda jikanta take yi

Ya,yanta ma bama magana dan ko na musu magana basa kulani nima saina nemawa kaina sauki wajen kyalesu salaha ce kawai da umar kemin magana jifa jifa suma sai idan takama ko an aikosu ko sunzo amsar abincin yan uwansu sai kuma bashir
Da muke gaisawa in mun hadu saina dade ma banganshi ba

Kuma abin takaici basamin magana amma baya hana ina gama girki kowanne ya aiko kwanon sa a bashi nashi haka nake zubawa kowa

A lokacinne kuma filin da ahmad yake nema zai siya yasamu ya siyi wani tangamemen fili sai dai ba kamar yadda yaso ba ba acikin gari yasamu ba a can wata sabuwar unguwa ne ranar ya dawo gida takaddun niya fara gwadawa cikin farin ciki na amshi takkaddun ina mai sa albarka tare da jero addu,oi

Ya kalleni yace kawo ta kardai kigani in ajiye in anjima in baba ya dawo saina je na nuna musu shida hajjo na mika masa

_*😍MAMAN DAN ALBARKA CE😍*_✍️
09/11/2022, 2:22 pm - Maman Dan Albarka Ce: *_WANNAN LITTAFIN NA KUDINE KI SIYA KIKARANTA CIKIN AMINCI AKAN FARASHI MAI SAUKI 300 KACAL TA WANNAN ACCOUNT NUMBER 2375144550 LAWALI AHMAD ZENITH BANK KITURO EVIDENCE TA WANNAN NUMBER 09138320449 INKUMA KATIN MTN NE SHIMA TA WANNAN NUMBER 09138320449_*

*_INKUMA DUKA LITTATTAFAN BIYU KIKE SO FANSAH 2022 DA KUMA TUSHEN MU DAYA ZAKI TURO 500_*

*🪴TUSHEN MU DAYA🪴*

_*😍MAMAN DAN ALBARKA CE*_

_*PAID PAGE 23*_

Kina nufin faisal dan alhaji ibrahim

Cikin tsoro ta daga kai

Magana zakimin da baki ba daga kai ba ya taso cikin shirin kaimata duka dan abin ya isheshi wanne irin abu kenan

Mama aysha ce ta tare shi kabi ahankali baban hajara nan ya koma ya zauna ya dafe kanshi

Da kyar ya dago ku tashi ku tafi zan tuntubi mahaifin yaron

Nan suka tashi uwar da yar cikin sanyin jiki ita salima ta saduda tayi nadama akan abin data aikata tashiga dana sani wanda aka ce keya ce

Sa'banin zainabu da ita tsabar bakin cikine da takaicin yadda yaci mata mutumci gaban kishiya da kuma rashin cikar burinta na zubar da cikin yasa ta tashi jiki a sanyaye da sake sake kala kala cikin ranta

Haka mama aysha ta cigaba da tausar sa inda ya yanke zai tuntubi mahaifin yaron insha allah

*************************

Wallahi fadime dawowa zanyi gaskiya nagaji kefa kika ce inyi hakuri komai ya dai dai ta naji shiru har yanzu gwara nazo ayi wacca za ai dan naga ke baki damu ba ni kobada asiri ba intunkare shi kai tsaye ai addini bai haramta mace tace tana son namiji ba gwara nazo ni in roke shi ya taimaka ya aureni kawai

Fadime dake sauraron hauwa da wautar da take shirin aikatawa ta daka mata tsawa ke dan ubanki duk kokarin danake bakya gani akan maganar aurannan naga ya tabbata saboda garajanki nasa kika koma sakoto wajen yaya da zama dan naga kina nan ma madadin abun yayi gaba sai batamin shiri da kike amma kima maganar dawowa to dan ubanki ki dawo ita uwar tashi kanta duk da asirin dake aiki jikinta takasa amince min har yanzu kamar tsoronshi take

Kindai san ahmad ba zai soki ba bai soki tun kina hauwar kiba sai yanzu

Gwara ki lallaba kibari abi komai a hankali

Kinga fadime wannan shegen yaron mai katon kai fa tunda nazo ya mannemin baya barina na matsa ko ina kamar dama ance masa nice uwarshi ina takaici fadime wallahi shi yasa nake son in dawo saboda naji kawu na maganar inhar zan dawo indauki dana in tafi dashi shi yagaji da rikon dan shege

Shi kawun naki kecewa haka ?

Shi ke cewa mana kinsan dai da yadda suka yarda na zauna da cikin yaronnan a wajensu har zuwa haihuwarshi da suka amsa da kyar wallahi na yarda yaronnan ya biyoni kamar tonuwar asirina nane dan sai ya hanani auran danake son yi ma

Kinga kibarsu kiyi zamanki inhar lokacin dawowar taki yayi zaki tahone bama da saninsuba kinga shikenan ankashe bakin tsanyar daga baya ni zan shirya inje in lallashi yayan indan bashi wani dan abu wallahi banason agano kin ajiye dan shege nayi nadamar rashin daukar mataki tun yaronnan na jariri

Shikenan fadime saina jiki amma wallahi banida burin daya wuce in auri ahmad

Nan suka yi sallama

*Wacece hauwa*?

Kamar dai yadda kuka sani fad'ime kawar hajjo ce tun zamanin zuwan su hajjo garin lapai hauwa yarinyar fad'ime ce ita ce diyarta
Ta farko sai kanwarta
Zainab mai bimata

Hauwa ta taso yarinya mara jin magana
Tun tana karama
Fad'ime ke dora mata
Tallar abinci a sanadiyyar
Haka idanunta suka
Bude da harka da maza
Dan duk yawanci inta
Fita da abincin tana riga k'anwarta zainab siyarwa
Sanadiyyar mazan dake
Mata juye konawa ta
Samo tana kawowa
Fad'imen fadime najin
Dadin hakan har gori
Takewa zainab akan
Bata maida hankali

Mahaifinsu ba ason ranshi suke tallah ba
Amma bashi da yadda
Zaiyi ne dan anriga anshanye shi sai abin
Da matar tace
Ahaka hardai
Suka zama yan mata

Lokacinne kuma
Hauwa ta maida bin
Mazan sana,arta sai ya zamana tama daina
Tallar sai dai a dorawa
Zainab
Chapter 37 · 0% Book details