← Book details Tushen Mu Daya Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 35 OF 78

Sashe 35

Tushen Mu Daya Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Illar yawan tsinuwa kenan kada kiga kina tsinewa ya,yan wasu ke naki bazasu lalaceba saboda kina takamar baki tsine musu ba koda baki tsine musu ba dole dalilin aibata na wani da kike saikiga nakinma bai shiryuba wasu iyayan ma adalilin sabo da zagin na wasu suke zagin nasu

Dan haka iyaye dan allah musan irin kalmomin da zamuna yiwa yaranmu musan irin abin daya kamata ya fito a bakinmu inma sun bata mana ne da muyi magana wata mummunar kalma ta fito a bakinmu gwara mu bisu da addu ar shiriya koda muna cikin bacin rai kam sai allah ya duba hakurin da mukai ya shiryesu sannan saimun dauke kanmu daga kan abin da ya,yan wasu ke aikatawa inmunga sunyi ba dai dai ba inbamu da hanyar da zamu tsawatar musu to mu bisu da addu ar shiriya in ita ma addu,ar bazata samu ba muyi shiru shiyafi alkhairi

Allah ya shiryemu ya shirya zuri,armu baki dayan musulmai badan halinmu ba amen

Bayan kammalawarta ne ta zubawa salaha inda kai tsaye tace ta koshi bata tambayeta metaciba ta ajiye taci gaba da harkarta inda ta dauko jakar data shigo da ita ta kwashe magungunan ciki da niyar sai gobe zata aiwatar da kudurinta

**************"*******"**

Allah yayi dare gari ya waye alhamdulillah yau na tashi cikin wani irin yanayi jikina sam baimin dadi zuciyata ba dadi sam saina alakanta hakan da rashin kiran gida da banyiba tun shekaran jiya naji lafiyar su

Bayan na kammala komai dan yanzu ina iyayin aiyukana duka saina dan kwanta dan ahmad ya dan fita akan maganar filin dayace zai siya wai ansamu wani amma ba a cikin gari bane shikuma yace yafison shi cikin gari

Ina,nan barci yayi gaba dani saina ganni wai gani ina tafiya cikin dokar daji sainaji ana kiran sunana ina jiyowa sainaga banga kowa ba naci gaba da tafiya kenan sai naga wani hannu ya tunkaroni banga mai hannun ba kafin ma in kauce ya daki cikina nan na tsugunna ina murkususu sai naga wata kyanwa tazo tana zagayeni

Daga nan ne na farka ina salati na hada uwar zufa na kalli kaina da jiki na saina ganni akan kujera nayi barci nikadai a dakin sai karar fanka nan na tashi ina mai shafa cikina ina naiman tsari da wannan mummunan mafarkin

Ina nan zaune sainaji sallamar ahmad ko tashi ban iyayi daga inda nake zaune ba saboda jikina da yayi sanyi ya karaso da ledar hannun shi ya ajiyeta a gefe wanda nasan mangoron da nace inasone ya yanemomin

Ya karaso kujerar danake kai ya zauna tare da janyoni jikinsa ya yane madam jikinne ko kuwa naga yau ko yar sannu da zuwan bansamu ba ya kare yana mai kai hannun sa wuyana yana tabawa ko zaiji akwai zafi

Ai jikin ma babu zafin ko ciwon jikinne in dan yi miki tausa

Nasan babu kyau fadar mummunan mafarki shiyasa nace eh jikinne
Kemin ciwo amma kafin ka danna min kakiramin gida mu gaisa da su baba nasan yau yana gida yau juma a kafin lokacin masallaci

Kice min dai kawai kewar kano dasu baba ce ta motsa kawai ya kare yana mai dauko wayarshi dake aljihu ya shiga kiran number baba bayan ya daga sun fara gaisawa tukun cikin mutumci ina jin dadin yadda yake girmama mahaifina sosai duk da shima babanshine amma abin namin dadi

Daga nan yabani muka shiga gaisawa inda ya bawa su ilham da bahijja wayar muka gaisa cikin yarinta ilham ke tambayata yaushe zanzo nace mata ina tafe karta damu nan tace inzanzo in siyomata abun dadi nace komai kike so zan siyo muku ilham

Bayannan muka gaisa da mama rukayya wadda sai idan na bugo na bukaci abata wayar tukun take amsa in banceba kota na gurin bata ko tari sai dai innace abata sai acemin aigata

Bayan mun gama sai muka shiga firada baba anan yake tambayata babu matsalar komai nace babu yace in akwai in fada masa nace babu komai muna zaune lafiya nan ya shiga samana albarka tare da addu,o,inshi wadanda nake matukar jin dadinsu

Shiyasa ko ina cikin kunci inhar zankira babanmu zannemeshi in rasa anan yake kara jadda damin in cigaba da riko da addu,a duk da yasan ni bamai wasa bace a wannan fannin

Muka yi sallma cikin farin ciki

Na bawa ahmad wayar ya shiga tsokanata wai aidai banice auta ba danake wani langabewa in muna waya da baba yakamata inbarwa su ilham

Na kalleshi ina mai antayamai hararar wasa aikwa kasan baba dai naji dani nice ta gaban goshin sa in ina gabanshi ni mantawa nake da wasu su bahijjah ma jina nake kamar jinjira na kare da murguda baki

Ya kyalkyake da dariya iyyee qaunah kinyi baki wai dama haka kike da tsiwa dan allah cigaba da magana wallahi burgeni kike bakiga ba da kina maganar nan cikin tsiwa wallahi saina ga kin kara kyau idanun nan da ake jujjuyamin su sainaji kamar kina juyamin zuciyata ne kina kara tura sonki da qaunarki cikinta

Nima dariyar na fara dan salon yadda yayi maganar awani marairaice sai yabani dariya ahmad akwai raha da son ganin ya farantawa kowa da yake tare da shi

Nace ni ai bana tsiwa

A a fa gata kinmin kiciga ba pls kinji

Nifa ban iya ba kaga ina mangwarona ni inna biye maka ba shanshi zanba
Na karasa maganar ina mai tashi na nufi laidar daya shigo da ita
.
Na bude mangwarone masu kyau jawur dasu cikin zumudi na juyo na kalleshi na gode sosai mijina allah ya biyaka ya kara budi da wadata ya tsareka daga sharrin masu sharri ya biyamaka bukatunka na akhairi ya bani ikon yi maka biyayyah ya bamu zuria dayyiba masu tsoron allah wadanda zasuji kanmu

Ya kalleni cikin jin dadin adduata yace amen ya allah yar aljannar matata
Nima cikin jin dadin sunan daya kirani nace na gode mijina dn aljannah

Nan da nan na wanke mangwaron na zauna na fara sha sai ya kawo ido ya zubamin can dai yaga bance mai gashiba
Sai cayayi nikwa anmanta dani ko bismillh babu

Nace lahhh ya hakuri kaga fa ga mangwronnan ga dauka kasha mana

A a haka kawai kice na zabe katoton kinga ni bani dai da kanki tunda nakine nace aikai ka siyo abinka fa

A a yanzu dai nakine sai yadda kkayi dashi

Na dauko guda biyu na mika mishi a a ni daya ma ya isa kishanye sauran duka.
.na kwa maida sauran dan nasan shanyewa zanyi tas

Da rana bayan nagama girki na kaiwa su hajjo na dawo ina kokarin muci abinci abin mamaki sainaji sallamar hajjo muka amsa abin da bata taba yiba kenan

Muka bita da kallo cikin mamaki dan bamu san da wacce tazo ba hannun ta dauke da kwanon silba

Ta karaso ai saiku daina kallona haka ko tunda ga ni muguwa nashigo angama boye boyen cikin kuma naji wato ni banida matsayin da zansan matarka nada juna biyu sai dai naji a waje saboda ka maisheni uwar banza ko

Ta karasa fadar tana mai kai kallonta ga cikina sainaga kamar tana harararsa

Ta ajiye kwanon akusa dani tunda ba a fadamin ba ni gashi na kawo miki wannan kisamu kici zogale ne na dafa dazu

Ta ajiye tana mai kokarin juyawa allah yagani inason zogale a rayuwata dan tun banida ciki indai nasameshi kamar nasamu nama dan wani zubin ya,yan huwaila kawar hajjo kan kawowa

To amma wannan bansan meyasaba saina shiga shakkar cinsa saboda hajjo bata taba min kyautar abuba sai yanzu

Na dago nace na gode hajjo

Dakin adana godiyarki ni badan ke nayi ba dan jikana dake cikinki nayi

Ta fice abinta madadin ta tafi saita samu jikin net ta makale tana jiran taga aminatu zata ci ko bazata ciba

Ahmad ya kalleni kinga abin danake fadamiki ko aidama nace wuyarta tasan kina da ciki zakiga ta sakko ki dau zogalen kici kinji

Nace to tare da kokarin jawo kwanon gabana

Haka kawai kuma sai mafarkin danayi yadinga fadomin

Hajjo dake jin duk abin da suke cewa cikin murna ta shiga cewa maza kici shegiyar yarinya yaudai wannan cikin badai ya kwana a mararkiba sai dai yabi kwata

_*😍MAMAN DAN ALBARKA CE😍✍️*_
09/11/2022, 2:22 pm - Maman Dan Albarka Ce: ,*_WANNAN LITTAFIN NA KUDINE KI SIYA KIKARANTA CIKIN AMINCI AKAN FARASHI MAI SAUKI 300 KACAL TA WANNAN ACCOUNT NUMBER 2375144550 LAWALI AHMAD ZENITH BANK KITURO EVIDENCE TA WANNAN NUMBER 09138320449 INKUMA KATIN MTN NE SHIMA TA WANNAN NUMBER 09138320449_*

*_INKUMA DUKA LITTATTAFAN BIYU KIKE SO FANSAH 2022 DA KUMA TUSHEN MU DAYA ZAKI TURO 500_*

*🪴TUSHEN MU DAYA🪴*

_*😍MAMAN DAN ALBARKA CE*_

*_PAID PAGE 21_*

Na bude kwanon har zansa hannu saina tuna ban wanke hannu ba na tashi na ce bari naje na wanke hannu .

Jin haka hajjo cikin farin ciki ta kunto kullin maganin dake bakin zaninta ta shiga barbadawa a bakin kofar tana ganin aikin ma ya,zo mata da sauki motsin aminatu dataji ne yasa garin sauri ta yarda tsumman da maganin ke ciki a gurin ta juya da sauri tana kokarin barin wajen

Na bude net kenan zan fito lokacin yayi dai dai da hajjo ta na shirin fita a wajen haka kawai naji hankalina bai kwanta da ganinta danayi ba to me kuma tazo yi ko dai bata tafi ba ina cikin sake saken ina kokarin sa takalmina cikin bismillah jinai wani uban tsntsi ya kwasheni nayi wata irin faduwa karar faduwata ne ya fito da ahmad cikin sauri

Subhanallah lafiya miko mai hannu kawai nake dan jina nake ko magana bazan iyaba dan wata irin azaba ke ratsani ga kasan marata danaji yana murda min ina cikin juyin ne hannu na yasauka kan wani abu kamar tsumma na damkeshi da karfi sakamakon murdawar marata

Ya kama hannuna ya kokarin dagani tashi lafiya? Me yasameki eh ? Garin yaya kika fadi jin nakasa wani yunkuri yasashi daukata baki daya yayi daki dani ya kwantar a kujera

Cikina kawai nake nuna masa ina murkususu shikuma duk ya rude ya rasa yaya zaiyi bari na kira hajjo

nayi saurin kamo hannunsa daga shirin tafiyar dayake ina girgizamai kai

Kamin addu a wayyoh shine abin dana iya fusgowa cikin jin wata irin azaba datake kara ratsani
Chapter 35 · 0% Book details