Sashe 1
Tushen Mu Daya Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
TUSHEN MU 'DAYA
MAMAN 'DAN ALBARKA CE
Bismillahirra manir rahim
Da sunan allah mai rahama mai jin kai ya allah yadda kabani ikon fara rubuta wannan littafin kabani ikon kammalashi cikin aminci da koshin lafiya ya allah kabamu ikon rubuta dai dai da abin da zai amfani al.ummar musulmai kabamu ikon isar da sakon da muke son isarwa ya allah kada kabamu ikon rubuta abin da zai yi silar rushewar tarbiyar wasu ka tsaftacemana alqalaminmu alfarmar annabin mu muhammad (s a w)
Free page 1️⃣
Bankado labulen dakin akayi da karfi babu sallama bare neman izini nayi saurin dago kaina da ke tsananin ciwo hawaye na zuba na kalli wadda tashi go sai huci take tana karemin kallo sama da kasa nayi saurin sunkuyar da kaina gabana na faduwa dan bansan da wacca ta shigo ba duk da dama na tsammaci shigowar tata amma banyi tsammanin ta yanzu ba
Ah lallai samun guri tashiga cewa tana tafa hannu cike da masifa wato dan nace kifito kiyi wanke wanken shine kika zo kika sa shi a gaba kina kukan muna furci kamar wadda aka ce ga ranar mutuwarki Ta juyo ta kalli Ahmad dake gefena wanda tunda ta shigo ya sunkuyar da kanshi idanunsa sun kada sunyi jawur
Ah lallai sallamamme wato tazo ta kawo maka karata ne kasata gaba kana kallo tana kukan munafurci kamar wadda na daka oh
ni Mero naga abin da ya isheni bai ishi allah ba yanzu ahmad kadai riga kazama shanyayye mijin hajiya yoh yaushe kayi auren da zaka nunawa matarka banida wata daraja da kima a idonka daga cewa kiyi wanke wanke sai yarinya tazo tasaka gaba wai ciwon kai ciwon kai takewa kuka don bakin makirci kaikuma ka kasa gwadamata darajata a matsayina na mahaifiyarka Hmm ayi dai mugani in tusa zata hura wuta
Ta kare maganar tata tare da juyowa kaina
Kekuma anna mimiya fito mu wuce dan iskanci kowa gidannan ya gama aikin sa ya wanke kwanukansa tsaf saini kika maida,sha sha sha har yanzu karfe 9am baki wankemin nawa ba so kike dai nazama kazamar karfi da yaji tashi nace
Zuwa lokacin hawayene kawai yake zuba a idona
Bansan me hajjo ta ke so dani ba a rayuwa wannan wace irin rayuwar kaskanci ce rayuwar da bantaba aunawa kaina ko kwatankwacinta ba Nayi nisa cikin tunanin halin da nake ciki
Kawai sai hajjo ta zuba mana ido dani da shidin da babu wanda ya kara cewa komai tana kallonmu
Yayin da ahmad ma ya lula duniyar tunanin halin mahaifiyarsa
Ya rasa yadda zaiyi da halin mahaifiyarsa tunda yayi aure ta canza da dabi,un da baisanta da suba sam baita ba tunanin cewa mahaifiyar sa zata iya aikata masa haka ba amma sai gashi ta hana masa kwanciyar hankali shida iyalinsa baisan me take so ba bayan duk sharadin data gindaya masa yabi ya mata abin data keso amma kullum sabon salo take kara fitowa dashi
Karar marin da ta saukewa Aminatu ne ya dawo dashi daga duniyar tunanin da yashiga
Wallahi kinyi tsararo tashi mu wuce wato rainin ya kai har ina magana kiyi banza dani yoh ko ubanki yayi kadan nace ubannakima Salisu yayi min kankanta inyi da shi tashi nace
Na dago dafe da kumatuna ina kallonta na juya na kalli ahmad Da idanunsa hawaye suka taru ya sunkuyar da kanshi
A sanyaye na tashi ina girgiza kai ita kuma ta tsaya bakin kofa ta daga labule tana jiran fitowa ta
Na wuce ta gabanta Jikina na bari ta bi bayana
Muna tafe tana zageni kasancewar akwai yar tazara daga Lungun daki na zuwa kofar dakinta yasa ta rigani isa
Ina zuwa na tarar ta shige daki nakai kallona gurin kayan wanke wanken wanda kamar wani kwanukan gidan biki
Na Dauki roba na dibi ruwa na duba cikin kwanukan ko kilin din wanke wanken babu a gurin na Doshi kofar dakinta na dan tsaya daga bakin nace
Hajjo kilin din wanke wanken fa? babu a gurin....
Kamar jira take na dire ta fara sababi ke ina naki da bazaki dauko ba ki wanke dashi ko ke kika siya Marowaciyar banza da wofi inzaki dauko ki dauko inbazaki dauko ba saini natashi naje gurin me siyan inji koshi yace inya siyi abu karki mana amfani dashi tunda ya zama shanyayye
Na juya jikina a sanyaye na koma lunguna na dauko kilin din banbari ahmad yasan da dawowata ba saboda karma ya tsayar dani
Na koma na fara wanke kwani kan da kamar bazasu kare ba ina cikin wanke wanken
Saiga Dan ladi ya fito Daga dakin dake jikin Bakin zaure yana mika na dago na kalle shi daga shi sai dan gajeran wando wanda ko gwiwarsa bai kaima ya kafeni da ido da wani kallonshi me kamada na tsana wanda bansan meye dalilin sa ba danni tunda nazo gidan yau sati na biyu banga abin dana tsare musu ba kona musuba na kauda kaina da sauri ina takaicin halayyarsu ta rashin kunya da da a da kuma rashin girmama dan adam da sam mahaifiyar su bata dorasu akan kyakykyawar hanya ba duk da cewa ya girmemin amma a matsayina na matar yayansu babu mai bani girma kullum burinsu su ganni cikin kunci
Ya ja dogon tsaki ya dau buta ya shiga bandaki
Naci gaba da wanke wankena can saiga umar wato autansu yazo ba magana naga yasa hannu ya birkito kwanukan dake ga bana ya nemo wata roba ya mikomin baidamu da wadanda suka zubeba bare ya hado kansu wannan robar zaki wankemin kuma ni gaskiya ki daurayeta sosai ko wanke wanken jiya duk warin Kilin na kalleshi yaron da baifi kanwa ta
Ta hudu ba shine yake sani abu kai abu inyafi karfinka bakada maganinsa sai allah
Haka na wanke na bashi na tattara wadanda ya zubar na karasa wanke wanken na kai kayan can kan wani tebur datake dora kwanika na dau tsintsiya cikin dauriya na gyara wajen
Na juya Da niyar in koma lungun da dakina yake kamar tana kallona
Sai naga an bankado labulen ta fito cikin isa da gadara tana kallona ke
na dakata da tafiyar ina jiran inji me zata ce gabana na faduwa ina addu ar allah yasa ba wani aikin zata hadani dashi ba
Kinga dawowa zakiyi ki jikamin bushashshen tumatir dinnan kafin kije ki kwanta ki tashi ya jiku
Na dawo nace ina yake tashiga daki ta dauko kullinshi a leda ta bani amshi na amsa naje gurin da muke dora girki dan bata da kitchen sai wani waje da aka dan zagaye na bude tukunyar da ta dora na rage ruwan ciki na zuba tumatir din ina jimamin hali irin na hajjo da mako kudi take amsa gurin mijina ba kadanba da sunan girki amma abin takaici ta kare da siyan bushashshen tumatir acewarta miyarshi tafi afki
Hajjo irin matannan ce masu shegen mammakon abin duniya ga yar banzar rowa ko abincine indai tayi kyautarshi to lallai bakin datayi sun amsa sunansu inkuma yarane sai dai in yayanta basu ciba take badawa tana da son ya,yan ta batason laifinsu inkaso kaga bacin ranta to lallai ka kawo karar ya,yanta komin munin abin da sukayi bazata taba tsawatar musu ba mutumce me kin gaskiya ta ko ina Ga sa ido akan mutane da rayuwar wasu
Batason taga cigaban wani indai ba ya,yanta bane
Rayuwar gidan rayuwace wata jirkitacciya gida ne wanda za a kirashi da gidan gandu Kuma yare ne duka gidan nufawa ne hajjo ce kawai bahaushiya irin ginin mutanen da dinnan ne kowa da bangarensa bangaren hajjo su biyune da ita da wata mata maman aisha
Kana shigowa gidan da dakunansu zaka fara tozali sai daga bangaren hannun hagu wani dan lungu ne anan dakina yake inda nini kadaice a bangaren
Daga bangaren dama kuma hanya ce da zata kai ka har zuwa ainahin tsakiyar gidan inda sauran mutanen gidan ne bangare bangare har shidda kowa da dan zagayenshi
Zama ne ake a gidan wani irin zama da banta ba ganin irinsa ba in har baki iya zaman camba ba kuma baki iya bada labarin gulma ba tofa kinci baya bazaki samu masu yin harka dake ba mutanen gidan basu da dangi da hajjo ko kusa ko nesa Asalima sudin yarene ita kadaice bahaushiya saidai wadansu daga cikinsu sunji hausa kawai zamane irin na zamanin da kazo nazo inda suka zama tamkar dangin juna a fili amma fa a boye ta ciki na ciki ne kowa da haushin dan uwan sa yake rayuwa......
Bayan na jika tumatir din na wuce dakina
Nayi sallama nayi yakai baki uku amma ahmad da ya lula duniyar tunani baisan inayi ba na lallaba naje ta bayanshi na karyi tsintsiya akasan gadon na tsugunna gefenshi ina dan sosa masa ita a kunnensa yayi firgigit ya juyo
na kyalkyale da dariya ya kalleni yana murmushi na dan tsuke fuskata nace kana nan kana sana,ar taka ko yakamata kadaina yawan sa tunani a ranka please
Hmm yace yana kallona ya kamo hannayena ya mikar dani ya ya jawoni zuwa cinyarsa nayi kokarin sauka yace a a tsaya mana nifa bazan yarda ba ina zaune kina zaune wani waje cinyata a koda yaushe ita
nakeson ta zama abin zaman ki inhar muna tare
Na sunkuyar da kaina cikin jin kunya haka na zauna yace kokefa yana leka fuskata yace Aminatu
na dago na kalleshi da Dara daran idanuna
Ya cigaba da cewa don allah kiyi hakuri abisa halin da hajjo take nuna miki kiyi hakuri nima ba ason raina bane da ina,da hali bazan bari amiki hakaba
Nayi saurin sa hannuna na rufe masa baki nace don allah kadaina bani hakuri hajjo mahaifiyata ce inbanyi mata biyayyah ba wazanwa kaga bani da wasu yan uwa anan sannan ni mama kallon uwa nake mata na dauki abin data kemin don taga ta isa danine shiyasa koda ban aure ka ba mama zata iya sani kuma ta hanani na hanu kaga don tamin haka aiba komai bane
Ya kalleni cikin jimami yana girgiza kai kawai wanda na zallar tausayina ne....
Nace bari na dan kwanta na huta