← Book details Munnubiya Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 99 OF 137

Sashe 99

Munnubiya Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Cikin katseta yace
“Ni duk ba wannan na tambayeki ba!
Akwai abunda ya faru tsakanin mu ko babu??
dats all I need to know ko kuma
ince inyi confirming daga bakin ki saboda already na riga na san komai.”
Ya k’arashe maganar tashi cikin tsananin b’acin rai.

Tabbas zuwa yanzu Kausar ta fahimci ta d’an fara yin galaba a kansa kuma ta lura kamar bai fahimci komai ba kamar yadda yake ik’irari dan a maganganun da ya yi yanzu ya riga ya kwafsa and again ta fahimci da ta yi maganar wannan rana ne ya fara burkicewa dan haka tashi d’aya ta san abunyi.A hankali ta matso kamar za ta shige jikinsa wanda hakan ya sa ya d’an ja baya yana watsa mata wani irin kallo..
Itanma shi take kallo ido cikin ido tace”Yash you really don’t remember anything??da gaske baka iya tuna komai??”
Ba ta jira jin amsar shi ba tace”bari in tuna maka!”
Wasu maganganu da bayanai ta fara yi masa na rashin d’a’a da tarbiyya!,a cewarta wai duk shi ya aikata hakan a gareta..cikin tsananin tashin hankali ya sa hannu da mugun sauri ya toshe mata baki yana kallon cikin idanunta yace”ba ki da hankali,ba ki san nan hanyar wucewar Daddy ba ne??”
Sai kuma ya cikata da sauri ya ture ta tashi d’aya ya nufi hanyar stairs d’in da zai sada shi da k’asa…har ya juyo zai sake yi mata magana sai kuma kawai ya sauk’a jikinsa yana wani irin karkarwa kansa yana mugun sarawa…”Innalillahi wa inna ilaihirrajiun”
Ya shiga ambata…da ya sani bai tunkari Kausar da wannan maganar ba yana so ya sake sakawa zuciyarsa salama ta hanyar tabbatarwa kansa ba abunda ya faru tsakaninshi da ita amma instead gashi ya taso wa kansa da tashin hankali..dan a kaff cikin maganganu da yanayin ta sam bai ga alamun rashin gaskiya ba.
Gaba d’aya hankalinsa ya tashi ya sake duburcewa
dan d’an guntun hope d’in dayake dashi yanzu kam ya rasa shi dan ya gama tabbatarwa gaskiya Kausar take fad’i…shiysa ya zab’i zai rungumi wannan mummunar k’addarar ya yi k’ok’ari ya cinye jarabawarsa kawai ba zai sake saka hope ko bincike ba……

Yana sauk’a da niyyar tafiya gida aka fara kiran sallah dan haka ya nufi masallaci…tare suka yi sallar da su Daddy waenda ana idarwa suka tilasta masa ya bisu domin su yi lunch tare.

Daddy ya daina cin abinci a k’asa saboda Mommy dan haka suna shiga suka wuce sama su uku yayinda dinning area na k’asan ya cika da kowa da kowa saboda Ummi ma zuwa yanzu ta d’an ware da taimakon hope da kwantar da hankalin da Hajiya mama suke ta bata,shiyasa take d’an shiga mutane har da ita ake cin abinci.

…
Ko da Yashjub ya wuce ya bar Kausar ciki ta shiga ta wuce bedroom ta fad’a bathroom domin ta watsa ruwa tana mai jin wani sanyi da farin ciki kamar an yi mata bushara da gidan aljannah…plan A ya kammalu successfully yanzu saura plan B!tunda an yi sati biyu ciki zai iya baiyyana kenan,gashi shima Yash d’in ya fara zuwa gida dama tanaso ayi komai a gaban sa ne dan haka ta shirya akan gobe inshaaAllah dai dai lokacin da ta san yana zuwa za ta yi abunda ta shirya…
Tana wannan tunanin tana jin wani tsantsar farinciki hakanan ta kammala wankan ta ta fito d’aure da towel…

Sai da gabanta ya yanke ya fad’i da ta ga Yassir zaune a kan gado idanunsa da fuskarsa sun yi jazur!!!
Ya tsoratata sannan yanayin sa ma ya tsoratata matuk’a..kamar mai jin tsoro haka nan ta k’arasa a hankali ta nemi guri ta zauna a gefensa tace”me ya faru?”
Ta yi masa tambayar a d’arare…

Sai da ya d’auki sama da minti d’aya tukunna ya juya ya zuba mata manyan idanunsa da suka yi jazur yace”Kausar change of plans..ba za mu tsaya har ki haihu kafin Yashjub ya mutu ba ya zamo dole ya mutu a yau!yanzu.”
Gabanta ne ya yanke ya fad’i hankalinta ya yi masifar tashi tashi d’aya yawun bakin ta ya k’afe…da mugun kyar ta samu ta ce”me ya faru?”
Cikin tashin hankali shima yace”kawai as my partner in everything na ga ya kamata in gaya miki ki sani!ki bari zan yi miki bayani amma not now sai in komai ya kammalu dan a yanzu ba zan iya ba Kausar Ina cikin masifa ba zan iya dogon bayani ba.”
Ya fad’i hakan yana mai mik’ewa da shirin fita,da sauri itama ta mik’e ta sha gabansa ta tsaya tace”Yassir kar ka yi abunda za ka tona mana asiri ka lalata komai ka tsaya ka nutsu ka yayyafawa zuciyarka ruwan sanyi ka fad’a mini ne ya faru mu san abunyi….dan Allah dan annabi.”
Ta k’arashe maganar kamar mai shirin fashewa da kuka.
Saida ya runtse fuskarsa cikin tafin hannunsa ya murtsuka ya fesar da wani zazzafan huci kafin yace”Yaran Grenade sun turawa Yashjub message yanzunnan nima suka turo mini evidence,sun tura masa videos har da wanda nake making agreements da basu kud’i duk sun tura masa ta watsapp komai da kika sani duk wani evidence sun tura,for now na san bai riga ya gani ba dan na duba na ga baya online…..
Kausar kar ki ce mini a’a ko kuma ki ce za ki kawo wata idear ya zama dole Yashjub ya mutu kafin ya ga sak’onnin nan ya bankad’a komai ya saka a kashe ni! Kisan wulak’anci cikin rashin gata.”

Karkarwa jikin Kausar ya d’auka…..ganin yana shirin fita yasa ta sake tare hanya tace”Yassir kar ka je garin kashe sa a kamaka!”
This time around cikin tsananin b’acin rai yace”wai ba kya fahimtata ne???duk baya nin da na yi miki ba kya ji na ne??an riga an tura masa ko na yi yunk’urin kashe sa ko ban yi yunk’urin kashe sa ba zai ga komai kuma kashe ni za a yi?dan haka gara in yi yunk’urin hopefully kuma in samu nasara this time around a samu ya mutu!”

Jikinta yana wani irin karkarwa tace”Yassir idan kuma suka turawa Daddy fa?shima binsa za ka yi ka kashe sa?ina ji maka tsoro kar ka je garin hanzari tsoro da fargaba kwab’armu ta yi ruwa!ka duba fa ka ga yadda kwata kwata plan d’in mu bai yi aiki a kan Daddy ba dan sam bai ji haushin Yashjub ba sannan ba mu riga mun ce cikin nan na sa bane ba ya ji ya sani!akwai a lot of things a gabanmu da ya kamata mu yi kar ka lalata komai ka saka mana fullstop dan idan aka kamaka komai ya zo k’arshe…misali yanzu ka je garin sauri a kamaka me kake tunani?,komai fa ya lalace mana kenan?”amma idan muka nustu muka yi tunani za mu samu maf…”

Cikin tarar numfashinta yace”idan ba a kama ni ba kuma fa?sannan idan muka yi slow aka kama ni?”

“Yassir a irin wannan situation d’in mutum have to assume the worst!!!
saboda Ana so ka shirya kare kanka ka shirya mafita ka san abun yi idan komai ya rincab’e,ba fa a abu sama ta ka!”.
Abun nan da ya faru ni a wajena da tunanina gyarasa it’s very easy kar ka rikita kanka ta kwab’a komai ka lala ta komai..a gani na dan sun tura masa tsaff za su iya gogewa tunda watsapp ne..Yassir kud’i fa aka basu suka karb’a suka yi maka aiki in the first place!all you have to do shine ka k’ara musu kud’i tashi d’aya za su manta da wani Grenade su bi ta watsapp d’in su goge tun da kace ba ya online ni kuma daga nan har zuwa dare ba zan bashi kwanciyar hankalin da zai hau watsapp d’in ba ma!.ai yana cikin gidan nan dan yanzu ma ta window Ina wanka sai da na hango motarsa a fake so bai tafi ba har yanzu..you just wait and watch..sannan ka nutsu dan Allah!!kashe mutum yana da buk’atar plan da shiri,ko kaza za a yanka sai an wasa wuk’a an tanadi ruwa ballantana mutum d’an adam!ba ka da plan ba ka da komai tashi d’aya kace za ka kashesa a rana d’aya wallahi ba ni da tantama hakan ba mai yiwuwa ba ne ba kuma sai an kamaka!kwanakin baya da ka yi yunk’urin hakan da tsararren plans har biyu ya mutu???sai yanzu a cikin rana d’aya ne kake son miracle ya faru?”.

Shiruu Yassir yayi yana mai fitar da huci kafin chan ya rungumeta cikin huci yace”I love you Kausar na gode da kika wayar mini da kai,tabbas maganar ki gaskiyace…but duk abunda kike planning make it fast saboda inaga masallaci kawai ya tafi daga nan zai wuce…”

“Okay bari in saka kayana”
Kawai tace,daga haka ta nufi closet d’inta ta zaro doguwar riga ta saka ta zare towel d’in ko undies da mai bata buk’ata ba haka nan drawer ta d’auko turaren da tunda cikin ya shigeta ta tsani warinsa ta fesa a palm d’in ta ta runtse da sauri dan tashi d’aya ta ji amai ya taho mata…Tana fara shiri Yassir ma ya fara waya da mutanen,ta san ba shi da enough kud’i yanzu shiyasa k’asa k’asa tace masa”ko nawa suka ce ya yarda za ta cika masa”
Daga haka ta saka Kai ta fice daga d’akin tana jin
mugun mugun haushinsa,a ko da yaushe idan ya yi yunk’urin kashe Yashjub ji take kamar ta kashe sa!.
Addu’ar ta d’aya Allah ya sa mutanen su yarda kar su basu problem ita kuma ko nawa suka ce za ta bayar ba ta so wani matsala ya taso ta koina kafin a yi aurenta da Yash.
Chapter 99 · 0% Book details