Sashe 90
Munnubiya Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Yassir ya fi kowa tashin hankali a cikin sati biyun da suka gaba ta,abubuwa sun taru ta ko’ina sun yi nasa yawa!….Sam bai ga alamun fushi ko jin haushin Yashjub daga Daddy ba kamar yadda suka yi zato shi da Kausar,Sannan Yashjub da Manubiya shiru kuma ya san ta ga message d’in da ya tura mata amma ko jiya da ya tambayi spy d’insa na gidan ce masa ya yi tana nan Yash d’in ma ya daina fita aiki….wani irin kishinta yake yi idan ya tuno
tana tare da shi gashi shi fa har ga Allah hak’urinsa ya k’are a kanta…ita kuma Hajiya mama da Daddy sun ce daga kansa har zuwa kan Yadira kowa ya zauna a gida kar wanda ya je musu for now a barsu su huta.
Gashi waenda aka kama akan batun lamarin case d’in estate ya yi
musu alk’awarin zai saka a sake su su gudu har yau abun ya gagara dan waenda yake tunanin zai bada cin hanci su taimaka mutanen su gudu sun ce babu ruwansu case d’in a hannu manya yake…Su kuma Yaran waenda aka kama d’in sun ce “hak’urinsu ya k’are dan haka sun bashi kwana d’aya tak ya yi wani Abun if not wallahi za su kai sunan sa da recording d’in wayoyin da aka dinga yi har ma da wasu videos da bai tab’a sanin akwai su ba..su tona masa asiri”
saboda horo mai tsanani ake yiwa oganinsu gashi an hana a gansu yanzu haka ma suna tunaninan kashe d’aya ne……..
Kausar ma jikin ta da sauk’i ko da suka je asibiti cewa aka yi ba sai anyi wani plastic surgery ba kawai magani aka yi ta shafa mata jiya kuma da ciwon ya warke ta fara shafa maganin scar saboda kar ta yi tabo a fuska.
Yashjub ma ya tara gaba d’aya footage na cctv camera amma tsoro da fargabar cikar zarginsa sun hana shi dubawa..
[17/09, 8:03 p.m.] Hauwajidda: MANNUBIYA
(Book 2)
Page 34
Na
Humayrah Bulama
Mikiya Writers Association.
“Na gaya miki dama,ni ne Mijinki…in da ace ba ki tsaya b’ata mana lokaci ba da tuni abubuwa da dama basu faru ba!.
Allah ya bamu zaman lafiya Jidderty”
Yusuf yana gama turawa Jidda message kamar haka ya juya ya nufi cikin masallacin yana zuba wani faffad’an murmushi yana ji kamar an yi masa bushara da Gidan Aljannah.
A gefen Baba ya nemi guri ya zauna,idaunsa a kan Baban Al’ameen wanda tun d’azu ya ke ankare da shi yana sane da shi ya san so yake a fasa auren a bawa d’ansa,har ga Allah bai yi niyyar yiwa Baban Al’ameen ko Al’ameen d’in wani abun ba amma abunda mutumin yake ta yi tun d’azu ya sa ya k’ullacesu kuma sai ya nuna musu waye Yusuf! bari a gama d’aura masa aure da Jidda a kaita gidansa lafiya Wallahi sai ya b’atar da su.
Ana shirin fara d’aurin auren.
Sojoji da y’an sanda masu fararen kaya sun fi mota ashirin suka danno kai cikin layin a dai dai wannan lokacin.
Sojoji uku da ss guda d’aya ne suka shigo cikin masallacin suka ce “kowa ya fito!”cikin dakakkiyar murya,aikuwa tashi d’aya waje ya hautsine,
cike da fargaba jama’ar suka fara kiciniyar fita ana hayaniya da tambayar “mai ya faru”
Baba ne ya juya da niyyar cewa Yusuf”mu je mu ji mai ya faru,a samu abun ya lafa sai a dawo a d’aura”..amma kamar walk’iya da ikon Allah sai ya ga babu Yusuf babu mai kama da shi bayan yanzunnan suka gama magana.
A b’angaren Yusuf kuwa tun da ya ga Sojoji hankalinsa ya yi masifar tashi,tsoro ya rufesa in banda dukan uku uku babu abunda k’irjinsa yakeyi, dukda kuwa ya san cewa fuskarsa is not known a cikin yaran black snake kuma he’s not wanted amma hakan bai hanasa tunanin watak’il shi aka zo nemeba,dan yanzunnan yaga message d’in Abokinsa ta inda yake cewa”an zo kama Black snake a airport ya yi yunk’urin guduwa an harbesa ya mutu sannan an bud’e wayarsa an fara binciken neman yaransa,dan haka a duk inda yake ya gudu kafin a samu komai ya lafa.”
Yana gama karanta message d’in ko numfashi bai ja ba ya ga Sojoji sun shigo shiyasa ana fara hayaniya ya sulale ya bi ta k’ofar liman da sauri ya fice amma yana fita yaci karo da wasu a ta gaban k’ofar saboda dama zobe suka yiwa masallacin….tashi d’aya suka damk’esa dan an raba musu hotonsa shiysa suka yi saurin shaidasa.
Baba Yashjub wanda k’arasowar sa kenan sai su Ya Musbah sojojin suka yiwa bayanin arresting Yusuf da aka yi……
…..”A cikin wayar black snake suka hararo Yusuf ta hanyar bibiyar chat d’insu da suka yi,an gano yana d’aya daga cikin manya manyan yaransa masu tayashi safarar kwayoyi da y’an mata dan yanzu haka ma a wannan ranar if not ba a kamasu ba to suna shirye shirye ne a kan shi Yusuf d’in zai taimaka a sacewa Black Snack wata Yarinya ‘Mannubiya’…..”
Dan haka za su tafi da shi kuma babu bailing har sai sun gama interrogating d’insa daganan idan suna so za su iya d’aukaka k’ara zuwa kotu kafin a yanke masa hukunci….
Suna ji suna gani aka datsawa Yusuf ankwa wanda yake ta turje turje aka wuce da shi,shi dai Baba bai gama gasgatawa ba amma su Ya Musbah da Yashjub wanda yake ji kamar ya bisa ya fara nad’a masa shegen duka tun a nan saboda tunanin sace masa mata ma da ya yi,duk sun yarda.
Kaka mallan kam har da kukan sa a take ya nemi adaidaita sahu ya nufi gida yana tafe yana kiransu Baba Habu a waya…..
Limamin ne ya matso ya yiwa Baba jaje kafin yace “yanzu a yi sanarwa Akan an fasa d’aurin auren kowa ya watse kenan?ko za a d’aura ko babu shi?”
Murmushi ya Nafi’u ya yi ya kalli Baban Al’ameen wanda ya k’araso yanzun yace”za a yi d’aurin aure yanzu amma ba da wanchan Angon ba,an chanja sabon Ango.”
Jinjina kai Baba ya yi yana jin wani nauyi yana sauk’a daga k’irjinsa dan har ga Allah da ya d’aura auren nan yau da bai san ta ya zai kalli Jidda ba,cike da kwarin guiwa ya kalli Limamin yace”sunan sabon Angon Muhammad Al’ameen Muhammad.”
Murmushi mahaifin Al’Ameen ya yi a fili yace “Alhamdulillah”
Daga haka suka d’unguma izuwa masallacin.
Jidda ne kawai da Siyama sai Muhsin wanda shima ya yi jigumm a cikin d’akin….
Kamar a mafarki ta ji ana sanarwa a loudspeaker”An d’aura auren Muhammad Al’ameen Muhammad da Maijidda Musa akan sadaki naira dubu d’ari biyu lakadan ba ajalan ba….
Wani irin bahagon numfashi ta fesar ta sake kwantar da kanta a kan cinyar Siyama wasu zafafan hawaye suka shiga gangaro mata a ranta tace”shikenan na zauce!!gashi dai k’iri k’iri da Yusuf aka d’aura auren nan na riga na sani amma sunan Al’Ameen nake ji…..”
“Jidda kin ji abunda kunnuwa na suka ji kuwa???”
Shiruu ta yi kafin ta tashi a mugun zabure ta mik’e ta zauna sakamokon abunda ita da Siyama da Muhsin suka ji an sake fad’a ana kuma maimaitawa a loudspeaker dai dai nan su Anty Umma suka shigo Anty Umma tana shigowa ta rungume ta haka ma Aisha wadda take waya da Nafi’u domin ta tabbatar….
Sai da ta yanke wayar tukunna ta sanar da su komai abunda ya faru…
Nan waje ya kaure da murna Jidda kuma ta fashe da kukan da kowa ya san na farin ciki ne…
Har cikin d’akin Ammi ta shigo ta rumgume Jidda ta sake neman yafiyarta tukunna tace”Bari ta tafi ta fara shirye shiryen tarbar amarya…”
Tare suka tafi ita da Mama domin su je su d’anyi shirye shirye….Zuwa yanzu Mama ta tabbatar Yashjub dai d’an gidan Imam Manubiya ta aura dan tana ganin su Yusra ta ga kamanni,ta dad’e da yiwa kanta alk’awarin fita daga harkar Imam da zuri’arsa amma kuma tana so ta ji ya Yahanasun take,dan haka ta tsara a kan za ta ke tambayar Manubiya halin da y’ar tata take ciki ba tare da ta bari ita kanta Manubiyan ta fahimci wani abu ba….
Akwai tafiyar da Al’ameen zaiyi zuwa Dubai nan da sati d’aya shiyasa ana gama d’aurin auren Mahaifinsa ya cewa Baba”sai nan da sati d’aya tukunna za su d’au amarya inshaaAllah daganan direct sai a wuce da ita airport”kamar ya sani sai ya d’aura da cewa”amma dai za su fara magana da Angon yanzun duk yadda suka tsayar zai kira sa.”
Aikuwa albishir yana zuwar ma Al’ameen bayan ya gama kukan farin ciki ba kunya ba tsoron Allah ya ce shifa kawai a kawo masa matarsa yau su zauna a nan kafin su wuce”
Dariya su Ammi suka yi suka kira su Inna suka sanar musu….k’arfe takwas dai dai aka kawo amarya Jidda side d’in Al’ameen da ke cikin gidan.
Sai da kowa ya watse tukunna ya shigo…farin ciki da tsantsar nishad’i masoyan suka tsinci kansu a ciki mara musaltuwa….tunda ya shigo ya yi hugging d’inta suka yi shiruu da kyar ya cikata suka yi nafila suka d’anci abinci daga haka ya ja ta ya sakata a jikinsa yana sauk’e ajiyar zuciya yana hamdala suka kwanta…..Jidda har ta fara fargaba..ganin awa d’aya awa biyu bai yi yunk’urin yi mata komai ba ya sa ta kwantar da hankalinta tana mai sauraron yadda k’irjinsa yake bugawa da k’arfi har zuwa yanzun,a haka suka kwana ranar in ka gansu kamar wanda aka cewa wani zai kwace masa ita ne,ita kam Jidda jikinta har ya fara tsami tsabar yadda ya ruk’umk’umeta…..