Sashe 117
Munnubiya Part 2 Complete Hausa Novel · about 7 min read
Sai da Baba larai ta yi sati d’aya tukunna Mommy ta basu izini suka fara nemanta sai dai kuma babu kalar kiran da ba su yi mata ba amma wayarta ba ta shiga kuma sun kira k’auyensu ance bata je ba dan haka hankalinsu ya tashi matuk’a.
A b’angaren Kausar da Yassir kuwa ko da yayi mata maganar aurenta da Yashjub nuna masa ta yi itama ba ta so kuma ta yi abunda ta yi ne saboda ta yi tunanin Yash d’in zai fara bata wani abun daga cikin dukiyar sa ko ya ba ta gida ya ce ta zauna a inda za ta je d’in…amma ita sam ba ta yi tunanin su Daddy za su yi musu aure ba.Dan haka ya taimaka ya taya ta nemo Yash ya sauwwak’e mata ita kam aurensa ba ya cikin plan d’insu.
Sai da Yassir ya nuna mata b’acin ransa na k’in tuntunb’arsa da ta yi kafin ta yi abun ita kuma ta basa hak’uri tare da alk’awarin ba za ta k’ara ba tukunna ya yi mata alk’awarin nemo Yash a duk inda yake ko ta message ne a samu ya sake ta…Hakanan suka rabu daga shi har ita babu wanda ya san ba aure ma tsakanin Kausar da Yashjub d’in.
Bayan kwana biyu ta san yadda ta yi ta bincika wayarsa ta d’auki number mutanen nan masu evidence ta b’oye numberta ta tura musu message tace”su turawa Yashjub da duk wasu mutanen da suke neman wanda ya yi aika aika a Estate d’in Yashjub za ta basu ko nawa ne.”
Saboda ita har ga Allah Yassir ya ishe ta kuma ta san idan ba kama sa aka yi aka kashesa ba to tabbas ba zai barta ta sakata ta wala ba.
Abuja su Manubiya suka fara zuwa kafin su gama shirye shiryen tafiya….sai bayan sati biyu tukunna suka isa Copenhagen Denmark suka yi settling
Cikin rarrashin da tsoron shiga Hakki ta shiga k’ok’arin fahimtar da shi cewa “ko ba komai fa Kausar matarsace!!”
Har ga Allah sai da ya yi mata bayanin da shi kansa sai a cikin jirgi da kwakwalwarsa ta d’an huta tukunna ya tuna sannan itama ta tuna tabbas fa da gaske babu aure tsakanin Kausar da Yashjub saboda ba a d’aura aure da ciki!!
A ranar tsakanin Manubiya da Yashjub ba za a ce ga wanda ya fi wani murna ba……daga nan suka kawar da duk wani b’acin rai suka shiga shimfid’a rayuwarsu mai dad’i a Copenhagen dan basu ga ranar dawowaba….
Mommy kuwa zuwa yanzu ta san me za ta yi game da auren Kausar da Yashjub…………
[17/09, 8:03 p.m.] Hauwajidda: MANNUBIYA
(Book 2)
Page 41
Na
Humayrah Bulama
Mikiya Writers Association.
A b’angaren Mommy kuwa zuwa yanzu ta san me za ta yi game da auren Kausar da Yashjub.
Ta riga ta san zuwa yanzu Yashjub ya san babu aure a tsakaninsa da Kausar..kuma ita kanta zuwa yanzu ta san ba ta da lokacin da zata ce sai sun cire Manubiya tukunna za su kashe Yashjub! shiyasa kawai ta ma hak’ura da sake k’ulla auren Yash da Kausar d’in a karo na biyu.
Ta dai ji Daddy yana cewa Ummi”Kausar d’in tana a matsayin matar Yash a idanun duniya har zuwa lokacin da za ta haihu.Gudun b’acin suna.”
So ita kuma kafin nan da zuwa lokacin da Kausar d’in zata haihu inshaaAllah barinta zai cika kud’irinta zai cika kuala ta san barin Kausar d’in ma da aka yi a mazaunin matar Yash d’in Allah sai nuna hanyar da za su yi taking advantage d’in hakan inshaaAllah..
Kawai ita yanzu wuyarta ta san inda Baba Larai take,she really needs her yanzu kam saboda ta riga ta gama tsarawa akan duk bala’i wuyarta Yashjub da Manubiya su sako k’afa a cikin k’asar Nigeria wallahi sai ta ga bayan su!!
Dole a yita ta k’are abun ya yi yawa kuma anzo gab’ar da dole ta yi musu hakan cikin gaggawa idan ba haka ba kuwa to tana cikin masifa!!!!
Zuwa yanzu idanunta sun rufe..as far as she knows Ita da Yassir suna cikin gadon Yashjub dan haka ba sai ta wani jira sun yi abunda suka yi an mallaka masa dukiya ba,iyaka kason da za su samu ma idan an raba gado ya isa!
Daganan su kuma su Daddy da Ummi da su Hajiya Mama duk za ta saka su a saiti InshaaAllah ta san me za ta yi musu,gara kawai a yita ta k’are……
amma kuma rashin sanin whereabout d’in Baba larai babban fullstop zai sakawa mission d’in nata saboda Baba larai d’in ce za ta yi komai tun daga kan dawowar da take so suyi da gaggawa har mutuwarsu.
Tsakanin Mommy da Yahanasu sam ba jituwa kwata kwata Yahanasun ta k’i yarda ta ba ta chance har y’an gidan sun fara lura da yadda Mommyn take binta ita kuma tana kaucewa…
Mommyn har da ce mata “InshaaAllah za a karya abunda aka yi mata a samu ta yi aure!”
Ita kuwa Yahanasu tace”dan girman Allah kar su karya komai!
su barta a yadda ta ke ta yi Imanin Ubangiji ne kad’ai zai iya yin ikonsa a kanta.”
Kamar yadda Mommy ta yi zato Yahansun ba ta tona mata asiri ba ammafa tun daga wnanan ranar ko had’a hanya Yahanasu ta daina yarda ta yi da Mommy,k’ofar d’akinta kuwa kullum a rufe.
…..
……Wata d’aya wata biyu tun su Mommy suna d’aukar b’atan Baba Larai abun kamar wasa har suka zo suka fara tsorata dan yau kwana sittin kenan babu ita babu alamarta wayarta ba ta shiga gashi suna tsananin buk’atarta dan Ya’isha ta d’aga musu hankali akan auren Najeeb da Siyama gashi Yash da Manubiya babu su babu dalilinsu ba ma ta jin za su dawo bikin,Yassir kam ya sake tab’arb’arewa company d’in da Yash ya bud’e masa ma ya tashi a aiki Hatta building d’in nasa ya sayar motocinsa masu tsada ma ya siyar kuma har yau ba a san Ina yake kai kud’in ba..
Kausar kam ba k’aramin Namijin k’okari take yi wajen danne zuciyar ta game da shi ba gashi mutanen da ta addaba da kira a kan su tona masa asiri a samu a kashe sa ta hutu!sun daina sauraronta kamar waenda ya yi musu tsafi!
A fannin lamarin Yash kuwa ita kad’ai ta san me take going through ta kira sa ta yi message amma duk baya shiga ba ya tafiya tsabar bala’i har depression ta kamu da!
da kyar ta samu ta nutsar da kanta ta ke shan magani ganin tana shirin haukacewa!!
Inda ace babu aurenta a kan Yash ya yi wannan dogon zangon da baza ta tab’u sosai ba
amma wannan zumar da aka lasa mata a baki aka janye shi yafi komai haukatata!!
……saboda Allah ace ranar da ake shirye shiryen kai ka gidan Miji mijin ya gudu kuma har yau bai dawo ba!(dan ita har yau ba ta san ba matar Yashjub bace ba ita.)
Dukda wannan bala’in da take ciki amma tana namijin
k’ok’ari wajen rik’e kanta da controlling kanta,zuwa yanzu ba ta da komai against su Mommy amma haka kurum take jin she can’t share matsalarta da su she can’t trust anyone anymore….. abunda Mommy ta yiwa Baba larai ma ya sanya Kausar d’in ta d’an tsorata da Mommyn,ta ja jikinta sosai
Doctor d’inta dai yace mata hakan sign ne na depression d’in da ta kamu da shi saboda ta yi going through a lot a rayuwarta da yawa shiyasa ba za ta iya sake trusting kowa ba(ta zama so secretive)sai dai sam ita ba ta wani yarda ba,ta fi raja’a akan kawai dai shekarunta da suka ja ne suka sanya ta yi wayo ta zamo silent ta kuma koyi rik’e sirrinta.
A kaff y’an matan gidan har ma da Mommyn babu wanda ya lura da cewa ba ta ma da lafiya saboda kamar yadda take cikin masifa hakanan suma kowa a cikin masifar take!
Su Yasira zuwa yanzu rashin aure ne matsalarsu dan auren Yadira da suka ga ya taho gadan gadan ya sake uzzura musu son aure a cikin zuk’atan su especially ma Yasira da ta fissu shekaru sai dai kuma ko talakan saurayi babu mai shi a kaff cikinsu,Ya’isha kuwa tata damuwar daban ce dan ji take muddin Najeeb ya auri Siyama a gaban idanunta to kuwa sai ta mutu!!!
Mommy kuwa nata tashin hankalin ya fi na kowa dan itama rashin auren nasu yana damunta amma ba kamar yadda komai ya rinchab’e mata ba!!
Ta ko’ina babu haske babu sauk’i babu nasara……Kausar d’in ma da ta shirya akan za ta yi mata Abu da Yashjub a kan Daddy gashi yanzu babu auren,kuma a yadda take ganin Daddy kwana biyun nan in dai ba irin wannan aikin aka yi ba tabbas akwai gagarumar matsala.