← Book details Munnubiya Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 77 OF 137

Sashe 77

Munnubiya Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Numfashi Baba larai ta fesar kafin tace”kar ki damu..Daddy yana fita na kira mutumin da muka ce ya saka mana ido a kansa,ashe ciwon hanta ne ya ke damunsa likita yace ba shi da sauran lokaci shiyasa yake neman Daddyn ya samu ya gaya masa gaskiya.”
Numfashi ta fesar kafin ta ci gaba da cewa”tunda dama mutuwa zai yi shiyasa kawai na cewa mutumin ya k’ara masa gudu zamu bashi naira miliyan d’aya,to dai a halin yanzu Ina tabbatar miki mallan lawal ya tafi kai balance dan mutumin a lokacin ce mini ya yi a take zai aiwatar da aikin dan gidan dama ba kowa shi mallan lawal d’in ne kawai da shi da jikarsa ita take jinyar sa to alokacin ya ga ta tafi kasuwa……yanzu miliyan d’ayan za a tura masa dan naga ya kirani d’azu Ina asibiti shiyasa ban d’auka ba.!Muna tura masa ni kuma zan kama gabana dan ba zan zauna ki ci gaba da lalata m….”
Cikin Jin dad’in maganganunta Mommy ta rungume Baba larai wanda hakan ne ya sa ta kasa k’arasa abunda take cewa,wani kuka Mommy ta fashe dashi tana cewa”na gode Larai na gode sosai ki bani accnt number miliyan biyu ma zan bashi wallahi….sannan zan gyara wallahi zan yi yadda kike so dan Allah kar ki sake cewa za ki tafi.”

Da kyar Mommy ta lallab’a Baba larai ta hak’ura da tafiya,daganan suka kira mutumin ya shaida musu cewa”Mallan lawal yana ma shirin shiga k’asa a halin yanzu dan wanka ma ake yi masa.”
Naira miliyan biyu Mommy ta tura masa a take daga nan ta nutsu tana sauraron hud’ubar Baba larai.

Da sallama Yasira ta turo k’ofar d’akin ta shigo,kafin ta k’araso ta zo ta tsaya a gabansu.
Kallonta kawai Baba larai ta yi ta maida hankalinta ga Mommy kafin tace”a baya da kika iya kwantar da Kai wacce kalar riba ce ba ki ci ba?yanzu kuwa kinga ai komai lalace miki yake yi saboda rashin tunani da lissafin da kika bawa ragamar rayuwarki,kuma bari ki ji ba ni da tantama a yau Yash ya dasa ayar tambaya a kanki wallahi saboda abunda kika yiwa Manubiya a gaban kowa ya na nuni ne da kin tsaneta dama tun asalin farko wanda hakan zai sanya ya fahimci dama chan pretending kike yi kuma bakin ku d’aya ke da su Yasira duk ba son matarsa kuke yi ba!dan haka yanzu ko ciwon yatsa Manubiya ta yi Ina mai baki tabbacin Yashjub ke zai zarga tunda dama ba wata shak’uwa ce a tsakaninku ba balle ya ki zarginku,kuma ko su Yasira sun je gidan ido zai sanya musu ya dinga d’arr d’arr da su ta yadda ba su isa yin komai ba shikenan kina ji kina gani Manubiya zama daram!
Hakanan abubuwa za su yi ta faruwa da mu,tunda kink’i ki bada goyon baya mu samu a yi abunda za ta tafi.
Shiysa na yanke shawarar in tartara ya nawa ya nawa in kama gabana tun kafin bomaboman da za su iya hallaka ni su fara fashewa.”

Ajiyar zuciya Yasira ta sauk’e kafin tace”Mommy nima gaskiya abunda kika yi yau ban ji dad’in sa ba….”
Cikin tarar numfashinta Baba larai tace”Yasira yo
ai har da ku!”
Jin jina kai Yasira ta yi kafin tace”ni kam zuwa yanzu Baba larai duk yadda kika ce inshaaAllah hakan za ‘a yi,saboda hakan ne kawai mafita,gara in yi tolerating d’inta in nuna ina sonta in ja ta a jiki na wata d’aya ko biyu akan mu rayu da ita har abada muna fama da ita tana janyo mana masifu kala kala,na tabbatar kashe Ya Yash da aka so yi a yau shima duk a cikin masifun da take tafe da su ne!.”
Cikin sauk’e ajiyar zuciya ta kamo hannun Baba larai ta ci gaba da cewa”dama ai ya san za mu je mu tayata gyaran gidan ko?”ba ta jira jin mai Baba laran za ta ce ba ta d’aura da cewa”zan yiwa su Yasmeen magana da su Yusra na yi miki alk’awarin inshaaAllah daga yau mun chanza zani,amma Ya’isha ba za ta bimu ba dan na san za ta iya b’ata mana komai…ki had’a duk wasu abubuwa da ya kamata inshaaAllah this time around ba za mu baki kunya ba ,za ki sha mamaki…”

“Allah ya yi miki albarka Yasira,zuwa dare zan ganku ke da su Yasmeen d’in kafin ku tafi”

Jin jina kai Yasira ta yi kafin ta kalli Mommy tace mata”Daddy yana son ganinki…”
Daga haka ta juya ta fita ta rufo musu k’ofar….

Tana fita Baba larai ta saki murmushi dan tabbas ta hango jajircewa a idanun Yasira,ta san kuma su Yasmeen ma za su yi mata biyayya inshaaAllah wannan karon akwai nasara….cikin jikin Manubiya za su fara farma a yadda Yash yake ji da cikin nan ta san easily za su samu matsala da shi da ita idan har suka nuna masa kamar Manubiyan ce ta zubar,but tayaya za su nuna masa hakan??dole su nemo reason da zai yarda da shi……
Tana wannan tunanin ta ji Mommy tace”bari in je…”
Kallonta Baba larai ta yi kafin tace”Juyin duniya!Khadija kar ki kuskura ki bari ya fahimci kin san wani abun”
Jinjina kai Mommy ta yi gabanta yana dukan uku uku ta juya za ta fita…cikin son kwantar mata da hankali Baba larai ta ruk’o hannunta tace”ki kwantar da hankalinki…”
Hawayen da suka b’allewa Mommy ne suka sanya ta kasa ci gaba da magana,a hankali ta rungumota ta shiga lalllashinta..fashewa Mommy ta yi da kuka cikin kukan tace “dan Allah dan annabi larai kar ki sake cewa za ki tafi,a wannan worst situation d’in larai idan kika tafi kika barni Ina makomata??…”

Ajiyar zuciya Baba larai ta sauk’e ta cikata tace”ba bu inda zan je amma Khadija kema sai kin chanja zani!kamar yadda su ka yi alk’awari dan Allah kema ki gyara…mu samu Yarinyar nan ta tafi daganan mu aura masa Kausar bayan shekara d’aya ko biyu idan ta haihu muka samu abunda muka so sai mu k’arasa shirin mu a samu a rufe chapter nan wallahi na gaji,sai abu d’aya ake yi yau kusan shekara nawa amma ba riba!”

Ajiyar zuciya Mommy ta fesar kafin tace”Larai I can’t trust Kausar with Yashjub anymore,a da na d’auka soyayyar da take yi masa mai sauk’i ce ko kuma lust ko wani abu makamancin haka shiyasa na yi tunanin idan suka yi shekara d’aya ko biyu ta samu abunda takeso ta haihu ta d’an zauna da shi ya fara fita a ranta to za ta iya yi mana abunda mukeso dan na san tunda ba ya sonta musguna mata zai ta yi…amma yanzu na fahimci masifaffiyar soyayya take yi masa,no matter what she’ll stick around and always love him unconditionally….abunda Yasmeen ta yi mini akan batun zubar da cikinnan ya sanya na fahimci Yaran nan ba za a dad’e ba kowacce za ta fara fito da nata view d’in tana jayayya da ni,kuma indai har Yasmeen y’ar cikina za ta iya yi mini hakan to abu mai sauk’i ne ga Kausar dan ta bijere mini,shiyasa na gama yankewa akan’babu maganar Kausar da Yashjub za mu san yadda za mun yi amma I can’t trust Kausar akan wannan Lamarin gaskiya…..”
Shiruu Baba larai ta yi kafin tace”to amma kuma ta ya za mu samu wanchan abun kenan?ko mun b’ata shekaru a banza kenan?ki duba future d’in Yassir ki sake tunani….”shiruu Baba larai da maganar ta d’an yi tunani kafin tace”to ko Manubiya za mu jira ta haihu idan ta haifa sai mu rik’e…….”

Cikin katseta da d’an b’acin rai Mommy tace”haba larai!ke fa da kanki ki ka sanar da ni illar kasancewar Manubiya a tare da Yashjub kuma gashi muna gani muraran!…besides ko dan masifar da wannan cikin da Uwarsa da Ubansa suka sakani a ciki wallahi dole sai ya fita!ko ana ha maza ha mata……”

K’ausar tana hawaye,a haka ta k’arasa side d’in Mommy ta shiga ta wuce parlourn ta nufi bedroom,har za ta tura k’ofar d’akin ta shige ta ji Mommy tana cewa”za dai mu san abunyi za mu nemo mafita amma cikin jikin Manubiya ya zama dole ya fita,sannan ba zan tab’a bari Kausar ta auri Yashjub ba!.”
Wani irin duhu duhu dishi dishi Kausar ta fara gani…ita da ta zo a kan ta cewa Mommyn ‘mai zai hana a yi tricking Yash ta samu ciki ta yadda dole sai ya aureta…’
amma shine take jin wannan batun daga bakin Mommy??
Dama ita ba ta yi shirin gaya mata tana da ciki ba dan ta san ba za ta yarda a aurawa Yash ita da cikin Yassir a jikinta ba,shiyasa take so ta bata wannan idear ta yadda ko shi Yassir d’in bai Isa ya san cikin nasa bane kawai kowa a tafi a kan cikin Yash d’in ne,ta samu ta rufawa kanta asiri burinta ya cika.Sam ba ta yi expecting haka daga Mommy ba,wato ta barta ta gama lalacewa shine yanzu take kyamar ta had’a d’anta da ita kenan ko yaya?
tabbas blood is thick! Ita kuma ta tabbata all alone….
Wani Irin kuka ne ya taho mata dan haka ta yi sauri ta juya gudun ma kar su jiyo ta ta nufi k’ofar parlourn hannunta a kan bakinta tana mai k’okarin hana sautin kukan nata fitowa.Kusan karo suka yi ita da Daddy wanda ya turo k’ofar parlourn ya shigo.
Shi ya wuce ya nufi d’akin ita kuma ta fice ta nufi d’akinta tana kuka kamar ranta zai fita.

A tsaye ya same su ita da Baba larai….sum sum haka Baba larai ta sa kai ta fice bayan ta yiwa Mommy wani kalar kallon da su kad’ai su ka san me take nufi.

Tana fita ya lumshe idanuwansa ya d’an bud’e kafin ya k’arasa kusa da ita yana mai kallon cikin idanuwanta yace”mallan lawal ya rasu”
Gefe da gefe ta kalla kamar irin tana tunani d’innan kafin tace”Daddy mai ya faru??? Kai fa ka ce a daina maganar nan kuma yau kai da bakinka ga shi ka kawo ta?”
Chapter 77 · 0% Book details