← Book details Munnubiya Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 134 OF 137

Sashe 134

Munnubiya Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read

A b’angaren Manubiya kuwa gaba d’aya ta gagara gane kan Yash!!tun ranar da Inna ta rasu ya chanja gaba d’aya kuma ba wai ita kad’ai ba kowa yake yiwa hakan….haka kurum sai dai ya yi shiruu ya zauna ya tusa mutane a gaba babu um babu um’um ya yi ta kallon kowa amma iyaka idanuwansa kad’ai idan ka kalla tashi d’aya zaka fahimci yana cikin masifa da tashin hankali…
Hatta office ma da Najeeb ya zo zai yi masa handing over cewa ya yi ya cigaba kawai ba zai iyaba……..
Shima da so ya yi ya chanjawa Manubiya gida amma sai Hajiya mama tace”kawai ya zo Mansion d’in Daddy su zauna a side d’insa na da dan tabbas yanayinsa yana mugun bawa har su su Hajiya maman tsoro gashi an yi tambayar duniya yace musu”he’s fine!!!”

Mommy kuwa har yau bata cire raiba……Ya’isha dai ta tafi dahirr ta ma cire rai….….amma tsohon yace mata”ta kwantar da hankalinta indai hular Manu aka d’auko
akayi aikin da ita to fa ta zuba ido
Anytime labarin rasuwar Manu zai risketa!!watak’il inna itama ta saka hular shiyasa abun ya shafeta kuma shiyasa aka samu delay na mutuwar Manubiya amma tabbas tana hanya itama….Su Yasira kuwa zuwa yanzu sun dawo daga rakiyar Mommy…babu Ya’isha babu labarinta zuwa yanzu idan suka yi mata maganar Ya’ishan ma fad’a take rufe su dashi…dukda sun san itama tana cikin masifa amma sam wannan ba abun da za su yi shiru bane dan haka Yasira ta shirya akan zata je ta samu Daddy tace masa ba fa su ga Ya’isha ba kuma Mommy ko maganar ba ta so ayi!!!
Ta san ko da matsalar ganin da take fama da shi aka barta ya isheta(dan zuwa yanzu kwata kwata idonta na dama ba ya aiki na biyun shima ya tab’u sosai)amma fa ba zata iya cigaba da yin shiru ba wallahi,dan this is a serious case.

A lokacin da Yasira suke maganar za su je su samu Daddy ita da Yusra Mommyn tana jinsu…
Shiyasa hankalinta ya sake tashi matuk’a,dama masifar rashin gani da tsohon ya ke ta amshe kud’inta ana ta yin magani amma a banza ta isheta ga Manubiya da ranta har yanzu Yash ma haka…a halin da take ciki dai yanzu ta ajjiye komai a gefe a samu ta fara gani tarr tukunna sai a yi komai su kuma su Yasira ta san ta rufe musu Baki a kan case d’in Ya’isha to amma kuma gashi yanzu kwatsam! Suna shirin jik’a mata aiki,har fa su Yasmeen ta hana zuwa gidan duk dan kar a tambayi Ya’isha a waya kuwa da suka ji shiru tace musu bata da lafiya ne ita kanta sai yanzu ta san tanada matsala fa dan Bata san me zata ce game da Ya’isha ba a gaba dan ba zai yiu ta yita b’oye b’oye forever ba.

A b’angaren Abbakar shima tunda aka yi rasuwar kusan kullum sai ya je musu gaisuwa da daddare lokacin da ya tabbatar ba zai had’u da Yash ba!
Ita dai Manu gaisawa kawai suke yi daga haka ta wuce d’aki dan abu da Abbakar sam ba ta so…to yanzu kuma ya isheta a waya yanason taimakon ta,ta yi blocking d’insa amma a banza a rana sai ya kirata sau bakwai da different layuka ga messages,dan ma Allah ya taimaketa Yash bai tab’a gani ba saboda shima he’s
not himself kwana biyun nan daina hankali kawai. …Ta san watak’il akan rashin lafiyar mahaifiyarsa ne da ya k’i ci ya k’i cinyewa (saboda ta ji anata maganar ciwon nata)
amma ita har ga Allah tsoron d’aukar wayar sa ma take yi,Shiyasa jiya da ta je gida ta tura Muhsin gidansu ya karb’o mata accnt number sa ta tura masa dubu d’ari amma kuma dukda haka Abbakar bai bar kiranta da tura mata sak’onni ba.

A b’angaren Kausar kuwa,tana nan cikin tashin hankali dan ga Yash da Manu a cikin gidan kusa da ita amma kamar basa nan…..ba ta Isa ta je inda suke ba kuma tun da suka zo
ko ganinsu bata yi ba,Yasmeen dai tana zuwa wajensu har Yadira idan sunzo amma shi kam saboda ita ko lek’owa bayayi itama Manu ya hanata shiga main cikin gidan kuma su Hajiya mama sun yarda da hakan,Daddy dai da asubah suke gaisawa Hajya mama kuma ta kan je musu da kanta…….

Tun daga kan Hajiya Mama har zuwa kan Yadira da suke yawan zuwa duk y’an gidan mamakinta suke yi dan ta ma fisu energy,Kwata Kwata ba ta jin nauyin cikin sannan babu alamun ciki ya d’auko tsufa a tartare da ita…….
Kwatsam yau suna zaune aka yi musu waya daga asibiti Kausar ta haihu ta haifi baby boy! Ba ma su san lokacin da ta fita ta tafi asibiti ba.

Ummi da Yasmeen ne kawai suka je asibitin…sai da Ummi ta firgita a lokacin da ta d’auki Yaron sakamokon tsananin kamannin da suke yi ita da Yaron hatta Yasmeen sai da ta lura da hakan dan haka kanta ya sake d’aurewa tamau da al’amarin Kausar da haihuwarta…

Basu dad’e da zuwa ba su Mommy suka k’araso dan haka suka yi mata sallama suka wuce gida kawai ko Yasmeen ma da Ummi ta yi tunanin zata d’an zauna bata zauna ba binta kawai itama ta yi.

Su kansu su Mommy sun yi mamakin tsananin kamannin Yaron da Ummi amma kawai sai suka bari a kan watak’il saboda tana yawan kallon ummin kullum ne,Mommy har da cewa”akwai wani d’an makwaftan su itama da ya tab’a yin kamanninta lokacin suna yawan shiga gidan!!”.
Daganan kuma suka hau murna aka fara zab’e zab’en suna aka zab’i ‘Alan’, ba kad’an ba sun ji matuk’ar dad’i da Yaron ya kasance Namiji dama tun tuni mommy take cewa ta yi scanning ita kuma tace bazata yi ba,gara kawai ta Haifa a gani.

Kausar ba ta b’oye musu abun da ta k’ullawa Manubiya ranar suna ba!
Su dai su Yasira basu ce komai ba,dan zuwa yanzu komai ya fita a kansu
Mommy ce ta bada goyon baya dama tana neman ta inda zata rage bak’in cikin Manubiya kafin a samu asirin ya kamata ta tafi forever…
Idan kuma ma ta mutu kafin ranar sunan to falillahilHamdu!!!

Daganan kuma suka shiga tattauna akan kud’in da zasu had’a bayan suna a samu Mommy ta ga likitan ido,dan suma zuwa yanzu al’amarin idon nata ya na tsorata su.

Bayan kwana d’aya aka kaiwa su Hajiya mama Yaron har gida ,Yash kuwa Ana ce masa za a kawo Yaron ya gani ya fita ya bar musu gidan sai dare tukunna ya dawo.Wanda hakan ya kusa haukata Kausar a lokacin da mai aikin nata ta dawo mata da Yaron take bata labari dan ita a tunanin ta Yaron ne zai sanya Yashjub ya zama close to her da ganan ta sameshi yadda take so……….

Itadai Yasmeen har gobe gaba d’aya mamakin lamarin haihuwar Kausar take yi ta lura kowa ma hakan take amma kawai ba a son yin maganar ne…kwata kwata jikin Kausar bai nuna alamun jego ba kuma duk girman Yaron ance bata samu tear ba sannan har zuwa ranar suna ruwan nono bai zowa Kausar ba hakanan akeya d’urawa Yaron madara.

Gagarumin suna aka had’a na gani na fad’a suka gaiyyace Manubiya…ita Manubiya da cewa ma ta yi bazata je ba shima Yashjub yace “ta huta kawai”
Saboda yau zasu je gida jibi arba’in d’in inna amma sai su Anty Umma sukace ta je kawai tunda sunan da yamma ne kuma ma har sun gama shirye shiryen sadakar da za a yi jibi…saboda idan bata je ba kowa mummunar fassaara zai yi mata tunda har sun gaiyyace ta to ta je kawai.
Dan haka ta tashi ta fara shiri.
Yash ya yi mata waya ya taho tanata sauri tana cikin shiri kiran Abbakar ya shigo wayarta a karo na ba adadi…..tun d’azu basu zauna ba shiyasa bata samu ta saka wayar tata a charji ba dan haka yana kira wayar ta katse ta mutu gaba d’aya!
Tabbas zai ga kamar kashewa ta yi kuma Abbakar bai yi deserving wulak’anci daga gareta ba ko ba komai yadda ya dinga d’awainiya da Inna da Baba bai kamata ta banzatar da al’amarin tasa mahaifiyar ba..har harbinsa aka yi a ranar da akayi case d’in black snake duk saboda ita da ahalinta…..tana cikin wannan tunanin Muhsin ya shigo cikin d’akin kamar ba zata yi ba sai
kuma kawai ta karb’a wayar hannunsa mai tochila ta saka sim d’inta a ciki ta kira asalin layin Abbakar….ga mamakinta yace mata dan Allah ta fito
da ma ya zo
ganinta ne yana neman alfarma a wajenta.”

So ta yi tace ya shigo amma ta san su Aisha ma sai sun yi mata magana muddin suka gansu tare shiyasa kawai ta fita tanata jero istighfari….A nan wajen ta samesa zaune a kan machine d’insa yana hangota ya mik’e ya nufota wanda hakan ya sanya jikinta sake d’aukar karkarwa….
Gaisawa kawai suka yi daga haka ta fito masa k’iri k’iri
tace “dan Allah ya daina yawan kiranta Mijinta baya son mu’amalarsu ya yi hak’uri kar ya janyo mata matsala….
Sosai ya nuna mata ya fahimta yace”ta yi hak’uri dama godiyar kud’in da ta tura masa ya zo yi mata sannan ta k’ara hak’uri da shi amma kud’in basu kai ba..aiki za a yi mata a zuciya yanzu haka dai cikin kud’ad’en da yake ta tarawa saura dubu d’ari biyu…..”
Chapter 134 · 0% Book details