← Book details Munnubiya Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 15 OF 137

Sashe 15

Munnubiya Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Ahaka Sofia ta yi ta gama ta ce musu sai zuwa anjima da magrib za ta sake dawowa daga nan ta yi musu sallama ta tafi ita
kanta tana mai mamakin improvement d’in Innar.

Da Mama da Siyama sai Aisha
su hud’u ne har Jidda suka zauna har rana lokacin da aka kawo kud’in auren Manubiya daga b’angaren Yashjub.

Maama ta yi matuk’ar mamaki da ta ji sati biyu kacal aka saka
haka ma Aisha da siyama,haka su ma Baba Habu da kaka Mallan wanda da da farko ya cewa Baba ‘’Ba zai je ba ai an ja musu layi a tsakaninsu’’amma tunda ya lek’a ya ga zunduma zunduman motoci a bakin masallaci hankalinsa ya tashi
haka nan ya je harda zagin Baba Habu akan ya ce’’shi fa ba zai je ba’’,haka nan ya azalzalo Baba Habun yace’’ai shine Babba ya yi hak’uri ya turawa Baba aniyar sa ya je ko dan zumunci’’da fad’a da lallashi ya jijjib’oshi suka nufi masallaci yanata sauri
dan karsu makara,ai kuwa jama’ar wajen sun ga ikon Allah a wajen Kaka Mallan.

Daddy da K’anninsa(Abhi) wanda ya iso daga uk jiya around 3:00am
sai Yassir da wani babban Abokin Daddy ne suka zo suka kawo kud’in(naira miliyan biyu)
aka saka rana nan da sati biyu inshaaAllah…kaff cikinsu babu wanda Kaka Mallan bai bi ya karb’i numbersa ba,duk kalar disgin da Yassir ya yi masa da b’ata ran da yake ta yi sai da ya hak’ura ya kula sa ya bashi wrong number,ya tsani tsohon ya tsani layin gaba d’aya
shi tunda yake a rayuwarsa
bai tab’a tunanin akwai
tsukukun layi irin wannan ba karakakaf layin gida uku ne manya sai masallacin da yake da kyau shima amma gaba d’aya ragowar gidajen kamar kango a ransa yace’’me Yashjub ya gani da ya zo nan??’’yayi wa kansa tambayar ba tare da yasan wa zai ba shi amsa ba Kafin ya d’an tab’e baki a ransa yace ‘’anyways shi ya sani atleast zai k’ask’anta kafin ya mutu dama nan ne ya fi dacewa da shi shiyasa ya zo nan d’in ya d’and’an k’ask’anci daganan ya mutu’’
Ko gama tattaunawa ba a yi ba
Yassir ya mik’e ya fita daga masallacin
Kallonshi kawai Daddy da Abokinsa suka yi kafin suka d’auke kai aka ci gaba da tattunawa.

Dakyar Baba ya yarda da buk’atar da Daddy ya zo da ita ta inda yake cewa’’Dan Allah kar su zo da komai Yarinyar kawai ake so
basa buk’atar kayan d’aki’’

Daganan suka tsayar nan da kwana goma za a d’aura aure inshaaAllah bayan Baba ya nemi a d’aura a nan masallacin sun amince.

Su Yaa Musbah ne suka tartare
Pepper chicken da su cake da doughnuts da lemukan da ya Nafi’u ya kashe uban kud’i ya yi order dan a cewarshi bai kamata a ji kunya ta ko wanne b’angare ba,ya san ba za su yi
abunda ya kamata su yiwa mutane masu uban arzik’i kamar su Daddy ba amma atleast ya kamata su kamanta

Har mota suka kai musu suka jibge Daddy ya na ta faman saka musu albarka da shi da Abokin shi daga nan suka yi musu sallama suka shiga motocin su suka wuce suka bar su Baba suna mamamakin Yassir!ko da ya shigo fa sune
suka gaida shi,tunda ya zauna a cikin masallacin bai ce komai ba hakanan ya had’e fuska yana kallon mutane akan hanci,ko irin murmushin nan bai yi ba lokacin da Daddy ya gabatar da shi a matsayin d’an uwan Yashjub wanda yake bi masa
daga k’arshe ma tashi ya yi ya fice gaba d’aya yanzun ma da suke yi masa sallama bai ko kalli in da suke ba ballanta su sa ran zai amsa har hannu kaka Mallan ya mik’a mishi amman ya wuce da sauri ya shige motarshi…..addu’arsu d’aya itace’’Allah dai ya sa ragowar y’an uwan Yashjub ba haka suke ba’’dan yanayin Yassir da yadda sam Daddy ya kasa tsawatar mishi ko da da ido ne ya ba su mamaki ya tab’asu matuk’a.Daddy dai ba shi da matsala amma sun lura hatta k’aninsa bai yi wani farin ciki da wannan hadi’in ba,
Gudun kar ma su kawo wani tunanin su je su janyo abu da bakinsu ne ya sanya gaba d’ayansu su ukun sukayi shiru ba wanda ya kawo zancen rashin da’ar Yassir,kowa kawai ya rik’e abun a cikin ranshi kawai.

Su biyu suka tartare
masallacin suka kunna turare
daganan ya Nafi’u ya d’auki jakar kud’in dama shi su Baba suka cewa ya k’arba tun lokacin da Abokin Daddy ya mik’o.

Da sauri kaka Mallan yace ‘’yanzu menene abun yi?’’bai jira an bashi amsa ba ya d’aura da cewa’’ku kawo kud’in akwai
wani Abokina da d’ansa yake kayan d’aki na gani na fad’a kunga sai a basa ya had’a mata komai mu samu mu fita kunya itama yarinya ta fi k’arfin gori kar ku biyewa Mahifinsa dan ya ce kar a kawo komai ya zama dole mu yi mata ko dan mu fita kunya.’’

Da mamaki Ya Nafi’u yake kallonsa daman tun d’azu ya k’ule da behaviorn da kaka Mallan d’in yake yi a gaban su Daddy gaba d’aya ya basu kunya sai wani zumud’i yake yi,shiyasa yana shirin ci gaba da magana yanzun Ya Nafi’u yace’’dakata Kaka Mallan
da kai da wa za ku fita kunya??’’bai jira jin amsar shi ba ya d’aura da cewa’’besides what are u even doing here?’’

Da sauri Baba Habu ya juya
ya fice gaba d’aya daga cikin masallacin

Cikin takaici ya Nafi’u yace
‘’Ba kai ka ce ba zaka zo ba jiya?ina har hantarar mu ka yi da muka je gaya maka?’’

Cikin fushi kaka Mallan yace
‘’Ka ci ubanka Nafi’u!ashe baka da hankali?banza d’an
karere kawai’’

Da sauri ya Musbah yace
‘’A’a kaka Mallan Nafi’u kam ba d’an karere bane a wannan lamari a ko wanne lamari ma na rayuwarmu Nafi’u ba d’an karere bane dan ya yi mana uwa da uba’’

Salati kaka Mallan ya rafka kafin yace ‘’Musa kana ji abunda suke yi min ba za ka
ce komai ba?’’
Sai kuma ya fashe da kuka daga nan kawai ya juya ya fita
yana cewa ‘’Dama amana nakeso in rik’e ammanm tunda bakwaso shikenan,kai musa ubanka yana chan kabari
amman na san an haska mishi wanna son datse zumuncin da kake k’ok’arin yi’’.

Numfashi Baba ya fesar ya girgiza kai yana msmakin yadda sam kaka mallan
ba shi da lissafi baya jin
shakkar ya ji kunya ko ya zubar da kanshi indai ta b’angaren abun duniya ne.

Kuma ya tabbata inda gari banza ne Nafi’u ya yi masa haka ya san da sai ya tara musu jama’a ya yi musu tijira amma dake yaga da akwai abu a wajen su shine ya kwantar da kai har da kuka,a hankali a fili yace’’Allah ya kyauta’’ yana aiyyanawa a ranshi inshaaAllah zuwa anjima zai je ya yi musu godiya da shi da Baba Habu,Allah ya sa su k’are lafiya.

Suna zuwa suka mik’awa Manubiya kud’in ta…kasa karb’a ta yi dan tashi d’aya fargaba da kunya suka rufe ta daga k’arshe ma sai ta saka musu kuka

Murmushi kawai duk aka yi ana kallonsu ita da Jidda da Siyama da Muhsin da suka shiga taya ta kukan.

Ya’ar tattaunawa aka yi su ya Nafi’u suka ce Daddy yace kar azo da komai amma dukda haka tunda ga kud’i nan ta samu sai a siya mata gado mai kyau da tsada da shi,Shi kuma da Ya Musbah da Baba za su siya mata y’an kayan kitchen dangin su flask sannan za su yi y’ar walima.

Kowa yayi amannah da hakan banda Manubiya sam ta k’i yarda a yi hidima ko wani kayan daki,dan ko da su ya Nafi’u ma suka fita cewa
tayi’’kud’in a barshi kar a siya mata komai,za ta bawa Baba ya Nafi’u da Ya Musbah jari bayan auren da shi.
‘Dama ta shirya za ta gayawa Yashjub ba za ta zo da komai ba to kuma yanzu tunda iyayenshi sun buk’aci hakan to Alhamdulillah’’

Murmushi Mama ta yi kafin ta matso ta dafa kanta tana jin
tsananin k’aunar Manubiyan a ranta,za ta iya cewa bata tab’a had’uwa da yarinyar da ta shiga ranta lokaci d’aya ba
kamar Manubiya tanada hankali da hangen nesa,ahankali Mama ta sauk’e ajiyar zuciya bayan ta dafa kanta tukunna tace’’Ba za ayi
haka ba Manu,ba zai yiu mutanen nan su kawo har naira miliyan biyu sannan ga sadaki a gaba da zasu kawo
amma kice ba za’a kai ki da komai ba,ni sai naga rashin dacewar hakan’’ta fad’i hakan tana mai juyawa ta kalli Inna kafin tace ‘’ko ya ki ka ce??’’
Lumshe ido innar ta yi ta bud’e alamun eh sannan a hankali ta d’an yi murmushi,murmushi suma duk suka yi kafin Aisha tace ‘’Nima na bi bayan su inna
gaskiya Manubiya kamar yadda baban khairat yace ya kamata ko gado wanda za ki saka a d’akinki d’an waje mai kyau a samu a siya miki,ki je da shi,ba dan komai ba ko dan kema ki dinga gani kina jin dad’i sannan atleast muma zamu ji dad’i bamu kai ki haka ba komai ba kuma ke kanki kin wuce gori,dukda dai na san a yadda suke da kud’in nan ba lalle su yi k’arancin tunani irin na k’ananun mutane ba
amman fa y’an uwanshi mata fa su shida yace miki ko?kinga kuwa ai mata ba‘a rabamu da k’ananun maganganu ba,dan haka gara kawai ki bari ayi miki wani abun su Baba Allah zai duba su suma’’.

Dasauri Siyama tace ‘’Nasan ma zai bawa ya Musbah aiki shi mijin naki inshaaAllah’’

Murmushi Aisha tayi kafin tace
‘’Ban d’au wannan akai ba
amman dai in ya bayar Alhamdulillah’’

Ba yadda Manubiya ta iya haka nan ta yarda ba dan ta so ba amma dukda haka sai da aka ware duba d’ari d’ari
akan zata bawa ya Musbah d’ari ya Nafi’u d’ari Baba d’ari
sannan ta ware kud’in saka Muhsin a makaranta,ba dan
Mama da Aisha sunso ba haka suka yarda suka yi respecting decision d’inta.
Chapter 15 · 0% Book details