← Book details Munnubiya Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 38 OF 137

Sashe 38

Munnubiya Part 2 Complete Hausa Novel · about 7 min read

Mik’ar da ita Iya ramma ta yi suka nufi Baba larai,suna
wucewa Inna ta yi sauri ta fice
daga parlourn.Tana fita ta saki
hawayen da take ta k’ok’arin rik’ewa….
Hatta Yadira sai da Manubiya ta je ta durk’usa a gabanta.

Tukunna Yassira tace “Alhamdulillah,muna iya wucewa da Amarya yanzu tunda ta nuna zatayi biyayya.
Once again,sorry fa!idan na b’atawa wasunku rai,Al’ada ce ta zo da hakan.”
Daga haka ta mik’e ta kalli Ummi tace “za ku iya fitowa da ita,ni na gama nawa.”
Tana gama fad’in haka ta d’auke d’ankwalinta da ta shimfid’a ta zauna a kai ta yi gaba,a take Yasmeen da Baba larai suka mik’e suma suka bi bayanta.Suna fita su Yadira ma suka fice.
Za’a fara maganganu da gulmace gulmace
Iya ramma ta yi sauri ta mik’ar da Manubiya ta nufi k’ofa da ita,ganin haka yasa Umman su Siyama ma ta mik’e haka ma
su Yahanasu.

Su Maman Baraka sun shiga
wajen Amaryar uncle basanan akayi show d’in,labari kuma yana zuwa musu da suka fito lokacin suka tarrar har an fito da Manubiya,sun so sun tarar sun ganewa idanunsu…..sallama suka yiwa Amaryar uncle suka bi bayan y’an kai Amarya,kar a yi babu su.

Babu yadda Manubiya bata yi ba amman haka tanaji tana gani suka hanata shiga wurin Inna wadda tun d’azu ta lura ta fita daga parlourn,ba tare da sun barta ta shiga d’akin nasu ba aka yi waje da ita aka saka ta a mota tanata kuka kamar ranta zai fita,Mata kuma sunata rangad’a gud’a!.

Yahanasu tana fitowa daga gidan su Manubiya ta d’au waya ta kira Yashjub….duk abunda su Yassira suka yi saida ta kwashe kaff ta gaya masa komai har abubuwan da suka faffad’a akan gadon Manubiyan d’azu da rana sai da ta fad’a masa.
Ran Yashjub idan yayi dubu tou yau ya b’aci shiyasa ko gama sauraronta ma bai iya yi ba ya kashe ya kira Yasira ransa a masifar b’ace yace mata”kar ta kuskura ko da wasa ta k’arasa masa gida!tunda mahaukaciya ce ita to ta kad’a kan ragowar mahaukatan su wuce gida in suka kuskura suka je masa gida wallahi sai ya ba su mamaki,Iyakar b’arnar da suka yi masa ya Isa haka kuma hakan ma su jira zuwansa gobe zai samesu they will answer to him…”

Tabbas yau mai rabata da Yahanasu sai Allah dan tashi d’aya ta san itace ta gaya ma Yash! Abunda basa so kenan
gashi kuwa tun yanzu ya fara korarsu yana cewa ‘kar aje masa gida’.

Sun kusan Isa gidan lokacin da ya kirata,haka nan tana ji tana gani ta kira Yasmeen da Ya’isha ta zaiyyane musu tace”su juya akalar motocin su su nufi gida,Ida suka isa gidan sai a tattauna,sai da suka yiwa Ya’isha da gaske tukunna ta yarda ta yi reserve dan da cewa ta yi wallahi sai ta je,haka dai ta hak’ura ta nufi gida tana jin kamar ta kama da wuta dan bala’i…..

Guiwa a mugun sace sannan zucyoyinsu fal takaici da bak’in ciki suka k’arasa gida Yasira tana ji tana gani next step d’insu ya tafi a banza dan akwai abunda ta kuma shiryawa za su yi a gidan Amaryar……

Maman Siyama da Iya ramma ne a gefe da gefen Manubiya,sai Maman
Aisha a gaba.
Kukan da takeyi sai da ta bawa kowa tausayi,Yassir kam wanda shine ya d’auki amaryar ba k’aramin mamakinta yake yi ba,dan shi bai yi tunanin Amare suna kuka har haka ba besides ita da za ayi mata gata!ita da za a
d’auketa daga wannan garbage d’in a kaita aljannar duniya ga kuma mijinta miji kmr Yashjub ta samu amma
shine take wannan kukan!…..shiyasa gaba d’aya mamakinta ya rufe sa ya shiga
tunani da kuma san ya nemo
ko dai akwai wani dalilin da ya sanyata kuka….
“Mu je”
Muryar Iya ramma ta katse masa tunani. Jin jina kai kawai ya yi daga haka ya kunna motar ya danna double signal,ragowar na gabansa da bayansa suna ganin haka suma suka tashi motocinsu da suka cika taff da jama’a suka sanya double signal suka fara k’ok’arin barin layin…..

Komawa ciki Siyama ta yi domin taje ta taho da su Jidda dan ta lura ba su fito ba.
Sir Najeeb sam bai yadda ya bud’e motarsa a kowa ba,ba ya so Siyama ta hango sa ta k’i shiga kuma ba ya so a cika motar dan bai shirya d’aukar kowa ba sai su d’in,shiyasa ya ji dad’i sosai da ya ga har an fara tafiya su basu riga sun tafi ba.Dan haka ya gyara motar tasa a dai dai k’ofar gidan.
Babu irin neman da Ya’isha ba ta yi masa ba….shi kam ya ganta sarai amma ya manna mata!dan tana d’aya daga cikin reasons d’in da ya d’auko mota mai tint kuma da ya zo d’in ya sake jin takaicinta dan tun daga farkon zuwan su har kawo yanzu da aka fito duk yana kallonsu,ba k’aramin haushi ta sake basa ba da yaga kalar shigarta!kayan jikinta da kuma yadda ta rufa mayafinta a iyaka kai
gaba d’aya jikinta a bud’e gashi ta yiwa lace mai mugun tsada d’inkin fitted gown matsattse har da tsaga a baya,a rayuwarsa ko bai san mace ba sam ba ya so ya ga ta yi irin wannan shigar.

Yana wannan tunanin yaga su Siyama sun fito ita da Jidda har da Munirat. Tsayawa kawai ya yi yana kallon yanayin shigar ta simple and cute so breathtaking!.
Yana kallonsu suka bud’e har motoci biyu amma babu guri.
Haka kawai dama Siyama ta ji motar datake fake a k’ofar gidan bata burgeta ba,ganin ana shirin wucewa a barsu
yasa taja hannun Jidda suka nufi motar,sai a lokacin ya sauk’e ajiyar zuciya.Bai ji dad’i ba da Munirat ta bud’e gaba ta shiga,ya so Siyaman ce ta zauna a gaba…tana shiga tace “laa!Ya Najeeb Ina wuni.”

“Alhamdulillah”kawai yace a hankali ba tare da ya kalleta ba dan baya so Siyama da take shigowa yanzun ta fahimci shi d’in ne.
Tana shiga ta rufe ta juya ta kalli Jidda tace “Da ikon Allah motar kuma empty ma”
Yana jin ta rufe k’ofar ya sa lock ya kunna motar dai dai itama ta fahimci ashe shi d’in ne dan gefen fuskarshi kawai ta kalla ta gane shi.Da sauri ya kunna motar ya bi bayan convoy d’in.
Yana ganin ta tana ta k’ok’arin bud’e k’ofar amman ta kasa,dariya ta basa dan yadda ya ga ta had’e rai ba kad’an ba ta burgesa,abunda ya kasa fahimta guda d’aya shine idan ta samu ta bud’e k’ofar motar shin fita za ta yi kenan a haka yana cikin tafiyar ko yaya?…..Murmushi ne ya sub’uce masa wanda duk saida suka ji,daga nan ba wanda ya yi magana haka suka d’au hanya motar shiruu
a haka har suka k’arasa gidan amarya Manubiya,dan already Yassira ta sa Yassir ya gayawa ragowar ba sai an je gidan Mommy an gaida ita ba direct kawai a wuce gidan amarya.
….
Ko da su Yasira suka fito daga motocinsu babu wadda ta iya cewa k’ala har Baba larai,hakanan suka nufi cikin gidan kowa da abunda take sak’awa a cikin ranta…..ba k’aramin dad’i suka ji ba da suka hango Daddy zaune a main parlourn k’asa yana kallo,tashi d’aya Ya’isha ta k’ak’alo hawaye ta k’arfi da yaji,ganin haka ya sa su Yusra yin kalar tausayi suma,yanayin su kawai Daddy ya kalla ya fahimci akwai matsala shiyasa ya kafe su da idanuwa har suka k’araso suka shiga gaishe sa,bai amsa gaisuwar ba sai tambayarsu da ya shiga yi akan “mai ya far?”.
nan kuwa suka zauna suka shirya masa k’arya da gaskiya…
A haka Mommy ta sauk’o ta samesu,ba k’aramin dad’i taji ba da ganin yadda Daddyn ya fusata matuk’a….ya na jin jina maganar tana kuma yi masa zafi…ta ya ana bikinka zakace ‘k’annenka kar su kai Amarya’har wani ‘kar suje masa gida’!.Tabbas da sake
dan ba zai yiu ba,dole ya san abunyi!,bai aurowa d’an sa wadda zata raba masa kan ya’ya ba ba wallahi…!

Hatta Baba larai zagewa ta yi suka yi ta shirya labarai ba kunya ba tsoron Allah dan ta san Daddy ba zai yi titsiye yace zai bi diddigi ba shiyasa suka shirga k’arya kala kala
kuma duk a bayanin nasu suna yi ne akan wai misunderstanding suka samu su da k’annen amarya shine Yashjub ya bi bayan k’annen matarsa har ta kai sa ga hanasu zuwa kai amaryar.

Sai da suka tabbatar Daddy ya hau ya zauna daram!tukunna
kowacce ta zame ta wuce
ciki.
Dukda bak’in cikin dake k’unshe a cikin zuk’atansu game da auran da Manubiya da Yashjub d’in kansa sai da suka ji kamar su taka rawa,dan a yadda suka ga yanayin mood d’in Daddy
sun san gobe akwai case!!!!

Direct d’akin Mommy Baba Larai ta wuce,a tsaye ta same ta kamar yadda ta yi zato…tana shigowa ta k’arasa inda take tace”Ya ake ciki”
Tiryan tiryan Baba larai ta zaiyyano mata yadda suka yi na k’akarin ganin sunyi ammman Yahanasu ta kafa ta tsare ta hana a yi komai….”

Dab’ass!!!
Haka Mommy ta zauna akan gado ta yi shiru kawai dan ta ma rasa me zata ce.
Chapter 38 · 0% Book details