Sashe 72
Munnubiya Part 2 Complete Hausa Novel · about 6 min read
Su Inna suna fita Yasira ta yi tsaki ta juya itama ta fita Daddy da Yassir ta fara kira suka yi magana tukunna ta kira wata k’awar ta wadda bata dad’e da yin aureba a nan estate d’in Yashjub d’in suke haya,dan haka ta kira ta ji ya abun yake sun samu sun fita safe ko?.
Ta ji matuk’ar mamakin yadda k’awar tata ta amsa wayar hankali kwance har da y’ar tsokana a ranta tace”to ko dai ta fita ba ta gidan ne dan haka a hankali a fili tace mata “kina ina?”
Sai da gaban Yasira ya yanke ya fad’i da ta ji k’awartata ta ce mata”Ina gida mana za ki zo ne?”
Zaro wayar ta yi ta kalla ta tabbatar da k’awar tata ta kira tukunna ta mayar kunnenta kanta tsaye tace’’ji na yi ance gobara fa ya tashi a estate d’innaku!yanzunnan aka kira Yash aka ce masa ga wuta yanata ci an gagara kashewa”
A rikice matar ta rafka salati kafin tace “to inaga gaskiya mak’iya ne, wani ne yake so ya yi luring nashi out a samu ya fita a kama shi ko dai wani Abu makamancin haka dan mu kam nan ko k’aurin wuta babu a nan gaskiya ki yi maza ki kirasa kice ya juya…..”
ai tun kafin ta rufe bakin ta Yasira ta yi maza ta kashe wayar a gigice ta shiga kiran Yashjub…ta jera masa miss calls sun fi takwas amma bai d’auka ba shiyasa hankalinta ya sake tashi dan zuwa yanzu tabbas ta gama gasgata maganar wannan k’awa tata,
tashi d’aya ta fashe da wani Irin kuka a ranta ta gama sakawa ‘shikenan an kashe Yashjub’……..
[17/09, 8:03 p.m.] Hauwajidda: MANNUBIYA
(Book 2)
Page 29
Na
Humayrah Bulama
Mikiya Writers Association.
..Ko kuma an yi kidnapping d’in sa!.
A rikice ta afka d’akin,suna nan a yadda ta bar su su uku Manubiya a gefe tana ta faman hawaye.
Cikin rikice Yasira ta k’arasa gaban Mommy tukunna tace
‘’Mommy Ina ga magauta ne suka kira Ya Yash!dan yanzunnan na kira frnd d’ita ta estate d’innasa,tace “babu wani gobara,shi kuma yanzu haka inata kiran sa a waya ba ya d’auka!inaga sun sace shi ko sun yi masa wani abun….’’
Ta k’arashe maganar tana mai sake fashe wa da wani irin kuka.
Manubiya kawai tsintar kanta ta yi a gaban Yasira a rikice tace
‘’Ki sake gwada kira InshaaAllah babu abunda ya same sa bara nima in kirasa idan bai d’auka ba mu yi message,na san in ya gani zai ki kiramu” ta fad’i hakan tana mai juyawa ta nufi wayarta.
Sai a sannan tukunna Mommy ta tashi ta tsaya a d’an rikice tace ‘’ikon Allah to Allah dai ya sa lafiya…babu komai ma ki kautata zato….”
Kafin minti sha biyar gaba d’aya hankalinsu ya sake tashi
dan babu kalar kira da sak’onnin da ba’a yi an tura masa ba amman sam ba ya d’aukar waya kuma bai yi responding messages d’in ba.
Banda kuka babu abunda Manubiya take yi tana kuka tana aikin kiran waya ba’a amsawa abun tausayi…
Suna a haka Daddy ma ya kira wayar Yasira yace “da shi da Yassir sunata kiran sa suma amma baya d’agawa but ga su yanzu suke barin gida za su je su duba estate d’in na sa..”
Yassira ce ta yanke shawarar ta sake kiran friend d’in tata inyaso ko mai gadin su ne ta sanya ya tayasu ya bincika ko Yashjub d’in ya k’arasa chan…gaba d’aya ta gigice haka ta shiga kiran k’awar tata.
Matar tana d’auka tace ‘’ya ake ciki Yasira?kun yi magana da shi?”
A tare da matar da Yasira suka fara jiyo hayaniya da ife ife…ta cikin background d’in Yasira take jiyo k’ara ta ban mamaki kamar ana fasa abubuwa da kuma na bindigu da ihun bayin Allah suna neman ceto….
A hankali jikinta yana wani irin karkarwa ta ji matar tace”Innalillahiwa innalaihirrajiun,Yasira kina jin abunda nake ji?bara in duba…”
Sai kuma a rikice taji tace”y’an bindiga ne suka shigo mana sun fi mutum d’ari…..”
K’arar harbin da Yasira ta ji ne ya tabbatar mata da k’awartata aka kashe dan a tare ta ji k’arar wani abu ya fashe kamar k’ofar aka fasa da kuma harbin….
K’amewa ta yi ta kasa cewa komai,tana sauraron yadda mutanen suke magana suna cewa”a sake duba gidan sosai idan babu kowa su yi sauri su kunnawa wannan ma wuta su tafi next house they don’t have much time…su yi su yi su tafi,yanzu Grenade ya yi masa waya yace su yi retrieving sun riga sun kashe gayen sun k’ona motarsa tun a bakin gate….“
K’afafuwan Yasira ne suka shiga kakarwa tashi d’aya ta gagara ci gaba da tsayuwa dan haka ta durk’ushe a wajen ta fashe da wani irin kuka.
Daidai nan Manubiya ta matsa kusa da ita kusan a tare ita da Ya’isha suka ce mata “m-m mai ya f fa rru!??’’
Suka yi mata tambayar a tsorace dan yanayin ta ya yi matuk’ar sake firgita su.
Da kyar ta iya d’agowa ta kalli Ya’isha ta yi mata bayanin abunda ta jiya faru sannan ta d’aura da cewa”na ji yana cewa gurnade ya ce sun kashe sa sun k’ona motarsa tun a gate,Ya’isha Ya Yash suke nufi shi ake so a kashe dama shiyasa aka yi k’arya da gobara aka ja sa wajen saboda su b’adda track d’insu kar a gane manufarsu.Ba y’an fashin gaske bane Ya Yash d’inmu aka shirya kashewa dama Wallahi…”
‘Sululululu’ haka Manubiya ta tafi ta fad’i a wajen sumammiya…
Mommy ce ta kira Daddy
a rikice ta ji muryarsa yana cewa“gasu nan sun zo shiga layin motocin sojoji suka taresu wai y’an fashi sun kaiwa estate d’in hari an hana su shiga sun ma rufe gate d’in layin gaba d’aya but gasu nan dai ana ta k’ok’arin shiga motocin sojoji biyu sun kutsa kai yanzunnan…”
Yadda su Yasira suka ji muryar Daddy yana yiwa Mommy bayani ta wayar yana kuka ne yasanya suma suka fashe da wani irin kuka.
Sun san Daddy ba lalle ya so su je wajen ba shiyasa ba su ce masa za su je d’in ba instead suna gama wayar da shi suma suka fice dan hankalinsu gaba d’aya ya yi wajen….a nan suka fice suka bar Manubiya a yashe a k’asa suka nufi estate d’in suna kuka gaba d’aya su ukun..
A Chan suka tarar da Daddy da Yassir suma duk hankali a tashe lokacin har an bud’e gate d’in layin wajen taff cike da sojoji da y’an kwana kwana dan kusan kaff gidajen sai da suka cinna musu wuta tukunna suka gudu ba a kama ko d’aya ba.! Yadda estate d’in ya k’one ya koma wani abu daban dole ya bawa mutum al’ajabi sannan ya sanya ka sake ka’daita Allah ka kuma tabbatar da cewa abun duniya da duniyar kanta ba a bakin komai suke ba.Su Yasira suna hango su Daddy suka k’arasa wajen su suna kuka shima Daddyn hawaye yake yi cikin sharar hawaye yace “akwai hope! ga dai motarsa chan a k’one da mutum a ciki amma gaskiya ba shi bane inaga kamar driver d’insa ne kuma shi har yanzu wayarsa tana shiga,amma wayar mutumin ciki ta k’one da na duba ba ta aiki.
Sannan munata dubawa har ciki amma kamar ma shi d’in bai zo nan ba kwata kwata.
Cikin jinjina kai Yasira ma tace “Nima Inada hope Daddy
dan yanzu ma na kirasa wayar tasa tana shiga,Allah dai ya sa ba wani abun ne ya same sa ba
dan gaskiya bai zo nan ba.”
Daddy ne ya kira asibiti
dama ga polisawa da sojoji a wajen dan haka ambulance suna zuwa aka fara fitar da deceased da injured abun ba dad’in gani dan mutane sunfi talatin waenda suka mutu
injured kuma wajen mutum goma……