← Book details Munnubiya Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 43 OF 137

Sashe 43

Munnubiya Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Gashi a gabanta tana kallonsa ga sanyin A c ga shauk’i ga kuma farin cikin an rabu da ita ta huta…sam ba ta san lokacin da barci ya kwasheta ba!ba ita ta tashi farkawa ba sai wajajen k’arfe 3 na dare lokacin da ta ji bak’on al’amari a tare da ita a ranta tace”kenan Yashjub wayo yayi mata sai da ya bari ta sakankance.
Shi kuwa Yash ba zai iya jurar ganin kukanta ba kuma tun d’azu a closet ya fahimci kukan zata yi masa muddin yayi yunk’urin yin wani abun.
Kamar kuwa ya san abun da ke ranta kenan.
…Tun tana magiya da lallashi har ta fara kuka hankalinta bai gama tashi ba sai da taji shima ya saka mata kukan yana lallashinta,ba abunda ya fi bata tsoro irin yadda ta ji yana yamutsa ta kamar ba ya haiyyacinsa kamar wani mahaukaci….da tafiya ta yi tafiya kuwa had’iyar zuciya kawai ya rage ba ta yi ba gashi a yadda ya koma mata ta san ko aljanace ita ba lalle ta iya kwatar kanta ba,bata tab’a sanin Yashjub mugu bane sai da ta ji yana shirin kasheta…duka cizo yakushi amman duk a banza sam bai ji ko d’aya ba dan a wannan gab’ar inda ace za’a saita masa bindiga to ko sunansa ba lalle ya kawowa ba!….
Tun Manubiya tana tunanin kalar jinyar da zata yi idan Allah ya bata ikon tashi har ta zo ta cire rai ta fara basa wasiyya had’e da shirme da surutai,shi kam ya san dai tana magana amman bai gane ko d’aya ba,yana so ya tausaya mata amman sam ya kasa.Sai da kyar da mugun kyar tukunna Manubiya ta samu ya sarara mata lokacin har an fara kiran sallah a masallaci…….

Shi kansa ya san yayi laifi amman kuma ba laifin sa bane
kasancewarta macen da tafi ko wacce mace a duniya ne
silar janyo mata wannan b’arna da aika aika da yayi…..sam bai yi zaton hakan ba dan tabbas komai ya wuce zatonsa an tashi kansa shiyasa ya gagara controlling kansa.
Ahankali yanajin yadda take numfashi da sheshshek’ar kuka da kyar ya samu ya janye daga gareta wanda sai da ta ji kamar ana zare mata rai ne,cike da kasala yana jin yadda kansa yake wani irin mahaukacin sarawa ya koma gefe ya kwanta cikin lumshe ido da sauk’e numfashi yace”Alhamdulillah”a fili.
Manubiya kuwa da ke kwance a gefensa ji tayi inama ace tanada k’arfi da lafiyar da za ta samu ta juyo ta rufesa da duka.
…..
Earlier
Tare motar Yahanasu da suke tare da Munirat suka shiga cikin mansion d’in da ta Yassir
lokacin twelve har ta d’an gota
Gidan shiruu baka jin komai sai k’arar mikano.
Ita Yahanasu sai yanzu ma ta tuna cewa makullin d’akinta yana hannun Yassira!tashi d’aya ta san za su yi case idan ta shiga dan itama yadda take jin zuciyarta a yanzu kam wallahi kaff cikinsu babu wanda zata ragawa.

Tana yin parking Yassir ma yana fitowa daga cikin tasa motar.
Tun da suka taho dama
Munirat ta riga ta gama deciding abunda za ta yi a cikin ranta dan haka ta juya ta kalli Yahanasu tace”Bara in karb’i sak’o na sai na shigo”.
Yahanasu ba ta kawo komai a ranta ba tace mata “to”
daga haka ta bud’e musu motar suka fito a tare ita ta nufi main door Munirat kuma ta bi bayan Yassir wanda ya nufi b’angaren sa….tana ganin Yahanasu ta shige ta k’ara sauri..
Sarai ya ga lokacin da ta biyosa amman ya yi banza da ita yayi wucewarsa kamar bai ganta ba,sai da ya zo shiga har ya zaro key ya ji tace
“Na san ka lura da ni”
Shiruu yayi kamr mai tunanin wani abun kafin ya zura key d’in ya bud’e k’ofar tukunna ya juyo yace “Munirat a gajiye nake sosai!Make it fast pls..wat do you want?”
Matsowa kusa da shi tayi
tace “har haka muka zama?
Make it fast?baka ma da lokacin saurarona?
Okay ba komai shikenan!”

Ta fad’i hakan tana k’ok’arin juyawa,rik’o hannunta ya yi ya janyota garesa har sai da fad’a jikinsa kafin ya tallafe k’ugunta da hannunsa d’aya yace”Ke fa kikayi pushing d’ina away,wallahi har gobe Ina sonki Ina k’aunarki
amman no matter what ba zan yi forcing d’inki into a relationship with me ba…..”

Gaba d’aya she’s uncomfortable dan tunda take wani Namiji bai tab’a yi mata irin wannan ruk’on ba idan ba shi d’in ba
amman
kuma so take su shirya,kar ta
turesa ko kuma ta hanashi rik’eta ya zama furious sannan ga maganganunsa
na ‘yana sonta’
Da suka k’ara narkar mata da zuciya shiyasa ta k’i motsi sam
tak’i cewa komai.

Hakan kuwa ba k’aramin dad’i ya yiwa Yassir ba dan haka ya sake hugging d’inta sosai yaci gaba da gaya mata k’arya da k’arairayi har da cewa”har zazzab’i da rashin lafiya yayi kwanaki duk a ta dalilint,idan ya ganta kamar zai mutu haka yake ji gashi ba ta kulasa shiyaaasa za ta ga kamar gudun ta yake yi!”..
sannan ya fito k’iri k’iri ya ce mata shi fa ba zai iya yin relationship d’in y’an k’auyen da take so su yi ba in dai har tana sonshi to ta sake da shi after all ai shi za ta aura at the end of the day so ta daina wahalar da kanta tana wahalar da shi,indai har ta yi trusting d’insa kuma shi takeson aura to a ganinsa ya kamata ta sake jiki da shi.!

Ko da ta yi masa maganar Kausar ma k’iri k’iri ba kunya ba tsoron Allah yace mata “shi ba komai tsakanin sa da Kausar ba sonta yake yi ba kawai dai sun shak’u ne tun yarinta”…..Sai da Yassir ya tabbata ya gama zurma ta ta kamu tukunna ya d’aura da cewa”I love you so so much,so very much only you Munirat”
Har cikin zuciya da jininta kuwa ta ji wannan kalmar tana yawo…… sai da ta lumshe ido ta sauk’e ajiyar zuciya tukunna tace”I love you too”ta fad’i hakan tana k’ok’arin zamewa jin yadda ya sake mannata a jikinsa,kallon fuskarta ya yi kamar bai fahimci son zamewa take yi ba yace “mun shirya ko?”
Jin jina masa kai ta yi tana murmushi,ahankali yace”bari in yi confirming to”bata ankara ba ta ji ya fara kissing lips d’inta.
Bata biye sa ba saboda shock
tsoro ga kuma bata saba ba.
Ya kai 1 minute tukunna ya rabu da ita yana mayar da numfashi ahankali yace”That’s more like it”
Ya fad’i hakan yana murmushi yana shafa kumatunta.

Ya lura da yadda jikinta ya d’au karkarwa tun d’azun har yanzu,sannan sam ta k’i magana taki ma ta yarda su yi
eye contact sam.
Ahankali yace
“Munirat,ko na b’ata miki rai ne?”Ya fad’i hakan yana lek’en fuskarta.
Dakyar ta iya cewa
“A ‘a”.
Murmushi yayi….he need rest kuma ya lura ba abunda za ta iya yi masa yanzu dan ya ga yadda ta shiga shock daga iya ka kiss
shiyasa cikin son sallamar ta yace
“Muje in raka ki,kema ki samu
ki huta ko?”
Ahankali tace
“Okay”
Gaba d’aya jikinta a sanyaye…..rik’e hannunta yayi daganan ya d’an janyo k’ofar entrance na side d’innasa
suka fara takawa yana d’an janta da hira amman ita daga ‘um’sai ‘um um’.

Sai da ya kaita kan kwanar da za ta sadata da main door d’insu tukunna ya d’ago hannunta yayi kissing yace mata”good nyt zan kiraki”
Ahankali ta d’anyi murmushi tace “Sweet dreams”
daga haka ya yi waving d’inta suka rabu.

Sai da ya b’acewa ganinta tukunna ta sauk’e wata nannauyar ajiyar zuciya….ta san yin hakan is wrong amman ba ta jin zata iya hak’ura da Yassir gaskiya!za ta biye masa
kuma inshaaAllah zata nuna masa rashin dacewar hakan along the way,ta san Yassir yana sonta dan haka idan ta sake d’ukar hankalinsa ta samu ya sake dulmiyawa a cikin kogin sonta to ta san za ta iya hana sa abubuwan da yake yi mata daga nan sai su yi tsaftataccen relationship d’insu su yi aurensu in ya so sai ta sallama masa komai ta kula da shi yadda ya kamata su samu happy ending.A ganinta hakan shine mafita
akan dai ace ta rabu da shi
bayan suna son juna,ba za ta iya zuba ido Tabbas kallonsa ba dan yadda ta ga ya fara nuna intrest akan Jidda ta san in ta bari aka tafi a haka shikenan sunanta sorry.Ba ta da mai bata shawara su Ummi tun kwanaki da ta ganta da Yassir sam suka daina sake mata ko hira Ummi da Yayarta sun daina yi da ita sun nace akan ta fito da miji,ba dan haka ba da ko yayarta ta tuntub’a da maganar amman ta san sam ba za ta fahimceta ba wani sabon case d’in ne ma zai taso,shiyasa ta yanke decision d’in ta da kanta,ta yi abunda ta ga shine dai dai.

Da wannan tunanin ta k’arasa bakin main door na mansion d’in ta danna,ganin a bud’e ne ma yasa ta tura zundumemiyar bullet proof door d’in ta shiga….
A tsattsaye ta samu kowa
Mommy da Kausar ne kawai babu sai Daddy amman har Ummi tana k’asan,amsa sallamar ta Ummi tayi kafin tace”Daga ina kike??”
Cikin tarrar numfashin Ummin tace”Waya na tsaya yi ne”

Kallonta Yahanasu tayi ta d’an yi shiru sai kuma tace “Mu je d’akinki,in kwana achan”.
Daga haka ta juya ta kalli Yassira tace “Ki dafa key d’in ki cinye dan Allah!”
Ta fad’i hakan tana k’ok’arin wuce ta.
Fincikota Yassirar ta yi ta dawo da ita gabanta ta tsayar tukunna tace”Inaga baki fahimceni ba Yahanasu!
bacci ne kwata kwata yau baki Isa yi a cikin gidan nan ba!
dan wallahi yadda kika shiga tsakanin mu da d’an uwan mu
ki ka d’aga mana hankali kema ba ki isa kin runtsa ba!.

Cikin fushi Ummi tace “baki da hankali ashe Yassira?”
Chapter 43 · 0% Book details