← Book details Munnubiya Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 9 OF 137

Sashe 9

Munnubiya Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Sai da suka tabbatar su innar basa buk’atar komai tukunna suka yi musu sallama suka fice
suna fita kuwa Baba ya matsa kusa da inna dan dama akwai maganar da yake so ya d’an tattauna da ita akan auren manubiya kafin su ya Nafi’u su k’araso suma su tafi….

Da kyar Manubiya ta lallashi kanta ta hana kanta kuka a cikin adaidaita sahu,a ranta ta shiga aiyyanawa’’kullum shi yake kiranta, da ta ga bai kira ta ba jiya kamata ya yi ace ita ta nemesa,Allah dai yasa bai karyeba Allah yasa bai ji wani mummunan rauni ba
Allah yasa babu abunda ya samu Yashjub…’’
In kuma ta tuno ance driver d’in shi har ya mutu sai ta ji
gaba daya hankalinta ya sake tashi.

Tsararren private hospital ne mai kyau sosai da had’uwa,sai da suka fad’i sunan sa da number d’akin da yake a ciki
a reception d’in tukunna aka raka su har bakin k’ofar d’akin.

Suna tsayawa a bakin k’ofar d’akin su Jidda suka tuna ba su siyo kayan dubiyar ba dan haka suka juya da sauri ba tare da sun cewa kowa komai ba saboda a yadda Ya Musbah yake a fusace kwana biyun nan sun san in suka ce ‘sun manta!’ sam ba zai yi la’akari da ‘har da shi aka yi mantuwar ba’
zai rufe ido ne ya ci k’aniyar su.

Suna juyawa ya lura dan haka ya juya shima ya bi su da sauri bayan ya cewa Manubiya’’ta shiga suna zuwa’’.Muhsin ma bin bayan Ya Musbah ya yi dan a yadda ya ga duk sun fita da sauri ya d’auka wani abun ne…
[17/09, 8:03 p.m.] Hauwajidda: MANNUBIYA
(Book 2)
Page 05
Na
Humayrah Bulama

Mikiya Writers Association.

Yana bud’ewa suka yi ido biyu da Yasmeen ahankali ya lumshe idanunsa ya bud’e kafin yace’’i wasn’t expecting you!’’

babu Mommy da Daddy a wajen ballantana ta yi rashin kunya shiyasa ta yi shiruu ta d’an sunkuyar da kanta k’asa,kafin ta d’an d’ago ta kallesa tukunna tace’’Yau ne ranar da na ke shigowa aiki nan asibitin,shine na ce bari in lek’o in duba ka’’

‘’Nagode’’
kawai yace da ita daga haka ya fara k’ok’arin maida k’ofar.

Manubiya tana jin muryar Yasmeen zuciyarta ta fara wani irin tuk’uk’i….yanayin conversation d’in su ba kad’an ba ya d’aure mata kai gashi ta ji yarinyar sai wani kashe murya takeyi tana wani lallab’asa……

Da sauri Yasmeen ta sa hannu
ta d’an tare k’ofar kafin tace
‘’Those are for you’’
Ta fad’i hakan tana mai nuna masa allurar hannun ta.

This time around b’ata rai Yashjub ya yi cikin d’an
fushi yace ‘’i’m fine,na warke. And if necessary
go get the doctor’’
A ranshi yace ‘’lalle ma yaran nan rainin hankalin nasu ya yi yawa,su gama basa raini da attitude a gaban mutane shine yanzu dan ta maida shi d’an cikin ta za ta zo kuma ko bada hak’urin rashin kunyar da ta yi masa bata ma da shirin yi.Kamar ma bata yi komai bama’’

Ta ji zafi sosai amman sai ta
dake ta d’an yi murmushi
kafin a hankali tace’’nima ai Doctor ce,kuma shi ya shiga surgery,just let me in i…..’’

Cikin fushi sosai yace
‘’Ke!ina miki wasa??’’
Bai jira jin amsar ta ba yace ‘’b’ace min a gani,kafin in karya ki a wajen nan’’.

Dai dai nan Jidda da Siyama suka k’araso wajen dan ba su
samu lemo da ayaban a kusa ba shine Ya Musbah ya karb’a suka tafi nema shi da Muhsin bayan ya balbalesu a titi kamar zai rufesu da duka.

Ahankali Yasmeen ta d’an sunkuyar da kanta ta fara k’ok’arin maida kwallar takaicin da take shirin yin nasarar zubo mata.

Sai da Jidda ta d’an rissinar da kanta
tukunna ta ce’’Ya Yash,Ina wuni’’
Haka ma Siyama

Jinjina kai ya yi kafin a hankali yace ‘’Alhamdulillah’’

Daganan ya juya ya shige bayan ya bar musu k’ofar a bud’e.
Kamar ba za su kula Yasmeen ba sai kuma jidda tace mata
‘’Sannu Ina wuni’’tunda koda dai ace likitarsa ce(dan sun ganta sanye da lap coat)
but tare suka gansu suna magana.

Dakyar ta iya d’agowa ta kallesu….kyawawan mata ajin farko masu ji da asalin kyau da k’uruciya gashi sai wani kalar k’amshi sukeyi su duka biyun
sai dai tashi d’aya yanayin kayan jikin su zai sanya ka fahimci suna cikin yanayi na rayuwa,sanye suke da dogayen rigunan Abaya bak’ak’e amma
tsabar yadda kayan sukaji ruwa har bak’in ya d’an fara komawa kamar kalar dark ash
sannan rabin stones d’in jiki duk sun goge,tashi d’aya ta ji gabanta ya yanke ya fad’i,kallon
da taga suma sunayi mata ne
yasanya kawai dakyar tace’’fine’’a cikin zuciyar ta tana tunanin’’to wacece budurwar Yash d’in a cikinsu’’
Sai da suka tura k’ofar suka
shige tukunna ta samu damar yin ido biyu da Manubiya
wadda itanma Allah Allah dama takeyi a d’an bud’a k’ofar ta samu ta ga wacece take magana da Yash d’inta haka yake disga ta.
A bud’e su Jidda suka bar k’ofar dan a tunanin su shigowa za ta yi

Har manubiya ta d’auke idanunta daga kanta amma
ita Yasmeen din ta kasa,kallonta kawai take yi tana sakewa….sanye take da dark army green din jilbab har k’asa,yanayin yadda ta yi parking gashinta ta d’aure igiyoyin jilbab d’in ba k’aramin kyau ya k’ara mata ba….…’’Hi Yasmeen’’d’in da sir Najeeb yace mata ne ya dawo da ita daga duniyar k’arewa Manubiya kallo,da sauri ta kawar da kanta ta mayar gareshi kafin dakyar ta samu ta d’an k’ak’alo murmushi tace’’Najeeb,
Ina wuni!’’
Ta fad’i hakan tana d’an murmushi.
D’an lek’awa ya yi,ya hango Yash suna gaisawa da su Jidda bai ga fuskokinsu ba
dan sun bashi baya ne iyakar
gefen fuskar Manubiya ya samu ya gani.

Juyowa ya yi ya kalleta kafin yace ‘’ya na ganki a bakin k’ofa?’’ya yi mata tambayar yana tsare ta da idanuwa

Ajiyar zuciya ta sauk’e kafin tace ‘’ko da na zo ma na kusan 20 minutes tukunna da kyar aka bud’e min,ashe madam ce a ciki shiyasa,Itace yayar tamu ko?’’ta yi mishi tambayar tana kallon Manu.
Direction d’in da yaga tana kallo ya kalla tukunna ya d’anyi murmushi ya juya ya kalli Yasmeen d’in sannan yace’’Yeah itace!ba ku gaisa ba ne?mu je cikin mana..’’

Girgiza kai kawai ta yi kafin tace ‘’Yace ma in ban bar nan ba sai ya karya ni,ma gaisa wata rana bara in wuce’’

Ta fad’i hakan tana d’an yin gaba sai kuma ta juyo tace ‘’am d’azu na ga miss calls d’inka sorry ina driving ne shine na saka wayar a silent’’

Ajiyar xuciya ya sauk’e kafin yace‘’it’s about Ya’isha!kin dai san halinta.Anyways na ga kamar kina sauri ki je kawai za mu yi magana anjima’’

‘’Ok’’kawai tace kafin ta juya ta yi gaba….

Shiruu Najeeb ya yi yad’an bita da kallo har ta b’ace ma ganinsa a ransa yana tunanin menene yake damun Yash haka ne,shi shi kad’ai iyayenshi suka haifa he always wish inama ace yanada siblings
shiyasa har gobe yake mamakin Yash ya rasa dalilin da yasa baya appreciating gift d’in da Ubangiji ya basa.

Girgiza kai kawai ya yi kafin ya shige cikin d’akin bakinshi d’auke da sallama,ahankali
duk suka amsa kafin Manubiya ta d’ago cikin girmamawa ta gaidashi

Murmushi yayi yace ‘’Lafiya ya
gida ya mai jiki?’’

‘’Alhamdulillah’’ta ce
daganan ta sunkuyar da kanta

Kusa da Yash ya d’an matsa tukunna yace masa’’Ya jiki?’’

Kamar ba zai amsa shi ba sai kuma yace ‘’Alhamdulillah,ai
na d’auka ba za ka shigo ba’’

Murmushi Najeeb d’in ya yi
kawai ya girgiza kai kafin ya mayar da idanunsa a kan su Jidda da suka ce masa ‘’ina kwana’’a tare,sai da numfashinsa ya yi sama
sakamakon ido biyu da sukayi shi da Siyama.Dakyar ya samu ya iya ce musu ‘’lafiya Alhamdulillah’’
sannan ya yi sauri ya d’auke idanunsa daga kan Siyama wadda ita bama ta san yana yi ba dan suna had’a ido ta sunkuyar da kanta.

Manubiya ya kalla kafin yace’’ya na ganku duk a tsaye?ku zauna mana
Itan ma sistern ki ce?’’

Ta san sun had’u da Jidda ranar a asibiti shiyasa ta fahimci Siyama yake nufi dan haka tace’’Eh,k’anwata ce,cousin
sister’’

Ahankali yace’’MashaaAllah’’
Sai kuna ya sake cewa’’ku zauna mana’’

‘’Tam’’
Jidda tace
daganan suka juya suka nufi sofa ita da Siyama suka zauna

Shi kuma ya zauna a gefen Yash kan gadon.
Manubiya ya sake kalla yace
‘’Amaryar mu ba za ki zauna ba ke??’’
Da sauri Yashjub ya juya ya na mishi wani irin kallo
Dariya Najeeb yayi kafin yace
‘’Sorry!’’sai kuma ya kalli Manu yace ‘’Amaryar Yashjub shi kad’ai!ki taimaka ki zauna’’

Ahankal ta juya da niyyar zuwa inda su Jidda suke amman sai
ya sa k’afa daidai inda za ta bi ta wuce,dukda k’afar ba ta wani kafeta sosai ba amma ta fahimci sarai abunda yake nufi
zuwa yanzu ta riga ta san halin Yash ta san ba k’aramin abu bane a wajensa yanzunnan sai ya ja mata ta ji kunya a gaban su Jidda muddin ta k’i yin abunda yake so
shiyasa kawai sai ta nemi waje ta zauna a kujerar mai jinya
tana mamakin sa a d’ayan b’angare na zuciyarta kuma
tana mamakin Sir Najeeb
mutumin da da ko kallon kirki baya yi mata daga frowning face sai ciccin magani
amman yanzu wai shine haka kamar zai goyata.

D’an zungurin Yash sir Najeeb d’in yayi ganin yadda yake kallon Manu
K’asa k’asa yace masa’’kar ka
cinye ta da ido mana..’’

Dariya Yash d’in yayi shima k’asa k’asa kafin kawai ya d’auke kansa daga kan Manubiya ya maida kan Najeeb yace’’wanne munafurcin Yasmeen ta shirga maka d’azu’’
Chapter 9 · 0% Book details