← Book details Munnubiya Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 25 OF 137

Sashe 25

Munnubiya Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Kamar yadda ta fita ta bar su Jidda a zaune haka ta shigo ta same su,sallama kawai ta yi suka amsa daga haka ta nemi guri ta zauna,suna ganin idanunta suka fahimci kuka ta yi,sun san idan suka fara bata hak’uri sake b’arkewa za ta yi da wani kukan shiyasa suka ja bakunan su suka yi shiru amma dukda haka ba su tsira ba dan kamar wadda aka daka hakanan ta fashe musu da kuka tashi d’aya. Hakan ya yi dai dai da shigowar su Aisha da anty umma da Mama da inna cikin d’akin,ahankali Aisha ta zauna a kusa da ita ta kamo hannunta tukunna tace”haba mana Manu kanki fa zai yi ciwo ki yi hak’uri haka nan mana,ke ki godewa Allah ma a garin za ‘a ajjiyeki waenda ake d’aukar su a kaisu wani garin daban su kuma su ce me??”

Cikin karb’ar zancen anty umma tace”wasu ma k’asar gaba d’aya ake bari da su kuma haka suke zuwa su zauna su rayu,ke kam gidanki ko da k’afa idan mutum ya zage tsaf zai je,ki yi hak’uri ki yi shiru karki ja wa kanki zazzab’i dama indai sunan ki mace to wannan rana tana jiranki……mu kanmu sai hankalinmu ya fi kwanciya idan muka kai ki d’akinki gobe inshaaAllah fatanmu shine ki yi biyayya ki nuna cewa mun baki tarbiyya mai kyau.”

Kamar zuga Manubiya sukeyi haka ta sake fashewa da kuka shiyasa suka hak’ura suka kyaleta anty umma suka fita ita da inna dan su ci gaba da shirye shiryen gobe Mama kuma Ammi ta kirata tace ta zo ta taya ta girki tana da bak’on cikin dare.

Suna fita d’akin ya rage daga Manubiya sai Aisha
Siyama da Jidda,sai da Aisha ta lallab’a Manu ta yi shiru da kyar tukunnan ta bud’e mata abunda ta shigo mata da shi
a flask ta bata tace “ta ci.”

Har ga Allah kayan nan sun fara Isar Manu dan wani irin ciwon mara take yi amma ta san ba ta Isa ta cewa Aishar A’a ba shiyasa ta hak’ura da kyar ta danna tana ji kamar za ta yi amai marar ta kamarza ta fashe.

Ahankali ahanakali Aisha ta samu ta d’an kwantar mata da hankali tukunna Manubiya ta d’an sake…..ana fara kiraye kirayen sallar magrib kiran wayar Yash ya shigo wayarta,ta yi mamakin ganin kiransa a daidai lokacin sallah amma sai ta d’auka cikin sanyin murya ta gaidashi,
Sai da ya sauk’e ajiyar zuciya tukunna yace”lafiya
Alhamdulillah”
Kafin ya d’aura da cewa”yau na shiga busy ban samu na dame ki da kira ba,”

Murmushi kawai ya ji ta yi a hankali

Shiruu ya yi kamar mai nazartar wani abun kafin yace”wa ya saka min ke kuka??.
Fad’a aka ta yi miki ko?”

Ahankali ta sake yin murmushi kawai. Numfashi ya sauk’e kafin yace”Aikuwa yanzun za’a sake yi mana wani,dan na san nasiha Baba zai yi mana,ya kirani akan yana buk’atar ganin mu a tare,Ina ma unguwar yace bayan magrib zai ganmu.”
Maganar sa ce ta katse jin ana shirin shiga sallah,shiyasa ya yi mata sallama yace ta zama
ready suna idar da sallah Baba zai gansu.

Sallah ta fara yi tukunna su Aisha suka taimaka mata ta chanza kaya zuwa super(exclusive)black colour d’inkin riga da zani,da ash chantily vail mai kyau kauri da tsada!.
D’aurin gaba ta yi irin wanda ake yayi ta rufa mayafin na ta har ka,kana ganinta ka ga amarya dan ta fito rass da ita kamar ka sace ta ka gudu dan tsananin kyau da haiba.
Tana cikin gyara sakun d’an kunnen ta ya Musbah ya lek’o yace ta zo su je ita ake jira.
Sai da ya kaita k’ofar parlourn su Siyama tukunna ya juya…ya so ya shiga ciki shima amma sai ya zab’i ya koma masallaci dan ya samu su rik’e kaka mallan a chan dan tun da ya ga Yash ya zo gaba d’aya hankalinsa ya tashi sun san indai ya shigo cikin gidan to sai ya je inda yake su kuma ba sa so ya je gudun kar ya kwafsa shiyasa da shi da ya Nafi’u suke ta jan sa da zance tunda yanzu yana kula su yana ji da su….dan su samu su yi buying time ma su Baba..

A zaune suke akan carpet su biyu suna magana Yashjub sai wani sussunkuyar da kai yake yi,amman ta na yin sallama bai san lokacin da ya d’ago ya kafeta da idanuwa ba…har ta k’araso ta zauna bai daina kallonta ba sai da tace”ina wuni tukunna ya yi snapping out da kyar ya ce “lafiya”daga haka ya sunkuyar da kanshi k’asa yana jin wani yalwataccen farin ciki yana ratsasa ta koina…..

…Nutsatsiyar nasiha Baba ya yi wa Yashjub da Manubiya tare da fatan alkhairi da sanya Albarka
Daga nan ya bawa Yash d’in amanar Manubiya……
Hatta Yash jikin sa sai da ya yi wani irin sanyi,Manubiya kam tun lokacin da Baba ya fara magana ta fara kuka.
Sosai kukan nata da nasihar Baba suka taru suka kashewa Yash jiki,shiyasa ya gagara d’agowa yana jin kamar shima ya fashe da kukan.
Sai da aka kiran sallar isha tukunna Baba ya sallameta shi kuma suka wuce masallaci shi da Yash.

Tana shiga d’akin nasu Aisha ta dafe kai tace”shikenan an dawo mana da aiki sabo”
Murmushi su inna da Siyama suka yi daga haka suka ci gaba da had’a jakar takeaway d’in da za a raba gobe inshaaAllah a wajen d’aurin aure.

Kamar d’azu yanzun ma
Aisha ce ta yi ta aikin lallashi,especially ma da ta tab’a jikin Manu d’in ta ji zafi rad’au,nan take hankalinta ya sake tashi……
Da kyar kuwa Manubiya ta samu ta yi sallah dan tashi d’aya zazzab’i da ciwon kai suka yi mata rufdugu,shiyasa Aisha ta ja ta zuwa d’akin su yaMusbah ta bata magani ta sha tukunna tace “ta kwanta anan”dan d’akin nasu ya cika da makwaftan da suka lek’o taya su aiki.

Ba ta dad’e da kwanciya ba bacci ya yi awon gaba da ita dan har da maganin bacci Aisha ta had’a mata da shi ai kuwa kasancewarta a gajiye kwana biyu ya sanya nan da nan baccin ya d’auke ta.
Ko da Yash ya kira Aisha ce ta d’auka,yana ji Aishar tace ta yi bacci ya ce “Alhamdulillah”dama aikin lallashi ya so ya yi kafin ya wuce but tunda har an lallab’ata ta yi bacci shikenan dan haka ya yi wa Aisha sallama da godiya daga haka ya kashe wayar ya wuce bayan yayi sallama da su Baba da kaka mallan………

Washegari.
A d’akin ya Musbah Aisha Manubiya da khairat suka kwana dan tunda Manu ta kwanta sai kiran sallar asubah ne ya farkar da ita,Aisha bata so ta tasheta shiyasa ta cewa su ya Nafi’u su tafi da shi da su Muhsin da ya Musbah yau d’akin su is occupied

Tana farka wa ta hango Aisha a kan daddum tana nafila,dan haka itama ta mik’e ta fad’a toilet ta kama ruwa ta yi alwallah ta d’auraye bakinta da iyaka makilin d’in da yake available ta fito tana jin yadda jikinta yake yi mata ciwo dan ba ta saba kwana da manyan kaya ba.

Har ta fito Aisha ba ta Ida ba…darduma itama ta nema ta shimfid’a a gefen Aisha itama ta tada ik’ama domin gabatar da nafila….ta na idarwa aka kira asslatu dan haka ta mik’e ta gabatar da sallar asubah….
Sai da suka kammala Azkar tukunna suka gaisa ita da Aisha, ta bata wayar ta..miscalls d’in Yash ta gani na jiya kafin Aisha ta d’auka sai wanda ya kirata around sha biyu na dare da kuma yanzu da asubah.
Sai da ta fara cire wayar a silent tukunna ta kira sa…ringing uku ta yi ta kashe dan ta san ko ta bari ya kai k’arshe ba d’auka zai yi ba.
Ko gama haske wayar ba ta yi ba ya biyo kiran,sai da ta d’an d’auki lokaci dai dai wayar tana shirin tsinkewa tukunna ta amsa. Murmushi ya yi kafin yace”sai an ja min aji tukunna za’a d’auka?kar ki damu gobe by this time na san babu maganar jan aji ko kunya a tsakanin mu dan tuni zan yi fata fata da su.”

Da sauri cikin san kawar da zancen tace”Ina wuni”
Ta fad’i hakan a ranta tana mamakin Yash,a da kamar ba ya magana amma ta lura tun lokacin da aurensu ya matso ya zama mai surutu,ko wacce Irin magana in ta zo bakinsa juye mata yake yi,gaba d’aya ya daina jin kunyar ta.”
Ta na cikin wannan tunanin ta ji yace”lafiya Alhamdulillah,matar Yash in the next 5 hours!7 minutes!37seconds inshaaAllah.”

A take ta ji gabanta ya yanke ya fad’i,tana son Yash amman ta rasa dalilin wannan fargaba da tsoron da suka lullub’eta tun shekran jiya suka k’i barinta,tun shekaran jiya hankalinta yake a tashe….
A hankali ta ji yace”baby!kin yi shiruu,ko ba a yau zan cire kunyar b…”
Cikin katseshi ta ce”na’aam!”
Sai kuma tace”inna tana kirana,bari inje?”
Dariya sosai ya yi dan ya fahimci zillewa take son yi,kylaleta kawai ya yi ba dan wayonta ba….cikin sanyin murya yace”ki gaida ita….”
Ahankali tace “sai anjima”
Yana wani irin blushing yace”Allah ya kaimu”
Daga haka Manubiya ta yi saurin kashe wayar ta d’aura a kan k’irjinta tana haki akai akai,dariyar da Aisha ta kwashe da ita ne ya dawo da hankalinta cikin d’akin sam ita ta ma manta da Aisha a d’akin wallahi….
Sosai Aisha take dariya kafin ta mik’e tsaye ta je ta ta tofawa y’arta da take ta bacci add’ua tukunna ta juyo ta kalli Manubiya cike da zolaya tace”Yarinya ba ki ga komai,ba ki ji komai ba.”
Tana gama fad’in haka ta sa kai ta fice abinta
Da sauri Manubiya ta cusa kanta a cikin cinyoyinta tana mai jin kunya!fargaba da wani irin yanayin da ba ta tab’a tsintar kanta a ciki ba.

Har Yash ya kashe wayar ya ajjiye a gefe bai daina blushing ba,ya jima a zaune yanata tunane tunane da zumud’i kafin ya mik’e ya fad’a bathroom.
Chapter 25 · 0% Book details