← Book details Munnubiya Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 78 OF 137

Sashe 78

Munnubiya Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read

K’ura mata ido ya yi,dama yana so ne ya ga reaction d’inta ko zai iya kamata da laifi amma babu alamun hakan a tartare da ita!
Ya san yadda Mommy ta kula da mahaifiyar Yahanasu suka zauna lafiya idan ya zargeta a kan incidence d’innan to bai yi mata adalci ba,amma kuma tunda mallan lawal ya kirasa d’azu ya fara basa hak’uri yana cewa yana son magana da shi to tun daga nan ya fahimci anya ba sharri aka k’ulluwa Khadijansa a wannan lokacin ba kuwa! sannan kuma kan sa ya d’aure matuk’a ta inda yana da tabbacin mallan lawal d’in ya mutu tun shekaru wajen ashirin da bakwai baya amma yanzu gashi ya ji sa a raye dan ko a mafarki idan ya ji muryar mallan lawal sai ya gane,shiyasa tashi d’aya ya tabbatar akwai k’umbiya k’umbiya a cikin al’amarin..
Khadija ba ta shiga ko mak’ofta sai tare da Mommy kuma ko hayaniya ba ta tab’a yi da kowa ba ita ba ma ta iya fad’an ba,duba da haukar da Mommy ta yi a lokacin da yace zai k’ara aure da kuma yadda ta shiryu lokaci guda ta rungumi Khadija tashi d’aya dama tun a wannan lokacin ya ke zarginta kuma ya ke ganin kamar akwai abunda ta ke shiryawa amma bai yi tunanin za ta iya yi mata wanchan sharrin ba!

Dan Khadija ko y’an uwa ba ta da shi balle ace wani ne ya yi mata sharri tabbas wannan aikin Mommy ne…
Sannan a cikin gidan ya yi waya da Mallan lawal ya san maybe Baba larai ce za ta gaya mata,shine ta kashe sa kenan??gudun kar asirin ta ya tonu?Tabbas kuwa indai hakan ya tabbata to bai ma san wanne kalar hukunci zai yanke mata ba!
Matsalar guda d’aya shine yadda ta yi d’innan ba dan shi da kansa gaba d’aya alamomi suna masa nunin kamar ita ce master ba,to ba dalilin da zai sanya ya zargeta.

A b’angaren Mommy kuwa in banda lugude babu abunda zuciyarta take yi!k’arfin hali ne kawai yake amma a mugun Muhsin hargitse take tun da ya shigo ta firgice…

“Daddy ka yi shiru”
D’in da tace ne ya katse masa tunani…
A hankali yace”yanzunnan ya rasu”
Wata zabura ta yi tace”innalillahi wa inna ilaihirrajiun,
Daddy dama chan bai rasu ba??me ya faru?kiranka ya yi?”.
Ta fad’i hakan ita kanta ba ma ta san ta fad’a ba tsabar rashin sanin tudun dafawa,kar ta yi shiru ya zargeta shiyasa ta zab’i ta yi maganar da ta zo mata.

Wani kalar mahaukacin bugawa zuciyar Daddy ta yi dan tabbas Mommy ta k’ulle kanta da kanta..ta ya aka yi ta san kiransa ya yi?

Jin jina mata kai ya yi yana jin kamar ya shak’e ta ya kashe ta right away,da kyar ya iya cewa”kira na ya yi ya ce in yafe masa yana buk’atar gani na da gaggawa.”

Zuwa yanzu yadda Mommy ta fara gumi ya gama tabbatar masa da komai,dama abunda ya zo tabbatar wa d’in kenan shiyasa ya zo mata a haka,cikin son sake ganin reaction d’inta yace”tun lokacin da ya kira ni ya fara magana gaba d’aya hankalina ya karkarta ne a kan watak’ilan Khadija ma tana raye.”

A take ya ga idanuwanta sun fara ciccikowa da hawaye kamar za ta yi kuka…da kyar bakinta yana wani irin karkarwa ta samu tace”Noo Daddy it can’t be,idan shi ya rayu ita ba zai yiu ta yi rai ba,ko ka manta yadda ita d’in da hannunka fa ka c….”
Yadda taga idanuwansa sun yi jaaa a take ne ya sa ta had’iye maganarta ta sunkuyar da kanta,kafin da kyar ta sake d’agowa tace”amma ban sani ba sai dai mu fara bincikenta,watak’il itanma she made it out alive..saboda ka san dama na gaya maka wajen yadda ya koma ba mu iya detecting ko da biro ba ballantana gawa komai ya kone k’urmus ruwa kawai muka yayyafa aka yi musu salla a haka…..”

Wuff kawai ta ga ya juya ya fita zuciyarsa ta na wani irin tafarfasa dan ya san tabbas idan ya ci gaba da zama to zai iya aikata abun ban mamaki ga Mommy…Mommy ta yi masa abubuwa daban daban tun daga kan yadda ta tilasta masa aurenta har kawo yanzu kullum a cikin b’acin ranta ya ke,amma bai tab’a tunanin za ta iya aikata haka ba,sannan gashi still k’ok’arin b’oyewa amma ya san ta yadda zai kamata dumu dumu yadda zai k’ulleta da jijiyoyin jikinta ya tona mata aisiri kowa ya ganta…hacking wayarta kawai zai yi ta yadda ko typing take yi sai ya gani.A nan ne kawai zai ji komai da take yi ya ga komai ya kamata dumu dumu ya tabbatar da zarginsa a kanta.
He really can’t believe this!he can’t believe Mommy ta saka shi ya kashe Khadijah da hannunsa ba tare da laifin ta ba,dan kamar yadda ita ma Mommy ta fad’a idan mallan lawal ya samu ya yi making out alive ita Khadijah ba ta Isa ta fita da rai ba.

Tabbas kisan kai it’s too easy for Mommy…shi kansa yana jin tsoron abunda zai yi mata Wallahi.

Kasancewar Yassir a napep ya taho ya sanya sai yanzu ya samu ya shigo cikin gidan…..

Yana zuwa a fusace ya haye sama ya nufi d’akin Kausar,zuciyarsa tana wani irin tafarfasa.

Kausar ta na wani irin kuka haka nan ta shiga d’akin ta ta fad’a kan gado…..ta yi kuka a wannan rana kamar ranta zai fita kafin ta mik’e ta fad’a toilet ta shiga wanke fuskarta a ranta kuwa ta gama aiyyanawa “wallahi
daga yau ita ma ta kanta za ta yi farin cikin ta kawai za ta duba!kowa ya yi ya kansa….inshaaAllah sai ta mallaki Yashjub ko ta halin yaya ne,daga nan za ta nunawa Mommy wacece Kausar,sai ta san ta yi betraying d’inta wallahi daga kanta ko d’an aiki ba za ta sake betraying ba.”

Tana wannan lissafin ta fito daga toilet d’in…a d’akin ta tarar da Yasira,cikin rashin kwarin jiki Yassirar ta mik’e ta k’arasa ta ruko hannunta kafin tace “ta zo ne akan ta yi mata gargad’in ta bi Yassir a hankali kar ta bari ya fahimci wani abun gudun kar yaje ya yi mata kwab’a.Dan yadda ya yi mata d’azu a asibiti ita kanta ta d’an tsorata gaskiya”da “to” kawai ta bi ta daganan Yasirar ta juya ta fita dan ta fahimci kamar Kausar d’in ta na buk’atar space.
Tana fita Kausar d’in ta girgiza kai a ranta tace’’kwab’a kuma ta nawa?bayan abunda ya aikata,’’wannan shine karo na biyu da ya so ya kashe Yashjub kuma ta lura Mommy ma ta fahimci wani abun amma ta ga kamar k’ok’ari ma take yi ta b’oye…

A hankali tana jin kanta yana wani irin mahaukacin sarawa
ta nemi guri ta kwanta.
Lumshe idanuwanta tayi
atake hawaye suka shiga sintiri a kan farar fuskarta
Wannan wacce irin rana ce ta risketa?…ga ciki tana d’auke da shi,ga Mommy wadda ta juya mata baya ga kuma Yassir wanda take zargi da wannan
shirmen a karo na biyu
sannan bata Isa ta tunkare sa da maganar ba dan ba ta so ya
fahimci wani abun
Sannan ga rayuwar Yashjub dake a cikin hatsari ga Manubiya ga shi Yashjub d’in ma kansa har yanzu ta kasa samun sa!,ta Ina za ta fara ne?dan abubuwan sun yi mata yawa.

K’arar bud’e k’ofar d’akin nata ta ji da mugun k’arfi dan haka ta tashi a d’an rikice duk da kuwa da ma ta riga ta san waye ne.
A tsaye a bakin k’ofar ta gansa yana huci kafin ya juya ya rufe k’ofar ya murza key tukuna ya nufota gadan gadan…
Duk tsaurin idon Kausar sai da ta tsorata dan haka tun kafin ya k’araso ta mik’e tsaye tana mai gyara doguwar rigar jikinta ta hau inda inda cikin in’ina tace’’Yassir I’m sick dan Allah ka bar….’’
Mahaukacin marin da ya d’auke ta da shi ne ya sanya ta gagara k’arasa maganar tata,sai da numfashinta ya d’auke na y’an seconds tsabar tsananin shock d’in da ta shiga,a rikice ta d’ago fuskarta da ta yi jajir ga shatin y’an yatsunsa sun fito rad’o rad’o a fuskar tata tace ‘’Yassir ni ka mara??’’
Cikin karsashi yace‘’appetizer ne wannan kar ki damu,if you like ki bari in yi miki tambaya ki yi mini k’arya…’’
Ya fad’i hakan yana mai kunce belt d’in wandon sa.
Cikin fushi tace “dukana za ka yi?baka da hankali ne?duk abubuwan da ka yi basu ishe ka ba???’’

Dakatawa ya yi daga nad’e k’asan belt d’in da ya ke yi around his fingers kafin ya d’ago jajayen idanuwansa ya zuba su akanta tukunna yace ‘’abubuwan da na yi?me da me na yi kenan?’’
Ya fad’i hakan cikin matsowa daff da ita yana mai tsare ta da dara daram idanuwansa da suka yi jajir hatta fuskarsa ta yi jaaa tsabar bala’i.

Ahankali ta d’an ja da baya dan a mugun tsorace take dashi
Sai da ta d’an kauda kanta gefe tukunna ta yi k’asa da murya tace’’ Wallahi zan tona maka asiri,in har ka tab’a lafiya ta sai kowa ya san kai ne ka tura y’an fashi estate d’in Yashjub yau’’

Cak!haka ya k’ame,kafin ya juyo da fuskarta cikin karsashi yace ‘’Kausar ni za ki yiwa sharri da borin kunya saboda kinga na kama ki dumu dumu?’’

Ganin yadda jikinsa ya yi sanyi kuma ta ga ta d’an samu galaba a kansa ne yasanya ta fincike fuskar ta tace’’ba iya wannan ba ma Wallahi har tayar motar sa da ka cire kwanakin baya sai na fad’a kowa ya ji ,tun da dama son da nake yi maka ne yasanya nake rufa maka asiri amma in har zaka iya d’aga hannu ka mareni to na san ka daina sona dan haka nima ban ga amfanin ci gaba da son ka Ina bin bayan ka ba ,’’
Ta fad’i hakan tana mai rushewa da wani uban kuka wanda yayi tsananin tasiri akan Yassir.
Chapter 78 · 0% Book details