← Book details Munnubiya Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 114 OF 137

Sashe 114

Munnubiya Part 2 Complete Hausa Novel · about 7 min read

A daren ranar Hajiya Mama ta bi jirgin k’arfe hud’u ta nufi Uk,duk da yadda abubuwa da suka wakana suka yi mata dad’i amma
tana so ta tafi…fushin da ta yi ta ga positive effects d’insa sosai a kan Daddy dan haka ta yanke a kan za ta tafi ta je ta yi ta yi musu addu’a Allah ya sa a dace in shaa Allah Mommy ta kusa ganin k’arshen ta kuma duk wasu abubuwa da ta rufe sai sun bankad’a a idanun kowa ya gani.

Ya’isha tafi kowa gigita da lamarin tafiyar Baba larai dan ta san Baba larai itace gatan su saboda yanzu haka aiki take yi mata a kan Siyama da Najeeb!!shikenan ta san ta shiga ukun ta itakam yanzu..Yasira ma ta gigita sosai dan itama ta san Baba larai d’in dai itace gatan su dan haka da daddare bayan ta bari Mommy ta d’an huce ta je ta sameta cikin son fahimtar da ita ta fara yi mata bayanin illar tafiyar Baba larai a garesu kuma ko ba komai bai kamata ace sun yiwa Baba larai haka ba!ko me kuwa ta yi musu ba ta yi deserving haka daga garesu ba.”
Cikin nuna halin ko in kula Mommy tace”Yasira ba fa ni na cewa Larai ta tafi ba ita da kanta ta yi zuciya ta ce za ta tafi shiyasa ni kuma ban hana ta ba besides abunda ta yi mini ma ya sanya dole in hukuntata in nuna mata iyakar ta dan haka indai na Isa in fad’a miki ki ji to ki tsame hannunki ki gaywa su Yusra ma duk su tsame hannayensu a lamuranta ko waya bana so ku yi mata,Allah na tuba idan banda failure me muke fuskanta aikin nata yanzu duk ya daina ci!”
Cikin mamaki da tsanannin rashin jin dad’in abunda Momyn ta yi ta kuma fad’a yanzu Yasirar tace”idan na fahimceki Mommy a yanzu dai Baba larai ba ta da wani amfani a gareki shiyasa kika b’ige da cewa kinaso ki hukuntata ne saboda na san inda ace a lokacin da Baba larai take ganiyar taimaka miki komai yake tafiya daidai ne to da ko me ta aikata a gareki ba za ki tab’a barinta ta tafi ba,me ye ma ta aikata miki yanzun da ya yi zafi har haka???”
Yasira ta yi mata tambayar cikin b’acin rai.

Mik’ewa tsaye Mommy ta yi ta nuna mata k’ofa tace”get out Yasira tun kafin ran ki ya b’aci!!!
Za ta yi magana ta kuma daka mata tsawa tace “get out nace!!!”
Juyawa kawai Yasira ta yi ta fita ranta a b’ace da takaicin Mommy dan ita a rayuwarta ba ta son mutum mai use and dump kawai idan ana tare to a kasance tare har abada through thick and thin kuma a taimaki juna amma ita Mommy bayaga use and dump d’inma da ta yiwa Baba larai,
tun ba yau ba ta lura da Mommy she’s just looking out for her self kawai using d’insu take yi…..

Sai bayan kwana d’aya tukunna Mommy ta je d’akin Yahanasu dan ta san zuwa lokacinta d’an huce.
A zaune ta sameta suna waya da Yashjub tana ganin ta shigo ta yi sauri ta kashe ta ajjiye wayar ba tare da ta kalletaba ta ce”bacci zan yi”
A hankali Mommy ta sauk’e ajiyar zuciya ta nemi guri ta zauna a kusa da ita ta kamo hannuwanta.
Kawar da kai Yahanasu ta yi,tsabar takaici da bak’in ciki ba ta san lokacin da hawaye suka shiga sintiri a kan fuskarta ba.

A hankali tace”na san na yi miki laifi Yaha amma ba laifi na bane ba completely.
Na shirya gaya miki komai in gyara tsakanina da ke amma da Larai ta fahimci hakan gudun kar asirinmu ya tonu sai ta je ta yi abunda ta yi ta kawar da tunanin ki daga gabana if not because of that Yaha da ba zan tab’a bari mu kawo war haka a hakan ba!
Amma yanzu komai zai gyaru Yaha saboda ke da kuma na fahimci Larai ta saka na cuce ki yanzu haka ba ta cikin gidan nan tun jiya saboda ke y’ata.

Na san this is a lot to ask for amma dan Allah ki dubi uwar da aka shiga tsakaninki da ita ba tare da saninta ba ki yi mini adalci ki bani chance Yahanasu….

Mik’ewa da sauri Yahanasu ta yi tace”dan girman Allah ki fita!ba na buk’atar gyaruwar komai a tsakanina da ke Mommy kawai ki bari mu k’arashe rayuwarmu a haka
Me ye ne ma ya rage??
You’ve missed out all the important stages na rayuwata da na fi buk’atar ki dan haka yanzu ban ga amfani idan kin gyara komai ba wallahi,I don’t need you in my life na riga na san ba kya so na ba kya k’aunata kin yi amfani da ni saboda ki samu abunda kikeso which u do dan haka na rok’eki da girman Allah kar ki nemi ki ja ni a jiki saboda ba zan janyu zuwa jikinki ba.
Dan haka kawai ki yi harkar ki nima in yi tawa harkar ba zan tona miki asiriba saboda unlike you idan na yi Abu yana damuna na san kuma duk lalacewa ke mahaifiyata ce dan haka muddin na bada gudummawar na zamo silar tafiyar ki prison to abun sai ya dameni har k’arshen rayuwata shiyasa kawai na zuba miki ido na ke jira Ubangiji ya yi ikonsa a kanki amma fa muddin ba ki daina treatning Yash da tsinuwa ba Wallahi kamar yadda na gaya miki shekaran jiya tabbas zan fad’a masa ba ke ce kika haifesa ba!
Saboda kamar yadda na san guilty conscious zai addabeni idan na fad’i abubuwan da kika yi aka hukuntaki haka zalika guilty conscious zai addabeni idan na bari bak’in cikin ki ya kashe Yashjub dan haka ki daina threatening d’insa!!!
daga nan ni da ke mu ci gaba da treating juna just like before iyakacin abunda nake buk’ata kenan daga gareki ba wai sulhu da fahimtar juna ba!
Kin riga kin cuceni wata shari’ar sai a lahira,Mommy ba wai iyaka hakki na ba wallahi ko da Hakkin Mama khadija kad’ai aka barki ke da Mallan lawal da Baba larai ya isheku…..”

Shiruuu Mommy ta yi haka itama Yahanasu…tun shekaran jiya da Yahanasu ta je d’akin ta ta yi threatening d’inta ta san tsaff za ta iya yin abunda ta fad’a shiyasa ta ke so ta lallab’ata..tana son y’arta kuma ta na so su fahimci juna Sannan da gaske ne Baba larai asiri ta yi mata ta kawar da Yahanasun daga ranta gaba d’aya amma ita Mommy a halin yanzu Babban tashin hankalinta shine kar Yahanasu ta tona mata asiri
Ta ji haushin Baba Larai kuma ta na so ta san ta yi mata laifi ta yadda ba za ta sake yunk’urin yin wani ba shiysa ta barta ta tafi kuma ta hana a nemota amma fa Yahanasu tana daga cikin dalilin da ya sanya ta yiwa Baba larai abunda ta yi saboda tana so Yahanasu ta gani ta san ta yi abu Babba haka duk dan ita sai dai kuma ta lura hakan ko a kwalar rigar Yahanasu gashi a iyaka maganganunta na yanzu ma ta lura Yahanasu fa ta san har case d’in abunda ta aikatawa Khadija….dan haka dole ta d’auki risk ta aikata dukkan abunda za ta iya ta samu ta yi manipulating Yahanasu ta shawo kanta su fahimci juna tun kafin ta b’allo mata ruwa.
A hankali ta ce mata ki zauna mu yi magana Yaha zan fad’a miki duk abunda na yi tare da alk’awarin ba zan sake ba..kuma na san idan kika ji bayani na za ki yi mini adalci idan kika fahimci dukkan nin abubuwan da na yi na aikata su ne saboda ku y’ay’ana.

Yahanasu ba ta zauna ba ganin ba ta da niyyar zaman ne ya sanya Mommy ta fara magana.
“Kamar yadda na fad’a ba zan b’oye miki komai ba saboda Ina so ki yarda da ni mu fahimci juna.
……….Idan ana maganar rashin jituwa da rashin zaman lafiya da rashin so da k’auna to shine asalin zamana da mahaifinku tun lokacin da muka yi aure…ko
Irin soyayyar na ta amarci bai nuna mini ba, k’arshen rashin mutunci da kyara shi Imam ya dinga nuna mini,tunda muka yi aure sam ba ya ja na a jikinsa ba ya nuna mini kulawa.

Ban rufe watanni biyu a gidan Imam ba ya tubure ya dage ya d’agawa kowa hankali shi fa sai ya k’ara aure…sai ya auri budurwarsa wadda na san yana masifar so kamar ransa dan k’iri k’iri ya kan ce mini saboda suna na ya zo d’aya da ita ne dalilin da ya sanya yake d’an kulani.
Babu kalar masifar da ban yi ba amma sai da aka d’aura auren nan lokacin ma da aka d’aura ba na nan ya kaini gidanmu yace a yi mini fad’a Abban mu kuma ya goyi bayansa aka mini horo mai tsanani ta inda aka ce ba zan koma gidan ba Ina ji Ina gani aka yi auren Khadija ta tare suka gwangwaje amarcinsu ni Ina gidanmu hankalina a tashe.
Chapter 114 · 0% Book details