← Book details Munnubiya Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 123 OF 137

Sashe 123

Munnubiya Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Sai da Yash ya je ya ga Manu tukunna ya wuce gida saboda dama tun jiya take rok’ansa ya barta ta yi kwana uku tunda gida ma za su chanja ai kuwa da ya barta ta ji dad’i kwarai amma kuma tana ganin yanayinsa ta fahimci akwai matsala dannhaka ta hau tambayarsa bai b’oye mata ba ya gaya mata cewa”Daddy ya kori Yassir kuma k’arshen abun bai yi dad’i ba dan har da Mommy itama sai da ta bar gidan”
,sosai Manu ta tab’u daga jin zancen da kyar ta taushi kanta sannan ta yi namijin k’ok’ari wajen kwantar wa da Mijin nata hankali tukunna suka rabu ya wuce gidan Daddy shi da Najeeb dan yana gidan suka zo shi da Siyama.

Ita Manubiya ba ma ta yi tunanin da Siyaman aka zo ba dan basu dad’e da yin waya ba bata gaya mata ba sai da su Yash d’in suka wuce tana shiga parlourn nasu daga parlourn Baba ta ganta a zaune ai kuwa nan suka hau murna har da hawayen farin ciki.

Sai da su Yash suka kama hanya tukunna ya tuna bai sanarwa su Manubiya rasuwar Baba Larai ba,dan haka ya bari a kan sai zuwa anjima sai ya gayamata ya san dole za ta kirasu ko ma ta je addu’arsa d’aya Allah ya sa kar Mommy ta yi mata abunda ta yi masa itama da ma gashi ba ta sonta.

A b’angaren Kausar kuwa zuwa yanzu ta gama sanin abun yi dan haka jimamin Baba Larai yana d’an sakinta ta kira Ya’isha tace”tana so ta had’ata da Abbakar akwai abunda zai yi mata”
Da kyar Ya’ishan ta had’ata da shi kuwa
Saboda last time Abbakar d’in ce mata ya yi “kowa kawai ya yi ta kansa daga yanzu!
dan plan d’in da suka had’a last time bai yi masa ba gashi ba su yi winning ba gashi kuma sai da yayi watanni uku a asibiti…”
Hakanan dai ita Kausar ta nace sai da aka had’ata da shi saboda shi ne kawai ta ga intention d’insu ya zo d’aya tunda yana son Manu itakuma tana son Yash dan haka za su taimaki juna,ta zauna ta yi tunani sam ba za ta wani biyewa Mommy ba wallahi!
Ba za ta iya hak’ura da Yashjub ba…kowa kawai ya yi ta kansa……….

Ita dai Yasira tana jinsu suna wayar da Ya’isha har aka tura number tana mamakinsu a ranta tace”wato dai wanda ya mutu ya riga ya tafi!duniya kuma kowa sai ya ci gaba da abunda ya saka a gaba.
Kalli yadda suka ci gaba da k’ulle k’ullensu kamar ba yanzunnan aka dawo daga kai Baba Larai kabari ba.”

Ita ma Yusra lissafin da take yi kenan.
Ita sam ba ta yi tunanin Kausar d’in ta san da issue d’in Abbakar d’in ba ma maybe Ya’ishan ce ta fad’a mata.

Su Yassir suna gama tafiya Mommy ta cewa su Yasira su zo su raka ta…su sun yi tunanin ma kayan abinci da abubuwan buk’ata za su sissiyo sai da suka ga ta d’auki hanyar inda za su je tukunna suka fahimci inda suka nufa…
Aikuwa suna isa suka shaida wajen…
Mutumin tsoho tukuff idan ka gansa ba za ka yi tunanin yana gani ba ma tsabar tsufa..hakanan ya k’araso inda suke dan suna yin parking suka ga ya fito yana zuwa yace”lale marhaba Khadija yau kuma ina Larai??”
Sunkuyar da kai Mommy ta yi ta girgiza kanta a hankali wasu siraran hawaye suka zubo mata….

Shiruu ya yi ya d’an k’ura mata idanu kafin yace”Allahu Akbar amma an yi babban rashi..Allah ya ji k’anta!mu je daga ciki”
Daga haka suka nufi ciki.

Shi wannan tsohon!wanchan bokan na k’auyen su Baba larai shi ne ya had’ashi da ita tun asalin farko kafin ya rasu kafin ta baro ma k’auyensu ta da who nan Kano inda yake…..idan abubuwa suka shige masa duhu ya kan tambayeta itama haka,har nan suna zuwa ita da Mommy idan aikin da suke son yi ya had’a da wanda mace ba zata iya yi ba sai su kawo shi ya yi musu.
….
Sai da ya sake yi mata gaisuwa ta amsa tukunna ba tare da b’ata lokaci ba tace masa”Yashjub ya yi aure ba ta samu abunda take so ba har yau kuma Yarinyar ta zo da farar k’afa mutuwar Baba larai na daga cikin masifun da Manubiya ta zo mata da shi saboda dama Baba larai tace
muddin aka aurota to fa an yi ta ganin bala’i kala kala.Yanzu haka ma ba ta gidan Daddy jiya ya yi musu korar kare ita da Yassir….”

Salati tsohon ya yi kafin ya janyo wata tukunya fall ruwa yana duba cikinta yana jimami….

Sun fi minti ashirin a haka kafin chan ya d’ago ya kalleta yace”ai kin yi kuskure!irinsu waennan ba a barinsu a doran k’asa!ai idan aka yi aiki ya k’i ci ya k’i cinyewa rabasu da duniyar ake yi tunda sun fi k’arfinka to ta ya zaka tsaya fafatawa da su ai ba zai you ba!”

Ajiyar zuciya Mommy ta sau’ke dan ba k’aramin dad’i ta ji da jin wannan batun ba saboda dama ita takanas abunda ya kawota kenan!!a yi ta ta k’are kawai.
Cikin k’aguwa tace”aikin gaggawa nakeso ka yi mana,ba na so Larai ta kwana uku a kabari ba tare da Yarinyar nan ta bi ta ba!”
Cikin tarar numfashinta Yasira tace”Mommy wai kisan Kai kike nufi??”

Murmushi tsohon ya yi kafin yace”to ai hakan kawai ce mafita!saboda Wallahi Allah muddin Yarinyar nan tana raye tou fa bala’i da masifu yanzu kuka fara gani!!!”.

K’ura masa ido Yasira ta yi kafin chan ta d’auke kanta ta mayar ga Mommy tace”Mommy mu je gida ma yi magana Plss dan Allah ki bar maganar nan!”.

Girgiza Kai kawai Mommy ta yi kafin ta ce”Yasira har yanzu ke Yarinyace..dan gashi duk abubuwan da suke faruwa a gaban idanunki ba kya gani!inaga sai na mutu kin binne ni tukunna za ki fahimci abunda muke nufi!!!”

Da d’an zafi Yasira tace”Mommy Manubiya b….”
Cikin katseta da tsawa sosai Mommy tace”za ki yi mini shiru ko kuma in kora ki waje????”

alamun ta yi shiru su Ya’isha suka yi mata dan haka kawai ta yi shiru ba dan ta so ba kuma wallahi wannan tab’argazar ba da ita ba ba za ma ta bari a yi ba…

Sai da Mommy ta yi kusan minti d’aya tana hararar Yasirar tukunna ta mayar da kanta ga tsohon wanda shima yake cewa Yasirar “ki tsaya ayi abu a nema muku mafita hatta rashin aurenku duk itace gashi nan na gani a nan!ko ba kwanan nan wanda za ki aura ya yi aure ba???”

Ita dai Yasira banza ta yi da shi Yayinda Mommy da Ya’isha suka aminta da maganar ta shi d’ari bisa d’ari…

Murmushi kawai ya yi ya mayar da dubansa ga Mommy yace”kar ki damu komai ya zo k’arshe inshaaAllah!”

Ajiyar zuciya Mommy ta sauk’e kafin tace”yanzu nake so a yi aikin..saboda na gaji na tsani…”

Cikin tarar nunfashin ta yace”sai dai a yi aikin a yau da daddare gobe a tashi babu ita!!”

Jin jina kai ta yi tace”hakan ma ya yi”

“To Alhamdulillah” yace kafin ya d’aura da cewa”yanzu akwai yadda za a yi in samu hularta???”

Kallon juna suka yi ita da Ya’isha suka yi shiruu kafin chan Ya’ishan tace”eh!!
Da me kuma??”

“Iyaka hula,kawai!
Ki tabbatr tana cirewa daga kanta kin kawo mini kai tsaye ba tare da kowa ya saka ba!
Shikenan abunda na ke buk’ata.”
Cikin yin serious da fuska sosai,ya ture tukunyar gabansa ya mayar gefe ya kallesu sosai yace”da farko dai inaso ku fahimci cewa shi RAI!!
Bayar da shi da karb’arsa wannan Ubangiji ne kad’ai ya isa bi’ma’ana Ubangiji ne kad’ai yake bayar da Haihuwa yake kashewa bayan shi babu wanda ya isa,duk bala’in mutum bai Isa ya kashe ko ya raya ba…”
Jimm Mommy ta yi tana jin wani sabon tashin hankali yana rifeta, kar dai mutumin nan yace ba zai iya yi mata komai ba kuma!!!
Tana wannan tunanin ta ji ya ci gaba da cewa”Abunda mukeyi idan matsala irin taki ta taso shine wannan aikin da zan yi muku a yanzu ammafa yanada matuk’ar hatsari kuma yana buk’atar taka tsantsan!”
Sai da ya sauk’e numfashi tukunna ya d’aura da cewa”ita wannan hula da za’a kawo itace nake so a kiyaye kar a samu matsala wani ya saka bayan ita Yarinyar saboda idan aka samu matsala to fa shi wanda ya saka bayan itan da wanda ya kawo duk su biyun aikin zai fad’awa kuma idan aka yi ba’a janyewa bima’ana idan aka yi an riga an yi ba a tab’a iya karyawa!!!”

Jinjina kai Mommy ta yi tace”na ji na fahimta inshaaAllah za a ayi taka tsantsan..ya aikin yake?”
Ta yi masa tambayar tana kallonsa.
Murmushi ya yi kafin yace”rik’e mata numfashi zan yi!…idan kaff likitocin duniya ne za ace su zo su taru a kanta babu wanda ya isa yace tana da rai saboda komai tsayawa zai yi.
Daganan Idan aka yi mata wanka akai mata sutura aka kai ta kabari aka binne muka tabbatar an kai ta ni kuma sai in saki numfashin ya dawo..kinga dai ai bata isa ta fito ba ko?sai dai ta k’arasa a chan!!”
Ya k’arashe maganar tasa yana sakin dariya…
Da sauri Yasira ta mik’e ta fita hankali a tashe ranta a masifar b’ace..Tabbas bayin Allah marasa Imani suna da yawa a duniya..ta ya mutum zai iya aikata haka a d’an Adam musulmi d’an uwansa?.

Wani sanyi da nutsuwa Mommy ta ji daga jin bayaninsa dan bata tab’a jin hukunci mafi dacewa daya dace ace ta yankewa su Manubiya ba kamar wannan!!!

Har za ta yi magana sai kuma ta tuna da su Yusra dan haka ta kallesu tace”ku d’an bamu guri!”

Sai da ta tabbatar sun fice daga cikin gidan gaba d’aya tukunna ta kallesa tace”Ana iya yiwa Namiji ma ko?”

Dariya sosai ya yi kafin yace”Yashjub ko?
Tsaff za ki yi masa shima amma shi gashin kansa za ki kawo.”
Chapter 123 · 0% Book details