Sashe 95
Munnubiya Part 2 Complete Hausa Novel · about 7 min read
Manya manyan flat house ne guda biyu iri d’aya gate d’insu d’aya ko wanne yana d’auke da 4 bedroom da 2 parlours da kitchen da dining area,ga babban tsakar gidan da ya ji interlock wanda atleast sai a gina irin gidajen uku a cikinsa.Har da d’akin mai gadi a kusa da gate d’in.
Ba kad’an ba gidan ya burge su Manubiya tashin hankalin da suke a ciki ne ya sa ba su tsaya santin gidan ba suka afka b’angaren da suka ga k’ofarsa a bud’e.
A chan waje kuwa sai da Yash ya tsaya tukunna ya fahimci limaman masallacin area d’in ne Baba yake tare da su…
Sai da suka gama suka yi sallama suka wuce tukunna Yash ya yunk’ura da kwarin guiwa zai lallab’a Baba amma instead sai Baban ya rigasa ya shiga had’a sa da Allah yana neman alfarmar indai ya d’aukesa a matsayin uba kuma yana ganin girmansa to kawai ya bar maganar ya yi wa su Jidda addu’ar samun zaman lafiya.
Sai da Baba ya tabbata ya d’aure Yash da jijiyoyin jikinsa tukunna ya barshi jiki a sanyaye…..
Tun daga nesa da ya taho ya Nafi’u ya fara murmushi dan ba kad’an ba ya ji dad’i a cikin ransa matuk’a
Dama d’azu da sassafe da ya je ya yi masa magana a take ya yi masa alk’awarin inshaaAllah zai zo,kuma dama tun a d’azun ya lura wannan karon ya Musbah ya ji fad’an da ya yi masa sosai shiyasa tun a lokacin ya ji sanyi da dad’i a ransa dukda kuwa uwar ramar da ya ga
Abokin nasa ya yi.
Sai da ya gama parking mashin d’insa tukunna Baba ya lura da shi ya gane sa…..k’uraaa masa ido ya yi gaba d’aya tashi d’aya tausayinsa ya lullub’esa dan kana ganinsa ka san yana cikin matsananciyar damuwa.A hankali Baba yake jin duk wani takaicin Ya Musbah da ya k’unsa yana warwarewa sakamokon fahimtar da ya yi tabbas ba yin kansa bane kuma shi kansa ba ya jin dad’in abunda yake yi d’in dan gashi gaishe da shi yake yi amma sam ya kasa kallon cikin idanunsa kamar ma kuka yake son yi.
Ahankali ya had’iye wani k’ululun abu da ya tokare masa mak’oshi yace”Alhamdulillah Musbahu”still yana kallonsa yana karantarsa.
Sai da ya sake yin k’asa da kansa kafin yace”ya k’arfin jiki ya fad’i hakan a hankali.
“Alhamdulillah”Baba yace daga haka ya maida dubansa ga Ya Nafi’u yace”Nafi’u na tura maka kud’in,ka je ka siyo gadon,kaka mallan kai yake jira tun d’azu ku kai gidan.”
A hankali Ya Musbah yace”Baba ba za a hak’ura da maganar nan ba,ka yi hak’uri dan Allah ka….”
Cikin fushi Baba yace”kai har yaushe ka zo ka ji halin da ake ciki da har za ka tsomo mini baki a cikin al’amurana?Kar fa ka kaini bango Musbahu kulaka da ka ga na yi ba shi yake nufin na manta abubuwan da ka tafka ba!”
Da sauri kaka mallan ma ya tsomo baki,dama d’azu ma saboda Yash ne ya yi magana shiyasa bai tanka ba dan haka yanzu ya samu bakin magana harda cewa “a cikin duhu aka kama Jidda da Al’ameen amma shine saboda rashin sanin ciwon kai still suke da bakin k’orafi ga Yusuf wanda ya ji ya gani ya rufe ido zai aureta a hakan.”
“Yashjub mu je ciki”
Baba ya ce,daga haka ya juya,har Yash zai bisa sai wayar sa ta d’au k’ara ganin sunan Daddy yasa yace”Daddy yana kirana bari in je in dawo kafin d’aurin auren.”
“To”kawai Baba yace daga haka ya shige cikin gidan dan yana so ya yi wanka ya shirya da wuri gashi har 9:00 ta yi.
Su Ya Musbah sun san shawo
kan Baba ba abu mai sauk’i bane dan ransa ba a b’ace ba ma idan ya turje babu mai sa shi ya bari ballantana yanzu da yake a fusace shiyasa gaba d’aya hankalinsu ya sake tashi suka cigaba da addu’a kawai..dan tunda har Yashjub ya sa baki ya k’i yarda to addu’a kawai za suyi ta yi su jira Ubangiji ya yi ikonsa ya ceto rayuwar Jidda.
28 September 1994
….zaune take a tafkeken parlourn gidan da ya ji kayan alatu daban daban…a cikin shekarun da ba su fi hud’u ba Mijin nasu bud’u yake samu ta ko ina Alhamdulillah..sun chanja gida ya gina musu bungalow guda biyu tafkeke iri d’aya a cikin gate da compound d’aya ko wacce da b’angarenta sai kuma boysquaters babba shima a ta gefe…ya siya musu gwala gwalai har motoci ya siya musu guda biyu iri d’aya zani kuwa mafi tsada na wannan zamanin shi suke d’aurawa ita da Abokiyar zamanta!sai dai fa ita duk wannan daula da ake ciki sam hankalinta ba a kwance yake ba zuciyarta babu dad’i nutsuwarta ba ta tare da ita sakamokon juya mata baya da Mijinta masoyinta abun k’aunarta ya yi tun lokacin da ta haihu shekaru hud’u kenan.
Tashi d’aya ya chanja mata ba tare da ta san laifin ta garesa ba.A yadda yake nunawa kamar har yanzu yana k’aunarta tunda yana masifar kishinta har yanzu kishi mai tsanani amma kuma ko kusa da shi baya so ta je..hantara kyara da tsangwama ne kawai yake shiga tsakaninta da shi gashi tsabar kishi ya maida ita kamar prisoner ko baranda ta fita indai mai gadi ko mai wanki wani ya ganta to fa ta shiga ukunta a ranar,hakanan tana ji tana gani Abokiyar zamanta za ta tambayi fita a barta amma ita ba ta Isa ba kitso kawai ta san tana zuwa bayan layi shima tare ita da Abokiyar zamanta.Ita sam ta kasa gane kan Imam kwata kwata dan kamar ma zarginta yake yi watak’il saboda ya san ba ya sauk’e hakkin ta da ya rataya a wuyansa shiysa yake zargin za ta je ta nema a waje…
A take hawaye suka shiga sintiri a kan kyakkyawar fuskarta,shin wannan wacce iriyar rayuwa ce??gashi ba ta da gurin zuwa da ma Imam d’in shine Uwa shine Uba kuma Masoyi a gareta yanzu kuwa abubuwan da yake nuna mata ita kanta ta san kora da Hali ne k’arara yake yi mata,ya gaji ita!
A da tana tunanin ta yi sa’ar Miji yanzu kam tabbas ta san ba ta yi ba,instead Ubangiji ya had’ata da mugun Miji Mugu ajin farko!
“Khadija wai har yanzu ba za ki bar kukan nan ba?na gaya miki addu’a itace mafita…wallahi Imam har yanzu bai yi miki rabin abunda ya yi mini ba,haka yake zai daina wata rana dan Allah ki yi k’ok’ari ki cire damuwa a ranki mana.”
Muryar Abokiyar zamanta wadda shigowarta cikin b’angaren nata kenan ta katse mata tunani.
A hankali ta d’ago ta kalleta daidai tana zama da Yaronta a hannunta.
Cikin sharar hawaye tace”ba komai Mommy,kar ki damu na san wata rana sai labari.”
Cikin son kawar da maganar dan zuwa yanzu ko lallashi ba ta so a cika yi mata gaba d’aya sai ta sake zama emotional dan haka ta d’an k’ak’alo murmushi tace”Yassir! Ina ka baro Yasira?ko tana chan tana sana’ar?”.
Ta fad’i hakan tana mai mik’awa Yaron hannu alamun ya zo gareta.
“Kamar kuwa kin sani..tun da Baba larai ta yi musu wanka ita da Yahanasu suka koma bacci har yanzu ba su tashi ba..”
Murmushi ta yi tace”Allah ya yi albarka ya had’a kawunansu”
“Am khadija ko za ki yiwa Hajiya Mama magana a samu Yashjub ya dawo..ya yi k’ank’anta a zuwa Hutu ya dad’e haka a wata k’asar gashi an koma makaranta.”
Dariya ta yi kafin tace”yanzu Mommy sai in kira Hajiya Mama in ce mata Yashjub ya dawo ya yi k’ank’anta?ai sai a ga rashin karar mu..ki yi hak’uri ita kanta na san nan ba da jimawa ba za ta dawo da shi..ke da ya kamata ace yanzu fafutukar ta yadda za ku shirya ma kike yi! idan ta ji mun ce Yash ya dawo ai bak’in jini za ki sake gogawa kanki har ni sai ta shafa….”
Shiruu Mommy ta yi kafin ta sauk’e wata nannuyar ajiyar zuciya tace”Allah ya sa mu dace”
“Ameen”Khadija ta yi ta fara yiwa Yassir wanda ta karb’a wasa shi kuma yana dariya.
“D’azu dai Daddy ya kori mallan lawal,ai dama na gaya miki yadda ya sakawa Yaron nan k’ahon zuk’a ba zai barshi ba.”
Shiruu Khadija ta yi kafin tace”yanzu kenan ta tabbata Daddy zargin na yake yi?”
“Ba zarginki yake yi ba Khadija masifar kishi ne kawai,ke dai ki yi ta addu’a sannan kamar yadda kika fad’a wata rana sai labari..
Ki yi ta sallar dare kina gayawa Ubangiji na san kina yi amma ki k’ara,jikina yana bani inshaaAllah yana dawowa daga Abuja za ku shirya komai ya zama labari…”
A hankali Khadija tace”Au ya tafi?”.
Jin jina kai Mommy ta yi kafin tace”bai yi miki sallama ba?”
Sai kuma ta kawar da zancen tace”bari in je in had’o y’an kud’ad’e in bawa mallan lawal,Yaron yana bani tausayi wallahi bashi da kowa fa maraya ne gaba da baya.”
Tana gama fad’in haka ta mik’e ta bar mata Yassir ta nufi k’ofa tana cewa “bari na je na d’auko.”
Daga haka ta fice….