← Book details Munnubiya Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 53 OF 137

Sashe 53

Munnubiya Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read

daga haka ya sa kai shima ya nufi cikin parlourn
A main parlourn gidan suka samu Mommy Baba larai Ya’isha da Kausar a zaune suna magana da alama mai mahimmanci ce,sallamarsu su ce ta sanya sukayi sauri duk suka d’ago suka zuba musu ido….tashi d’aya yanayin fuskar Ya’isha ya sauya ganin Yashjub d’in ne ma ya ruk’o wa Manubiya jaka.
Da sauri ita kuma Kausar ta mik’e ta wuce sama
Yayinda baba larai ta mik’e ta fara cewa “Lale marhababiki Amarya surukar mu
Yashjub bismillah mana k’araso!ku shigo ciki ya ka barta nan bakin k’ofa a tsaye”
Ta fad’i hakan tana nufar su tana Isa ta kamo hannun Manubiya ta zare a cikin na Yashjub ta ja ta suka nufi cikin parlourn.
Dakyar Manubiya ta iya janye idanuwanta a kan Baba larai
sarai ta shaida ta itace suka ce sai ta d’urk’usa sannan duk wani mai hankali yana kallon fuskarta tashi d’aya zai shaida ba farin ciki takeyi da auren ba,amma kalli yau itace kamar zata cinye ta! tabbas waennan shaid’anu ne wato idan a gaban Yashjub ne ba za su nuna mata k’iyayya ba kenna dan ta lura da Yasira ma d’azu saida ta bari babu Yashjub a wajen tukunna ta gaggaya mata maganganu.
A gefen Mommy daff da ita Baba larai ta zaunar da Manubiya kafin tace”bari in je in kawo muku ruwa,sannu Amarya lalle marhaba”
Ta fad’i hakan tana wucewa da sauri har da d’an yin tuntub’e. Yashjub ne ya d’an tsani da ita ya sanar da ita batun kayan zak’’i dan haka ta karb’i makullin motarsa tace bari ta nuna su gwaggo su kwasa su saka a kitchen.

A hankali Ya’isha ta mik’e kamar ba itace ta baro gidan d’azu tana fushi ba ta k’arasa wajen Yash tace “kawo jakar ni in rik’e mata”
Ta fad’i hakan tana mai amsar jakar.

Tashi d’aya kawai sai ya ji kunyar Mommy ta kama sa dan haka ya cika mata jakar ya k’arasa inda Mommyn take ya zauna a gefen ta dai dai nan su Yassira ma suka fara sauk’owa da alamar Kausar ce ta gaya musu Yash d’in ya zo,tare suka sauk’o gaba d’ayansu har da Daddy da alamun tare suke da shi a saman,shi Yashjub ma bai yi tunanin Daddyn yana nan ba ya d’auka yana office duba da yadda shi baya nan Yasira ma ya ga yau ba ta je ba.

A hankali Manubiya wadda tun d’azu ta ke jin nauyin zama a kusa da Mommy ta d’an sullub’o daga kan kujerar tace “Mommy Ina wuni”

Saida Mommy ta yi namijin k’ok’ari dagasken gaske tukunna ta iya dafa kanta a hankali tace “lafiya y’ar albarka ya bak’unta”
“Alhamdulillah”tace a ranta tanajin wani sanyi dan yadda Mommyn ta yi mata ta ji dad’i sosai ta fahimci itan tana sonta ba kamar su Yassira ba..ta san dama zuwa d’auko ta da kai lefe ba hurumin Mommy bane amma da aka d’aukota tace “a wuce da ita ba sai ta zo ta gaida ita ba!” da kuma yadda take kiranta a waya amma ba ta amsawa ya sa ta d’an ji tsoro ta shiga damuwa da tunani..

Muryar Daddy ce ta katseta jin yana cewa”Manubiya mik’e ki zauna a kan kujera mana,tashi
kinji”

Murmushi ta yi sai da Yashjub wanda shima yaketa zuba murmushi dan ba kad’an ba ya ji dad’in yadda iyayen nasa suka nuna kulawar su ga matar tasa,tukunna a hankali ya d’an sunkuya ya kalli Manu yace “mik’e ki zauna mana
Daddy yana magana”
Tukunna ta mik’e ta zauna a kusa da Mommy inda take tun farko tanajin wani nauyi da girmanta yana ratsa ta,dai dai nan su Daddy suka k’araso suka zazzauna,shima saida ta durk’usa har k’asa tukunna ta gaidashi ya amsa da kulawa.
Da sauri yace”Ummi bata sauk’o ba Yassira jeki ki kirata”
sai kuma ya zaro waya yace “Bari in kirata”ya fad’i hakan yana dialing number Ummi,ba ta dad’e tana ringing ba ta d’auka.
Tana d’auka yace “ki zo munyi bak’i”daga haka ya katse kiran yana mai tambayar Manubiya “ya bak’un ta”
Cike da girmamawa da kunya suke amsa shi.
Suna a haka Munirat suka sauk’o ita da Ummi.
Da sauri Munirat ta k’arasa ta je ta zauna a kusa da Manubiya tana “oyoyo antyn mu ashe kune Ina wuni”
sai kuma ta kalli Yash ta gaidashi.
Kamar yadda Manubiya ta yiwa Mommy da Daddy haka ta zamo ta gaida Ummi itama,
ta kuwa ji dad’i dan haka ta shiga tambayar ta ya sabon waje ya su Innarta…. mik’ewa Yash ya yi yace”Bara mu lek’a Yahanasu,ya jikin nata?.”
Da sauri Mommy tace”da sauk’i!.Munirat ta kai Manubiya wajen Yahanasu kai kuma ka zauna munada magana da kai!”
Shiruu ya d’anyi da sam bai ji dad’i ba ya san Manubiya zataga kamar an ware ta ne…
Yana cikin wannan tunanin suka mik’e ita da Munirat suka nufi d’akin Yahansu jiki ba kwari.

Lumshe ido Yashjub ya yi har suke shige bai bud’e ba..
Muryar Daddy ne ya dawo da shi daga duniyar tunanin da ya lula jin yana cewa”Yash,mai ya faru yau ka koro k’annen ka daga zuwan su na farko?”

Da sauri ya bud’e idanuwansa ya kallesa sai kuma yayi kan Yassira a zuciye.
Da sauri Mommy ta mik’e ta tsaya a gaban Yasirar tace”ai ni za ka daka ba ita ba!tunda nice nan na gayawa Daddyn naku ba ita ba!”

Ummi ba ta san kan labarin ba
ba kuma ta san abunda ya faru ba amman tashi d’aya ta fahimci laifin su Yassira ne…baya ga haka saboda Allah ta ya Daddy zai biyewa Mommy a zuwan Yashjub da Manubiya na farko gida a fara da case!
Su da ya kamata ace sun saka su a gaba sun yi musu fad’a da nasiha sannan sun yi k’ok’ari wajen basu chance su fahimci juna amman kalli yadda tun farko aka sallami Manubiya akace a rakata d’akin Yahanasu saboda Allah wanne irin rashin lissafi ne wannan?,ya suke tunanin Yarinyar za ta ji saboda Allah…..
Ta san inhar ta zauna to tabbas za a yi fad’a da ita
shiyasa ta mik’e tace
‘’Am Daddy bara in d’an baku guri dan Allah”tana gama fad’in haka ta wuce sama bata yadda ta kuma had’a ido da Daddyn ba….sai da ta had’a da sauk’ar AlK’urani da addu’o’i tukunna ta daina jin matsananciyar tsanar sa,haka kurum ta samu sun shirya shima ya daina fushi da ita da kyar !
ba ta ga dalilin da zai sa ta zauna a wajen da zata fad’i abunda zai ji haushi su yi fad’a su sake komawa ruwa ba.

“Ta fi Nono fari”Mommy tace a cikin zuciyar ta kafin ta maida hankalin ta ga Yashjub wanda ya ke cewa Yassira da ta b’oye a bayan ta “k’ara ta kika kawo?
ke ba ki fad’i abunda kuka yi ba?”
Cikin tarar numfashin sa Daddy yace
‘’Mai sukayi?’’

Tun kafin Yash yayi magana
Ya’isha tace
‘’Wallahi Daddy bamuyi komai ba,dama tun da mukaje ta tare hanya ta hanamu wucewa sai da ya zo tukunna ta matsa.
Ina ga yanayin fuskar ta ya kalla dan tanata faman kumbure kumbure shine ya kira Yasira ya ce ta kwashemu mu tafi’’

Wani irin takaici ne ya lullub’e Yashjub wanda ya sa ya ji kamar ya finciko Ya’isha daga kusa da Daddy ya feffella mata mari…ya godewa Allah da ba a kusa da shi take ba dan ya san yau da sai ya illatata!
Ganin Yaran suna neman haukatasa ne yasa ya koma ya zauna ya dafe kansa da ya fara sara masa.

Gyaran murya Daddy ya yi kafin yace”Yashjub!!tun wanchan ranar a asibiti na fad’a maka kar ka bada k’ofar da matar ka za ta raina y’an uwanka!and again a washegarin ranar da ka yi aure ma sai da na rok’ek’a da kaina akan kar ka bada k’ofar da kawunan ku zai rabu a ta dalilinta amman naga that’s exactly what you are trying to do. Sam!ban ga dalilin da zai sanya dan ka yi aure ka tsame y’an uwanka a jikin ka ba ba zai yiu ba ba zan zauna in zuba ido zumuncin ku ya tarwatse ba saboda rashin tunanin ka da kuma gigin giyar soyayyar da ka kurb’a.”

Yashjub ji yayi kamar ya d’aura hannu aka yayi ta faman zunduma ihu…ta ya Daddy zai biyewa waennan Yaran ya hau kan maganganunsu ya zauna daram sannan ji fa tone d’insa sai kace na mace yana magana kamar ta mata
yanzu wannan d’an k’ank’anin abun har ya kai a titsiyesa a gaban su haka…….

Muryar Daddy ce ta katsesa jin yana cewa”ina sauraron ka,
ka fad’amin exactly abunda ya faru.
Ku kuma”
yayi maganar referring to su Yassira yace”kar in ji bakin ku
har ya gama magana.”

Wato dai a gaban Yaran nan za a yi masa haka!alk’alanci kenan Daddy zai yi musu shi da k’annen sa….

“Ina jin ka mana!”
Ya ji muryar Daddyn a d’an zafafe.

A hankali ya d’ago ya kalli Daddyn yace”Ba su kula ta ba.
Kaff cikin su saida na yi magana tukunna Yadira ta gaida ita‘’

Da takaici Mommy tace
“Saboda ba su gaida matar ka ba shine ka koro su daga gidan ka??’’

Cikin son fahimtar da ita yace
‘’Mommy saboda sun rainani kuma sun ki su yi abunda nace a gabanta sun nuna min ban Isa ba shiyasa na koro su
Baya ga haka Mommy taya za su je har gidan ta su k’i su kulata sannan kuma ni da kaina in ce su yi su k’i yi
Maatata ce fa!’’
Ai ko da ace ba za su gaida ita ba da ko ‘Hi’ ya kamata su ce mata…..”

Cikin tarar numfashin sa Ya’isha tace
‘’Daddy cewa ya yi duk sai mun gaida ita har Yasira da Kausar,kuma fa ita ma bata kula mu ba how yake expecting mu mu gaida ita?.”

Throw pillow Daddy ya jefawa Ya’isha cikin fad’a yace
“Ba na ce bana son jin bakin kowa ba?”
Chapter 53 · 0% Book details