← Book details Munnubiya Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 17 OF 137

Sashe 17

Munnubiya Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Sai chan dare tukunna suka d’auki hanyar gida bayan ya loda na lodawa ya kira wani driver d’insa ya yi assigning an tafi kai kayan da za a kai gidan amarya…ta gaji lik’is dan haka ta na gishingid’ewa bacci ya kwasheta.
Ahankali ya d’an tab’o Muhsin wanda suke ta hira da drivern dan har sun saba sosai kamar wasu sa’anni,sai da ya juyo tukunna Yash ya d’aura yatsarshi akan bakin sa alamun su yi shiru kar su tasheta,jinjina kai Muhsin yayi ya juya yana murmushi bai gama sanin meye so ba amman yana jin dad’in yadda ya Yash ya damu da Addar su,shima drivern ya gani kuma ya fahimci mai Yash yake nufi shiyasa ya yi shiruu ya bada himma a tuk’in da yake yi.

A hankali kamar mai shirin d’aukar cracked egg haka Yash ya d’auki wata suite d’insa dake a cikin jakar kujerar driver ta baya ya d’an matsa kusa da ita kad’an ya lullub’a mata dan ya lura ba ta son sanyin.

Manu bata da nauyin bacci
shiyasa yana rufa mata ta farka amma ba ta bud’e idanunta ba…ta ji dad’i a ranta,duba da yadda yanzun suka gama fad’a kuma yayi fushi da ita amma kalli yadda yake kula da ita,ba ta son yin fad’a da shi amma ta lura idan ba hakan ta yi masa ba to ba zai hak’ura ba ba zai bar maganar ba!. Saboda Allah ta ya dan su Baba sun aura masa ita sai kuma kawai aga sun kwashe kaya su koma gidan da ya ce ya basu,a ganinta hakan ba dacewa bane ba,ta san sun zama family amman kuma idan suka yi haka ai sun sake da yawa,idan ma zai basu gida gaskiya ba yanzu ba besides ta san ma Baba ba zai tab’a yarda ba…

Tana wannan tunanin ta ji an yi
parking an kashe motar,ta na ji Muhsin ya yi musu sai da safe da godiya ya jidi laidojin gabansh ya fita dan haka ta yi saurin bud’e idanunta dan ta lura ba shi da niyyar tashinta,dai dai nan drivern ma ya fita kenan..da sauri tace’’mun gode sai da safe daga haka ta fara kokawa da shegiyar handle d’in da ta rasa dalilinta na k’in bud’uwa a koda yaushe idan ta ja.
Murmushi ya yi kafin yace’’kar mu rabu muna fad’a mana,ai tunda kin nuna bakyaso ba zan sake yin maganar ba,amma ki yi tunani akai pls’’

Jin jina kai kawai tayi ta ci gaba da k’ok’arin bud’ewa

Murmushi ya yi yace’’ba fa za a bud’e k’ofar nan ba sai kin yi min murmushi.’’
Jin tayi shiru yasanya cikin wata kalar kasalalliyar murya ya ce’’kin san Allah zan yi miki cakulkuli’’

Sai da ta zabura sosai kamar ya riga ya yi mata cakulkulin tukunna ta juyo kamar za ta fashe da kuka tace’’dan Allah ka yi hak’uri,dare fa ya yi ka bud’e min’’

Ganin yadda ta fara fita a haiyyacintane ya sanya ya fahimci kad’aicewar nasu ne ba ta so,dan haka tashi d’aya ya sa hannu ta gaba ya bud’e mata sannsn ya bud’e tashi k’ofar ya fice da niyyar za gaya wa domin ya bud’e mata amman tuni ta yi wuff ta fice dai dai shikuma ya zagayo,tashi d’aya ya ji ta sauk’e wata nannuyar ajiyar zuciya kamar wadda ta yi
y’ar tsere,murmushi kawai ya yi yana mamakin yadda daga sun zauna a mota iya su biyu duk ta bi ta gigice a ranshi yace’’Yarinya za ki yi bayani ne’’.

Duk taurin kanta kuwa sai da ta yi masa murmushin nan tukunna ya kyaleta.

Da shi da ita da driver suka yi jidon ragowar siyayyar da ya yi mata har soro ya ajjiye mata
yana sake mamakin gidan tukunna ya bata wata jaka mai d’an karen kyau yace”invitation ne a ciki ta bawa su Baba zai turo mata na waya ma sai ta tuttura shi kam ba wanda bai riga ya turama a cikin friends d’insa ba”
Karb’a ta yi tana mamakin zumud’i irin na Yash kafin yayi mata sallama
suka rabu yana jin kamar ya d’auke ta su koma.
Tabbas inda ace irin wata d’aya d’in nan aka saka aurensa da Manubiya tou da sai ya bai san ya zai yi ba kafin ta zo….wata kalar zazzafar k’aunace ta ke d’awainiya da shi the more yana getting to know her the more k’aunar ta take sake dagargaza mishi lisaafi! tunani! da zuciya…..

Sai da ta zo shiga kuma tukunna ta fara fara kame kame,ba k’aramin dad’i ta ji ba da bata ga Baba a d’akin ba,amma dukda haka sai da ta d’anji nauyi dan kasa had’a
Ido ta yi da inna illa kawai sai
taje ta durk’usa ta gaida ita daganan ta cewa Jidda ta zo ta tayata d’aukar kaya dan Muhsin yana shigowa ya fad’a toilet.
Ahanya take tambayar Jidda ko su Baba sun yi fad’an daren da ta yi amman sai ta ji jiddan tace mata a’a besides ai ba ta yi dare sosai ba.
Sai a sannan ta sake,su ka kwashi kayan suka kai ciki.

Sai da Jidda ta je ta kira Siyama tukunna hankalinta ya kwanta,tare suka ware ledojin da komai,ita Manubiya sai da suka ware ma tukunna ta ga gift d’in Muhsin(agogo mai tsananin kyau na maza)da wayar da ya saka mata ba tare da saninta ba
iPhone mai kyau k’irar wadda ake yayi,shiyasa a take ta kirasa domin ta yi masa godiya har ga Allah gaba d’aya Yash ya sa ta fara jin wani iri dan gaskiya ita dai hidimar ta yi yawa..tana fara masa godiya kuwa ya chanza topic d’in dan dama yace mata ta daina yi masa godiya ba ya so!ba k’aramin dariya ya bata ba da ta ji yace’’ta je aiki,ta na da report’’
da farko ta d’auka da wasa yake yi sai da taga ya dage tukunna ta tabbatar da gaske yake yi.
Aikuwa sai da ta yi da gaske tace’’ga skul da za su koma soon dan ba’a ba su wani hutu mai tsayi ba ga kuma hidimar biki dan Allah ya yi hak’uri ya bari ta tura masa kawai’’
tukunna da kyar ta samu ta shawo kansa ta lallab’asa ya d’aga mata k’afa amman da cewa ya yi sai ta je.

Daga nan ta ji ya yi shiruu kamar mai tunanin wani abun dan haka ta shiga tambayar sa menene,sai da k’irjin ta ya buga da ta ji yace‘’Abbakar ya tab’a cewa yana son ki ne??’’
Sai da ya sake cewa’’umm???’’
Tukunna da iyaka gaskiyarta tace’’A’a”

Numfashi ya fesar kafin yace’’can I ask you a favor???”

Ahankali ta samu da kyar tace’’sure!anything’’saboda yadda ta ji tashi d’aya muryarshi ta chanja sannan ranshi ya b’aci.

Cikin katse mata tunani ta ji
yace’’ko gaisawa ba na so ki sake yi da shi”

Sai da ya sake cewa”am I asking for too much?”tukunna ahankali tace”A’a”sai kuma tace”ba ma ya yi min magana fa,ya daina kulani”cikin tarar numfashinta yace”saboda kishi ne ai yasa ya daina yi miki magana saboda ya ji an fara maganar aurenmu yanzu kuma ya ga za’a koma skul shine ya je ya karb’i transfer,yanzunnan Najeeb yake gayamin ya samu transfer,bakiga kalar wahala da kud’in da ya kashe ba amman haka ya bi a gaggauce ya yi transfer”

Shiruuu Manubiya ta yi tana jin wani takaicin Abbakar yana taso mata a tunaninta da kuma ganinta sam alk’awari bai ce haka ba wato
ma gudun ta yake,a ranta tace”idan ma wani abun na yi mishi ai kamata ya yi ya neme ni da zancen mu sasanta bawai ya yi irin wannan abu haka ba’’ dan ita kwata kwata ba ta yarda da maganar Yash da ya ce “saboda kishi ne ya sanya shi ya yi transfer ba….”

Cikin son kawar da zancen Abbakar d’in Manubiya ta sako wata hirar dan ya b’ata mata rai ba kad’an ba,da
kyar kuwa ta samu mood d’in Yash ya chanja har yake bata labarin “ai Najeeb ma ya samu wani zazzafan appointment zai bar skul d’in”,ta kuwa yi murna sosai dan ko ba komai sir Najeeb ya taka muhimmiyar rawa a rayuwarta…..

Sai da Manu ta tabbatar Yash ya huce sosai tukunna suka yiwa juna sallama,kamar za su cinye juna don so haka nan su ka yi sallama ko wannen su cikin tsananin so da shauk’in d’an uwansa.

Tana gamawa su Siyama suka tisa ta a gaba da tsokana abun mamaki har da Muhsin,ita sai a lokacin ma ta fara data sanin yin wayar a gaban su.

Sai da Baba ya zo ta nuna mishi komai ya sanya albarka bayan ya gama fad’an hidimar ta yi yawa tukunna suka b’are wayar aka jonata a chargi

Dan jidda tace”tayi maza ta kwashe important abubuwa ta cire layinta a tshohuwar wayar ta bata dan ta ma riga ta zama tata……

Har k’ofar side d’in su Siyama suka rakata dan lokacin da ta zo tafiya dare yayi sosai,tukunna suka koma nasu d’akin..

Yashjub yana gama waya da Manu dai dai ya shiga bedroom d’inshi kenan kiran Daddy ya shigo wayarsa,yana d’auka ya ji muryar Daddy yana cewa”ka zo parlour na,Hajiya Maama na son magana da kai”

Yadda Yashjub ya ji murya Daddy dama sai da gabansa ya yanke ya fad’i shiyasa ko wanka ya gagara yi tashi d’aya ya juya ya nufi side d’in Daddyn yana jin yadda k’irjinsa ya ke bugawa akai akai.

A zaune ya same ta ita da Daddy da Ummi da mom da Abhi.
Sai da ya gaishesu one by one suka amsa tukunna ya nemi guri ya zauna.
Yana zama Hajiya Mama ta yi gyaran murya tukunna cikin lallashi tace”Yash! da ni da iyayenka gasunan mun yanke shawarar za’a d’aga bikinka za’a k’ara wata uku a kai sakamokon matsalar gocewar k’ashi da ka samu kar ka yi gaggawa ka bi komai a hankali a je a samu a duba ka sosai dan a gaskiya ban gama yarda da gyaran da suka yi maka a nan ba,ka yi hak’uri ka bari a d’aga bikin,lafiyar ka ta fi komai ka warke garau tukunna sai a yi komai cikin nutsuwa da kwanciyan hankali ka ji d’an albarka”
Hajiya Mama ta k’arashe maganar cikin tsananin lallami.
Chapter 17 · 0% Book details