← Book details Munnubiya Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 136 OF 137

Sashe 136

Munnubiya Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Mik’ewa tsaye suma su Manu suka yi ita da Huda dan mutane sun fara hayaniya da guje guje kowa ya nufi k’ofa…
Da gudu Kausar ta je ta karb’e Jaririn daga Hannunsu ta fashe da wani irin kuka…
babban sojan da aka zo da shi ne ya d’auki mike ya yi harbi sama yace kowa ya zauna wanda hakan ne ya nutsar da mutanen wajen…maid d’in da suka kama da Yaron ya saka aka kawo masa gaban hall d’in itama..dalla dalla yayi musu bayani akan cewa”satar sark’a aka yiwa ogar su matar da suke gadin ta to kuma suna shirin shigowa ne suka kama wannan maid d’in da jaririn zata fita da shi a buhu…tace musu sakata aka yi aka bata mak’udan kud’ade,dan haka kowa ya zauna za ta nuna wadda ta turota!!”

Ko da wasa sam Manubiya ba ta yi tunanin ita zata nuna ba…a cikin zuciyarta tanata alhinin rashin imani irin na masu satar yara….
Kawai tana k’ok’arin zama kwatsam tana d’agowa taga maid d’in ta yi pointing saitin ta!!
A rikice ta juya ta kalli gefe da gefenta amma babu kowa ita d’ince dai….Bata Ida fita daga shock ba mutumin ya nufota gadan gadan har da ankwarsa……

Aslam ne kad’ai ya rage zuwa wannan lokacin a cikin Abokan Yash bai tafi ba dan ragowar k’uluwa suka yi da attitude d’in Yash d’in kawai suka yi masa sallama da barka suka wuce!ya k’i dariya ya k’i basu baby su gani ya k’i tsayawa a yi hoto,sannan gaba d’ayansa a rikice yake kana ganinsa…shiyasa kawai suka basa space suka wuce……..

Da sauri Aslam ya nufi sojojin da Manu dan ya lura Yash bashi da niyyar yin komai!!!
Kawai ya tsaya ne ya k’ame….

Yana zuwa ya warce ankwar ya yar yacewa sojan”Atleast ka yi bincike sosai mana dan kawai ta fad’i abu shikenan sai mu hau kai mu yarda?ka san wacece wannan d’in da kake shirin arresting?”
Da gudu Kausar ta yo kan Manubiya tana kuka wai zata daketa da kyar aka rik’eta aka hanata tab’ata su Mommy suka janyeta aka fita da ita tana cewa”Allah ya isan Yaronta da ta saka mata a cikin buhu wallahi Allah sai ya yi musu hisabi muguwa azzaluma saboda ita bata haihu ba shine zata kashe mata nata!!!”

Ita dai Manu uffan ba ta ce da su ba tunda sojan nan ya nufota da ankwa har kawo yanzu kawai ta k’ame a wajen ta kasa cewa komai!!babu wanda ya fi bata mamaki kamar Yashjub wanda kawai ya tsaya ya kafe su da idanuwa ya gagara cewa komai!!!

Shi kuwa Yash bak’in cikin Kausar ne ya ke jin kamar zai kashesa,bayan jama’ar da ta tattaro ta nunawa duniya d’an nasa ne shine hakan bai yi mata ba sai da ta had’a da wannan makircin!?
Ga kuma Mommy wadda wata zuciyar take ingizasa da kawai ya had’ata da sojoji tunda gasu gatanan watak’il zai ji sauk’in azabtuwar da zuciyarsa takeyi!!
Gashi shaid’an sai sake hasko
masa moment d’in Manu da Abbakar na d’azu yake yi a kwakwalwa da Idanunsa.
Tsabar bala’in da yake a ciki kasa ma motsi ya yi…ga dai Manu da Aslam yana kallo amma kwata kwata ya gaza tab’uka komai ya kasa Isa garesu ko yatsar sa kasa d’agawa ya yi..

Sai da Aslam ya yi da mugun gaske shima ya nuna musu k’arfin iko suka fahimci wayene shi!
Tukunna suka hak’ura bazasu tafi da Manu ba!
Dai dai nan ogar tasu k’awar Kausar tace”to a yi binciken sark’arta tunda an gama case d’in jariri…..
Haka kurum da Manubiya ta juya ta hangi Jakarta chan a yashe wadda bata san ya aka yi ta fad’i ba tashi d’aya jikinta ya bata nan ma an gama k’ulleta ne aikuwa ana fara bincikena jakankuna da akazo kan tata aka duba tashi d’aya akaga dankwaleliyar sarkar k’awar Kausar a ciki….
Suna tamabaya batayi musu ba tace musu “jakarta ce”
Aslam ya san sharri aka yiwa Yarinyar amma kuma duba da yadda mai sark’ar take influencial ya sashi kawai yin shiru dan ya san bata da mafita amma inshaaAllah zai san abunyi…..
Huda tana kuka kamar ranta zai fita itama Manu haka,hakanan suka kaita har office d’insu a motarsu dan Aslam ya nemi alfarmar su bari su kaita da kansu su kuma sun yarda!
Ba wai kukan sharri ko arresting d’inta da akayi manu take yi ba…tana kukan yadda aka wuce da ita ta gaban Yash amma bai ce komai ba bai tab’uka komai ba….
…
Babu yadda Aslam bai yi ba amma duk inda ya zaga ya zagayo sai ya ga ba fa zai iya fitar da Manu ba ga Hudan ta d’aga masa hankali sai kuka take yi,ko magana ma ta kasa yi duk ta gigice……
Shi kansa tausayin Manu d’in ya addabesa kunyar kallon ta ma yakeyi shiyasa kawai yace mata bari ya mayar da Hudan gida(dan zuwa lokacin dare ya yi sosai)
kar ta d’aga hankalinta zai san abunyi….Huda ta so ya barta tare da Manubiya har a san abunyi amma yace mata “A’a su tafi gidan”
Hakanan ta bata kwarin guiwa,daga haka suka fita suka tafi suka barta ita kad’ai a wajen cikin masifa tsoro da tashin hankali dan ma a office aka ajjiye ta ba a cell ba.

Ana tafiya da Manu k’awar Kausar ta yi mata waya ta sanar da ita.
A gate su Mommy suka ajjiye Kausar suka wuce…su kansu Mommy da Kausar d’in sun sha jinin jikinsu dan yadda su Yasira suka had’e rai suka k’i kulasu ya ishi ya sanya su fahimci ba su ji dad’in abun ba….

Tana shirin shiga ita da mai aikin ta da jaririnta kawai ta ji an fincikota ta yi baya kamar zata fad’i sai kuma ya mayar da ita ya buga mata kanta da jikin gate d’in yana huci….suna had’a ido da shi ta kalli mai aikin nata tace”wuce mini ciki da Yaro”
Sai da Yarinyar tagama shiga tukunna ta kallesa tace”Yassir!I wasn’t expecting you!”
Sake matsowa daff da ita ya yi tukunna yace”na ji labarin abunda kika aikata a Yarona saboda baki san ciwon sa ba ko?
Wallahi wallahi Kausar ko da wasa kika sake yunk’urin cutar mini da Yaro to ba zaki sake ganinsa ba! Mahaukaciya kawai!”
Daga haka ya sake bugata da jikin gate d’in har sai da ta yi k’ara tukunna ya juya ya wuce,dan a mugun zuciye yake dama…har yau Daddy ya ma k’i ya sauraresa duk ya bi Abokan Daddyn yace su yi masa magana ya yi laifi ne a shirya su dan Allah amma dukda haka ko saurarensa Daddyn bai yi ba gashi he’s broke!!!
like totally…..
Motarsa tana barin wajen Kausar ta yi tsaki,a ranta tace”na dai kusan ya da kwallan mangoro in huta da k’uda!”
Saboda ta gama shawo kan su grenade ta basu 4 million gobe inshaaAllah za su saki videos d’in Yassir polisawa sojoji dss duk sai sun turamawa….

Yassira ce ta sanar da Yahanasu halin da ake ciki!
Ita kuma Yaha ta sanarwa su Daddy da su Ummi da su Ya Musbah…
Abbakar da Ya Musbah ne suka fara zuwa dan a lokacin suna tare aka kira Ya Musbahn.
Suna shiga suka ganta a zaune ita kad’ai ta yi shiruu ta zabga uban tagumi, waani irin tausayinta ne ya lullub’e Abbakar bai san lokacin da. Hawaye ya zubo masa ba!!

Tana d’agowa da ta gansu kawai sai ta fashe da wani irin kuka ta tashi ta k’arasa ta fad’a jikin ya musbah tana kuka abun tausayi fad’i takeyi”na hak’ura da Ya Yash na hak’uba da shi har abada a gabansa aka tafi da ni amma bai ce komai ba!
Ina sonshi kamar Raina amma wallahi na hak’ura da shi mak’iya ba za su tab’a barinmu tare ba!”

Sosai Abbakar ya ji guilty conscious ya lullub’esa,tunda aka ce masa an kama Manubiya hankalinsa ya tashi dan hakan baya cikin tsarinsu…
A ransa ya shiga cewa”Tabbas ya biyewa sharrin zuciya ya cutar da wadda yakeso da sunan so…
Tabbas Manu bata yi deserving haka daga garesa ba idan ya ajjiye soyayya a gefe ko dan friendship d’insu sam bai kamata ya yi mata haka ba….
What was he even thinking? ta ya akayi ya bari shaid’an ya rinjayi zuciyarsa har haka???
Ta ya ya kasa gane Manubiya ta Yash ce ko da ya aureta zuciyarta ba tasa baceba!ba zai tab’a samunta yadda yake so ba sai dai ya wahalar da kansa da ita ya lalata musu rayuwa da farincikinsu gabad’aya…kallifa yanzu a halin da take a ciki amma cewa takeyi ‘tana son Yash kamar ranta!!!’
How can he be this selfish to the person who stood by him through thick and thin his first sannan kuma last love?!”
Bai yi auni ba kawai ya ji hawaye sun wanke masa fuska da sauri ya juya ya fita zuciya fall danasani!…….

Kusan duk a tare su Anty Umma Baba Daddy Yaahanasu suka isa wajen har da Duputy Governor saurayin Yahanasu wanda tana gaya masa ya taho…ai kuwa yana saka Baki a al’amarin aka saki Manu tare da bata hak’uri…..

Sai a lokacin ne kuma Yash suka zo shi da Aslam wanda ya je ya dadd’akosa a event centre d’in (dan kowa ya watse amma shi ya kasa tafiya,yana inda duka barshi)
bayan ya ajjiye Hudan.
Hakanan Aslam ya gaggaya maasa abunda matar tasa tace…yace masa duk sharri ne gashi gashi Hudan duk ta gaya masa komai ita Kausar ce ta saka d’anta a buhu ita maid d’in bakinsu d’aya sannan jakar Manu babu komai a cikin ta! Huda ta gani.
saka mata sarkar aka yi daga baya yanzu su fara zuwa idan abu yak’i ci yak’i cinyewa sai su je su d’auko Huda ta bada sheda….

Suna zuwa suka tarar an sake ta suna ma shirin tafiya!
Sai a lokacin Yashjub ya ji kamar ya rufe kansa da kansa da duka!!!
Da mugun kyar ya samu ya d’aga k’afafuwansa ya nufe ta yana zuwa dai dai inda take ta juya ta kamo hannun Ya Musbah tace masa”take me home!pls…”
Zai yi magana tace masa”plsss”hawaye suna masu bin k’uncinta
Chapter 136 · 0% Book details