← Book details Munnubiya Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 69 OF 137

Sashe 69

Munnubiya Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read

As far as he knows,su Yasmeen ba za su tab’a yi masa k’arya ba kuma ba za su cutar da shi ko Mannubiya ba…dan ko kwanaki da aka yi ta case yanzu ya fahimci saboda Kausar suka yi ta abubuwa amma yanzu gashi da ya dage da addu’a ai sun shiryu sun dawo saiti dan yadda suke yiwa Manubiya tun zuwansu har kawo yanzu ya ji dad’i kwarai ya fahimci suna sonta yanzu….shiyasa har ga Allah tunda suka ce ‘babu ciki’ya yarda kuma ba ya so ma wani likitan ya zo ya kuma duba ta ya ce ‘babu cikin’ saboda shi kad’ai ya san kalar disappointment d’in da ya ji a lokacin da Yasmeen tace ‘babu cikin’….
ya san kuma a b’angaren Manubiya itama haka ne…..

Da waya Yasmeen ta kira Yusra tace ‘’dan Allah ta duba cikin bed side d’inta na left akwai wata green Leda ta d’auko ta kawo mata
Allurar tsayar da amai ne a ciki da su paracetamol”.

…Already dama sun riga sun gama had’a plan d’insu shiyasa suna gama wayar su Baba larai suka yi sauri suka bawa Yusran ledar allurorin da su Yasira suka je suka siyo,ta karb’a ta sauk’o ta nufi d’akin Yahanasu da shi….

Ita dai Mannubiya ta yi shiruuu tana ta istighfari a cikin ranta dan lokacin da Yasmeen tace ‘bata da ciki!’ kad’an ya rage ba ta yi sab’o ba….haka shima Yashjub ya yi shiruuu ran sa a mugun dagule….yayinda Yasmeen take jin inama akwai wani waje da za ta gudu ta b’uya dan wallahi har ga Allah ba ta son yin allurar! ba ta son ta kashewa Yashjub Baby!,she can’t believe wai yau itace take shirin yin kisan kai,that too Babyn yayanta.!

Suna a haka Yusra ta yi sallama ta shigo ta mik’awa Yasmeen laidar allurorin.
[17/09, 8:03 p.m.] Hauwajidda: MANNUBIYA
(Book 2)
Page 28
Na
Humayrah Bulama

Mikiya Writers Association.

Yahanasu tana fita ta nufi sama side d’in Daddy…dan wallahi sai dai fa a yi ta! a cikin gidan nan amma ba za ta bari Yasmeen ta d’irkawa Mannubiya allura ba tare da an tsaya likitan kwarai ya zo ya dubata ba
Ya za’ayi mace tana irin wannan aman ga jiri ga fever sannan kuma amarya amma tace wani ‘ba ta da ciki!’
Ta san ba ta yi aure ba kuma bata da experience amma tanada shekaru da hankalin da zata iya banbance mace mai ciki da mara ciki.
In banda tsabar rainin wayo a ta ina aka tab’a tabbatr da ciki da rashin sa ba tare da an yi test na jini ko na fitsari ba!…

Ba b’oye b’oye tana zuwa ta cewa Daddy “ga Yasmeen chan za ta yiwa Mannubiya allurar tsaida amai ba tare da ta duba ta ko ta bari Likitan da aka kira ya zo ya dubata ba.”
“Kuma allurar tana da k’arfi sosai!ba a cika son yin ta anyhow ba”.

Shiruu Daddy ya yi kafin ya mik’e ya ce “mu je wajen nasu.”

Kusan a tare Daddy suka k’arasa bakin k’ofar shi da Mommy wadda duk yadda ta so yin fushi ta bar Yasira ta yi dealing da Yasmeen sam ta kasa hak’ura sai da ta sak’k’o a yi komai a gaban idanunta.
Tun ba ma da Yasmeen d’in ta kira Yusra tana cewa ta kawo mata ledar ba dan a lokacin sai da Mommyn tasa Yusra ta tambayeta tace “akwai?”
Ita kuma tace mata ‘yh’kawai ba tare da ta bari su Yashjub d’in sun gane ba.
Shiyasa sam ta gagara sukuni ta sake burkicewa ta sauk’o ta nufi d’akin Yahansun a gigice a hakan ma wai Baaba larai ta ce mata ta nutsu ta yi controlling kanta…

Su Daddy suna shiga itama ta shige
dai dai Yasmeen tana shirin zurmuk’awa Manubiya allura a cinyar hannu.

D’an dakatawa ta yi ta tsaya kawai tana kallon su
Suna had’a ido da Daddy yace
‘’Yasmeen an yi duk wasu gwaje gwaje da suka kamata ne???ku je asibiti a yi test har na jini mana’’
Wani kalar kallo Yassira ta shiga jifan Yahanasu da shi dan ta san ita ta je ta kirawo Daddy.
Mommy kuwa ta fi jin haushin Yasmeen! ji takeyi kamar ta je ta rufe ta da mahaukacin duka dan in da ba ta tsaya delay ba da tuni komai ya kammala.
Sannan yanzu da ta ga sun shigo tun da har ta riga ta kai allurar kan cinyar hannun Manubiyan meye nata na wani tsayawa ta d’ago instead of kawai ta soka ta juye mata ruwan allurar..dama chan ba ta son yi ai shiyasa ta lalata musu komai!…
Har wani duhu duhu take gani tsabar tashin hankali,ganin bakin Yasira take yi yana motsi alamar tana yiwa Daddy magana amman ba ta san ma mai take fad’a ba dan ba ta jin komai tsabar masifar da ta shiga.
Tana k’ok’arin ta bud’e Baki ta san dabarar da za ta yi su samu Daddy ya bari su yi allurar cikin sauk’i ta ji muryar Yash yana cewa
‘’Ok,d’an bani 2 minutes,’’ sai da ta kalle sa tukunna ta fahimci waya yake yi,sai da ya ajjiye wayar tukunna ya kalli Daddy yace‘’Am Daddy family Dr ya zo
Ince ya bari shikenan tun da kace asibiti za’aje ko?’’

‘’No,bar shi ya shigo d’in kawai tun da ya riga ya zo.Ya’isha je ki shigo da shi
Idan ya tafi sai a wuce asibitin,ba dad’i ka kirawo babban mutum ya baro aiki ya zo kuma a ce ya koma.’’

Wata kalar zufar da ta ketowa Mommy sai da Yahanasu ta ganta b’aro b’aro a kan goshinta tsabar yawan ta.

Cikin in ina da rashin sanin tudun dafawa Mommyn tace
‘’Daddy nake ganin gara a ce ya tafi
Namiji ne bai kamata ya tab’a matar aureba….”

“Ya’isha je ki shigo da shi mana!’’
Daddy ya fad’a da d’an k’arfi kamar ma bai san Mommyn tana magana ba dan ya fara k’ulewa da ita
Ya ga alama tana neman zarce gona da iri tun lokacin da ya goya mata baya a kan case d’in Yashjub da su Yasira ya bata goyon baya ita da su Yasira,ya ga alamar kamar so take ya dinga biyeta akan komai….bayan shi ba wai bayan ta ya bi ba ko a wannan lokacin yana da nasa dalilin shiyasa….

Ganin har ya na shirin fita amma su basu da niyyar fita ne ya sa cikin kakkausar murya ya kalle su yace
“A bar Yahanasu Manubiya Yashjub da Yasmeen a d’akin kowa ya fito….jikin Mommy har karkarwa yake yi zuwa yanzu..
ta riga ta san one more move daga gare ta to tsaf Daddy zai b’aro jirginta shiyasa kawai ta hak’ura ta yi kalmar shahada ta fice ta wuce sama d’akin ta direct.

Ita dai Mannubiya ba da ban Daddy ne da kan sa yace ‘a duba ta’ ba to da babu abun da zai sa ta kuma tsayawa a duba ta dan ba ta son ta sake ganin wani disappoint d’in a idananun Yashjub…

Su Daddy suna tsaye a parlourn Ya’isha ta shigo da Doctor,suna gama gaisawa da Daddy ta wuce da Doctor d’in ta kai sa har d’akin ta fito, itama ta nemi guri ta zauna hankalinta chaaa a tashe.

A Chan d’akin kuwa Dr yana shiga suka hau gaisawa da Yashjub sai da ya kuma yi masa Allah ya sanya alkhairi tukunna cikin zolaya yace
‘’Ai ba wani abun tada hankali bane amai is a normal thing a pregnancy but bara dai in duba .”

Shiruu duk suka yi kafin ya fara dubata sai da ya kuma tambayar abubuwan da suke damunta da date na last period d’inta ya ji tukunna ya matsa kusa da ita
Kamar yadda Yasmeen ta ga alamun cikin a tattare da ita hakanan shima amma bai fad’a musu ba
Instead sai ya zaro pt a cikin box d’insa ya basu yace “gashi ta je ta gwada”

Cikin son fahimtar da shi Yashjub yace “Yasmeen fa ta duba ta yanzu ba ciki ba ne”

Da d’an mamaki Dr d’in ya juya ya kalli Yasmeen kafin yace “da me kika duba ta??”

Dibi dibi ta hau yi kafin tace ‘’ban ji a pulse d’inta ba sannan na ga bp d’inta bai yi kamar na masu ciki ba”
ta fad’i hakan tana addu’ar Allah ya sa kar ya haddasa mata case.
Sai da ya k’ura mata ido sosai
kafin cikin d’an b’acin rai yace ‘’Doctor Yasmeen kin san abun da kike yi kuwa??a bp da pulse dama ake ganin ciki???
What else ki ka yi bayan BP d’in da kika gwada??”.
Cikin nemawa kanta mafita tace
‘’Duk na gigice ne na ga tanata amai I wasn’t myself shiyasa..gaba d’aya duk ta bani tausayi…”

Cikin fushi yace
‘’Really??!,yanzu idan aka kawo miki family member d’in ki in a critical condition Ashe ba za ki iya yin abun da ya kamata ba?are u really this weak!!!”

Ahankali Manubiya ta d’an dafe kanta sakamokon sarawar da yake yi mata tace “wash!!!”
Sai da ya gama watsawa Yasmeen kallo tukunna ya juya ga su Yashjub ya shiga yi musu bayanin yadda za su yi amfani da pt d’in.
Suna wucewa cikin toilet d’in ya juya ga Yasmeen ya shiga yi mata fad’a had’e da yi mata nuni da abubuwan da ya kamata ta fara yi next time idan an kawo mata patient a irin wannan condition d’in Sannan yace ta cire fargaba ta daina saurin giigicewe dan za ta jawa kanta problem dan ko shi tbh yau kam he is very disappointed in her!”

Su Yashjub suna shiga toilet d’in Manubiya ta kalle sa tace
‘’Ko dai za mu ce masa mun yi kawai?
Ba na son gwadawa ni kam har ga Allah.’’
Ta fad’i hakan tana hard’e hannuwanta a k’irji.

A hankali Yashjub wanda ya samu hope da kwarin guiwa daga jin yadda Doctor d’in yace “Yasmeen ba ta gwada yadda ya kamata ba”ya matso kusa da ita yace
“Ki taimaka ki gwada! pls…for me?’’

Shiruu ta yi ta d’an sunkuyar da kanta k’asa tace “to ka fita”

Wata dariya yayi yace “Yarinya ba ki da wayo ashe….”
Chapter 69 · 0% Book details