← Book details Munnubiya Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 35 OF 137

Sashe 35

Munnubiya Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read

“Haka ka yiwa taka kenan??”
Yashjub ya yi masa tambayar ba tare da ya kalle sa ba dan
zuwa yanzu hanakalinsa ya tafi kan y’an yatsun ta da take
wasa da vail d’inta da su,tun ranar da ya rik’e mata hannu a office d’insa yake muradin ranar da zai sake samu ya rik’e,shiyasa without thinking twice ya ruk’o hannun nata cikin nasa duka biyu.
A tare duk su biyun suka sauk’e ajiyar zuciya wanda duk sai da sukaji sai kuma ta yi sauri ta sunkuyar da kanta k’asa….jin shiru ba a fara d’aukar hotunan bane yasanya Yash ya d’ago dakyar ya zubawa me hoton lumsassun idanuwansa.

Najeeb ya kalla wanda ya ce masa” ka d’auke su a hakan mana” tukunna ya matsa ya fara saita camera…..wajen kalar biyar zuwa shida aka yi musu,shikam me hoto yau ya ga amarya mai lullub’i.
Sai da aka gama yi musu su biyu tukunna su Jidda ma suka shiga, Yassir kuwa har da zama kusa da ita,aka yi musu su uku…wanda zaman da yayi a kusa da itan saida ya sanya Yashjub ya ji kamar ana zare masa numfashi. Najeeb kam ya san halin kayansa shiyasa ya tsaya a tsaye a gefenshi akayi musu.

Zuwa yanzu hatta masu hoton sun lura da yadda Najeeb yake kallon Siyama wadda gaba d’aya take a takure da shi shi kuwa sai wani nan nan yake da ita abun har mamaki ma yake bata…shiyasa ita da Jidda harma Aisha suka d’an fara fahimtar inda mutumin ya dosa .

Masu hoto suna fita Aisha tace
“Yauwa mu zamu wuce,muna d’an sauri akwai kayan jere da za mu kai gidan nata”

Da mamaki Yashjub ya d’an d’ago ya kalle ta kafin yace”ai all the rooms are full”
Sai kuma ya kalli Manubiya yad’an matsa hannunta dake a cikin hannayensa har yanzu kafin yace”Baby ba mun riga mun gama shirya komai dake ba?me ya kawo zancen kaya kuma??”
Yayi mata tambayar yana murza hannunta dake a cikin nashi.

Itakam Manubiya kasa ma cewa komai ta yi dan yadda yake yi mata da hannu gaba d’aya ya burkita mata lissafi shiyasa duk yadda ta so sai ta gagara cewa komai.

Wani shu’umin murmushi Yashjub ya yi mai had’e da dariya kafin ya sake cewa”
Babyn Yashjub,kin yi shiru….”

Dariya Sir Najeeb yayi kafin yace”Keys d’in suna hannu na,za mu iya barinka anan ko??”

“Yeah,”
kawai yace ba tare da ya kalleshiba dan har yanzu idanunsa suna kan Manu yana murmushi sannan yak’i ya daina murza hannunta.
Sai da Najeeb ya sake sakin murmushi tukunna ya kalli Siyama yace “muje za a san inda za a saka kayan”

“Dagaske Najeeb ba waje ka sani kuma”
Yashjub d’in ya fad’a still ba tare da ya kallesa ba.

Cikin sigar zolaya Aisha tace
“kai dai ka ji da amarya ka barmu da jere”

“Yauwa abunda nima zan fad’a kenan”
Siyama tace hakan tana d’an dariya.
Murmushi Najeeb yayi kafin yace “Ashe kin iya magana”
Ya fad’i hakan yana kallonta
wanda ya sa ta d’an ji kunya.

Yashjub ya yi tunanin Yassir zai zauna da shi amman sai ya ga shima ya mik’e yana cewa”bari mu je gidan,sai anjima”
“Okay”kawai Yashjub yace
a ranshi yana aiyyana
“In dai har Yassir ya nuna yana son d’aya a cikin yaran nan
InshaaAllah zai tsaya mishi yaga ya aura”dan ya lura da yadda suka nutsar da shi a cikin awa d’aya kacal. Yasan tunda har so ya chanja sa ya maida shi mutum mai walwala raha da dariya to ya yi imanin inshaaAllah so zai iya chanja Yassir shima ya nutsar da shi ya shiryar da shi.

Yash bai ma san sun fita ba sai da ya ga d’akin ya k’ara haske tukunna.
A hankali ya d’an cika hannunta ya kamo k’asan vail din ya d’aga shi sama,ko a kan kafad’unta bai bar sa ba sai da ya kai chan k’asa tukunna ya ajjiye shi akan kujerar kawai
ya shiga kallonta.

Ahankali tana mai jinta duk a takure ta d’an juyo ta kallesa kad’an…..d’inkin babbar riga ne a jikinshi na wani irin yadin da bata tab’a ganin irin sa ba tunda take a rayuwarta.
Yanayin kwalliyar d’inkin anyi sa ne da bak’in zare mix with white,da d’inkin da yad’in da kwalliyar d’inkin sunyi mugun tafiya da imanin ta…..ba ta san yanayin d’inkin maza da kyawunshiba asalima ba burgeta yakeyiba amman wannan kam ta yi declaring nashi as the best dan ya matukar yi masa kyau,wankan nasa ya bi jiki.
Ya murza bak’ar hula kmr zanna bukar itadai bata san ko akwai hula zanna bukar kuma bak’a ba amma yau ga ta anan,sannan hatta cuff links da agogon sa ma duk bak’ake ne ga kamshin mayataccen turarenshi wanda tun lokacin da ya shigo cikin parlourn
shi ya fara yi mata sallama….kallonshi take yi sam
ta gagara d’auke idanunta a kansa,wani irin kyau kwarjini da haiba ta ga ya k’ara…..ahankali kwakwalwarta ta shiga tariyo mata moments d’insu tun daga farkon had’uwarsu a office d’in sir Najeeb har kawo yanzu da yake zaune a kusa da ita a matsayin mijin aurenta…ahankali ta lumshe idanunta a cikin zuciyarta ta shiga godewa ubangiji dan tabbas idan akwai the most lucky mace a duniya to ta yi crowning kanta above her dan ba kowa bace take samun chance ta auri true love d’inta ko first love amma itakam ta samu,sannan kalli kyan Yash kud’i aji ilimi and everything amma ita ya zab’a ita ya so it’a yakeso ya yi rayuwa da……….

“Na yi kyau har haka ne???”
Muryar Yashjub ta dirarwa dodon kunnuwanta
Wanda shima dakyar ya nemo numfashi da nutsuwarshi ya sakawa gangar jikinsa tun lolacin da ya bud’e fuskar tata…..ta yi wani irin kyau wanda tsayawa fad’a ma b’ata baki ne,tabbas Manubiya itace rayuwarsa shiyasa ya kasa daina tasbihi hamdala da hailala ma Allah subahanahu wata’ala da ya mallaka masa ita a yau.
“Yahayyu ya Kayyum ka bamu tsawon rai mai amfani ka sa mu tsufa tare kasa kar Manubiya ta riga ni mutuwa
dan ban san ya zan yi rayuwa idan babu ita a duniyar nan ba”
Ya yi adduar a cikin ransa yana mai k’are mata kallo!.

Ahankali ya ji tace”Ina wuni…”
Bata samu damar d’aura komai ba sakamokon sallama da shigowar Muhsin a tare hannunsa d’auke da lemuka.

Kunya ce ta kama Yashjub…shi da yake Ango ya zo ya shantake gashi har an kawo masa lemo!shiyasa ya cewa
Muhsin d’in “ya maida shi kam
tafiya ma zai yi.”

Muhsin yana fita ya janyota jikinshi yayi hugging dinta wanda hakan yasa duk sukayi shiru,a hankali dai dai cikin kunnenta yace”Allah ya bamu zaman lafiya” daga haka ya cika ta ya yi kissing forehead d’inta yace”thankyou”
tukunna da kyar ya daddage ya yi kokawa da zuciyarsa ya cikata ya mik’e da sauri dan ya san idan ba da saurin ya mik’e ba tou tabbas sai ya k’ara jan lokaci…….Ahankali yace mata “sai Allah ya kaimu anjima”
Daga haka ya sa kai ya fice.
Allah ya so shi babu mutane sosai dan sai da ya fito tukunna wata sabuwar kunya ta lullub’e shi ya ji kamar ya nutse a wajen.

Earlier (11:45am)
Tun k’arfe goma lokacin da aka sallamo Kausar suka dawo gida gabad’ayansu suka gaza sukuni kamar wasu masu zaman makoki haka suka koma,Kausar kam k’arshema d’aki ta mik’e ta shige ta rufe kanta.
Hankalin Mommy bai sake tashi ba sai da ta kira Daddy ya tabbatar mata da an d’aura auren….tashi d’aya ta gaza nutsuwa k’arshe ma kawai sai ta kama hawaye,ba ta yi tunanin za ta shiga damuwa kamar haka ba,duba da yadda suka hak’ura suka tsara dakatar da komai har sai Manubiyan ta shigo tukunna su d’aura a inda suka tsaya.

Suna zaune a d’akinta itada Baba larai Yassira ta shigo ta same su
Numfashi Yassirar ta fesar kafin ta k’araso ta zauna a kusa da ita tukunna tace “Mommy idan Ina ganin ki a haka za ki sa inje inyi shirme a wajen d’auko yarinyar nan,ku ne kuka ce mu kwantar da hankalinmu amman ganinki a haka gaba d’aya ya na nema ya dawo min da komai sabo.”
“Ta ya kuke so mu yi welcoming d’inta with open arms bayan gashi muna ganin yadda ta zama reason din kukan ki!”

Ajiyar zuciya Baba larai ta sauk’e kafin ta kalli Yassira tace”dan Allah kar ku dawo mana da hannun agogo baya mun riga mun gama magana,yanzu ki bar jan lokaci mu samu mu je mu yi abunda za mu yi a gidan kafin ta tare, na riga na gaya muku idan har ta tare ba’ayi ba to gaskiya akwai matsala!
ki yi sauri ki je ki cewa Yahanasu ta baki makullai da frames d’in da suka siyo ita da ummi a kasuwa za ku had’a ku kai gidan tare da flasks d’in da kuka siya kuma…..na ji d’azu ummin tana ce mata ya kamata a kai a kafa kafin zuwan amaryar,so ki yi sauri ki karb’o…

Saida Yasirar ta fesar da wani bahagon numfashi tukunna tace”okay Baaba”daga haka ta sa kai ta fice.

Sai a sannan Mommy tace”ni kam da kun yi abun nan tun a jiya…
“Ai dole sai a ranar da za ta tare tukunna za’ayi,karki damu ba za a samu matsala ba…..”
Baba larai ta bata amsa.

Ahankali cikin mutuwar jiki tace”kin tabbatar zuwan nata ba zai yi affecting surrukana ba ko?
Sai da Baba larai ta sauk’e numfashi tukunna tace”na gaya miki ai…ita Manubiya tana tafe ne da fad’uwar ki a bayanta,muddin ta zo ta zauna ta yi rayuwa a cikinmu to komai naki sai ya tab’arb’are a hankali a hankali za kiyi ta shiga bala’i kala kala kuma babu ranar farin ciki….amma inshaaAllah da izinin Allah mu kuma ba zamu bata ikon dad’ewa a cikin gidan nan ba ballantana har matsala tafara tasowa…kuma dukda haka still Ina ta add’ua inshaaAllah babu abunda zai taso har ta zo ta tafi.
Zuwan nata ma dan bamu da yadda za mu yi tunda akwai rabon zaman a tsakaninsu..kinga ai yadda akayi ta shan fama amman duk ya tafi a banza,but inshaaAllah na yi miki alk’awari ba za ta yi dogon zango a cikin gidan nan ba.
Ina fatan kin fahimceni???”
Chapter 35 · 0% Book details