← Book details Munnubiya Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 40 OF 137

Sashe 40

Munnubiya Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Da mamaki Siyama ta tsaya kawai tana kallonsa kafin da kyar tace”Are you listening to yourself??”
Bata jira ta ji abunda zai ce ba ta d’aura da cewa”za ka rabu da ita saboda ni??”

Da sauri yace”Yeah” sai kuma ya sake cewa”tun ba yau ba Ina…”
Girgiza kai kawai ta yi cikin katse sa tace”pls………”sai kuma ta runtse idanunta kafin ta kama handle d’in k’ofar tace “zan fita!”

Da sauri yace “You ask for the truth …”

Bud’e idanunta ta yi kamar zata fashe da kuka tace
“Ka bud’e min k’ofa in fita!wai ta ya kake expecting in yi trusting d’inka?ka bar wata saboda ni!ka ga kenan in ka had’u da wata in the future nima ka yi dumping d’ina ban Isa in ce zan ji haushi ba!”

“Ba haka bane abun namu it’s complicated,ki fahimceni dan Allah”

Cikin takaici ta kallesa sosai tace
“Complicated how???”

Tashi d’aya zuwa yanzu Najeeb ya fahimci ya riga da ya jagula komai da hannunsa,ga shi ya lura Siyaman ta zuciya sosai dan idanunta da kan hancinta ya d’an yi jaa!,shiyasa kawai ahankali ya sa hannu a gefen seat d’inshi ya bud’e mata motar,yana shirin
ce mata’ya bud’e’
ya ga ta bud’e ta fice da sauri dan yana dannawa ta gane ya bud’e ne.
A ranta tace baka da abun fad’a ai dole ka bud’e min
Mayaudari kawai…….

Juyawa kawai ya yi ya jingina a jikin kujerar da yake zaune a kai ya yi shiruuu….One thing is for sure ba zai tab’a iya hak’ura da Siyama ba,ko menene zai faru sai dai ya faru amman Siyama belongs to him da izinin Allah. Kawai dai kmr yadda ta fad’a anya ba zai zalinci Ya’isha ba idan ya yi hakan?ga shi shi harga Allah
ba zai tab’a iya auren mata biyu ba tsarinsa na mace d’aya tun farko bayaga haka a yadda yakejin soyayya da k’aunar Siyama 99%da kuma yadda yakejin na Ya’isha da bai wuce 5% ba ya san idan ya had’asu su biyu a matsayin matansa to tabbas akwai matsala dan ya san ba zai tab’a kwatanta adalci ba.
Ko a lokacin da yake tare da Ya’isha shi dai ya san yana sonta amman bai san zafin so
da asalin mene shi so d’in ba
sai a kan Siyama…..

Kaff y’an kawo amarya ba bu wanda bai shiga shock ba dan tun daga gate da compound suka fara ganin ikon Allah….an san dama Mijin yana da kud’i duba da yanayin kud’in
da aka bayar lokacin da aka zo saka rana da kuma lefe
amman sam ba su yi expecting haka ba,dan a kaff cikin su 5% ne kawai suka tab’a sanin akwai Irin gine ginen nan ma a Nigeria,ga furnitures kamar ba za a mutu ba!Tabbas Manubiya ta dandalo arzik’in
dan a kaff area d’in su ba y’ar da ta tab’a dandalowa….Ah lalle kam dole dangin miji suce da durk’usa uwarta kuma ta amince yo idan sune ko kwanciya akace y’ar su ta yi ai sai ta yi wallahi,Irin wannan aljannar duniya haka gida kamar ba a Africa ba…..
Haka nan dai suka dinga mamaki da zancen zuci
waenda ba za su iya dannewa ba kuma suka koma gefe aka shiga tattaunawa.

Tun case d’in Baraka da ya Musbah su Maman Abbakar ba kula su Manubiya sukeyi ba
sai yau!yadda Maman Baraka ta ga Manubiya ta samu duniya ya sa hankalinta ya sake tashi ta kuma bada goyon baya akan y’arta ta koma gidan ya Musbah dan ko banza yanzu kam Musbahu ba shi da nauyi a kansa dan ta san duk Manubiya za ta d’ebe maybe suma su samu su dandala……

Ba a fara barin gidan Manubiya ba sai wajajen 11
na dare…shima kuma sai da
Yash ya kira Najeeb yace
“Idan bai zo sun fara kwasar jama a suna maidawa gida ba wallahi zai shiga gidan da kansa ya ce musu dare yayi”

Tsaff Najeeb ya san Yash zai aikata shiyasa ya mik’e ya dauk’i makullin motarsa ya fice
gaba d’aya gab’ob’in jikinsa na masa ciwo,ga tension da tunanin ta Ina zai fara da Siyama da Ya’isha dan gaba d’aya kansa ya d’aure….
….
Zuwa yanzu gidan ba kowa daga Manubiya Jidda sai Yahanasu da Aisha da Siyama da Munirat….Su Najeeb sun tafi kai wasu a cikin mutanen su dawo.
A tunanin su su za su d’auki su Siyama ma su maida su gida nan kuwa ba su san already
sun cewa su ya Nafi’u in sun gama za su yi musu magana.

Suna zaune gaba d’ayansu
sukaji kmr an shigo parlourn bedroom d’inta,dan haka da sauri Yahanasu ta lek’a,dariya tayi kafin tace”Au Yassir!ashe kai ne ai na yi tunani angon ne”

Bai damu da yadda ta tsaya ta tare k’ofar d’akin ba haka ya kutsa ya fara k’ok’arin shigewa,ganin kmr zai shige jikinta ne yasa ta d’an matsa tana cewa”babu kyau fa shiga d’akin Amarya”.

Sai da idanunsa suka sauk’a akan Jidda da yake ta faman nema tun d’azu ya samu ya d’an nutsu tukunna ya juyo ya d’anyi mata murmushi
kafin yace”Really
Inji wa?”

Ya fad’i hakan yana me maida kwayar idanunsa ga Jidda wadda ta had’e rai ta tamke fuska amman fa a chan k’asan ranta tsorone ya lullub’eta…dan tun d’azu ita kuma take ta k’ok’arin b’uya gudun kar su had’u,yanzu kam tana ganinsa gaba d’aya hankalinta ya tashi!
Sam bata son Yassir,dan idan akwai mutanen da bataso ta gani yanzu Yassir ne Sai su Yassira.

Muryarshi ta tsinkaya kawai yana cewa”Jidda muje
Ko”
Ya fad’i hakan yana kallonta.

‘Dum!!!’
Haka k’irjinta ya bada kafin
a ranta tace
“Lalle wannan mutumin bashi da hankali…yanzu shi har yana tunanin zata iya tsayuwa a k’ark’ashin inuwa d’aya dashi bayan abunda yayi mata talkless of har ta bisa…ta bisa ya k’arasa rungumar da d’azu bai samu access ba kenan…

Yahanasu ce tace”Ai sun kira brother d’insu zai zo ya d’auke su”
Sai da ya d’anyi shiruu kafin
yace”Am..siyan baki za su yi,
Yash yana k’asa,a yadda
na gansa d’innan na san idan ba su yi sauri sun sauk’o k’asa ba to za su yi loosing kud’in siyan bakin…da kyar muka
tsaida shi da ni da Najeeb
kema ku yi sauri ku wuce
ku basa space dan na lura a matse yake..”

Da sauri Yahanasu tace
“A’uzubillahi”
Sai kuma ta kai masa duka.
Kaucewa yayi yana dariya
Idanunsa suna akan Jidda wadda ta runtse idonta
da k’arfi tana mamakin rashin kunya da tsaurin ido irin
na wannan bawan Allah.

Ahankali Munirat ta sunkuyar da kanta k’asa…a ranta tana aiyyana shin decision d’in da ta yanke anya kuwa ta yiwa kanta da rayuwarta adalci kuwa.So take yi kawai wani ya bata go ahead yace ta yiwa Yassir duk abunda yakeso amman daga Ummi har sister d’inta sun kora mata zazzafan warning akan Yassir sun ce ta rabu da shi,sun k’i ma su tsaya su saurareta kuma tun ganinsu tare da Ummi ta yi gaba d’aya sun k’i su sake da ita balle su ji cikinta sosai ta yadda za su fahimce ta…ita kuma gaskiya ba za ta iya rayuwa babu Yassir ba,ga shi ta lura ko ta kanta ma ya daina bi ta san kuma yana samun guri a wajen Jidda shikenan ta ta ta zo k’arshee….
Ba ta Ankara ba ta ji hawaye ya zubo mata da sauri ta yi firgigit ta sake yin k’asa da kanta tukunna ta sa hannun ta goge,sai a sannan ta ji muryar
Yahanasu tana cewa”Munirat ko bacci kika fara ne daga sunkuyar da kan da kika yi yanzun nan?”
Sai da ta d’an gyara fuskarta
da style tukunna ta d’ago tana murmushi tace
“A’a”
Daga haka ta mik’e tsaye tana gyara mayafinta.
Shi Yassir harga Allah sai yanzu ma ya ganeta,shi fa idan ba ganinta ya yi ba wallahi mantawa yakeyi da ita.
Ya san sun had’a ido da ya shigo amman sam hankalinsa ba ya wajen shiyasa ma bai wani fahimci ita d’in ce ba.

Aisha cewa ta yi ba zata je ba haka ma Yahanasu,sai da Yahanasun ta saka baki tukunna da kyar Jidda ta mik’e ta yarda za ta je,ba kad’an ba k’irjin Munirat ya dinga bugawa dan ba ita kad’ai ba Hatta su Aisha sai da suka lura da yadda Yasir ya ke bin Jidda da ido…..babu yadda bai yi a barsa ya ga fuskar amarya ba a cewarsa “ai shima zai iya yaye lullub’in tunda k’anin ango ai ango ne”amman k’iri k’iri Yahanasu ta hanasa….haka nan yana ji yana gani ya hak’ura suka fita,ya so ya ga fuskarta sosai wallahi dama yanzu ne chance d’insa na yau dan ya san Yash ba zai tab’a yarda ya rakosa ba.

Yassir ya so ya d’an wanke kansa a wajen Jidda amma sam ta k’i ta basa chance d’in ya yi mata magana haka ta mak’ale a tsakiyar su Siyama har suka sauk’a.

A k’ofar parlourn chan k’asa dama Najeeb ya tsayar da Yashjub k’iri
k’iri ya hanasa shigowa ko cikin parlourn yace“wallahi yau sai yayi al’ada,gashi ya tusa shi a gaba da tsiya da zolaya…tun Yashjub yana fushi wai ko Najeeb d’in zai hak’ura har ya hak’ura ya d’an fara dariya kad’an kad’an.
A haka su Siyama suka sauk’o suka samesu,sai da ya hangesu tukunna ya bar Yashjub ya shigo ya zauna…

Shiruuu parlourn ya d’auka bayan duk sun zauna, su
Siyama basu tab’a sanin ma yadda ake siyan baki ba,
Munirat kuma tana d’an shakkar Yashjub sannann ga tunanin Yassir shiyasa ta yi shiru.

Tashi d’aya suka fahimci bama su iya siyan bakin ba shiyasa kawia Yassir ya fara dariya k’asa k’asa

Ganin za a rainasu ya sa Siyama ta yi k’arfin halin cewa
“Siyan baki za mu yi”
Murmushi duk sukayi kafin
Najeeb yace “Ai ba ku za ku yi siyan bakin ba mu ne za mu yi,ko??”
Yayi mata tambayar yana murmushi

Nan ma duk shiru sukayi dan dama itace me d’an baki to kuma Najeeb ya sako baki shiyasa ta ja tayi gumm!

Ganin suna b’ata masa lokaci ne ya sanya Yashjub dag’owa ya kalli Munirat yace”Munira bani acc number d’in ki”

Dariya sosai Najeeb da Yassir sukayi.

Cikin nutsuwa ta karanto account number
Yashjub yana shirin turawa
Najeeb ya ce masa” wait mana!ba kaara?bari inyi ai wannan
aikin mu ne ba naka ba..”
Chapter 40 · 0% Book details