Sashe 89
Munnubiya Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Tabbas wannan abu ne mai nauyi na tashin hankali da ya sameta dan za ta iya cewa bata tab’a shiga rikici da k’unci kamar yau ba amma kuma ya zama dole ta bawa mijinta support sannan kamar yadda ya fad’a tabbas so ake yi a raba su,dan haka ita kuma duk rintsi duk wuya ba za ta bud’e k’ofa a shiga a raba su ba…..da izinin Allah.
Wani irin zafi da rikitaccen tashin hankali ta ke jinta a ciki amma ya zame mata dole ta danne kanta ta taushi zuciyarta ta tsaya musu…dan haka cikin sharar hawaye ta sa hannu ta rungumo sa itama kamar yadda ya yi mata tace”I trust you! kuma babu wanda ya Isa ya rabamu ba zan bada k’ofa ba…duk runsti duk wuya ba za mu karaya ba.Abunda ya faru jiya babban al’amari ne amma na dad’e Ina neman tukuicin da zan k’ara maka na k’aunarka tsakaninka da Allah a gareni ban samu ba..
Ya Yash a matsayina na matarka Ina so ka saka a ranka kamar babu abunda ya faru tsakaninka da Kausar ka goge hakan a kwakwalwar ka nima na goge!ina so mu manta da duk wani takaici da bak’in ciki na daren jiya….indai saboda ni ne kake damuwa da fargabar mai zan yi tunani ko mai zan ce a kan case d’in to inaso ka san cewa Manubiya ta goge komai ba ta rik’e a rai ba bata saka a gaba ba babu komai a gabanta sai burin farantawa mijinta dan haka ka cire damuwa ka cire bak’in ciki mu ci gaba da rayuwar mu cikin farin ciki…inshaaAllah da ni da kai har abada ba za a ji kanmu ba.”
Kuka sosai Yash ya ke yi ya k’ank’ameta a jikinsa yana godewa Ubangiji da ya basa mar’atussaliha….ya ma rasa bakin magana in banda sake ruk’umk’umeta babu abunda ya ke yi yana ji kamar ya maida ita cikin cikinsa.
Shiruu Mommy ta yi har sai da Ya’isha tace”hmmm..mu shiga Mommy za ta ci ubanta ne!.”
Tukunna suka d’an gyara daga tsayuwar lab’en da suka yi suka fara knocking.
Gaba d’aya Mommy kanta ya d’au zafi tabbas Manubiya fa sai sun sake tsayuwa a kanta sun k’ara k’arfi fiye da tunani dan tabbas Yarinyar nan ba ta wuce tunani su gashi shegen naci gareta…ita da ta zo ta d’anyi b’arin zance akan case d’in a samu ta ji ta yadda za ta d’aga hankali har sai ta ji komai daga nan su yi baram baram da Yashjub ta tafi sai gashi an samu wani d’an albarka ya tura mana message ma gaba d’aya amma dukda haka ji abunda take cewa!..tana da tabbacin Kausar ce ta turo message d’in! tabbas dama tundaga jiya ta fahimci Kausar is up to something,ta d’an ji zafin yadda ta tsame su daga plans d’inta ta fara yin gaban kanta ita kad’ai amma kuma da wata wainar gara wata!da Manubiya gara ta bi bayan Kausar sau million ma dan haka a nan za ta tsaya!a yadda ta ji furucin Manu na yanzu ta riga ta gama deciding abunda za ta yi….ba dare ba rana ita da Baba larai za su duk’ufa daga yau! Wallahi indai ta haifu cikin uwarta da ubanta sai ta juyawa Daddy lissafi ya aura wa Kausar Yashjub daga nan sai ta ga k’arshen soyayya sai ta ga k’arshen naci za ta ga yadda Manu za ta yi idan Yash ya k’ara aure za ta ga k’arshen maratussalaha da Manubiya ta ke playing….
Yadda yashjub ya karb’esu ita da Ya’isha sai da suka sha jinin jikinsu…ga Daddy ya juya musu baya yanzu kuma Yashjub tabbas Manubiya ta tabbata mugun tsuro a cikin family d’insu amma ba komai inshaaAllah komai ya kusan zuwa k’arshe.
An riga an yi abunda suka zo yi
shiyasa kawai suka yi musu sallama suka fito jiki duk ba kwari ba kad’an ba attitude d’in Yash ya tab’asu Mommy ta d’an tsorata akan kar fa kwab’arta ta yi ruwa dan muddin Yash da Daddy suka zargesu suka juya musu baya suka fara gano su to fa akwai Babbar matsala dan haka dole ta tashi ta tsaya tun wuri ta gyara abunda ya fara lalacewa a tsakaninta da su Yashjub ,Yashjub ya auri Kausar Manubiya kuma ta kama gabanta…..
Gashi ta nemi fad’a kacha kacha da Daddy amma ba komai za ta gyara inshaaAllah….
Bayan sati biyu….
Babban abunda ya fi d’agawa Ummi har ma da su Yahansu hankali shine guduwar da Munirat ta yi…haka kurum kwanaki tara da suka wuce ta rubuta wasik’a akan ‘kar a nemeta ta tafi ba za ta dawo ba’ har yau babu inda ba a duba ba babu Munirat babu mai kama da ita,Ummi sai da ta yi sati d’aya a asibiti tukunna aka sallamota tsabar masifa…su Yasira kuwa an samu abunda ake so k’iri k’iri a gabanta suke yi mata dariyar mugunta suke cewa karuwanci Munirat ta tafi…
Mommy ta so su shirya da Daddy amma abunda ya yi mata sai da ya sakata a al’ajabi dan korar kare ya yi mata da ta je d’akinsa kuma har yau ko kallo ba ya shiga tsakaninsu in kuwa ya kalleta to harara ce! ko abinci ya daina ci a dining d’in k’asa duk dan saboda ita.Wannan al’amari ba k’aramin d’aga mata hankali ya yi ba har y’ar rama sai da ta yi gashi Yash da Manu shiruu ba a jin kansu su da suka zubar da cikin suka k’ulla sharri saboda ya koreta amma sai take gani kamar hakan ma sake had’a kansu waje guda ya yi! su Yasira kuwa ana sallamar ta a asibiti Hajiya Mama ta ce su dawo gidan Ubansu shiyasa gaba d’aya ta sake burkicewa gashi ta ga hajiya mama ba ta da ranar tafiya dan da farko sunyi tunanin rako Junior ta yi ta d’anyi sati d’aya ta koma…Kwanciyar Hankalinta d’aya zuwa biyu a yanzu na farko ta riga ta san Manu babu ita babu haihuwa,sannan al’amarin Kausar da Yashjub akwai haske dan aiki tuk’uru suke yi babu dare babu rana dukda ita da Kausar d’in ba su fahimci juna ba har yanzu saboda ta yi tambayar duniya ammawkullum amsa d’aya Kausar d’in take Bata itace”Yashjub raping d’inta ya yi”tsabar ta raina wa Mommyn hankali,shiyasa ita kuma ta rabu da ita ta d’au fushi da ita ko taimakon nan ma da suke yi mata ba ta sani ba.
Su Yasira ma sun d’an ji haushin abunda Kausar ta yiwa Yashjub gashi suma da suka tambayeta amsa d’aya ta basu irin wadda ta bawa Mommy shiyasa suka daina kulata suka yi fushi da ita…ita kam ko a jikinta dan idanunta sun rufe ba ta damu da kowa da komai ba babban burin ta a halin yanzu shine ta ga ta auri Yash daganan kowa ya yi ta kansa.
Abhi ma ya zo dan Daddy da kansa ya kirasa da ya ji labarin yana Niger sun je wani aiki yace dan Allah idan sun gama ya biyo Nigeria,Dan kwana biyu gaba d’aya Daddyn a hargitse yake ya rasa me yake yi nasa dad’i kansa ya d’au zafi shiyasa ya hana Hajiya Mama tafiya yake kuma buk’atar Abhi d’in shima a kusa da shi.
Junior da Ya’isha ma an saka musu rana nan da wata uku su Siyama ma jiya aka je aka yi tambaya aka bayar aka saka ranar auren wata uku suma……
Ko da Junior ya tunkari Yassir game da zancen Yash tashi d’aya Yassir ya faiyyace masa komai bai b’oye ba!saboda ya San ya riga ya fahimta.
Cikin tsananin b’acin rai Junior ya hau zaginsa yace bai yi expecting zai iya yiwa Yashjub haka ba ya yi sauri ya gyara mistake d’insa wallahi ko ya tona masa asiri.!
…..A lokacin da suke makaranta akwai wani video da Yassir d’in ya tab’a yiwa Junior shi da wata Yarinya da yake so ta k’i sauraronsa…sai da suka bata abu ta sha ta bugu tukunna aka yi video d’in na rashin d’a a!Yarinyar naked abun dai babu kyan gani..y’ar Nigeria ce y’ar manyan mutane gidansu babban gida shiyasa a wannan lokacin suka dinga blackmailling d’inta da wannan video d’in ko me suka ce suna so ta yi musu sai ta yi idan suka kirata dole ta je..ba kalar tujarar da Yarinyar nan ba ta gani daga garesu ba har aka samu ta gama makarantar ta kama gabanta ba tare da sun saki video d’inba..a wannan lokacin an yi ne akan za a yanke fuskar junior da jikinsa a saki video d’in ita kad’ai.To yanzu kuma Yassir ya tabbatar wa Junior duka su biyun zai bari ya saki video d’in ya nunawa kowa har su Daddy da Yadira daganan sai ya ga ta yadda zai auri Yadira..
Bai ga alamun wasa a fuskar Yassir ba kuma ya san tsaf zai
Iya tunda har ya iya yin dakon video d’in har kawo yanxu saboda shi Junior ya san sun goge video d’in sam bai yi tunanin Yassir yana da shi har yanzu ba….
Sai da suka yi kacha kacha ranar tukunna suka rabu baram baram ba ma a b’angare d’aya suka kwana ba dan Junior k’aura ya yi ya koma side d’in Yashjub inda Abhi yake.
Tambayar duniya ya cewa Abhi ba komai yana zama kusa da shi ne kawai dan haka ya rabu da shi ba dan ya yarda ba.