← Book details Munnubiya Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 68 OF 137

Sashe 68

Munnubiya Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Mommy tana fita Yasmeen ta kalli Baba larai tace ‘’ Baaba ki yi mata bayani dan Allah”

Da sauri Yasira wadda k’arasowar su yanzu gurin tace
“Mai ya faru?
Kallon ta ta yi ta kalli Ya’isha kafin ta shiga zaiyyane musu abunda ya faru….
Kamar Ya’isha za ta rufe Yasmeen da duka haka ta shiga surfa ruwan bala’i tana cewa”Ashe baki da lisssafi ban sani ba? Har yaushe kika santa da har za ki tausaya mata dan wanann ba wai Yashjub kike tausayawa ba ita kike tausayi.
To bari ki ji in gaya miki idan har wanann Yaron ya zo duniya wallahi ko k’ofar gidan wata rana baki isa ki taka ba!,kin ga daganan sai in ga ta k’arshen zumunci da tausayin d’an d’an uwa!
Ki na gani dai kwanan ta uku tal a cikin gidan amma da muka je korar mu ya yi!
Ki bar ganin wai Daddy ya tsawatar masa yanzu ance mu je anytime wallahi a kwana a tashi watarana Daddyn ma bai isa ya ce komai ba,indai Yarinyar nan ba ta yi waje ba to ba mu da kwanciyar hankali a cikin gidan nan
Ke kin san su waye talakawa idan suka samu guri kuwa???
sai ta raba sa da kowa ta handame komai daga ita sai y’ay’an ta
gashi uban dukiyar family karakakaff duk tana hannun sa’’

Cikin son fahimtar da ita Yusra ma tace
‘’Yasmeen tunda har ga abunda Mommy tace miki ki yi kawai mana kin fi ta sanin daidai ne?’’

Ahankali Yassira wadda tun d’azu ba ta yi magana ba , ta fesar da iska kafin ta kalli Yasmeen ta ce ‘’ki rubuta za mu je mu siyo yanzu ni da Ya’isha…abun da Babba ya hango k’arami bai Isa ya hanga ba’’

Cikin rashin jin dad’i Yasmeen d’in tace
‘’Wai me yasa baza ‘a samu mutum d’aya a cikin ku wadda za ta kalli issue d’innan daga point of direction d’ina ba??”

Wani wawan tsaki Ya’isha ta ja kafin tace
“Ai dama na riga na sani,na san sai kin yi taurin kan naki da kika saba!
Yasira kawai ki zo mu je zan yi
browsing mu siyo kuma wallahi idan muka kawo dole sai kin yi
dan babu wanda kika Isa ki gwadawa taurin kai anan!.’’
Tana gama fad’in haka ta juya ta fice fuuuu zuciyar ta kamar ta b’ullo waje.

Still cikin son fahimtar da su Yasmeen tace
‘’in da ace mun san zamu aikata haka da bamu barta har ta rayu dashi a wata k’asa daban ba
Infact da bamu barta ma ta shigo gidan ba.”

Cikin tarar numfashinta Baba larai tace
“Yasmeen ke shaida ce wanne irin abu ne ba a yi ba amman sai da ta shigo
Y’an uwan ki da mahaifiyar ku sun fiki gaskiya fa….”

Cikin katseta Yasmeen d’in tace”to Baaba sai ku duba ku ga yadda akayi ta fama d’in amma sai da auren nan ya d’auru shin ba za ku yi lissafin watak’il wannan cikin shine rabon da ke a tsakanin su wanda Ubangiji ya k’addara sai sun yi auren kuma sai ya zo duniya ba??ba za ku yi tunanin mai za ta kasance da mu idan muka dage muka ce sai cikin ya fita ba??”

Shiruu kawai Baba larai ta yi tana kallon ta.
Ahankali Yasira wadda itama tun farko tsarin bai yi mata ba tace
‘’ Yasmeen ki yi abun da ake so ki yi kawai!!as far as I know Mommy ta fi ki sanin duk waennan abubuwan so definitely akwai abun da ta hango sannan kuma inaso ki sani duk yadda za ki so Yashjub bai kai yadda za ta so shi da shi da abun da zai Haifa ba,dan haka tun da har kika ji tace haka akwai dalili Babba!
We re suppose to stick together kar kanmu ya fara rabuwa tun a nan!
mun fi ki yawa dan haka Ina shawartarki da ki yi hak’uri ki yi abunda kowa anan yake so ayi.’’

Shiruu d’akin ya d’auka kafin chan Yasmeen ta sauk’e ajiyar zuciya tukunna ahankali tace”okay!bara in rubbuto”
daga haka ta juya ta fita.

Ahankali Yasira ta fesar da iska…ta rasa ganin ta inda abunda suke shirin aikatawa ya kasance daidai ya kuma dace ace su yi!
Tabbas itama a cikin zuciyar ta a bayan Yasmeen take d’ari bisa d’ari
Amman kuma akwai abunda Mommy ta hango tabbas!
wannan shine dalilinta na bin bayan Mommyn dan ta san in dai Mommy za ta iya cewa a kashe d’an d’an cikin ta
to tabbas lamarin Yashjub da Manubiya ya wuce tunanin su,ya fi k’arfin iyakar abunda ta gaya musu suka sani.
………..

Bayan kamar 40 minutes,
Su Yashjub suna zaune har da Yahanasu wadda ta kawo wa Mannubiya tea take sha suka ji ana knocking.
Sai da Yashjub ya kalli wayar sa ya ga likitan bai kira sa ba tukunna ya kalli Yahanasu yace “ta bud’e maybe su Mommy ne”
Ai kuwa tana bud’ewa suka yi
Ido biyu da Yasira Yasmeen da Ya’isha.Ba musu ta matsa musu suka shigo..sai da suka fara yi wa Manubiya ya jiki tukunna Yasmeen tace “Mommy ce tace ta zo ta duba ta”
Cikin tarar numfashinta Yahanasu tace
“Ai Likita yana hanya”

Murmushi Yasira ta yi ta matsa kusa da Yashjub da Mannubiya da suke zaune a bakin gadon tace’’Manu ya akayi kika bari ya kira Dr bayan gamu da soon to be consultant a gida?Yasmeen matso ki duba ta Mommy tana jira,ta ce in ta kama sai a wuce asibiti.
Gaba d’aya hankalinta har mu duk a tashe yake…aman da ta yi ai dole a dubata da wurwuri in ma k’arin ruwa ne a yi mata dan na san she’s weak’’.

Shiruu Yashjub ya yi kafin chan ya d’ago ya cewa Yasmeen d’in “matso mana mai kike jira?”
Sai kuma ya kalli Ya’isha yace
‘’ki je ki cewa Mommy jikin nata fa da sauk’i ta kwantar da hankalinta”.

Murmushi duk suka yi banda Yahanasu da gaba d’aya hankalin ta yake a tashe
Har ga Allah ta gama shiryawa akan ko da ace cikin ne to za ta san yadda za ta yi ta lallab’a Yashjub su b’oye har sai ya d’an yi kwari tukunna a fad’a
amma gashi yanzu su ne ma za su fara sani
Sannan yadda suka dad’e a saman nan ba su sauk’k’o ba bata da tantama plan suka gama had’awa….
Tana wannan tunanin ta ga Yasmeen ta matsa kusa da su ta shiga duba Mannubiya dama har da abun auna hawan jinin ta ta taho da ragowar abubuwa.
Duk wani gwajin da ya kamata sai da Yasmeen ta yi mata.
….Tun a kan pulse d’in Mannubiya Yasmeen ta jiyo alamun ciki ga kuma ragowar gwaje gwajen da ta yi mata waenda suma suke nuni da hakan
shiyasa tashi d’aya gaban ta ya yanke ya shiga fad’uwa dan ba ta san ya za ta yi ba sannan ba ta san ma ta Ina za ta fara ba…

Cike da murmushi da tsantsar farin cikin da ya baiyyana a iyaka kan fuskar ta Yasira ta matso ta ce ‘’good news ko?pls tell me I’m about to become an aunt.’’
Ta k’arashe maganar tata da y’ar guntuwar dariya kwance a kan fuskarta.

Murmushi Yashjub ma ya yi yana jira kawai ya ji ance masa Mannubiya na d’auke da ciki ne amma instead sai kunnuwansa suka jiyo masa muryar Yasmeen d’in tana cewa’’A’a gaskiya ba ciki bane ba, dan in da ace shine da zan ji yanayin pulse d’in ta ya d’an chanja sannan ragowar gwaje gwajen da na yi mata suma duk ba su yi detecting pregnancy ba,inaga gajiya ne da fever…
But first bari in fara yi mata allurar tsaida aman nan dan da na duba idonta gaskiya she’s very weak sannan ba ruwa a jikin nata zata iya fainting anytime from now.!”

Gaba d’ayan su jikinsu sanyi ya yi especially ma Yashjub wanda ya gama kwallafa rai ya gama yarda akan kawai cikin ne, ganin yadda Mannubiyan ta yi ne ya sa cikin son bata kwarin guiwa ya samu dakyar ya aro jarumta yace’’ok,dama nima na yi tunanin gajiyar ce, a ina za’a siyo allurar?
A samu a yi mata da wuri a samu ta d’an ci wani abun ta kwanta ko?”

Cikin tarar numfashinsa Yahanasu tace‘’Ina ga gara dai a jira Doctor d’in ya zo shima ya dubata tun da kaga shi Babba ne!
sai a san da me da me ya kamata a bata.”

Da sauri Yasira tace ‘’ba ki ji abuna itama Yasmeen d’in tace ba?
Iyaka allurar tsaida amai za ta yi mata saboda itace emergency ana buk’atar a tsayar da gaggawa.’’

Cikin katseta Yahanasu tace’’Yasira allurar tsaida amai fa tanada k’arfi sosai! ki bari a yi kwak’kwaran bincike kafin a fara d’irka mata abubuwa’’

Murmushi Yasmeen ta yi sannan tace”Na yi duk gwaje gwaje fa
In da ace akwai ciki ko na sati d’aya ne to da zan gani zan kuma fahimta, kar ki manta Gynea na yi specializing a.
Also allurar da zan yi mata yanzu ba ta da wani k’arfi iyaka tsayar da aman za ta yi.’’

Zuwa yanzu ran Yahanasu ya b’aci kuma ta sake tabbatarwa akwai abunda suka shirya dan haka tace
‘’Ai nima ba cewa na yi ciki ba cewa na yi ki tsaya dai a yi kwakkwaran bincike dan wannan gwajin da kika yi bai kai ace ya yi detecting komai b..’’

A hankali cikin katseta Yashjub yace
‘’Yaha Mommy ce ta aiko su kar k….’’
Juyawa kawai ya ga Yahanasun ta yi ta fice daga d’akin da alamun ranta ya b’aci.
Shiruu kawai Yashjub ya yi,
sam bai ji dad’in abun da ya yi mata ba amma kuma ba ya so Mommy ta yi fushi..
Shiyasa ya bari akan idan su
Yasmeen d’in sun gama zai je ya bata hak’uri,gara ace ita ta yi fushi ta bar case d’in akan su Yasmeen su je su gayawa Mommy ta ga kamar ya sace mata guiwa ne daganan ta yi fushi.
Tunda sun ce ita ta turo su kuma ta na chan hankalinta a tashe ya san idan ya hana su bazata ji dad’i ba…
Gara Yahanasu ya san ita za ta fahimcesa idan ya je ya bata hak’uri zuwa anjima…
Chapter 68 · 0% Book details