← Book details Munnubiya Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 80 OF 137

Sashe 80

Munnubiya Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Girgiza kai ta yi kafin tace
“Yassir ba zan iya yin wani abortion d’in ba fa,ai ka ji dai da kunnenka abunda Doctor yace mana the last time ko?…ko kana so mahaifata ta lalace tun kafin na fara tara iyali??
Besides
ai ni na sha gaya maka dama a ko da yaushe ba son rabuwa da babyna nake yi ba hak’uri kawai nakeyi ina biyeka.”
A hankali ta kamo hannunsa ta d’aura a kan cikinta tace
“This is our child,
kasancewarsa jininka ya sa na ji Ina matuk’ar k’aunarsa
saboda tsananin son da nake yi maka ba zan iya rabuwa da shi ba,wallahi ban tab’a jin so da k’auna bayan wanda nake yi maka ba sai a kan cikin nan!”

Damk’e hannunta ya yi da k’arfi dan ba kad’an ba
maganganunta sun shige sa sun yi tsananin tasiri sun ci galaba a kansa.
Ya jima maganganunta suna ratsa sa kafin a hankali cikin kwantar da murya yace
“Kausar!!
Daddy will kill me
Mommy ma Allah kad’ai ya san mai za ta ce…me”

Cikin katseshi tace
“Are u just thinking about yourself??”

Da sauri yace
“Of course not!.
Baby I’m also thinking about you mana
ban san wanne kallo duniya za ta yi miki ba!sannan kema ba wai sauk’i za ki samu daga wajen su Daddy ba.
Kinga dama da ni da ke muna da bak’in jini a wajen Daddy idan ya ji wannan batun ban san mai zai yi mana ba.
Ke da kanki kince 1% kawai gareni,na tabbatar idan Daddy ya ji wannan batu tou kashina ya bushe
Ni da shi babu taimako babu zaman lafiya daganan har abada
In that case
Yash will remain the king!…
Tayaya kike tunanin zan kula da ke da Baby idan hakan ya faru?
Kausar my company is not that good sannan a wajen Daddy ma 1% gare ni,idan muka haihu
while not yet stable
ya kike so Babyn namu ya rayu??
I love you sannan nima inason Babyn nan amman
we need to make sure munada plan da better future d’in da za mu bashi kafin mu yanke shawarar kawosa duniya”.

Shiruu duk sukayi kafin chan Kausar tace”Yassir na san abunda zan yi but har yanzu bani da tabbacin ko ka yarda dani d’ari bisa d’ari…”

Ahankali yace”Kausar mun rufe maganar nan fa!na yarda da ke mana”

“Ka tabbatar?”

“Na tabbatar“
Ya bata amsar yana kallonta
sannan ya d’aura da cewa
“Na fad’a miki na riga na yarda da ke Kausar,kawai dama inaso in yi confirming ne shiyasa na sake yi miki wachchar tambayr amman tun shigowata cikin d’akin nan da kika fara yi mini maganar farko tashi d’aya na yarda dake.Baki ga ban yi miki denying batun estate da cire taya ba?ko so kike in yi miki confessing??”
Ba tare da ya jira jin mai zata ce ba yace ‘’ok I did it’’
“If to say
ban yi trusting d’in ki ba kina tunanin zan fad’a miki haka ne?”

Ahankali ta sauke ajiyar zuciya tana ji inama ta saita record a lokacin da yake confession d’innan da ta ajjiye as evidence d’in da za ta nuna ta tura sa prison bayan ya gama taimaka mata ta auri Yash…but with time inshaaAllah kafin ya gama taimaka mata amfaninsa ya k’are a wajenta za ta san yadda za ta yi ta sanya shi ya k’ara confessing!”

Ahankali ta gyara zamanta ta fuskancesa sosai
tukunna ta fara magana
“Yassir
Inaso ka cire kishi
da negative thinking ka duba future d’inka sannan Ina so ka san cewa ko ka yarda da wannan shawarar tawa da zan fad’i maka yanzu ko baka yarda ba ni dai ba zan tab’a zubar da cikin nan ba.

Akwai hanyar da za mu bi
mu haifi Babyn mu ya rayu cikin farin ciki…kuma hanyar ka sani itace silar warwarewar duk wani k’uncinka
amma we need to stick together sannan mu yarda da juna kafin komai”.

Jinjina kai yayi
alamun yana jinta kuma yana fahimta.

Ahankali ta sauk’e ajiyar zuciya tace”ka ce Daddy zai ji haushinka zai yi fushi da kai
watak’il forever idan har ya ji maganar cikin nan ko??”

Jin jina kai kawai yayi

“Good!
What if Yashjub ne a matsayinka??”

Da k’arfi yace
“What!!how??”

“Relax
I mean what if we frame him!.
Ka ga na farko
Ni kaina Daddy zai ji tausayi na
sannan zai yi fushi da Yashjub
Above all
zai shirya da kai ya janyoka a jikin sa sanna idan Yashjub yana tunanin wannan Babyn sa ne
tsaf za mu yi amfani da hakan
mu samu abunda mukeso”

Shiruuu kawai Yassir ya yi ya dafe kansa kafin chan ya d’ago ya kalleta tukunna yace
“Taya za ki yi hakan??
Taya hakan zai faru ??”

“Good
Bari kaji step one”
Ahankali ta matso ta zaiyyane masa komai…

Da farkon murmushi ya fara yi sai kuma ya mik’e tsaye yace
“Inaa! Kai!!!
no ba zai yiu ba.”

Mik’ewa ta yi ta rik’e hannunsa cikin son fahimtar da shi tace
“Nothing will happen between us”

“Yeah I know,but just the fact that za ki kwanta waje d’aya da shi that too n**kd,inaa Kausar ki kawo wani plan d’in gaskiya banda wannan.”

Murmushi ta yi tace
“Yasir a lokacin da abun zai faru fa ba ma ya cikin haiyyacin sa
balle ma ya gane komai.
Kuma that’s the only way da za a kamashi red handed.
Kar ka bari kishi ya rufe maka ido mu kasa cimma burin mu.”

Shiruu ya yi kafin yace
Kausar,ta ya zan bayar da d’a na a wani?
Tunda idan fa kika haihu
kowa Yashjub zai ce shine uban Yaron..ta yaya zan yi claiming rights d’ina a matsayin Uba?”

“Yassir ko wanne family suna da nasu secret d’in let’s this be ours(da ni da kai)..
Ka duba ka ga fa sau biyu kana attempting kashe Yashjub amma hakan bai yiu ba kuma dukiya har yanzu tana hannunsa,a gani na don ka hak’ura wannan Yaron ya zama nasa na shekara d’aya ko months mun samu da dabara da sharri da abubuwa komai ya dawo hannunka,it’s normal ai…
A da kai kad’ai ne ka ke ta had’a plans d’inka kana failing yanzu kuwa zan taimaka maka na san za mu yi winning.
Idan Daddy ya ga Yash ya mutu ga kuma jaririn Yaro mara gado bani da tantamar tashi d’aya Daddy zai tartara komai ya saka a sunan Yaron kar ka manta yadda Daddy ya ke ji da Yashjub dan wani abu ya shiga tsakaninsu sun yi fad’a ya daina kulasa ba shi zai sanya ya k’i son d’ansa bayan mutuwar sa ba.

Ka fahimce ni Yassir wins ne da mu ta ko wanne angle a cikin plan d’innan fa…kaga Yaro dai yana hannu na kuma kai zan aura at last komai ya zama naka Yashjub ya tafi sannan Yaro kuma ya taso a hannnun iyayensa mu kula da shi mu haifi k’annensa ya taso cikin ahalinsa,mai ya fi wannan riba??”

Shiruu Yassir ya yi kafin yace
“but idan kuma ita wachchar matar tasa ta haihu kinga mun yi 2 zero ko?dan kowa d’anta zai kwallafawa rai na san.
Tunda by now he’s supposed to be dead ta yadda zan ga bayan cikin amma ya k’i mutuwa a yadda yake gadinta d’innan ni ko ke bamu isa zuwa ko kusa da ita ba ballantana mu yi wani abun….

Murmushi Kausar ta yi kafin tace”don’t ask me Y and how,kawai inaso ka cire cikin Manubiya a lissafi dan wallahi ba ta isa ta haihu ba…kawai ka yi trusting d’ina when I say cikin nan ko one month bai isa ya k’ara a jikinta ba….”

Ajiyar zuciya ya sauk’e kafin yace”I trust you Kausar.”

Murmushi ta yi tace”Thankyou..na san maganin da xa mu yiwa Yash amfani da shi zan rubuta
sunan sai mu je tare da ni da Yasmeen
amman ita kanta ba zan bari ta gane menene ba kawai zan
ce mata wanda ya ke sakani bacci ne akai mini recommending sabo.
Za ta nuna id card d’inta mu siyo maganin saboda ba za su
tab’a bani ba ni it’s super strong.”

Kallonta yayi sai kuma yace
“Da wuri haka?”

D’an zaro ido ta yi kafin tace
“Yassir tou sai yaushe?
Ai ba wai yanzu yanzu ba but inaso komai ya zama ready
ta yadda Ina ganin opportunity komai zai kammala.
Manya manyan jajayen layukan da suka fito B’aro B’aro a kan tsinken
nan ya na nuni da cewa cikin nan ya kwana biyu a jikina
Idan ba da kyar ba ya fi 1 month.

Kuma kaga idan ma zan ce inada ciki sai fa kamar irin 2 weeks haka bayan incidence d’in…

Shiruu yayi kafin chan yace
“Okay kausar
duk yadda kika ce hakan za a yi”.

Murmushi ta yi kafin ta yi hugging d’insa tace “Thankyou Yassir.
Thanks for trusting and understanding me”

A ranta kuma tace”Ashe ba ka da wayo…wannan plan A ne dole da kai za’ayi plan B kuwa ni kad’ai zan yi abuna dan ana tabbatar da cikin nan aure Yash ba zai zama abu mai wahala a gareni ba sai dai kawai ka ji a salansa…
Ya zama dole nima in nemi farin cikina in tsayawa kaina kuma in yi protecting Yash daga sharrinka…….”

“Tabbas ya fahimci Kausar kuma ya yarda da plan d’in dan akwai nasarori a tattare da plan d’in…..sannan zaifi jin dad’i idan Yash ya mutu da tabo da mugun suna.”
Yassir ya aiyyana hakan a cikin ransa yana mai sake saka saka ta a cikin jikinsa

Yashjub yana fita,d’akin ya rage daga Manubiya sai Yahanasu….a hankali Yahanasu ta mik’e ta k’araso inda take ta zauna a gefen gadon tukunna tace”me zan zuba miki??”
Zama Manu ta gyara ta ruk’o hannun Yahanasu kafin tace”Yaha Ina buk’atar taimakonki”
Shiruu Yahanasu ta yi ta d’an k’ura mata ido dan kamar ta fahimci mai za ta ce,kafin da kyar tace”anything! Manu..”
Chapter 80 · 0% Book details