← Book details Munnubiya Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 44 OF 137

Sashe 44

Munnubiya Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Kafin Yassira wadda ta juyo a fusace ta yi magana tuni Ya’isha ta amshe cikin tsiwa ta fara cewa”Haba ke kuwa!wai
ashe kwata kwata kwakwalwarki bata d’aukar lissafi ke!.
Magana ake ta y’an uwa!,tun d’azu sai ce miki ake yi ki
wuce ki tafi d’akinki amman
kin nace sai da kika ji komai
kuma hakan ma bai ishe ki ba tsabbar shishigi kin wani tsomo wa mutane baki,
Ina ce Daddy dakansa yace
‘ki fita harkar kowa kuma in family suna magana ki daina saka baki’.?”

With full confidence Munirat ta taho tace”Ya’isha!tou ai ni a ganina idan aka bar family d’in za su yi b’arna da shirme tunda basu san abunda ya dace ba
shiyasa Ummin take saka muku baki dan idan aka barki Allah kad’ai ya san kalar dak’ik’ancin da za ku yi”

Dasauri Ummi ta damk’o hannun Munirat ta tura ta tace “wuce ki tafi d’akinki kafin na makeki”
Dan yadda ta ga Yusra da Ya’isha sun yo kan Munirat ta san idan bata yi wani abun ba tsaf za su rufeta da duka.

Za ta yi magana Ummin ta daka mata tsawa tace wuce”Nace ki wuce!”

Da sauri Yasmeen tace”ai sai ta wuce d’in mu gani idan saman ubanta ne ya gina!.Kun je kun gama yi wa mutane shishshigi kun k’ulla k’ullalliya shine yanzu zaku ce za ku
kwana lafiya?ai ba ku taki zaman lafiya ba dan haka bacci bai ganku ba,masifa da tashin hankali ne ya ganku!”

Cikin fushi Munirat tace”Okay!yanzu na gane matsalar ku
ko kuma ince matsalolinku!
Na farko baku samu yadda kuke so ba
na biyu kuma Ya Yash ya fatatttake ku shine kuka zo zaku d’aga mana hankali zaku hana mutane bacci saboda tsabar bak’in ciki da k’unci kun rasa Ina zaku sa ranku shine kuke so ku huce a kanmu ko?.
Ai ba mu muka ce ku zama bad people ba,have it been u guys are nice da duk haka bata faru da ku ba.Kuma abunda ban gane ba shin idan mun tsaya d’in mai hakan zai k’are ku da? kawai kar mu yi bacci shine burinku ko me??
kuna jin abunda kukeyi kuwa?
kowa fa ya na jin hakan ya san kawai kuna neman in da za ku yi venting anger d’inku ne,haba mana!ku gyara abun naku ta hanyar yin something not lame
kmar haka!”
Fincikota Yusra ta yi da dukkan k’arfinta daga gaban Ummi,
Ummi ta yi mamakin yadda Munirat ta zabgawa Yusran mari dan ba ta yi tunanin wannan audacity d’in da ga Munirat d’inba…..

A chan sama kuwa,tun d’azu da Baba larai ta cewa Mommy “ba su yi komai a gidan Yash ba suka dawo”shikenan Mommyn ta koma kamar robot,dukda Baba ta kawo sabon plan amman sam ita gani take tunda basu yi wanchan na farkon ba shikenan ta shiga uku!zuwa yanzu so take ma ta yi kuka amman sam hawaye sun gagara fitowa daga idanunta.Ga kuma yanzu da ta yi wa Kausar bayanin dawowar Manubiya da Yash cikin gidan tukunna a samu a yi komai….a tunanin Mommy Kausar za ta yi murna da hakan amman sai ta ga sab’anin hakan dan tashi d’aya Kausar d’in ta birkice ta shiga ce mata tace”Ashe ma bata da burin raba auren Yash da Manu tunda har ba zata iya korarta a wanchan gidan ba har sai an kuma d’aukar lokaci an barta ta dawo nan kafin nan ma maybe ta dawo da ciki shikenan komai ya lalace mata dan ta san indai Manu ta samu ciki to ta gama cin riba a kansu……ita kawai ta lura ja mata rai suke yi suna yi mata wayo dan haka yanzu kawai abunda Mommy za ta yi mata shine ta kira Yash a yanzu ta ce masa ya saki Manubiya if not sai ta tsine masa,indai har Mommy ta yi hakan to ta yarda ba raina mata hankali suke yi ba,idan kuma bata kira Yash ba wallahi sai ta bar gidan a yau kuma ba zata sake ganinta ba!”
Hankalin Mommy idan ya yi dubu tou ya tashi,ta san idan ta yi hakan tabbas Yash zai saki Manubiya amman ko hauka takeyi ba za ta tab’a yin abunda hakan ba saboda ta san yin hakan kamar ta kashe relationship d’inta da Yashjub da Daddy ne,dan kowa bak’in ta zai gani kuma ita kanta Kausar d’in muddin hakan ta faru to Yash ba zai tab’a yarda ya aureta ba har abada hatta su Yasira ta san sai bak’in jinin ta ya shafesu watak’il ma ya tartara kayansa ya tafi ya koma uk ya zauna a chan shikenan ba za a sake ganinsa ba har abada.Shiyasa ta fara k’ok’arin fahimtar da Kausar d’in cikin lallami.
Ganin hakan ya sanya Kausar ta wuceta da sauri tana wani Irin kuka ta d’auki wayar ta da makullin mota ta fice da gudu gudun ma kar Mommyn ta yi yunk’urin tsaida ita,a ranta ta gaka yanke decision ‘wallahi sai ta bar gidan a yau!.’

Dai dai nan ne kuma Munirat ta zabgawa Yusra mari suna shirin rufar mata suka ga Kausar ta sauk’o da mugun gudu tana kuka Mommy ma wadda ta biyo ta tana kiran sunanta tana hawaye sharr kamar an kunna famfo.

Da sauri Yassira ta k’arasa bakin main door ta tsaya dan taga nan Kausar d’in ta nufa,durk’ushewa Kausar ta yi a daidai gaban Yasira tace”Yasira dan girman Allah ki matsa in fita,idan na ci gaba da zama a cikin gidan nan mutuwa zan yi ba zan tab’a iya zama a gida d’aya da Yash da Manubiya suna tare ni kuma ina kallonsu a gefe,yanzu haka ma baki san ya nake ji ba,na san suna chan tare!duk da haka na yi k’ok’ari na danne kai na amman naga Mommy so take yi sai na mutu tukunna za ta kyaleni”….muryarta ce ta sark’e sakamokon numfashinta da ya d’auke dan haka ta kasa ci gaba da magana ta shiga kokawar janyo numfashinnata .

A hankali Yassira ta durk’usa a wajen k’asa k’asa tace”Kausar kar ki yi disgracing kanki,kalli
yadda su Ummi suke kallon….”

Cikin tsananin fushi tace
“Disgrace my foot!su kalla mana!ina ruwana so kike in yi pretending bayan kowa idan ya ganni ya san Ina cikin tashin hankali kuma na kasa kuma kun kasa yi min maganin matsalata?…akwai disgrace da rashin gatan da ya fi wanda nake a ciki??”

Ahankali Yasira ta janyota ta shiga lallashinta.
Kamar Kausar d’in zata mutu tace “Ina ta k’ok’arin ganin na yi picking pieces of myself nayi staying strong amman shine
kuma duk da haka wai Mommy
saboda ba ita ta haifeni ba
ta zo tana ce min wai Manubiya za ta dawo nan!
Wanne irin rashin adalci ne wannan?.Ba ku ma da shirin korarta kwana kusa kenan sannan ta ya zan iya zama ta dawo nan Ina kallonsu tare a waje d’aya a d’aki d’aya da Yash!?”

Ganin yadda su Yahanasu suka zuba musu ido ne yasa Yasira tace”calm down mana Kausar,ki zo mu je….”
Fincikewa Kausar d’in ta yi cikin tsananin fushi
tace “Stop telling me to calm down!tun yaushe kuke cemin in yi calming down in yi shiru za ku san abunyi amman har yau shiru???inda ace ke ce ko su Yusra na san da tuni Mommy ta uzzurawa Baba larai an yi an wuce wajen…….”
Da sauri Mommy da Baba larai suka k’arasa inda take k’asa k’asa suka shiga yi mata magana amman inaa kamar zuga Kausar ake yi gashi sai d’aga murya take yi tana ta yi musu b’aramb’atama.

Takaici ne ya rufe Yassira
ga Munirat Ummi da Yahanasu sun tsura musu ido,shiyasa ba ta san lokacin da tace “Useless munafukai kawai!kun wani tsaya kun tsurawa mutane ido”

Yahanasu ta ji zafin zagin amman sai ta danne ta saki dariya kafin tace”Ku fa kuka ce kar mu yi bacci yau,ko ba kune kukace kar wadda ta bar parlourn nan tsakanin mu nida Munirat ba!”

Cikin fushi Yassira ta k’arasa inda take ta tsaya a daff da ita
tace” Yahanasu ki kiyayeni!
Wallahi ki kiyayeni!.
Mara Imani mara tausayi kawai!na tabbatar misery d’in Kausar ne yasanya ki farin ciki da dariya haka,muguwa azzaluma!”

Murmushi Yahanasu ta yi kafin tace”Sam ba abunda ya saka ni dariya ba kennan,farin cikin ganin yadda kuka fara tonawa kanku asiri ne yasanya ni dariya Yassira ramin k’arya ai dama k’urarre ne!”

Cikin fushi Yasmeen ta matso ta ce “I have said enough Yaha”kafin tace “Da ke da Ummi da Munirat ku wuce ku bawa mutane waje.

Tun zagin da Yasira ta yi musu dama Munirat tazo k’arshen wuya,Ummi kuwa ji ta yi da ta sani da tuni ta yi sama abunta…cikin b’acin rai Munirat ta ce”Saboda kar mu ji more of your dirty secret ko?wai ni Yasmeen wa kuka haifa a cikin mu ne?,ni ko Yahanasu ko Ummi?dan naga yadda kuke yi mana magana kamar irin kun samu ya’yan cikin ku d’innan”
Ta fad’i hakan tana matsowa daff da su.

Yassira a k’ufule take
shiyasa tashi d’aya ta rufe Munirat da wani irin mahaukacin duka,kamar
jira Yasmeen take itama ta sa hannu dama ta tsani Yarinyar,
haka Yusra itama dama a wuya take.Hatta Ya’isha da Yadira shiga sukayi sukai mata rubdugu.
Yahanasu da Ummi ne suka fara k’ok’arin kwatar Munirat,without thinking twice su Yasmeen suka fincikosu dama haushin Yahanasu suke ji shiyasa suka fi rufar mata suka fi laftarta,itama Ummi sai da suka kai mata duka a Kai suka kaita k’asa.

Dai dai nan Daddy ya fara sauk’owa k’asan sakamokon hayaniyar da ya jiyo.Wata mahaukaciyar tsawa ya daka musu wadda ta sa suka d’an tsaya sai da suka d’ago suka had’a idanu da shi tukunna suka ja da baya suna huciii,har Mommy wadda ta matso kwatar Yahanasu.

Duk yadda Ummi ta so kasa daurewa ta yi,ba ta san lokacin da hawaye suka fara sintiri akan kumatunta ba…..wajen Ummin Daddy ya fara zuwa ya d’an shafa inda ya ga Yassira ta kai mata duka akai,wajen har ya d’an yi jaaa.
Chapter 44 · 0% Book details