← Book details Munnubiya Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 63 OF 137

Sashe 63

Munnubiya Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Ahankali Daddy ya ce”Allah ya kaimu”daga haka ya kashe wayar ya dafe kansa…he really can’t believe Yashjub ya d’auke matarsa sun yi nesa da su saboda ba ya so a nuna mata ta yi laifi kuma bayaso ma a ga laifinta a kan komai,tabbas da alama Yarinyar nan ta juya kwakwalwar Yash kuma son da yake yi mata ba na wasa bane dan tabbas zai iya rabuwa da kowa akanta dan ga alama nan….
Dan haka zai yi iyaka bakin k’ok’arinsa wajen ganin ba ta raba sa da d’ansa ba inshaaAllah daga yau ba zai sake ba shi reason d’in da zai yi tunanin barinsu saboda ita ba…
Shikenan fa yanzu da bai ankare da wuri ba da sai dai Yash ya zo yi musu sallama,dan tsaf zai yi transferring komai nasa garin da yake so ya je ya ci gaba da business d’insa da rayuwar sa a chan su ya barsu a nan.
Tabbas ya yi regretting aurawa Yash Manubiya dan gashi tun ba a je koina tana pulling Yash away from them amma tunda aikin gama ya riga ya gama kuma ba komai inshaaAllah ba zai sake bawa Yash reason d’in da zai guje su saboda ita ba.

Tsaraba sosai suka shiga jida a Cyprus dan sun kusa wuce wa Uk inshaaAllah.

Sarai Manubiya ta fahimci dalilin Yash na tambayar ta akan batun period d’in ta kusan kullum
Ko last week har asibiti suka je yace a yi musu checkup d’in su malaria da komai amman ita sai da aka had’a mata har da scanning
Da farko abun dariya yake bata dan ita a ganinta ko wata uku basu cika ba amman ace har ya fara k’ulafucin ciki sai dai kuma yadda ta ga yanayin sa tun jiya da ya ga ta fara period d’inta abun ya bata mamaki matuk’a dan tun jiya taga ya zama so silent da kyar yake iya dariya sannan ko bacci bai yi ba a jiyan dan ko da ya tashi ya yi sallar dare ya ida kasa komawa ya yi har asuba.
Yanzu kuma da safe tana kitchen ya shigo ya ce mata “ya tafi jugging”
bayan da tare da ita suke fita kullum..kafin ma ta gama yi masa a dawo lafiya har ya sa kai ya fice daga kitchen d’in.
Ajiyar zuciya ta sauk’e ta juya ta ci gaba da aikin ta jiki duk ba kwari tana ta tunani…a haka ta kammala ta jere abincin a kan dining daga haka ta juya ta nufi d’akin su domin yin wanka.

Ta ji matuk’ar tsoron ganin sa da ta yi a d’akin zaune a kan gadon dan batayi tunanin har ya dawo ba,ba ta ji shigowar sa ba sannan bai ce mata ya dawo ba kuma idan sun fita jugging d’in sukan d’an jima kafin su dawo…

Ta na wannan tunanin ta ga ya sakar mata murmushi kafin ya mik’a mata hannu alamun ta zo garesa.
Ahankali ta d’an matsa kamar mai jin tsoro ta zauna a kan cinyarsa…cikin cusa fuskarsa cikin wuyanta yace
“Morning wife!”

Ba ta amsashi ba sai da ta mik’a masa tata gaisuwar tukunna .
Sannan ta d’an kalle sa ta ce
“Kanada damuwa! mun ce ba za mu dinga b’oyewa juna komai ba.
Talk to me Dan Allah”.

Saida ya d’an shafa cikinta ya kalli cikin tukunna ya d’ago ya kalleta yace”Na ji har yanzu shiru ne!.
Baki tab’a shan wani magani mai k’arfi ba ko da na malaria ne? Ko mu je a duba ki sosai sosai..kin san yawanci y’an mata fa kunada matsalar da ku kanku baku sani ba sai likita ya duba da ikon Allah sai kiga an dace…”

Shiruu ta yi ta sunkuyar da kanta k’asa alamun ta shiga damuwa shiyasa tashi d’aya kamar zai yi kuka yace “Shiyasa fa kika ga na kasa yi miki maganar tun tuni
Banason b’acin ranki ni kuma har ga Allah a matse nake inji good news…”

Murmushi ta yi tace “ba b’acin rai bane kawai dai nima kasa na fara tunani ne..”
Sai kuma ta d’an yi shiruu kafin ta sauk’e wata nannauyar ajiyar zuciya tace”Mu yi addu’a !mu yi ta addu’a!”

Daga haka tayi shiruu ta fa’da duniyar tunani….itanma babban burinta a yanzu shine ta ga babyn ta da Yash amma gashi shiru har yanzu, da farko tana gani kamar ya yi wuri amman itanma yanzu ya jefata a damuwa…wat if ta kasance a cikin matan da basa haihuwa ya kenan?ta san shikenan ta rasa soyayyar Yashjub
Dan a yadda ta ga k’ulafucin son haihuwa a kwayar idanun sa ba lalle ya iya zama da ita kad’ai ba tare da yara ba sannan ba lalle ya ci gaba da sonta kamar yadda ya ke yi ba.
Yashjub ya riga ya saba mata da zazzafar soyayyar sa
Idan ya juya mata baya ba ta san ya zata yi ba.
Da sauri a cikin ranta tace
“Ya Allah ka sa zan haihu nima Ya Allah ka bamu y’a y’a masu albarka.”

Ahankali yace”kar fa ki saka damuwa a ranki
Ki yi hak’uri idan na d’aga miki hankali”
Girgiza kai kawai ta yi tace “ba komai”ta d’an yi murmushi daganan ta mik’e ta fara shirin ta shi kuma ya fad’a toilet yin wanka.

Har ya fito a yadda ya shiga ya barta hakan ya dawo ya tarar da mood d’in ta shiyasa ya yi ta janta da wasa yana k’arfin halin ganin ta sake dan shima a damuwar yake
Ya san it’s too soon amman mostly ana samu da wuri ai.

A haka suka yi breakfast d’in kowa da abunda yake tunani kafin yace “ta zo su je su d’an kammala shirin tafiyar tasu dan jibi suke so su wuce uk su duba jikin Na’ima su yi musu two weeks inshaaAllah daga nan sai su wuce Nigeria.

Ko da suka fita gajiya ga ciwon marar period d’in da take yi ne ya sa Yash ya dawo da ita bayan ta gama duk abunda ya kamata shi kuma ya koma.

Sai dare ya samu ya dawo
Washegari komai nasu ya kammala ta inda zasu bar Cyprus nan da kwana biyu.

A cikin kwana biyun nan saida Yashjub ya san yadda ya yi ya cire mata damuwa dan ya lura tunda ya yi maganar ciki hankalin ta a tashe yake.
Ba wai dan hankalin nata ya kwanta ba ta sake ta ke walwala dan ta lura ba zai barta ba idan har ba ta sake d’in ba
Amman a chan k’asan zuciyarta tana da damuwa da ta duk’ufa gayawa Allah.
Tun daga nan zaman su ya dawo kamar farko in ka gansu kowa wasai dan shima Yash d’in daurewa yayi sosai ya ke k’ok’ari wajen b’oye tasa damuwar.

A ranar tafiyarsu Manubiya ji ta yi kamar kar su tafi.Ta ji dad’in Cyprus kwarai ta ji dad’in gidan ta ji dad’in rayuwar da sukayi fiye da komai a rayuwarta rayuwar da ta tabbata ko wacce mace idan ta samu za ta ji dad’i za ta yi alfahari da sannan zata ajjiye a kwakwalawar ta har k’arshen rayuwarta.
dan tabbas rayuwa ce mai tsada mai dad’i da mutun bai Isa ya mance ba…

Da rana wajajen 2:34 british airways ya sauk’e su a Heathrow Airport London.

Suna fitowa Yashjub ya hango Junior ya nufosu yana murmushi dan haka shima ya sake rik’e hannun Manubiya suka nufe sa.

Yana zuwa ya yi hugging Yashjub kafin ya juya ga Manubiya suka gaisa cikin girmama juna daga nan suka nufi inda ya yi parking motarsa da su da waenda suka d’aukar musu luggage d’insu.
“Ga inda ake k’anin miji mai hankali”
Manubiya ta fad’i hakan a k’asan ranta.

A bakin wani babban gida mai d’ankaren kyau Junior ya yi parking ya danna horn
kafin mai gadi ya ja musu suka nufi ciki.
A bakin entrance na shiga babban parlourn gidan suka tarar da Hajiya mama tana jiran su….tunda Manubiya ta fito ta kafeta da ido ta shiga yaba Yarinyar a ranta gata da nutsuwa dan tunda ta tunkaro ta kanta yake a k’asa kuma tana lure da yadda ta zame hannunta a cikin na Yashjub a hankali a time d’in da ta lura da ita.
Murmushi tayi lokacin da suka k’araso Manubiya tana shirin durk’usawa Hajiya mama ta yi sauri ta tarota ta sakata a jikinta ta rungume
dai dai nan mom ma ta fito…haka itama ta yi hugging Manubiya cike da so sunata murna kamar za su maida ita ciki kafin su nufi cikin parlourn da ita
Saida suka zazzauna tukunna Manubiya ta samu da zamo daga kan kujerar ta gaida su da girmamawa
murmushi kawai sukayi suka amsa
kafin Hajiya mama ta d’aga Kai ta kalli Yashjub tace
“To fad’o mini a ka…yau kenan miskilancin ta kaina ya biyo”.

Da sauri Junior yace
“Inaaaaa!Hajiya mama ai this a new B Yashjub fa”ya fad‘i hakan yana mai nuna Yash kafin ya d’aura da cewa”ai ya daina miskilanci yanzu,tunda fa muka taho yake zubawa sweetheart d’insa surutu yana nuna mata wajaje da favorite places d’insa.
Love ya chanja sa ya koma mai surutu”
Dariya duk sukayi yayinda Yashjub ya d’an yi murmushi ya na mai sunkuyar da kai a ranshi kuwa shi kansa yana mamakin yadda soyayya ta chanja shi.
Sai da ya kuma yin wani murmushin mai cike da ma’anoni tukunna ya kalli Hajiya mama yace”Ba fa ki kulani ba
A bakin k’ofa kika barni kika ja hannun kishiyar ki ko ‘hi’ baku ce min ba daga ke har mom..”
Murmushi mom ta yi ta mik’e ta k’arasa ta je ta yi huggin nashi tace”welcome welcome”
Daga nan ya yarda ya bita ta zaunar da shi kusa da ita.
Lek’awa Hajiya mama ta yi ta rankwashe sa tace
“Da wani katoton kan sa!wa za ka yi wa shagwab’a??”
Kwashe wa da dariya Junior ya yi dan haka Yashjub ya d’ago yana masa irin kallon ‘ka fa fita a idona’d’innan wanda ya sa Junior d’in saurin gimtse dariyar tasa ya shiga yin ta k’asa k’asa sai kuma duk aka sa dariya
banda Yashjub wanda ya ke kallon Manubiya da kalar tausayin irin ‘har da ke ake mini dariya’…….
Chapter 63 · 0% Book details