← Book details Munnubiya Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 125 OF 137

Sashe 125

Munnubiya Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read

A b’angaren Kausar ma tana chan tana ta shirinta…akwai wata k’awarta y’ar babban jami’in tsaro mai fad’a a ji a Nigeria da kewaye da ta ga hoton baba larai itama tazo yi mata gaisuwa,
Ta yi mamakin ganin ta da ciki tsoho dan haka ta tambayeta ba’asi itakuma Kausar d’in tace”Yashjub ta aura amma har yau kishiya ta hanata tarewa”
Dan haka k’awar tata tace ta kwantar da hankalinta za ta taimaketa.. yanzu haka
Ita kanta tanada sojojin da idan ta saka suka k’ulle mutum Wallahi ba Yashjub ba ko
waye bai Isa ya fito da shi ba,yanzu abunda za a yi ta bari idan ta haihu ranar suna za su k’ullawa Manubiya sharrin sata inshaaAllah indai sojojinta suka tafi da ita ba a Isa a karb’ota ba sai ta dad’e sosai in lokacin sakinta ya yi suka ga dama sai su sakota kafin nan ita kuma Kausar d’in inshaaAllah ta gama samun Yashjub ta saka shi a corner har abada…”.
Sosai Kausar ta ji dad’in plan d’in dan haka ta bari akan sai ta haihu d’in sai ta had’a har da abunda suka shirya ita da Abbakar za su yi d’azu a yita duk a lokaci d’aya ta yadda ko bibiyarta ma Yash d’in ba zai yi ba kuma dama still akwai abunda ta shirya zata yi wa Manubiya a kan Yaron nan ma ta san dole abun ya sake zama effective…
InshaaAllah kafin ta fito ita kuma ta san yadda ta yi ta ko wacce hanya ta aure Yashjub,tunda har ga d’a a tsakani kuma babu Manubiya ta san aurensa ba zai yi mata wahala ba inshaaAllah.
Sosai ta ji dad’I hakanan suka rabu ita da k’awar tata tana ta murna ranta fess kamar an yi mata bushara da gidan Aljannah.

A b’angaren Yassir shima yanzu ya sake hawa ya koma gidan jiya..saboda da farko ya ji tsoro matuk’a amma yanzu da ya d’inke da Abokinsa ya gaya masa komai ya samu goyon baya d’ari bisa d’ari daga wajen Abokin sai zuciyarsa ta sake bushewa especially ma daya tabbatr video d’in a iyaka family yake yawo bai je ga hukuma ba tashi d’aya tsoronsa ya kau!
Kuma ya ji Mommy tana cewa sharri aka yi masa dan haka zai fake da sharrin aka yi masa ya dage har sai su Daddy sun yarda ya samu su shirya.. da ga nan zai yi mai kankat dan Abokin nasa yace”InshaaAllah zai tsaya masa zai taimaka masa su ga bayan Yashjub kuma ba za su sake tura wani ya kashesa ba!saboda kar a sake samun matsalak kamar lokutan farko! Next time kawai sakawa za su yi a d’auko musu shi su kashe sa da hannunsu.
But first ya samu ya fara wanke kansa ya shirya da su Daddy daga nan sai su k’addamar da shirinsu saboda yanzu wani abun yana samun Yash shi za a zarga.”

A ranar da daddare Ya’isha tana tafiya daga gidan su Manu itama Baraka ta je ta karb’o garin maganinta wanda za ta barbard’a ta haukatar da Inna dan yanzu tace ba za ma ta sakata jinya ba haukatata za ta yi dan sai ta fi wulak’anta idan ta haukace akan jinya.
Sam ba ta da mu da sharad’in bokan ba da yace mata”idan ta b’arbad’a abun Inna ba ta bi ta kai ba to itace za ta haukace”
Tashi d’aya tace masa “ta amince!”
Hakanan ta zube masa mak’udan kud’ad’e ta amso ta taho saboda ta san a inda za ta zuba ta yadda dole innar sai ta bi ta kai, ai abun ma ya zo mata da sauk’i tunda yace”kowa zai iya bi kawai dai ta tabbata itama Innar ta bi ta kai.Kuma awa ashirin da hud’u abun zai yi bai lalace ba saboda yana da k’arfi.”
Dan haka ta gama tsarawa a bakin k’ofar ban d’akinta za ta zuba ta san ko cikin dare ko da safe ko da rana dole ta shiga ta yi uzuri ta yi alwallah!ai Inna ta tafka babban kuskure da ta bata access da bedroom d’inta…hakanan tana ta sak’e sak’e a ranta ta iso gida jakarta kawai ta ajjiye, ta nufi cikin gidan…a nan ta samesu duk d’insu gaba d’aya har Baba ana hira,inna kuma tana zaune a kan darduma tana lazimi dan har ta yi shirin barci.
Tana shiga suka fara tambayarta ya jikin maman Abbakar d’in tace da sauk’i,daga nan ta fara rarraba ido lucky for her Manubiya tace mata”ya yi barci yana d’akin Inna,in kun zo tafiya sai in d’auko miki shi.”

Ita ba ma shi take nema ba amma daga jin hakan ko gama rufe Baki ba ta bari Manubiya ba ta yi ba ta yi wuff ta mik’e ta afka d’akin tana mai cewa”ai
yanzu za mu tafi ma bari in d’auko sa!”
Tana shiga ta tura k’ofar ta mayar ta rufe,sai da ta zuzzuba tukunna ta mayar cikin bra d’inta ta d’auki mai sunan Baban ta fito ta yi musu sallama ta tafi yau ko jiran ya Musbah ma
Bata tsaya ba…shima kuwa ya zauna sai da ya gama zancensa da Hadiza tukunna ya koma kuma da ya je ya balbaleta da masifa dan bai
san da zancen zuwanta dubo maman Abbakar da daddare ba sam ba ta tambayesa ba,sannan yace”idan Inna tana cikin d’akinta to za ta iya shiga in har kuwa ba kowa a cikin d’akin kar ta sake afka mata d’aki kamar yadda ta yi d’azu tun da d’akin ba na sa’arta bane ba!”
Saboda shi har ga Allah haka kurum bai yarda da shigar tata da ta yi ba da yanayinta na yau gaba d’aya bai yarda da shi ba.

Ga mamakinsa har k’asa ta durk’usa tace”ya yi hak’uri ba zata k’ara ba!”

Ita kuwa a ranta cewa tayi “kar ka damu,zuwa gobe mai karekan ba za ta sake samun dama ba!daganan wallahi ko
kara idan na ajjiye baka isa ka shallaketa ba.!!”.
[17/09, 8:03 p.m.] Hauwajidda: MANNUBIYA
(Book 2)
Final Episode.

Na
Humayrah Bulama

Mikiya Writers Association.

Idanunta biyu a lokacin Yaron ya dameta da kukan yunwa dan rabonsa da abinci tun jiya kafin ta tafi wajen makeup.
Kamar ba zata je ba sai kuma ta mik’e ta nufi k’asan..

Duk mik’ewa su Ummi suka yi suna buk’atar k’arin bayani…tashi d’aya Ummi ta tafi Luu zata fad’i sakamokon ganin Munirat da ta yi ta shigo tana hawaye,da sauri Daddy ya yi saurin rik’eta shima ya mayar da hankalinsa ga Munirat cikin kid’ima yace”Munirat!!”
Duk sai a lokacin su Yasmeen suka lura da ita Kausar kuma ta yi turuss ta ja ta tsaya ta gagara k’arasowa k’asan idanunta kyam!! a kan Munirat….

A zuciye Yash ya k’arasa ya fincikota ya wurgota tsakiyar parlourn wanda sai da ta kai k’asa ta zube tsabar yadda ya yi cilli da ita….cikin tsana da kyama ya k’arasa ya tsaya a gabanta ya ce mata”ina d’anta????”

Gaba d’aya kowa kansu ya yi dan babu wanda ya fahimci inda Yash d’in ya dosa….
Ganin an zagaye su asirinta yana shirin tonuwa ne ya sanyata ta mik’e cikin in ina tace”Ya Yash D’an wa kuma???ban gane ba..”

Mahaukacin Marin da ya zuba mata sai da hancinta da bakinta suka fashe cikin tsawa yace”Kausar ina d’anta!????”
Dafasa Daddy ya yi jikinsa yana karkarwa yace”Yash me kake magana akai haka ne mai ya faru??
Dai dai nan Hajiya mama da Yadira waenda suka ji ife ifensa suma suka sauk’o k’asan……

Jikinsa yana wani irin karkarawa yace”Daddy ka barta ta bani amsa sannan ta yi bayani da bakinta!!
Sai kuma ya kalli Kausar a karo na uku ya daka mata tsawa yace”Kausar ina d’an Munirat???”

Luuu Ummi ta tafi da zube!!saboda dama ita tunda Munirat d’in ta shigo da ta kalleta ta fahimci kamar haihuwa ta yi kuma sai da Yash d’in ya fara waennan maganganun tukunna kwakwalwarta ta shiga tariyo mata alamomi da dama data gani a tartare da Munirat d’in kafin ta gudu……

Salati duk y’an parlourn suka d’auka dan suma sun fara d’aukar haske yayinda Kausar ta fashe da kuka ta durk’ushe a wajen tace “wallahi ni bansan mai kake magana a kai ba…..”

Zuwa yanzu Yahanasu da Manu da Munirat sun samu Ummi ta farfad’o dan haka Munirat ta mik’e ta k’arasa inda take ta tsaya tace”Kausar baki fahimci abunda yake nufi ba?har kin manta yadda kikayi ta kuka kina rok’ata in rufa miki asiri kenan???”
Kallon kallon aka fara yi kafin Daddy ya shiga gaban kausar ya tsaya a gaban Munirat yace”ki yi mana bayani dalla dalla!”
….
Hawayenta ta share kafin ta fara magana”Daddy ku yafe mini na biyewa sharrin zuciya da son da nake yiwa Yassir na jefe kaina halakar da nakasa fuskantarku da tabon ya sanya sai da na gudu na bar gidan nan dan ba zan iya facing kowa ba!!
Yassir ya yaudareni da kalmar so ni kuma na biye masa…haka muka taru da ni da shi muka dinga tafka b’arna har ta kaini ga samun ciki,kuma Likita ya tabbatar mini muddin na yi yink’urin zubarwa to kodai in mutu ko kuma in rasa mahaifata…shiyasa na dawo na samu Yassir dan a lokacin ma har mun rabu…sai da na dinga kuka a gabansa Ina magiya jinina ya hau
na shiga masifa mai tayin yawa tukunna ya yarda zai taimakeni,hakanan ya kaini wani gida flat mai two bedroom ya zuba mini kayan abinci ya yi gaba yace idan na haihu in kirasa sai mu kai Yaron gidan marayu…….
Ban sake ganin Yassir ba sai da cikina ya cika wata na biyar kwatsam suka zo mini da shi da Kausar suka ce min Kausar ta yi b’ari suna buk’atar idan na haihu in bata Yaron a samu a rufawa juna asiri…da farko ban yarda ba dan ko da Yassir yace za a kai Yaron gidan marayu jinsa kawai nake yi amma na gama tsarawa Ina haihuwa zan bar garin da d’a na mace ko namiji saboda Ina matuk’ar son abuna.
Magiya kuka da kuma nuna mini alfanun yin hakan da yadda za mu taimaki juna da Kausar da Yassir suka yi ne ya sanya na chanja ra’ayina na amince idan na haihu Kausar sai ta karb’a ni kuna sai in dawo gida gareku ba tare da kowa ya san abunda ya faru da ni ba in yi rayuwa ta kamar farko.
Chapter 125 · 0% Book details