← Book details Munnubiya Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 28 OF 137

Sashe 28

Munnubiya Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Adaidaita sahun su Siyama tana yin parking
motocin Abokan ango suka k’araso suma wajen guda goma.Ba k’aramin dad’i Siyama ta ji ba da taga babu motar Najeeb a ciki,abunda ba ta sani ba kuwa ashe mota ya chanza…d’azu da Yahanasu ta yi shirin kiransa ashe ya shiga ita bata sani ba,daga jin yadda Siyaman take bada excuse tashi d’aya ya fahimci dodging d’insa take yi,shiyasa ya chanjo mota mai tint yana tunani da addu’ar shigarta motar dan yana buk’atar su fahimci juna a yau ya wanke bak’in fentin da tayi masa.
Ana ajjiyesu ya hange ta kuwa,murmushi ya yi yana jin wani sanyi yana ratsashi,
ya san ya yi mata laifi
kuma Ya isha ta b’ata mishi sunanshi a idon Siyama
amman kuma abunda tayi
wanda yake nuni da kamar kishinsa ne takeyi hakan ba k’aramin dad’i ya yi masa ba….

Ba kad’an ba Munirat ta girgiza da ganin gidansu Manubiya
hatta su Jidda sai da suka d’an fahimta,gudun kar su ji ba dad’i ne ya sanya ta yi sauri ta ware dan ita kawai mamaki ta d’an yi ba wai kyama ko wani abun ba dan ta san da talaka da mai kud’i duk Allah ne ya yi su.

Kudin yana cikin jakar jidda shiyasa ta tsaya sallamar mai napep d’in su Siyama kuma suka ce bari suyi sauri suje su sanar dasu a fara shirye shirye.

Tana gama bada kud’in ta juyo kenan kawai ta ga mutun a tsaye a daff da ita.Ba ta d’ago ta kalli fuskarsa ba
amman tabbas ta fahimci shine sannan ga k’amshin turarensa da ta sanshi da shi
shekara da shekaru!
She’s not suppose to be feeling this way!kamata ya yi ace babu wani sauran son sa da k’aunar sa da ya rage dede da kwayar zarrah a cikin zuciyarta sai dai kuma tashi d’aya ta ji komai ya dawo mata sabo kamar ma bai tab’a yi mata laifi a rayuwa ba haka takeji a halin yanzu,ba ta da wani burin da ya wuce ta d’ago ta kalli kyakkyawar fuskarsa ma’abociyar murmushi wadda ta bada gudun mawa matuk’a
wajen sace zuciyar ta!
ta yi misssing d’insa sosai sannan ta tabbatar wa da kanta har yanzu tana son abunta amman kuma ba zata iya ignoring abunda ya yi da kuma wahalar da y’an uwanta suka sha duk a ta dalilinsa ba.!
Dan haka da sauri ta yunk’ura za ta matsa shi ma ya yi sauri
ya sake shiga gabanta ya tsaya har sai da goshinta yad’an bugi k’irjin sa!.

She’s trying real hard amman tabbas ta ga alamun
Al’ameen ya rantse sai yayi breaking d’inta….ba ta san
lokacin da hawaye suka fara sintiri a kan kyakkyawar fuskarta ba tana jin wani irin yanayin shauk’i k’auna tausayi mai tafe da rashin jin dad’in hakan da ta ke ji game da shi.

Wata nannauyar ajiyar zuciya ta ji ya sauk’e kafin yace
“Ba ki ma yi missing d’ina ba ko?takura miki ma nayi ko?
Jidda kin tsanesu har haka
ko kalllona ma bakya son yi?”
Ya k’arashe maganar tasa a hankali sannan kamar mai shirin fashewa da kuka!.

Sai da ta yi kokawa da zuciyarta tukunna ta samu ta d’aga mishi kanta alamar ‘EH’.
Shiruuu yayi kamar baya wajen
shiyas ta d’an d’ago ta kalle sa,ba ta yi zaton ganin hawaye a idonshi guda d’aya ba amman sai ta yi sauri ta saka a ranta crocodile tears ne sannan ta yi saurin mayar da kanta k’asa….
So take ta ce ya matsa ta wuce amman ta kasa saboda asalin gaskiya sam bata k’aunar matsawa daga gareshin.
Ajiyar zuciya ya sauk’e
tare da fesar da numfashin da har sai da ta ji calm scent d’in numfashinsa kafin yace”Na san dole za ki ji haushina dole
za ki yi fushi da ni amman ba ki san yadda na ji da kika ce ko ganina bakya son yi ba,a tunani na mun wuce haka!.
Amman ba komai laifina ne
na d’auki blame d’in saboda Jidda bakya laifi a wajena kin riga kin sani.Alfarma d’aya nake nema a wajen ki
dan Allah dan Annabi kiyi min adalci ki taimaka ki bani lokaci
In yi miki clearifying komai
dan Allah pls”
Ya k’arashe maganar tasa yana mai had’e hannayen sa biyu waje d’aya alamun rok’o ba tare da ya damu da a waje su ke ba.

D’agowa ta yi ta kallesa da idanuwanta da suka cicciko da hawaye kafin tace
”Ya Al Ameen!
ni da kai
ba zai yiu ba!.
Baka san halin da ahalina suka shiga ba duk a ta dalilin biyewa son zuciya da nacin mu,idan
akwai alfarmar da zan rok’a a duniya a halin yanzu daga gareka shine ka fita a harka ta ka hak’ura dani ka rabu dani har abada dan girman Allah”

Da sauri yace”Jidda kin san ba zan iya ba”
D’an matsawa gareta ya yi wanda hakan yasanya ta ja baya da sauri,kamar zai fashe da kuka ya share fuskarsa da duk hannunwansa biyu sannan
ya d’an ja hanci kafin yace”Pls just one more chance!I’ll make everything right I promise
sannan zan yi miki clearifying komai,na san
kina jin haushi na ne akan rashin nemanki da na yi tun bayan tafiya ta,Inada reason Jidda kuma na san idan kika ji za ki yi min uzuri”

Sunkuyar da kanta ta yi sosai ta share hawayenta daga haka ta zagayesa dan ba ta ga amfanin tsayuwar tasu ba,ita kunya ma takeji wani a cikin y’an gidan su ya ganta da Al’ameen.

Tana wuce sa ta ji ya rik’o vail d’inta,da sauri ta juyo da niyyar ce masa ya cikata amman sai ta gagara sakamakon ido biyu da suka yi da Ya Musbah.
Tashi d’aya ta rikice wanda hakan yasa Al’ameen d’in waigawa shima,shi kansa sai da ya d’an ji kunyar Musbahu dan haka ya d’an lumshe ido ya bud’e kafin ya k’arasa juyawa gaba d’ayanshi.Ganin yadda Ya Musbahn ya k’i kallon either of them instead kawai ya tsurawa hannun Al’ameen wanda ke rik’e da mayafin Jiddan ne ya sanya Al Ameen d’in cikata a hankali,daga haka ya d’an fesar da numfashi ya kallesa sosai tukunna ya mik’a masa hannu alamun su yi musabaha.

Ba tare da ya kallesa ko hannunsa ba ya cewa Jidda
“Wuce ki shiga gida!”

Kamar jira takeyi
kuwa hakanan ta wuce wuff
har tana d’an tuntub’e.

Bata san ya sukayi ba amman ko da ta je gaff da shiga gidan ta juyo ta tsinci Ya Musbah ne yana magana da Al’ameen d’in kuma daga gani ba maganar dad’i bace dan ran Ya Musbah a mugun b’ace yake yi masa
maganar har yatsa taga yana nunawa Al’ameen d’in.

Tana shiga d’akin su ta fara nufa,ba kowa daga Inna sai Mama sai wata y’ar tsohuwa(iya ramma).Inna tana had’a y’an ragowar kayayyakin Manubiya da suka yi saura tana hawaye Mama tana zauna a gefenta suna rarrashinta ita da iya ramma.
Anan ta zauna ta shiga taya Inna suna yi suna hawaye duk su biyun sun k’i ma su ji rarrrashin da ake ta yi musu.

Jidda ba ta yi mintina uku da zama ba…suna gama zuge akwatin wayar Mama ta hau k’ara,cikin mutuwar jiki ta k’arasa ta d’auki wayar a hankali ta kara a kunnenta dan duk su Inna sun gama kashe mata jiki…
“Subahanallah”
Suka ji Mama ta ambata kafin tace”ki yi hak’uri ki daina kuka gani nan zuwa.”

Tana ajjiye wayar Inna ta mik’e ta na share hawayenta kafin ta shiga tambayar ta “mai ya faru?”

A gaggauce tace mata”Ammi ce ta kirani wai in zo mu kai Al’ameen asibiti yanzunna haka kurum yana shiga gida ya yanke jiki ya fad’i…dama ni tun da ya dawo wallahi na lura kamar ba shi da lafiya kullum wani iri nake ganin sa.”
Cikin rashin jin dad’i ta k’arasa ta rike hannun Inna kafin tace”ki yi hak’uri inna,na so in zauna na raka Manubiya d’akinta,amman Alhaji baya nan dole suna buk’atata!”

Da sauri Inna tace”kar ki damu ki je ba komai hakan ma wallahi na gode kwarai Mama,Allah ya basa lafiya”

Ahankali ta jinjina kai tukunnan ta yi musu sallama ta wuce,sai da ta fita tukunna Inna ta lura da yadda Jidda ta cusa kanta a cikin cinyoyinta jikinta har wani irin vibration yake tana wani irin silent kuka kamar ranta zai fita,ajiyar zuciya ta sauk’e dan dama sai da ta saka haka a ranta daga jin bayanin Mama….a hankali ta k’arasa kusa da ita ta zauna tukunna ta sa hannu ta d’ago fuskarta wadda ta yi dagaje dagaje da hawaye da gumi har ma da majina,sai da ta share mata fuskartata tukunna ahankali sosai tace”kin had’u da shi ne yanzu?”

Cikin kuka Jidda take kallonta tana so ta yi magana amman sam sai ta gagara shiyasa kawai sai ta afka jikin Inna ta sake fashewa da wani Irin kuka abun tausayi.

Ajiyar zuciya wannan tsohuwar ta sauk’e kafin ta k’araso kusa da su ta ci gaba da lallashinsu dan ita ba ta ji abunda innar ta ce da Jiddan yanzu ba……Sun jima sosai matar tana lallashinsu kafin da kyar aka samu Jidda yi shiru ta shiga sauk’e ajiyar zuciya a jere a jere.

A haka Siyama ta shigo ta same su itama idanunta sun yi jaa alamun ta taya Manubiya kuka,sai da ta k’arasa kusa da su ta zauna jikinta duk a sanyaye tukunna tace”Umma tace wai ace miki iyayen ango sun zo,a je a ce musu su shigo ne?

Dum!!
Haka duk su biyu suka ji k’irjin su ya buga.
A hankali Inna ta kalli Jidda tace mata”su je ita da Siyama su shiga da su parlourn su Siyaman. “
Ba su dad’e da fita ba itama suka fita ita da wannan Iya ramma wadda ta tilasta mata dole suka wuce parlourn su Siyama tare…..

Su Jidda suna fita da Baba larai suka fara cin karo tsaye
a bakin motar Yassira tana zazzare ido tana k’arewa gidan kallo fuskar nan a yatsine.
Chapter 28 · 0% Book details