← Book details Munnubiya Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 88 OF 137

Sashe 88

Munnubiya Part 2 Complete Hausa Novel · about 7 min read

An kai ruwa rana kafin da kyar aka samu ta farfad’o….ruwa Dr ya sake jona mata ya fita ya je ya kwaso wasu allurai ya yi mata har da ta barci…Sai da bacci ya yi awon gaba da ita tukunna ya sauk’e wata nannuyar ajiyar zuciya ya juyo ya kallesu yace da Ummi”jiya jiya na gama ja muku kunne akan d’aga mata hankali ko?za fa ku ja wa yarinyar nan stroke da k’arancin shekarunta idan ba ku yi wasa ba!,jininta maimaikon ya sauk’a hawa yake kuma yi ku kiyaye fa!.”

Cikin d’aurewar kai Ummi tace”lafiya fa muke zaune da ita muna magana,na ga ta fara duba wayarta sai kuma na ga ta mik’e daga haka ta tafi ta fad’i a k’asa.”

Numfashi ya fesar kafin yace idan ta farka ku kira ni Allah ya rufa asiri”kawai.
Daga haka ya sa kai ya fice.
Shiruu duk suka yi suka zubawa Manubiya ido kafin Yash ya mik’e da kyar ya k’arasa ya d’auki wayarta a k’asan gado inda ya ga ta fad’a ,matsawa Yahanasu ta yi saboda itaama wayar tata take shirin dubawa….
Yana bud’ewa ya ci karo da sms daga bak’uwar number ta inda aka sanarwa Manubiya abunda ya faru jiya tsakaninsa da Kausar tiryan tiryan tun daga farko har k’arshe….
Jifa ya yi da wayar cikin fushi yace”enough is enough!!!”
Sannan ya fara k’ok’arin fita.
Da sauri Ummi da Yahansu suka tare sa dukda Ummi ba ta ga message d’inba itama zuwa yanzu kwakwalwarta ta bata me ya gani.
Sai da suka yi da gaske tukunna suka iya tsayar da shi dan ya zuciya matuk’a ransa ya b’aci….
Cikin muryar fushi yace”Ummi ki barni in je in same su komai ma ya ishe ni,Wallahi sai na sauya musu kamanni tunda basu san dai dai ba!”

Cikin rarrashi tace”Yash wa za ka tunkara? Me za ka yi musu?”

Ba tare da sanin inda ya dosa ba ma yace”na san a tsakanin su Yadira so
just let me…..”
Hawayen da suka shiga zubo masa ne ya sanya shi kasa ci gaba da magana sai kuma ya nemi guri ya zauna ya dafe kansa”me na yi musu da zafi haka?me yasa y’an uwana suka tsaneni suka tsani farin ciki na?”
Sai da Ummi ta share hawayen da suka zubo mata tukunna ta k’arasa gefensa kan sofar ta zauna cikin sanyin murya tace”kar ka ce haka Yashjub,ba ka ta tabbaci…”
Cikin katseta yace”Ummi su ne!idan ba su ba wa ya san maganar in ba y’an gidan mu ba?yaushe aka haifi Yaran nan da za su zama mugaye makirai kamar haka?me na tab’a yi musu da za su yi mini haka?”

Shiruu Ummi ta yi dan ta ma rasa bakin magana.Ahankali Yahansu ta matso tace”Kamar yadda Ummi ta fad’a Yash ba lallai su bane ba,ka bi komai a hankali kamar yadda na gaya maka jiya…”ta san ko da ace su d’in ne Mommy ce ta zuga su suka aikata kamar kullum amma kuma ba ta jin a tsakaninsu ta fi tunanin Mommyn ce da kanta ya aikata wannan d’anyen aikin.
Itama cikin katseta ya mik’e yace”Yaha to
waye idan ba su ba?Daddy wanda ya haifeni?ko kece?ko Ummi?ko kuma Mommy?….”
Shiruuu ya yi kafin a hankali ya sunkuyar da kansa k’asa yace”damn it!!”
Sai kuma ya koma ya zauna ya yi shiruuu.

Kasa ci gaba da zama a d’akin Ummi ta yi dan ba ta san ta Ina za ta fara ba..ba ta so tana shigar musu Irin wannan case d’in.
Shiyasa ta kalli Yahanasu ta ce”bari in je Allah ya rufa asiri,Yash k’addara kowa da kalar tasa ka yi k’ok’ari ka cinye jarabawarka.”
Daga haka ta d’au Jakarta ta fice…ba ta da tantama wannan aikin Mommy ne.

Tana fita yace”ki je kema,idan ta tashi zan ji da ita,I can face her…”

Cikin tausayawa tace”Yash ka yi hak’uri”

Wani kalar murmushin da ya fi kuka ciwo ya yi kafin yace”Yaha hak’urin nake yi a ko da yaushe amma wani abun dole aga weakness d’ina!…tunda nake a rayuwata ban tab’a jin labarin uwa irin Mommy ba,I’m not sure yet Akan abubuwan da ta yi mini sannan ta saka su Yasira suka yi mini amma Yahansu tashin hankalin da nake a ciki ba kad’an bane ba saboda Ina jin tsoron ranar da zargina zai tabbata Yaha ban san ya zan yi ba.
Ina jin tsoro in ji sunada hannu a case d’in estate d’ina!
Ina jin tsoro in ji sune suka yi chatting da Abbakar suka bawa Manubiya magani….shiysa nake ta k’ok’arin gocewa amma message d’in nan da aka turo tabbas na san su ne wannan kam ba ni da tantama kuma hakan ya sanya na sake yarda sune suke yi mini abubuwan da na kasa fahimtar ribar su idan sun tarwatsa ni!”
Ya fad’i hakan yana mai sakin kukan da yake ta k’ok’arin dannewa,rungumesa Yahanasu ta yi itama a take wani irin kuka ya kufce mata…Tabbas ta san zafin da Yashjub ya ke ji a yanzu da ya fahimci Mahaifiyarsa ba ta son sa sannan ba ta damu da shi ba ba ta damu da farin cikin sa ba saboda she went through the same thing kuma har gobe tana rayuwa ne a cikin pain d’in….
Sun jima suna kuka babu mai rarrashin wani kafin da kyar Yaha tashiga lallashinsa tana basa baki…cikin sheshek’ar kuka tace”Yash har gara kai!
InshaaAllah na san akwai ranar da za ta zo maka wadda za ka fahimci Mahaifiyarka ta na son ka ba son kashe ka take yi ba tana son dukkanin abunda kake so infact tana son ka fiye da komai da kowa a duniyar nan!
Unlike me! da zan rayu and have to live with the fact that mahaifiya ta ba ta sona ba ta k’aunata ba ta damu da ni ba ta yi using d’ina to get what she wan…”
Cikin katseta Yashjub yace”Yahanasu ki daina cewa haka!babu kyau kin san fa ta rasu kar ki k’ara mata nauyi…kwakwalwata ba za ta iya tuno mini ita ba amma a ko da yaushe hajiya mama tana sanar da ni ita d’in mutumiyar kirki ce,kar ki ce za ki shiga abunda ya faru tsakaninta da Daddy har ta kaisa ga cewa TV ‘kar mu sake ko da ambatar sunanta ne!’ wannan tsakaninsu ne kuma kinga har yau ba mu san menene ba balle mu shiga!
kawai ke dai har ma da ni kamata ya yi mu bi ta da addu’a da fatan samun aljannah…dan Allah Yaha kar in sake ji kin yi wannan furucin game da mahaifiyar ki!.Mommy kuma tunda Allah ki ka ce nasan gagara misali ne….dan haka nima zan yi addu’ar abunda kika fad’a d’in ya tabbata zan yi addu’ar Allah ya sa duk zargi ne kawai muke yi ba gaskiya ba.”

Kallonsa take yi tashi d’aya wani Irin yanayi na tausayi k’unci da rashin jin dad’i suka lullub’eta.Ba ta san lokacin da ta afka jikinsa ta fashe da wani sabon kuka ba.!

Sun jima a haka kafin da kyar suka samu suka lallashi junansu ta sake jaddada masa”ya bi komai a hankali kamar yadda suka gaya masa kar ya d’au mataki a kan kowa ba tare da kwakkwaran shaida ba.”

Awannnin Manubiya biyu tana barci kafin suka ga ta fara motsi…duk su biyun tashi d’aya k’irjinsu ya buga kafin Yash ya dake ya mik’e ya k’arasa ya zauna a setin kanta bakin gadon yacewa Yahansu ta je ta kira Likitan.

Tana gama bud’e idanunta Doctor ya shigo…yana nan inda yake aka gama dubata Dr d’in ya fita.

Yana fita tun kafin su yi magana ta kalli Yahanasu tace”d’azu kin ce za mu yi magana.Dan Allah Yahanasu kar ki ce mini akan maganar message d’in da aka turo mini ne dan Allah Yaha ku ce abunda aka rubuta a jiki k’arya ne.”

Yahanasu tana shirin yin magana Yash ya ce “gaskiya ne.”
A hankali ta saki wani irin kuka mai cin rai….mik’ewa Yahanasu ta yi ta fice zuciyarta sam babu dad’i.
Sai da Yash ya sauk’e wata nannauyar ajiyar xuciya ya had’iye wani abu mai d’aci da ya mak’ale masa a mak’oshi tukunna tiryan tiryan ya fara zaiyyano duk wani abu da zai iya tunawa wanda ya faru a jiyan bai b’oye mata komai ba…

D’ari bisa d’ari ta yarda da shi sai dai kishi takaici da bak’in cikin da suka tarar mata ne suka sanya take jin zuciyarta kamar za ta hantsilo ta fito waje har wani Jan numfashi take yi yana kufce mata.

Dai dai nan Mommy ta ja ta tsaya a bakin k’ofar ita da Ya’isha waenda zuwansu kenan.

Kamar zai fashe da kuka yace”mun so mu d’an jinkirta saboda yanayin jikinki daga baya sai mu gaya miki amma kuma sai aka turo miki message.Ga gaskiya nan na faiyyace miki ita Baby da message d’in nan da aka turo miki da kuma abunda ya faru da ni ya kamata ace kin fahimci so ake yi a raba mu dan Allah dan Allah Annabi kar ki bada k’ofa ki yarda da ni plss dan Allah….”
Chapter 88 · 0% Book details