← Book details Munnubiya Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 120 OF 137

Sashe 120

Munnubiya Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Parlourn taff cike daga Mommy sai Kausar wadda take ta uban bacci ba ma ta san sun dawo bane kawai babu.

Shiruu kowa ya yi har su Yadira da basu san me ke faruwa ba!

Yayinda su Daddy suka tsura masa idanu kawai.

Cikin nutsuwa Yassir d’in ya k’araso ya nemi guri ya zauna ya fara kallonsu one by one dan zuwa yanzu kam ya san something is definitely wrong.

Gyaran murya Abhi ya yi kafin ya kalli su Yasmeen yace “ku d’an bamu guri”

Girgiza kai Daddy yayi yace”ka barsu Abhi,Ina buk’atar shaidu.”
Bai jira d’aukar lokaci ba ya kallesu one by one yace”ina so duk ku zama shaidata!
Daga yau har gaban abada babu ni babu Yassir!!!”
Sai kuma ya kalli Yassir d’in yace”mintuna arb’ain na baka ka tartara ya naka ya naka ka bar mini cikin gidana!!!!”.

Da mugun sauri Yashjub ya juya ya fita Yayinda su Yusra suka kaure da kuka suka shiga rok’ar Daddy suna basa hak’urin ya taimaka ya bar Yassir ko me ya yi bai yi deserving haka ba!….dan Allah ya janye maganarsa.

Daina ji Yassir ya yi na y’an sakanni…
Ya riga ya san duk inda aka je aka dawo su grenade ne Ummul’abaisin wanan mummunan al’amari da ya faru da shi a yanzu,dama ya san delay d’in da ya yi wajen sakar su dole ya yi facing consequences amma kuma a tunaninsa 3 million d’in da ya bayar ta isa ta yi silencing d’insu.
Innalillahi wa inna ilaihirrajiun ya shiga ambato a cikin ransa dan bai ma san mai zai yi ba ya zai yi ba mai zai ce ba!!!!.
Is this really happening to him kokwadai mafarki yake yi….zai iya cewa tunda yake a rayuwar sa bai tab’a zama helpless cikin matsanancin tashin hankali ba irin wannan!!
Na farko ya san tabbas an san me ya yi na biyu kuma yanzu shi idan ya fita ta ina zai fara?
Ba shi da halin da zai iya ciyar da rai biyu,besides da ma ya gama tsarawa ita kanta yanzu kam sai dai ta ci gaba da ciyar da kanta dan last kud’in hannun sa ne ya yi amfani da su ya je Abuja ya dawo……

Da farko zuciyarsa tunzurasa ta fara yi akan ya yiwa Daddyn bori yace”babu inda zai je sannan yace sharri aka yi masa amma kuma indai videos da voice d’in da mutanen suka turo masa shi suka turawa su Dad tou tabbas bai Isa ya fara cewa sharri baneba..Idan ya yi hakan kamar ya sake tsunduma kansa a wani sabon bala’in ne…so it’ll be better for him ya yi laying low a halin yanzu da halin da yake a ciki.

Cikin fushi Abhi yace”we are morethan disappointed in you Yassir ban tab’a tunanin za a samu b’ata gari a cikin zuri’ar mu ba!dan haka tun kafin mu fara yi maka baki ka b’ace mana daga gani a yanzu yanzu ba sai anjima ba!.”

Dai dai nan Mommy ta sauk’o k’asan.

Wani Irin rikicewa parlourn ya yi da koke koke hatta Yahanasu sai da ta yi hawaye kafin daga bisani ta mik’e ta shige d’akinta.

Dai dai nan Mommy kuma tana k’arasowa cikin parlourn ta tsaya a tsakiyarsu ranta a mugun b’ace hankalinta a masifar tashe jikinta yana wani irin karkarwa tace”Ashe dama gulma da munafuci aka shirya shiyasa na ganku gaba d’aya kun yi family kun zo????”

Bata ga mik’ewar Daddy ba sai k’arasowar da yayi ya d’auketa da wani mahaukacin mari!!
Cikin tsananin fushi hargagi da hargowa yace”dabbancin naki yau har ta kan Mahaifiyata ya biyo Khadija!!!saboda ke mahaukaciya ce wadda ba ta san wa ya yi mata gata ba shine a gaban idanunmu za ki furta wannan kalmar??
Waye ya ke yi miki munafurcin??”
Ya yi mata tambayar kamar yana shirin rufeta da duka!
Tashi d’aya Mommy ta sha jinin jikinta tashin hankalin da take a ciki ya sake hauhawa…Tabbas a yadda ta ga Daddy ya fusata d’innan ta san muddin ta biye masa to fa za ta janyowa kanta matsala….
Shiyasa tashi d’aya ita ta sauk’o a take ta fashe da kuka ta durk’ushe a wajen cikin kuka tace”ka yi hak’uri Daddy dan Allah ka yi hak’uri b’acin rai da tashin hankalin jin abunda kak’e ik’irari ga Yassir ne ya janyo hakan amma ka yi hak’uri da abubuwan da na fad’a ba zan sake ba sannan da n Allah ka yiwa Yassir adalci hak’uri ko me ya aikata a ganina bai chanchanci hakan daga gareka ba!”

Da mugun sauri Yassir ya mik’e ya fice..inshaaAllah tunda har Mommy ta sauk’o ya san za ta san abun yi.

Cikin kuka Ya’isha ta tari numfashin Daddy tace “Daddy ka yi hak’uri akan komai,dan Allah.
Sannan ka duba yadda fa ka ke yiwa Mommy!!!ka sanyata ta durk’usa haka a gaban kowa!!
a gani na kamar yadda ranka ya b’aci muma namu fa zai b’aci idan ka tab’a mana mahaifiya!”
Cikin tsawa junior yace mata”bar nan kafin na yi ball da ke!!
Manya suna magana kina saka musu baki that too ‘rude tone’!!”
Harara ta zabga masa wanda hakan ya sanya ya mik’e ya nufota gadan gadan,cikin bashi kwarin guiwa Hajiya mama tace”kana zuwa ka rufeta da duka kar ka raga mata!!”
Ganin yadda ya taho kuma ta san tsaf zai aikata ne ya sanya ta mik’e ta bar wajen da gudu ta haye sama tana sharar hawaye.”
Tsaki Hajiya Mama ta yi tace”marar kunyar banza”
Sai kuma ta kalli ragowar tace”duk wadda na sake jin muryarta a cikin ku za ta sha mamaki.”

Yayinda Daddy ya had’iye wani abu mai d’aci a mak’oshinsa da kyar ya juya kawai ya k’arasa ya d’auki wayarsa ya fara k’ok’arin playing video d’in da sauri Abhi yace”ka yi hak’uri ba sai kowa ya ji ya gani ba”
Cikin fushi Daddy yace”tabbas Abhi ya kamata kowa ya ji ya gani sabida idan ba haka ba wannan makirar matar sai ta k’unsa k’iyayyata a zuk’atan dukkannin jama’ar gidan nan dan cewa za ta yi Yassir bai yi mini komai ba hakanan na koresa,kalli fa kukan kissa da kisisinar da take yi bayan itace silar komai!
Muguwar zuciyar ta da gurb’atacciyar tarbiyyar ta su suka janyo komai dan haka kawai ka bari kowa ya ji ya gani.”
Daga haka ya wuce ya k’arasa inda take ya cilla mata wayar yace”bud’e ki kalla ,kalla ki ga abunda rashin tarbiyyar da kika yiwa y’ay’ana ya janyo mana!!ki duba kiga abunda Yassir ya aikata a d’an uwansa…..”
Tarin da ya sark’afe sa ne ya sanya ya gagara ci gaba da magana…
Da sauri Abhi da Hajiya mama suka k’arasa inda yake suka ruk’osa suka kaisa kan kujera suka zaunar Junior ya yi saurin matso masa ruwa daga dispenser ya kawo….
Shiruu parlourn ya d’auka in banda sheshshek’ar kukan Mommy da na su Yassira ba ka jin komai!!.

Mommy ce take kallon video d’in amma iyaka voice d’in Yassir da bayanansa sun fahimtar da kowa na wajen abunda ke faruwa!!!

A tare Yasmeen da Yadira suka mik’e suka bar wajen suna wani irin kuka kamar ransu zai fita dan ba ma su san abun cewa ba.

Da kyar aka samu Daddy ya dawo dai dai,tarin ya d’an lafa…cikin gajiya da komai ya d’ago ya kalli Hajiya mama yace”ki gafarceni Hajiya mama ba zan iya ci gaba da zama da matar nan k’ark’ashin inuwa d’aya ba!”
Gaba d’aya a tare Yasira
Yusra da Mommy k’irjinsu ya yi wani irin mahaukacin bugawa..Ummi kuwa ta san me Daddy zai yi dan ya dad’e da gaya mata matsayin Mommy a cikin gidan dan haka ta mik’e da sauri ta wuce sama…..

Har ga Allah Junior ya ji dad’in abunda ya faru da Yassir amma kuma sam bai ji dad’in abunda yake da shirin faruwa da Mommy ba shiyasa ya ce”Daddy koma me Mommy ta yi ka yi hak’uri…”
Cikin tarar numfashinsa yace”Junior ba ka san me ta yi ba!!!”
A hankali yace”Daddy ta ci albarkacin y’ay’anta!!!”

Girgiza Kai kawai Daddy ya yi yace”not anymore!!!
Daga haka ya kalli Mommy yace”shekaru 32 kina zaluntata Khadija..na san nima wasu lokutan na kan sab’a miki ta hanyar nuna soyayyar wata fiye da taki ko kuma nuna halin ko in kula da nake yi a kanki amma Khadija wannan ma duk laifin ki ne!saboda kin san ba na sonki ba na k’aunarki amma haka kika tilasta mini zama da ke…tsakanina da ke wata shari’ar sai a lahira dan wallahi ko da zunubin tarbiyyar Yarana da kika lalata a ka barki ya isheki!!
Duk wata cutarwa da kika yi mini da su Ubangiji zai saka mana!!
A alamarin Khadija
Sam ban kama ki da komai ba Tabbas kin yi k’ok’ari wajen kare kanki amma na san komai laifinki ne kuma shima zaki had’u da Ubangiji zai yi mana hisabi mu uku ya bi mata hakkinta wanda a ko da yaushe idan na tuna hankalina tashi yake yi matuk’a amma dole na san sai na fuskanci Ubagiji da wannan tarin zunubin da kika yaudareni kika sanya na aikata …..
Kukan da ya kufce masa ne ya sanya ya gagara cewa komai kafin da kyar ya samu ya ci gaba da cewa”zamu had’u da ke a lahira!!!but for now Khadija bana k’aunar in sake jin ko da labarin ki ne dan haka ki bi Yassir ku b’ace mini da ga gani har gaban abada ba na so in sake jin ko da muryoyinku ne!!!!!”

Tabbas wannan itace rana mafi muni a rayuwar Mommy…wani irin kuka take yi tana janyo numfashinta da mugun kyar….duhu duhu kawai take gani!!
tabbas ta san Idan ta biyewa Daddy tsaff zai sake ta a take a yanzu shiyasa ta yanke shawarar tafiya kamar yadda ya buk’ata tun kafin ta b’intike igiyoyin aurenta ta tonawa kanta asiri ta tarwatsa kanta….gara ta samu ta je ta yi sabon shiri a samu ya biyota ya rarrasheta ya d’aukota da kansa ya dawo da ita gidan, daga nan kuma ta san abun yi saboda ta riga ta san ba kowa bace silar wannan bala’in da take a ciki face Manubiya,dan haka dama ta gama tsarawa tunda ta k’i fita daga rayuwar Yashjub gara kawai su mutu tare cikin gaggawa……tun kafin su zamo ajalinta…..
Chapter 120 · 0% Book details