← Book details Munnubiya Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 75 OF 137

Sashe 75

Munnubiya Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Kamar ba zai ce komai ba
sai kuma kawai ya lumshe idanuwa ya bud’e yace‘’d’azun Ina fita sai na tsaya waya,a gani na gwara in tafi da ambulance da sojoji da k’arin y’an kwana kwana…Ina tsaye Ina waya na ga driver d’ina ya zo ya yi parking dama na aike sa ne akwai takardun da zai karb’o mini,yana zuwa ya yi mini knocking glass ni kuma na bud’e masa d’ayan k’ofan nace ya ajjiye takardun a wajen….a nan ne ya ji wayar da nake yi ya fahimci abunda ya ke faruwa an haka ya tsayar na gama wayar ya jajantamin yace mu je tare…motar da ya zo da ita ta fi gudu kuma duk na b’ata lokaci wajen yin waya shiyasa na karb’i makullin nace masa ya maida wannan cikin asibiti ya yi parking sai ya zo
mu tafi…
Ina ga magana sai na ga su Innaa sun fito gashi arean nan ba a samun abun hawa shiysa na cewa drivern nawa ya fara yin gaba ni kuma na tafi kaisu gida.”
Sai da ya d’an yi shiruu ya d’an kalli Manubiya kafin ya d’aura da cewa “muna zuwa muka tarar Baba ba shi da lafiya shine na mik’a su asibiti…”
Cikin tarar numfashinsa Mommy tace ‘’saboda uban ta bashi da lafiya shine ka gagara d’aukar wayar uwarka da ubanka??”
Da sauri yace “a’a Mommy ba haka bane,garin kiraye kirayen wayar da na dinga yi ne saboda yadda na rikice inaga na saka wayar tawa a silent
sam ban ji kiran ku ko d’aya ba wallahi.”

Wani irin kallo Mommy take yi masa kafin chan kawai ta juya ta fice kamar wadda za ta tashi sama ba tare da ta sake cewa komai ba.
Hakama Yassira ta matso da da’n guntun hawayen ta wai “she almost died d’azu da ta yi tunanin wani abun ne ya same sa ashe shi yana chan yana hidimar gabansa ya barsu hankalinsu duk a tashe kuma ya zo amman ko ya nuna damuwar sa akan d’aya daga cikin su gaskiya abunda yake yi bai kamata ba sam! it’s either ya gyara ko kuma su d’au mataki dan wallahi tsaf sai su fice a harkarsa shima saboda gaskiya abun nasa ya yi yawa ta san shine babba akanta amma dole ta gaya masa ‘he is wrong!’.”
Tana gama fad’in haka ta juya itama a fusace ta fice ..
haka suka juya one by one suka fita zuciya a kumbure.
Su ne suka yi rashin mutunci amma tun daga kan Mommy har izuwa kan Yadira babu wadda ta ji zuciyarta ta d’an yi sanyi ji suke yi kamar su mutu dan tsabar bak’in ciki
Takaici da tsanar Manubiya ta rufe musu ido ta hanasu walwala Yasira da Ya’isha har ma da Mommy ji suka yi inama ace bata farfad’o daga sumar da ta yi d’azu ba kawai da ta wuce lahira…..

…Yarinya sai ka ce y’ar gwal?ace estate d’in ka ya kama da wuta amma ka tafi hidimar iyayenta ba ka je ba sannan da ka gama still ba ka je estate din naka ba ka dawo wajenta saboda ka ji bata d’aukar waya!tabbas ba lalle ma ya san da mutuwar driver d’insa da batun y’an fashin ba tunda har yanzu bai tsaya ya nutsu ya saurari kowa ba ballantana ya ji bayani……

Su Ya’isha suna fita Manubiya ta sauk’e ajiyar zuciya ta juyo ta kamo hannunsa.
Tun kafin tace wani abun yace
‘’Ki yi hak’uri,dan Allah Baby ki yi hak’uri,komai zai yi daidai inshaaAllah kar ki sa damuwa a ranki”
Ahankali ta d’an yi k’asa da kanta kafin tace’’ kar ka sa komai a ranka dan Allah,k’addara dama tana zuwan ma bawa ta ko wacce irin hanya
InshaaAllah Ubangiji zai mayar maka da abunda ya fi estate d’in ka.”
Sai kuma ta kallesa tace”InshaaAllah ma duka ne ya k’one ba,sannan Allah ya sa ba a rasa rai ba,I’m fine now..ka je ka ga halin da bayin Allah suke ciki….”

Jinjina kai yayi ya jata suka k’arasa bakin gadon suka zauna sannan yace‘’ba gobara bane,Najeeb ya ce mini,y’an fashi ne but yanzun zan je inshaaAllah sai in ji komai…”
A hankali tace”Innalillahi wa inna ilaihirrajiun…”
Shiruu ya yi ya d’an k’ura mata ido ya san idan ya zurfafa zancen itama za ta fara zargin abunda yake zargi sannan hankalinta ya tashi kamar yadda nasa yake a tashe maybe ma fiye da nasa d’in,shiyasa ya sauk’e ajiyar zuciya yace”Allah ya tsayar a iya ka hakan…”
Ahankali tace “ameen” hankalinta duk a tashe.
Cikin ruk’ota izuwa jikinsa yace”sannan kar ki damu businesses d’ina have been successful tun farkon shekarar nan har kawo yanzu dan inaga na samu abunda zan iya gina estate d’in ma biyar…ban saka komai a raina ba na karb’i k’addara.
Ko da ace ban samu income da ci gaba a business d’ina ba to banga dalilin da zai sanya in ji takaici ko in shiga damuwa saboda na rasa estate ba.
Ubangiji na ya yi mini ni’imomi masu tarin yawa a wannan shekarar…kinga na farko ya bani ke har da k’aruwa gashi mun samu,sannan abubuwa na da business d’ina sai bunk’asa suke yi
kina ganin dan estate guda d’aya ya k’one zan ji haushi?ai ya bani abunda ya fi estates dubu Baby tun da na same ki”.

A hankali Manubiya ta tafi jikinsa ta kwantar da kanta a kan k’irjinsa ta yi shiruuuu.
For the second time ta ji ya sake cewa “ki yi hak’uri a kan abunda Mommy ta yi miki dan Allah’’

Ahankali tace ‘’ba komai fa,iyaye basa laifi,sannan kai a matsayin ka na Mijina ka daina bani hak’uri ka fi k’arfin haka a waje na.”

Shiruu duk su biyun sukayi kowa da abunda yake tunani..

“Dan Allah ka kaini in ga Baba’’
Muryar Manubiya ta katse masa rikitaccen tunanin da yake yi.Shiru ya yi dama wallahi ba dan Mommy ta tambaya ba da ba zai fad’a mata ba
Su kansu su Innaa cewa suka yi kar ya gaya mata saboda kar ta d’aga hankalin ta.
Muryar ta ce ta sake katse masa tunani jin tana cewa
‘’Dan Allah” a hankali kamar za ta fashe da kuka.

Numfashi ya fesar kafin ya sake rungumeta da kyau yace’’ok zan kai ki amma maybe sai gobe kinga kema baki da lafiya yanzu bara in kira Doctor ya fara duba mini ku tukunna kin ji
ki kira su a waya kar ki sa damuwa zai samu sauk’i inshaaAllah….’’. Sai da ya lallab’a ta sosai tukunna da kyar ta hak’ura a kan goben za ta je dan haka ta d’au waya ta shiga kiran su ,ya ji sun yi magana da Jidda da Inna har ma da Siyama amma bai ji sun yi magana da Ya Musbah wanda tun da ya je gidan kafin su tafi kai Baba asibiti ake ta kiran sa yana cewa”gashinan zuwa”shiruu ya yi sai da ya gama had’a one plus one tukunna ya kalli
Manu yace mata “Ya Musbah bai je bane??har yanzu?”.
Diriricewa ya ga ta d’an yi dan ita kanta lamarin na Ya Musbahu ya fara d’aure mata Kai dan a bayanin Jidda ta fahimci su hud’u ne kawai a wajen Baban yanzu haka gashi idan ta kira sa a waya ba ya d’auka

Dukda shima yana fama anada tasa damuwar amma haka ya daure ya danne tasa cikin nutsuwarsa ya sake ce mata “akwai wani abun ne?is there anything I can do to help?saboda jinin Baba fa ya hau ne sosai”.

Tashi d’aya tun kafin ya gama rufe bakinsa ta fashe da kuka,cikin kukan tace “dan Allah ka kai ni in gansa”
Numfashi ya fesar yace”to bari in kira Doctor ya zo ya duba min ku,tukunna sai in ga ko zai iya barin ki ki fita yanzun”
Daga haka ya mik’e ya fice yana ganin dishi dishi tsabar tension…

Yana fita ta kira Jidda shi kuma ya na fita Ya Nafi’u ya kira dan tabbas ya lura family d’in Manu suna cikin damuwa…
Da farko ya Nafi’un b’oye masa yayi sai da Yashjub d’in ya nace tukunna ya zaiyyane masa komai halin da ake ciki,halin Baraka da yadda ta janye Ya musbah da kuma yadda y’an uwan Baba suka sako shi a gaba..ba su ajjiye wayar ba sai da suka yi wa tufkar hanci daganan suka yiwa juna sallama bayan ya Nafi’u ya yi wa Yashjub alk’awarin zai sanya Baki ya lallab’a su Baba su yarda su k’arbi gidan da Yashjub d’in ya basu su koma..

Ba k’aramin lallashi likitan ya yiwa Yashjub ba da ya ji batun Manu har ta suma amma ba su sani ba,ya san ba laifin sa bane ko na nurses tunda sun gama yi mata allurai kuma ita da Mijinta suka barsu a d’akin sannan da aka zo fita ba a kira kowa ba amma hakanan ya yi ta bawa Yash d’in hak’uri dan ya lura ran sa a b’ace yake.

Dama ba so yake yi ta fita d’in ba aikuwa likitan yana zuwa da ya duba ta yace”ba zai yiu ta fita yau ba gaskiya jikin ta ba kwari”…

Hakanan da kyar ya samu ya sake lallab’ata ta hak’ura dan jikinta duk ya yi sanyi daga wayar data gama yi da Jidda yanzu
Dan Jiddan ta gaya mata komai itama…….

Yahanasu Yash ya kira ta zo
ta zauna da Manubiya yayinda shi kuma ya nufi estate d’innasa….
Chapter 75 · 0% Book details