← Book details Munnubiya Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 132 OF 137

Sashe 132

Munnubiya Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Girgiza kai yayi ya sa Hannu ya d’auko Babyn robar tukunna yace”gaskiya kunyi kuskure amma bansan ta Ina ba!sai dai kuma yadda y’ar tsanar ta yi bak’i hakan yana nuni da aiki ya ci ya kama,kuskuren ne ban fahimci ta ina kuka yi ba
Saboda tunda har ya shafi Ya’isha tou tabbas akwai wani abu da kuka yi ba daidai ba.”
Sai kuma ya kalleta yace”ke fa??lafiya kike jin ki dai ko??”

Jinjina masa Kai ta yi da farko sai kuma tace”idanuwana dai suna ta yi mini dishi dishi tun d’azu!!!!”

Jin jina kai ya yi ya sauk’e ajiyar zuciya yace”idanunki ne kenan zasu tab’u,sai kuma ya mayar da gabaki d’aya hankalinsa gareta yace”idan kinaso za a iya karyawa amma in aka karya ba lalle a sake yi mata ya kamata ba sannan babu tabbacin Ya’isha za ta tashi sai dai mu gwada sa’ar mu!”

Kuka ta fashe dashi tace”kamar ya zaka ce mini Ya’isha ba za ta tashi ba!!idan fa Yarinyar nan ba ta tashi ba wallahi na san duk su Yasira sai sun fahimci komai kuma ba za su tab’a yafe mini ba k’arshentamasu tona mini asiri…”
Cikin tarar numfashin yace”ai
dama sai da na gaya miki aikin yana buk’atar taka tsantsan yanada hatsari….”
Cikin yi mata nuni da babyn robar yace”dan ci kam aiki ya ci…amma kuma halin da Ya’isha ta shiga yana nuni da aiki ya riga ya fara tab’arb’arewa kenan…..kuma zamu iya warwaresa….ta you Ya’isha ta tashi ta you kuma ta tafi kenan amma tabbas Manubiya za ta tashi ita wannan a rubuce yake…..”
Cikin tarar numfashinsa tace”to mu bari mana sai an kaita sai mu warware a tare!”
Girgiza Kai yayi yace”sam ba haka abun yake ba..kuma ni yanzu mintuna uku ne ma
suka ragemini zaki ga y’ar tsanar nan ta kama da wuta (idan har ta kama da wuta to baza a iya warware wa ba)saboda abun ya fita daga hannuna,daga nan!!
dan haka ki yanke hukunci da wurwuri kin riga kin lalata komai da ke da y’ar ki aiki ba ya hannuna kuma….”

Shiruu ta yi kafin tace”idanuwan nawa da na fara ganin dishi dishi a haka zan dauwwama?”

Shiruu ya d’anyi kafin yace”akwai taimakon da zan baki,inshaaAllah za a dace”
Cikin sake jeho masa wata tambayar tace”tashin Ya’isha k’ila wak’ala ne ko?”
Jinjina kai ya yi yace”Bari ki ji ba zan b’oye miki ba Ya’isha ba ma na jin tanada rai dan haka ba zan iya yin komai a kai ba saboda kun damalmala komai ne,gashi kuma bamusan ma ta ina matsalar take…ga dai aiki ya yi yana ci…to shafarta da abun ya yi ne matsalar shiyasa abun zai fi k’arfina!”

A hankali Mommy ta lumshe idanuwanta hawaye suka zubo cikin d’acin zuciya tace”ka bar shi kar ka karya!!!”
Ta ji tsananin zafin mutuwar Ya’isha tabbas amma da ta tuna abunda ya ke faruwa da Manubiya a halin yanzu sai ta d’an ji sanyi ko banza ta san kwalliya ta biya kud’in sabulu!!!!….

Ba ta dad’e da gama rufe bakinta ba Babyn robar ta kama da wuta tana jin tsohon yana cewa “yanzu shi kansa kam bai san ranar da numfashin Manu zai dawo mata ba aiki ba a hannunsa yake ba sun riga sun damalmala komai!!”

Itadai Mommy ta ji sanyi a ranta tunda ba a warware ba ta san duk bala’i ko nan da shekara nawa ne Manubiya ba ta Isa ta fito ba!.

Da shi da ita suka yanke shawarar gara su binne Ya’isha maganar ta tsaya a iyaka su biyu dan idan wani ya sani tofa a kwai matsala
Inyaso
Mommyn sai ta ce ta aike ta k’auye kafin su san abun yi,shi kuma inshaaAllah zai rufewa duk wani wanda zai d’aga mata hankali wajen tambayar ‘Ina Ya’isha’ Baki.

Hakanan suka je wani k’ungurmi daji ya hak’a rami yana shirin d’auko Ya’isha ya sakata a ramin aka kirasa.
Kiran mai matuk’ar mahimmanci ne dan haka yace ta yi masa hak’uri dole
zai tafi ta k’arasa sakata ta rufe ramin ta koma gida,hakanan ya wuce ya barta a wajen jikinsa yana karkarwa dan babban mutum ne ya kirasa ya san a k’allan a lalace yau sai ya samu sama da miliyan biyu…..

Tsoro da fargabar dajin gata tare da gawa ne suka sanya Mommy saka Ya’isha cikin ramin anyhow,ko gama rufewa ma ba ta yi ba hakanan ta yi sauri tabar wajen jikinta ya na karkarwa tana kuka.

Bata wani jima da komawa gidan ba su Yasira suka dawo…
Jikinsu daga ita har Yusra duk a sanyaye suka gaisa tana mai bin Mommyn da wani irin kallo daga ita har Yusran kafin chan ta d’an yi waige waige tace mata “Ina Ya’isha?” hakanan
Mommy ta had’e fuska tace musu”ta turata k’auye!tunda sun hana a tsayar da numfashi ta turata k’auye zata yo musu mai sauk’i…”
Shiruu Yasira ta yi kawai Tana kallonta…sam ba ta son ta zargi Mommy amma kuma considering abunda ya faru ta ji ta gani a jiya ya sanya hankalinta ya kasa kwanciya hundred percent da Momyn tun lokacin da ta ji labarin rasuwar Inna…
Ta jima tana tunani kafin tace mata”I hope bakiyi komai ba Mommy”
cikin alhini ta d’aura da cewa”Mahaifiyar Manubiya ta rasu yau!,ki shirye mu je,mu yi musu gaisuwa.”
Daga haka ta mik’e da niyyar kimtsawa ta fito su tafi.
Shiruu ta ga Mommyn ta yi ta shiga mugun shock kafin kawai ta ga ta mik’e tsaye.
K’iri k’iri ta hau bori tace musu
“ba zata je ba suma kuma ta hanasu zuwa tace ai suma su Manubiyan jiya ba su zo mata gaisuwar Larai ba!”
Da mugun mamaki Yasirar ta bi ta da kallo har ta shige cikin bedroom d’inta ta banko k’ofar…
Tana shiga ta sak’ala key k’irjinta yana dukan uku uku,ta durk’ushe a nan bakin k’ofar…
kar dai maman manubiya ce ta rasu ba manubiya ba…Gidan babu wuta bata jona wayarta ba babu charji shiyasa bata samu ta yi confirming ba dama tun d’azu…inna lillahi wa inna ilaihirrajiun kenan yanzu duk wani effort da sacrifices d’inta sun tafi a banza kenan?
Kaii inaa ba zai yiu ba,inshaaAllah ma ba haka bane ba inshaaAllah Manubiya da mahaifiyarta tata ne suka mutu tare…amma kuma inda Manubiya ta rasu ai da Yasira zata gaya mata…..
Wani Irin bugawa k’irjinta ya shiga yi gashi zuwa yanzu dishi dishi sosai take gani ga wani irin juyawa da kanta yakeyi dan haka ta mik’e da kyar ta k’arasa kan gadonta ta kwanta ta lumshe Idanuwanta tana jin kamar ta saka hannu a cikin k’irjinta ta kwak’ulo zuciyarta ta jefar tsabar azabar da ta ke yi mata………
Bata da wani ragowar hope d’in da ya wuce tirsasawa zuciyarta’ta tsaya ta d’an jira zuwa anjima zata ji labarin mutuwar Manubiyan itama’.
Saboda she can’t even begin to imagine Manubiya ba zata mutu ba!effort da sacrifice d’inta sun tafi a banza!.

Tabbas Yasira ta tsorata kuma ta shiga al’ajabi da lamarin Mommy ko bayan shigar Mommyn d’aki har Yusra ta wuce d’aki ita tana nan a zaune ta ma kasa motsi kafin da kyar ta zaro waya ta Kira Manu ta yi mata gaisuwa tace “zasu zo inshaaAllah”
Daganan ta kashe wayar ta yi shiruuu…chan ta zaro wayar ta ta danna kiran Ya’isha!
Ta san Ya’isha tanada taurin kai amma zata gwada lallab’ata a samu ta hak’ura da aikin da Mommy ta turata yi kawai ta dawo,ba wai son Manubiya take yi ba amma Mommy ta wuce gona da iri tun kafin ta kai kanta ga halaka ya kamata a dawo da ita saiti,Wanne Irin bala’i ne har ka tashi mutum gari ya gari dan kawai ya je ya yo maka asiri ya dawo!har mai ya yi zafi haka…….
Layin Ya’isha yana shiga ga mamakinta kawai sai ta jiyo k’arar wayartata a d’akin da Ya’ishan ta kwana dan haka ta mik’e ta shige….ko da ta je d’akin ta duba ga wayarta har da charger da su AirPod d’inta da watch duk ba ta d’auki ko d’aya ba sannan kayanta ciff suka ba ta d’iba ba daga gani tun jiya ba ma ta tab’a ba…dan haka kawai ta juya ta fita ta je ta shiga buga d’akin Mommy…
ta fi mintuna ashirin a wajen har Yusra itama ta fito ta jona ta tukunna aka samu Mommy ta bud’e,yadda suka ganta dagaje dagaje sannan idanunta duk kwantsa sai da abun ya basu tsoro ya basu mamaki dan haka Yasira ta ji zuciyarta ta d’an yi sanyi amma dukda haka sai cewa ta yi”Mommy ki gaya mini tsakaninki da Allah Ina Ya’isha saboda na duba d’akinta Hatta wayarta ba ta d’auka ba!!”

Shiruu ta yi dan ita sai yanzu nema kwakwalwarta ta bata duk waennnan abubuwan…..da kyar ta nemo mafita tace musu”da k’aramar wayata ta tafi saboda hanya, kaya kuma ta d’auki dogayen rigguna biyu. Dan Allah Yasira ki bar ni in huta mana bakiga situation d’ina ba???
Ki huta kema ki zo ki je mini pharmacy ki siyo min maganin ciwon Ido saboda wannan d’ayan har na daina gani da shi sannan ki fita ki nemo min chargi ina buk’atar in yi waya da gaggawa….Yusra ke kuma ki d’aura girki…”
Tana gama fad’in haka ta juya ta rufo k’ofarta hankali a masifar tashe………

Sai azahar tukunna Yash ya zo…zuwa wannan lokacin kowa ya fara jin tausayin gwaggo Suwaiba saboda sun fahimci zafin abun ne ya sanyata yin hakan dan kwata kwata ta k’i bari a nad’e inna a yi mata sutura…..ta zama kamar wata tab’abb’iya.
Manu tana zaune a parlourn ita da su Siyama da su anty Umma suna kuka su mama kuma sunata lallab’a gwaggo Suwaiba Baba ma yana gefe shi da Ya Musbah in banda hawaye babu abunda suke yi sun ma kasa tsawatar mata!
Suna a haka Muhsin ya shigo yace wa Manubiya “ga Ya Yash a waje yace ta je…”
Manu tana mik’ewa Gwaggo Suwaiba tace mata “tace masa tana son ganinsa ya shigo”
Sannan ta kalli su Baba tace “dan Allah tana buk’atar magana da Yash shi kad’ai…….”

Sai da suka gama kukan su shi da Manu ya lallab’a ta da kyar tukunna ta iya gaya masa sak’on gwaggo Suwaiba ya d’an yi mamaki amma kawai sai ya bi bayan Manu ta yi masa rakiya zuwa cikin parlourn.
Chapter 132 · 0% Book details