← Book details Munnubiya Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 42 OF 137

Sashe 42

Munnubiya Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Har suka nufi stairs bai ajjiye taba kuma bashi da niyyar ajjiyetan dan haka tace
“Inada nauyi fa”
Kallon d’an mitsitsin bakin nata yayi da idanunta da suke a lumshe har yanzu kafin
yayi murmushi yace
“Ni kuma Inada k’arfi..”

Bai ajjiyetaba sai da suka shiga cikin kitchen tukunna ya ajjiyeta a hankali,da kyar ta d’an zame hannayenta da ta sak’ale wuyansa da su suna masu shak’ar numfashin juna,sai da ta daidaita tsayuwar ta tukunna ta fara k’ok’arin bud’e idanunta.

Facing juna sukeyi itada shi
shiyasa tana bud’e idon suka had’a ido yana yi mata murmushi kafin yace”I made it for you”
A hankali ta fara juyawa tun kafin ta gama juyawa tayi facing mini dining table d’in
ta fara murmushi ba wani uban
decoration yayi mai yawa ba just simple and elegant amman ya yi masifar tafiya da imaninta…….flower bouquet ne mai asalin kyau a ajjiye a kan dining d’in da card a ciki,sai ballon guda d’aya babba da aka sak’ale ta sak’k’o kan dining d’in da rose’s masu kyau
zub’e a k’asa da kuma kan dining d’in sai abincn da ya jera a kai drinks da chicken sai
candles da ya kunna y’an kad’an a kan dining tabble d’in.
A hankali ta ji ya yi hugging nata ta baya
kafin yace “Hope you like it”
Murmushi tayi ahankali ta jinjina masa kanta alamun ‘yes!’

Ajiyar zuciya ya fesar yace
“Alhamdulillah”
Kafin ya sake kwarin ruk’on da yayi mata yana mai sauk’e ajiyar zuciya a jere a jere.
A hakan suka tsaya kowannen su yayi shiruu kawai.
Ita ta fara kawo k’arshen shirun sakomakon yadda ta ji yanayin tsayuwar tasu yana shirin chanjawa shiyasa ta d’an muskuta,numfashi ya fesar kafin yace”Oh sorry
Mu je ki ci abincin ko?”
Ahankali ta sa hannu ta fara d’aukar note d’in jikin flower ta shiga karantawa,ai kuwa har da y’ar kwallarta dan ba kad’an ba kalaman soyayyar da ya rubuta suka shige ta suka ratsata…cikin jan hanci ta juyo tace”Thankyou,I love it and I love you more..”
Wani irin blushing ya shiga yi tukunna suka yi hugging juna a wajen suna ji kamar su cinye juna dan so,sun jima a haka kafin ya ruk’o hannunta suka k’arasa kan dining table d’in suka zauna…Sam Manu ba ta ji dad’in cin abincin ba kuwa dan a kan cinyarsa ya d’aura ta kuma shi ya dinga bata a baki tana ci yana bata labari kala kala
Childhood d’insa da schools d’in da ya yi,sai da ya ga ta d’an sake kuma ta ci sosai
tukunna yace “suje su yi sallah”…..Loma d’aya kawai ya iya yi shikam kuma hakan ma dan ta tilasta masa ne saboda sam shi kam ba zai iya wani cin abinci ba,ba wai baya jin yunwa bane kawai dai ya riga ya san bakinsa ba zai iya d’aukar taste d’in komai ba a halin yanzu.

Ganin kmar zai yi mata kuka ne yasa ta hak’ura ta tsaya kallon ikon Allah
Babba yana shagwab’a!
Sai da ta rurrufe ragowar abincin ta saka a dank’areren fridge d’in kitchen d’in tukunna ta yadda su fita d’in dan har ga
Allah bata so su fitan gashi gaba d’aya kunyar shi ita takeji ma shiyasa taketa k’ak’alo aiki.

Shi kam kallonta kawai yakeyi
yana rik’e da hannunta har ta yi ta gama.

Ganin yana shirin d’aukarta kamar d’azu ne ya sanya ta fincike hannunta ta fice da sauri tana murmushi…murmushi shima yayi ya
fito a kitchen d’in yana y’ar dariya yace”First position fa nakeyi a race lokacin Ina skul!
Are you sure
zaki iya tsere min??”
Yayi mata tambayar yana nufota da d’an sauri

Sai da ta d’an rik’e k’asan gown d’in jikinta tukunna ta d’iba a guje ta yi sama
wanda hakan yasa ya fashe da dariya sosai dan bai yi expecting za ta iya gudu kamar haka ba shiyasa kamar jira yakeyi ya bita shima a guje.

Batasan lokacin da tayi ihu ba
sanda ta juya ta ga har ya kusan kamota saboda
ba kad’an ba taji tsoron yadda ta ga har ya kusa kamotan,dan haka ta k’ara k’arfin gudun nata….saida suka kai cikin bedroom d’inta tukunna ya samu nasarar cafkota!da sauri tace”Yi hakuri dan Allah”.
Dariya yayi sosai kafin ya d’auketa d’in da bataso….direct ya nufi toilet da ita,sai da suka shiga cikin shower glass tukunna ya ajjiyeta ya kunna gaba daya shower d’in da suke cikin wajen ya daidaita d’umin ruwan.

Nervousness ne yasanya ta kasa cewa komai ta sunkuyar da kanta k’asa tana jira ya fita
ta samu ta yi wanka dan tana
buk’atar yin wankan….Ahankali taji ya matso ya zare d’ankwalin kanta za ta yi magana yace mata “shhh…”
Har sark’a da d’ankunne sai da ya cire da ribbon,sai da ta ga
yana shirin cire gown d’in tukunna ta san da gaske fa yake,ba ta gama shiga mamaki da al’ajabi ba sai da ta ji ashe shi wankan ma tare yake so su yi…..da kuka da lallashi ta samu ya kyaleta ya fita da kyar,sai da ta fito har closet ta zuge glass d’in wajen ta mayar ta rufe tukunna hankalinta ya d’an kwanta ta koma cikin massive bathroom d’in ta rufo k’ofar…. brush ta fara yi da sabon toothbrush d’in da su Aisha suka jera mata
tukunna ta yi taking warm bath
cikin nutsuwa da kwanciyar hankali ta d’auro alwalla ta fito.
Ta san Yashjub zai yi fushi amman idan ta fito sakawa k’ofarta key zata yi
sa k’arata da safe dan wallahi wani irin fargaba kunya
da tsoro ne suke adddabarta
sannan sai hauhawa sukeyi,ita sai yanzu ma ta ga wautarta da bata yi sauri ta bisa ta rufe k’ofar tata ba d’azu sanda ya fita.
Tana wannan tunanin ta fito daga cikin bathroom d’in
d’aure ta d’an guntun towel gashin kanta na d’igar ruwa dan ya riga ya jik’a mata shi tun d’azu,tana k’arasawa tsakiyar closet d’in suka had’a ido da shi ta cikin glass d’in sanye cikin jallabiya fara k’all!yana durkushe yana bubbud’e
akwatunan ta yana neman abu
motsin ta ya ji shiyasa ya
d’ago ya kalli wajen ai kuwa suka had’a ido.
Ja ta yi ta tsaya chak
ta kasa gaba ta kasa baya.
Murmushi kawai ya yi ya d’auki
hijabin nata da yake nema ya mayar da akwatunan ya rufe ya mik’e ya nufi inda take….yadda yaga duk ta diririce sai da ta basa dariya
da tausayi,shiyasa yana zuge glass d’in ya k’arasa inda take
ba tare da b’ata lokaci ba ya ware hijabin nata ya nemo
wuyan ya zura mata.
Ai kuwa har ajiyar zuciyar da ta sauk’e sai da ya ji kafin ahankali yaji tace “thankyou”
Murmushi kawai yayi yana kallonta yana mamaki da tunanin ta yadda zai sa ta d’an saki jiki da shi ta cire wannan tsoron….jin jina mata kai kawai ya d’an yi kafin yace” welcome,mu je ki yi alwallah muyi nafila”

Ji ta yi kamar tace masa’ita bama ta sallar’sai kuma kawai tace “Nayi”
Jinjina kai yayi daga haka ya kama hannunta suka fita waje cikin d’akin.

Akan kafet d’in ya shimfid’a musu darduma ya tada ikama suka gabatar da sallar nafila raka’a biyu….ya jima yana addu’o’i kafin ya juyo gareta
ya d’aura hannunsa a kan goshinta nan ma ya yi addu’a
tukunna ya gyara zama sosai yana fuskantar yace
Ta mishi karatu yana son jin k’ira’arata….Suratul Mulk ta karanto masa tun daga farko har k’arshe…kamar kuwa kar ta daina haka ya ji,kafin shima yace ta zab’i inda takeso ya karanta mata..ganin ba zata iya magana ba yasa ya karanto mata Suratul Ibraheem
Shiruu ta yi tana sauraron yadda yake karantun bisa ka’ida kamar wani shahararren malamin ne yake karatu haka ta ji,ita har ga Allah duba da yadda ya girma a Uk sam ba ta yi tunanin yana da ilimi har haka ba.
Tambayoyin da suka shafi addini ne suka biyo baya,ba kad’an ba shima ya yaba da ilimin addininta dan haka ya sake godiya ga Ubangiji…. ya ji dad’i sosai yadda matarsa ta kasance mace mai ilimin addini saboda hakan yana da fa’idodi da yawa.
Ganin tana hamma ne yasa yace “Ta tashi ta shirya ta kwanta dan ya lura a gajiye take”
Yadda ta mik’e zumbur!lokaci guda sai da ta basa dariya.
Yana kallonta ta ta d’auki manyan manyan kayan bacci ta shige closet d’inta…drying kanta ta fara yi da hair dryer da su Aisha suka jera mata tukunna ta saka kaya…har ta
fito bai yunk’ura ba kuma bai ce mata uffan ba instead sai kawai ya girgiza kai yana mamakin kayan baccin da ta saka abun takaicin ma har da hula kuma wai a hakan ma sai wani kakkare jikinta take yi…..yana a nan kan dardumar ta zo ta wuce ta haye gado ahankali tace masa”sai da safe”
“Za kiyi bayani ne”
Ya fad’i hakan a cikin ransa
A fili kuma yace”Allah ya bamu
Alkhairi”
Wani sanyi ta ji a ranta ganin bashida niyyar yi mata komai,cikin nutsuwa ta ja quilt d’in dake shimfid’e a kan gadon ta lullub’e duk jikinta da shi,har kanta.
Tsorone ya kamata jin ya mik’e ya je ya kashe wuta kuma bai fita ba,tana cikin tunani da zullumin son jin fitartasa ta ji ya yaye fuskar ta dake cikin bargon kafin yace”Kar ki rufe har fuskarki”
Sai kuma ya durk’usa yayi kissing forehead d’inta yace “good Nyt”
Har da d’an murmushi ta yi mishi wannan karon ahankali tace”nyt”
tana kallonsa ya koma kan dardumar ya ci gaba da karatu.
K’are masa kallo kawai takeyi
tanajin yadda sonsa yake sake shigar ta…ita ala dole tana b’oyewa ne a bargon kar ya gane kallonshi takeyi
ba ta san gaba d’aya hankalinsa yana a kanta ba
duk abunda tayi yana kallon ta.
Chapter 42 · 0% Book details