Sashe 73
Munnubiya Part 2 Complete Hausa Novel · about 7 min read
Bayan kamar awa d’aya wajen ya cika taff da jama’a dan har su Baba larai duk sun k’araso suma kowa in ka kalla hankalin sa a tashe.
Dukda cewa zuwa wannan lokacin sun tabbatr da cewa Yashjub ba ya wajen dan kaff jama’ar dake yashe a harabar wajen da gefen gefen titin a lokacin da abun ya faru an shaida identity d’insu amman kuma rashin amsa wayar ta sa ne ya fi komai d’aga musu hankali a halin yanzu.
Dan haka Daddy ya kalli Yasir wanda duk hankalin sa ya gama tashi da rashin ganin gawar Yashjub…cikin dafa kafad’arsa yace ‘’ka kwantar da hankalin ka Yassir inshaaAllah babu abunda ya samu d’an uwanka,ka nutsu ka yi addu’a ka ji ko? dan ni kam zuwa yanzu inda hope ‘’
Ahankali Yassir ya had’iye wani k’ululun tashin hankalin da ya toshe masa mak’ogwaro kafin yace ‘’To Daddy’’.
Cikin fesar da huci Daddy yace ‘’d’an sake gwada kiran sa mu gani”
Still yanzu ma a hankali ya sake cewa “to Daddy”
Daganan ya matsa gefe k’irjinsa yana dukan uku uku dan baya k’aunar ya kira a yi rashin sa’a ya ji muryar Yashjub safe and sound!..Hatta seconds da komai sai da aka k’irga from inda yake to the estate sannan ya bada numbobin motocinsa duka incase ma
Idan ya chanja mota,kuma sai da suka yi waya da mutanen suka ce masa gashinan ya shiga estate d’in yanzu tukunna suka fara aikin amma bai ga alamun sa a wajen ba!sai driver d’insa wada yanada tabbacin bai cika yawo da shi ba,mai ya faru???where is he????adduarsa d’aya Allah ya sa a wani wajen suka danna gawarsa shiyasa ba a gani da wuri ba!…Allah ya sa a nemota yanzunnan a duk inda take a cikin estate d’in a fito da ita dan tabbas zuciyarsa za ta iya tarwatsewa idan akace Yashjub ya yi getting out of this one alive and safe…
Da kyar ya samu ya d’an nutsu tukunna ya zaro wayarsa daga aljihu,hannunsa har karkarwa yake yi haka ya danna kiran Yashjub..bugu biyu a na uku ya d’auka yace ‘’Yassir! kuna Ina??’’
A hankali Yasir ya lumshe idanuwansa wasu zafafan hawayen bak’in ciki da na tashin hankali suka shiga silalo masa…
Sai da Yashjub ya sake cewa ‘’Yassir ba ka jina ne?kuna Ina??”
tukunna da kyar da mugun kyar ya samu ya iya had’a kalmar ‘’ga mu nan duk a estate d’in ka’’
‘’Okay gani nan zuwa but bawa Manubiya wayar first Inata kiran ta ba ta d’auka!is she fine??”
Shiruu ya yi ya d’an kalli Daddy wanda ganin kamar waya yake yi ya sa ya tunkaro sa
Cikin tsananin rikici Daddyn ya ce “shine??ya amsa?”Sai kuma ya sa hannu ya karb’i wayar.
A take ya lumshe idanuwa wasu hawayen farin ciki suka zubo masa jin muryar Yashjub safe and sound yana cewa ‘’Yassir,ka yi magana mana!Ina Manubiya take?ka bata wayar”
Dai dai nan su Mommy ma suka k’araso wajen,suna masu tambayr su “shi ne?ya d’auka?”.
Sai da Daddy ya jin jina musu kai yace ‘’eh’’ tukunna ya maida hankalinsa ga Yashjub wanda ya rikice ta waya yana tambayar ‘Ina Manubiya?’ya ce
‘’Yash Manubiya ba tana asibiti ba? ka nutsu mana she’s fine ai ko?….”
‘’Daddy tare na barsu ita da su Mommy na fita,and she was very worried a time d’in,sannan yanzu na ji Yassir yace duk kuna estate meaning har da su Mommy kenan kuma ita ban ji ta ba sannan Ina ta kiran wayar ta bata d’agawa..”
Yashjub ya zaiyyane masa hakan a rikice.
‘’Slow down Yashjub” Daddy ya ce kafin ya d’aura da cewa ‘’relax!!ok..”tukunna ya juya ga Mommy yace ‘’Ina Manubiya??”
‘’Tana asibiti”kawai tace da alama ran ta a b’ace yake kafin ta d’aura da cewa
“Duk ya bi ya d’agawa mutane hankali kalle mu gabad’ayan mu a rikice shine tsabar rashin sanin ciwon Kai zai ishemu da Manubiya!Manubiya!!,
Mannubiyan baby ce?goyota yake so mu yi mu taho da ita crime scene irin haka salon shima idan mun yi hakan yace za ‘a cutar da ita??”
Numfashi Daddy ya fesar kafin yace”yanzu fa lokacin murna da farin cikin kasancewarsa safe and unharmed ne godiya ya kamata mu yi wa Allah,ba wai haushi ya kamata ki ji ba‘’sai kuma ya maida hankalin sa ga wayar da yake yi yace ‘’Yashjub Manubiya tana asibiti mu kuma muna estate d’in ka”.
Without thinking twice yace ‘’okay bara in je asibitin’’ daga haka ya kashe wayar kitt!!!.
Shiruuu Daddy ya yi ya kusa minti d’aya da wayar a kunnen sa…kafin da kyar ya zaro ta ya mik’awa Yassir jikinsa a matuk’ar sanyaye….ya rasa dalilin da ya sanya no matter how ya kauce ya goce duk dan a zauna lafiya dole shi kuma Yashjub sai ya fito fili ya nuna masa Manubiya ta fi su matsayi a wajensa itace za ta zo first a sama da kowa da komai na rayuwarsa..he can’t help it but to think anya idan ya yi sake ganin Yashjub d’in ma ba zai gagaresa ba kuwa wata rana?!….
Yahansu ce ta ce
“Daddy mu je asibitin,chan ya nufa ko?”
Saida ya juyo ya kalle ta tukunna ya d’aga mata Kai alamar ‘eh’ da ‘to’ daga haka ya wuce cikin tsananin mutuwar jiki.
Yana wucewa Ummi ta bi bayansa bayan ta bawa Munirat makullin motarta ta ce ta taho a ciki dan tanaso ta d’an fahimtar da shi dalilin da ya sa Yashjub d’in ya yi haka saboda ta fahimci ya ji haushi.
Tana wucewa suma suka fara shigewa motocin su suna bin bayansu.
Wajen ya rage daga Yasira sai Yassir da Mommy da Baba larai
Mommy tsananin mamakin yanayin Yassir da kuma b’acin ran Yashjub ne suka hanata motsi har sai da Baba larai ta tab’o ta tace “mu je ko?”
tukunna ta samu ta d’auke kan ta daga kan Yassir da kyar
suka nufi motar Yasira.
Suna zuwa ta bawa Yassir key amman sai ya zauna a wajen mai zaman banza yace “ta ja su kawai”
dan shi kam ba ya jin hannun sa zai iya d’aukar makullin ma ballantaana aje ga jan motar.
A rikice Yashjub ya k’arasa cikin asibitin ko parkin mai kyau da ma’ana bai yi ba hakanan ya fito ya rufe motar ya afka ciki dan tun d’azu dama ya tsinci kanshi da fara jin tsananin fad’uwar gaba yanzu kuwa da yake ta kiranta bata d’auka kuma ya ji bata tare da su Mommy he can’t help but ya yi tunanin wani abun ne ya sameta
Yana dialing number yana wani irin gudu gudu sauri sauri haka ya afka cikin d’akin.
Sai da numfashinsa ya kusan d’aukewa da ya shiga ya ganta yashe a k’asa wan war kamar matacciya,k’amewa kawai ya yi ya tsaya ya kasa gaba ya kasa baya.
Kafin da kyar da taimakon addu’o’in da yake ta jerowa ya samu k’afafuwansa suka basa had’in kai wajen k’arasawa inda take a rikice ya durk’usa,hannu sa yana wani irin karkarwa haka ya kamo hannunta ya d’aura a ta wajen pulse d’inta
A take ya saki wata k’akk’arfar ajiyar zuciya sai kuma ya rarumo gorar ruwa ya b’intike kan ya shiga shafa mata
yana d’an tapping fuskarta still hankalinsa a mugun tashe.
Wani nannauyan numfashi ta ja ta fesar idanunta a rufe ta shiga magana a rikice a tsorace ‘’Mijina!dan Allah Mommy ku ce ya dawo,mu je mu nemosa,babu abunda zai same shi, Ya Yash d’ina idan ya bar ni wallahi mutuwa zan yi”
Kallon fuskarta kawai yake yi yana jin wani kalar tausayi da tsantsar k’aunar ta tana dad’a ratsa shi, a hankali wata kwalla ta ziraro ta biyo ta sauka a kan fuskarsa..cike da taka tsantsan ya d’agota ya saka ta a jikinsa wanda jin k’amshin turarensa da kuma jinta a jikin Mijinta ya sanya ta dawo haiyyacinta ta yi sauri ta bud’e idanuwanta domin ta tabbatr wa kanta da shi d’in ne?
A hanakali ya d’ago fuskarta yana kallon cikin idanunta yace ‘’babu inda zan tafi in barki, inshaaAllah muna tare har gaban abada.”
A hanakali ta lumshe idanunta tana hawaye tana jin wani sanyi yana ratsa ta..
…Da farko gefen kumatunta ya fara murzawa kafin daga baya ya matso da fuskarta sosai garesa cikin shauk’i k’auna da bege ya had’e bakin su waje d’aya…..
Kamar ance ‘action’haka su Kausar suka antayo cikin d’akin gaba d’ayan su.
Da sauri Daddy ya juya ya fita har yana d’an tuntub’e,ya riga ya gan sa ya ga he’s fine,very fine ma kuwa!
Dan haka ya nufi mota ya wuce gida ya bari akan idan Yash d’in ya koma gida sai ya ji komai daga bakinsa.
Daddy yana wucewa Yashjub ya saki Manubiya ta hanyar yin k’asa da ita ya saka ta a cikin k’irjinsa yana maida numfashi a hankali ba tare da ya juya ba yayin da ita kuma kunya ta sanya ta sake ruk’unk’ume sa ta cusa kanta sosai a cikin k’irjinsa.