← Book details Munnubiya Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 85 OF 137

Sashe 85

Munnubiya Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Cikin d’an b’acin rai Inna tace”wallahi zan iya dafa Al’k’urani akan akasi aka samu,Haba Baba Jidda fa?ashe da ma ba ka yi mata sanin da za ka iya shaidarta idan irin haka ta taso ba?sannan kalli fa abunda Yusuf d’in ya yiwa Yarinyarnan har ta kaisa ga sumar da ita amma shine za ka d’auke ta ka aura masa ita? A ganinka hakan dai dai ne?
Sannan idan kace Yusuf a bayan mu yake ka ji ka gani ya zama mijinta me za ka ce a kan baba habu surikinta,wanda hatta yau da ya san tashi za ka yi a kusa da su kuma saboda su bai tsaya kun yi rabuwar arzik’i ba?”

Cikin tsananin fushi Baba yace”na riga fa na gama magana!babu wani abunda ya Isa ya sakani in chanja ra’ayina,na tabbata inda ace Musbahu ne ya ganta a yadda Yusuf ya gansu ita da Al’ameen da shima abunda zai aikata a gareta kenan tunda hakan ne dai dai…to shi Musbahu ya gudu ya yaye kansa da kansa dan hakan idan Yusuf ya hukunta Jidda a matsayinsa na yayanta hakan bai zama laifi ba….”

Cikin kuka inna tace”ta ya sumar da Jidda ya zama ba laifi ba?”
Da mugun k’arfi Baba yace”Aminatu!!!!!”
Cikin fushi ya d’aura da cewa”ba na son jayayya ki barni in ji da abubuwan da suke damuwa…ba na so in sake fuskantar tirjiya daga gareki,ina umartar ki da ki yi mini biyayya a yi auren nan a gobe a kaita d’akinta idan ba haka ba wallahi wallahi wallahi za mu samu gagarumin sab’ani da ni da ke!”
Yana gama fad’in haka ya juya ya fice…

A hankali Jidda ta mayar da idanunta ta rufe…tana jinta kamar ba a duniyar ba…tunda take ba ta tab’a jin Baba ya d’agawa Inna murya ba sai yau duk a ta dalilin ta…ta na son Al’ameen sannan ta san idan ta auri Yusuf tabbas bak’in ciki ne ajalinta amma kuma inshaaAllah ko alamun tashin hankali ko kuma yunk’urin kare kanta ba za ta yi ba…ta fahimci inna ta yarda da ita ta yi trusting d’inta Manu ma ta san za ta yarda da ita Baba kuma za ta barsa ya aurar ta a Yusuf d’in indai hakan zai sa ya huce,inda rabon wanke kanta wata rana shima zai fahimci ba wani abun suke yi da Al’ameen ba….za ta yi masa biyayya inshaaAllah dan tunda ta fara tirjiya a Yusuf ta nuna Al’Ameen take so babu abunda relationship d’inta da Al’Ameen d’in yake ta janyowa Ahalinta sai masifa………..

Siyama ba ta so kwana a gidan Manu ba amma haka suka tursasa ta gaba d’ayansu abun mamakin har su Yasira waenda suka yi musu k’abe k’abe ko motsi suka yi idanunsu a kansu yake ….su dai su Manubiya kawai sun zuba musu ido ne suna kallon ikon Allah da rashin wayonsu dan wannan rashin wayo ne saboda yadda suke yi kowa ya riga ya san they are up to something shiysa daga Manubiya har Siyama suke ta addu’o’i da neman tsari daga sharrin su…dukda kuwa d’azu Yasira ta bawa Manubiya hak’uri ta ce “ta yi hak’uri akan abubuwan da suka yi mata duk sharrin shaidan ne kuma sun fahimci itace zab’in yayansu ta yi hak’uri inshaaAllah hakan ba za ta sake faruwa ba they wants to start a fresh with her”amma hakan bai sa Manubiya ta yarda da su ba…kawai dai ta bita da murmushi tace mata “komai ya wuce”

Dukda gwaggwo ta zo hakan bai sa sun yi shirin tafiya ba..shima kuma Yashjub bai ce musu komai ba ya rabu da su amma dukda haka idanunsa a kansu yake.
Ko da dare ya yi su da kansu suka tsara cewa’Siyama ta kwana a d’akin Manubiya na da,su kuma za su zauna a d’akin da Yadira ta zauna’.Gwaggo kuma dama tana k’asa d’akin bak’i.

Murmushin yak’e Siyama ta yi dan ta yi tunanin a wajen kwanan ma za su nanik’e musu ne…Yasirar ma gudun kar su ga suna ta manne musu ne ya sanya wannan karon tace a yi hakan.

Sun mik’e kenan kowa za ta tafi ta kwanta wayar Manu ta fara haske a karo na biyar daga zaman su zuwa yanzu,duk tsura mata idanu suka yi sai da ta yi musu murmushi tace”sai da safe”daga haka ta juya ta nufi sama tukunna suma suka wuce d’aki.

Suna shigewa Manubiya ta dawo da sauri ta Isa gaban Siyama wadda ke k’ok’arin shiga d’aki itama tace”Siyama dan Allah ya ake yin blocking mutum,na kasa”
Kallonta ta yi kafin tace”ki duba goggle”kamar ba za ta tambaya ba sai kuma tace”wa za ki yi blocking haka jikinki har yana rawa”
“Abbakar”Manubiya ta bata amsa a tak’aice tana mai daddana wayar hannunta kafin ta d’aura da cewa “ya ishe ni da kira,wai dan Allah yana buk’atar taimakona. Kin san shi kuma Ya Yash ya ce ba ya so ko gaisawa in yi da shi”
Ta faiyyace mata hakan a lokaci guda tana k’ok’arin blocking Abbakar dan har ta gano yadda za ta yi.

Shiruu Siyama ta yi tana tunanin”ko dai ta gaya mata Mahaifiyarsa ce a kwance a gadon asibiti rai a hannun Allah, ta san shi yasa yake ta kiranta.
Ko kuma kawai ta rabu da ita inyaso ita da Jidda sai su san yadda za su yi su karb’i kud’in a hannunta su basa dan ta san kud’i yake so.”
“Done!”
D’in da Manubiya tace ne tana haki kamar wadda ta yi y’ar tsere ya katsewa Siyama tunani.Daga haka Manubiyan tace mata sai da safe ta juya ta haye chan sama.

Sai da Yusra ta ji Siyama ta shige ciki ta rufo k’ofa tukunna ta juya ta nufi su Yasira waenda suka tsura mata ido tana wani irin murmushi….tana zuwa ta zaiyyane musu abunda kunnuwanta suka jiye mata Manubiya da Siyama suna cewa…ji suka yi kamar an yi musu bishara da gidan aljannah!Tabbas Allah ya na son su,saboda dama neman hanyar da za su bi su nunawa Yash kamar Manu ce ta zubar da cikin da kanta suke yi yanzu kuwa Yasira tana jin wannan batun tashi d’aya ta san abun da ya kamata ta yi dan haka ta cewa su Yusran gobe duk runtsi su yi ta kwak’umarta har sai sun ga password d’in wayarta daga nan kuma sai su nemi number a wayr tata,saboda ita gobe za ta fita office…Yadira tana da kwakwalwa shiyasa tashi d’aya tace mata d’azu dai da yake ta kira ta ga number 090443 ne farkon number k’arshen kuma ba ta gani sosai ba
”Ba damuwa,Allah ya sa ba ta yi deleting history d’in ba idan muka d’au wayar time d’in kawai za mu duba na san lokutan da ya kikkirata ai”
Cewar Yasira.
Cikin tarar numfashinta Yusra tace”ko ta goge ma ni na san inda zan shiga in dubo,Allah ya kaimu goben da rai da lafiya.”

Baba larai suka kira suka sanar mata sannan suka d’aura da cewa”Sun fara zuba abubuwan da ta basu a duk abincin gidan,sannan ba za su samu matsala wajen jefa mata tablet d’in a ruwa ta sha ba saboda lucky for them ba ta shan bottle water ko na dispencer iyaka ruwan borehole kawai take iya tara a cup ta sha sakamokon laulayin ciki shiysa easily d’azu tana ajjiye cup d’in kafin ta je ta dawo suka jefe mata kwayar ba tare da sun farga ba daga ita har Siyama,to dai da ta dawo ta d’an yi sip biyu daga nan ta ajjiye maybe taste d’in ne ta ji ya chanja mata shiysa suka yanke shawarar raba kwayar gida uku saboda kar ta gane,to dai a halin yanzu sun zuba mata a gorar ruwanta na borehole uku da ta tara ta saka a fridge za ta dinga sha…”

Murna a wajen Baba larai abun ba a cewa komai..ji take kamar ta zuba ruwa a k’asa ta sha…kafin tace”amma Yasira cctv fa?”
Dariya ta yi tace kar ki damu Baaba ba zai tab’a ganewa ba ta cikin fridge d’in muka saka kuma ba direction d’in cctvn take kallo ba…murmushi ta yi tace”MashaaAllah Alhamdulillah,Allah ya ci gaba da taimakon mu”
daga haka ta mik’awa Mommy,itama duk da tashin hankali da fargabar Daddy sai da ta yi farin ciki matu’uka ta yi ta sanya musu albarka daga k’arshe suka yi sallama suna masu hango silver lining….

A b’angaren Najeeb da Siyama kam a ranar kusan kwana suka yi suna waya…da kyar ta samu ya yi mata sallama suka katse kiran nan da nan bacci ya yi awon gaba da ita yayinda shi kuma ya duk’ufa Nafila…Tabbas ya manta rabon da ya shiga farin ciki kwatankwacin wannan..shiysa ya kwana sallah yana godewa Ubangiji sannan yana rok’onsa ya tabbatar da aurensa da Siyama!…

Ya Musbah kuwa da ya yi alk’awarin zuwa ko alamar sa babu kuma bai yi waya ba,har cikin dare sai da ya Nafi’u ya gawada kiransa amma bai d’auka ba saboda ya Nafi’u ya lura har da takaicinsa ne suka tarar wa Baba ya birkice musu lokaci guda haka…shi kam zuwa yanzu ya daina jin haushin Ya Musbah instead tausayinsa yake ji kuma inshaaAllah zai taimakesa ya fitar da shi daga kaidin Baraka..shiysa ya shirya zuwa gidan nasa gobe da sassafe dan shi da Yashjub dama sun riga sun san gidan…zai je ya samesa su fara ceto rayuwar Jidda da take shirin fad’awa halaka a gobe daganan zai san abunda zai yi dan abun na Baraka ya zama abun tsoro.
[17/09, 8:03 p.m.] Hauwajidda: MANNUBIYA
(Book 2)
Page 35

Kallonsa kawai Daddy yake yi yana nazarinsa,tashi d’aya ya fahimci tabbas dagaske tricking d’insa Kausar ta yi…tunda
ya haifi Yashjub bai tab’a ganin tsoro firgici da tsananin
tashin hankali k’arara a tare dashi ba sai yau.

Ahankali ya rik’e sa yace”Mu je sama ka huta,ka kwantar da hankalinka ka ji ko?ka sasssauta zuciyarka ka bi komai a sannu”
….
Shiruu ya yi yak’i motsi
dan baima san me Daddyn yake cewa ba sam ba ya fahimtarsa tsabar tashin hankali…
“Mu je Yash”
Daddy ya sake cewa.
Sai a lokacin tukunna ya bar kallon k’ofar da Mommy ta bi ta fita ta fice daga d’akin…runtse idanunsa ya yi ya d’an jima a haka kafin ya bud’e,bai yarda ya kalli Daddy ba ya fice
da sauri….
Chapter 85 · 0% Book details