← Book details Munnubiya Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 92 OF 137

Sashe 92

Munnubiya Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Shiruuu gidan ba kowa dan haka Manubiya suka ajjiye flask d’in girkin da suka yo suka nufi sama side d’in Mommy,kamar ko da yaushe ita da Baba larai sai Ya’isha suka tadda a parlourn nata..zuwan Hajiya Mama ba notice ya d’aga musu hankali matuk’a ga kuma Daddy wanda yake bin diddigin Mommy kamar ba gobe…
Ba yabo ba fallasa suka gaisa kafin Mommy ta kalli Yadira tace”ta raka Manubiya wajen Hajiya Mama su gaisa.”
Suna fita ko tambayar ta su Mommyn ba su yi ba Yusra tace”yanzu haka ma cikinta ciwo yake yi,ba ta dai fad’a ba amma tun safe take rik’e ciki idan ya murd’a har sai ta durk’usa”
“MashaaAllah,Alhamdulillah!!”
Baba larai tace cike da farin ciki,kafin ta d’aura da cewa”tunda na ga matar nan da safe hankalina ya tashi dan na san tsaf za ta iya cewa ku dawo gida..”
With full confidence Yusra tace”ai aikin gama ya riga ya gama yanzu kam..dan duk wani ruwa nata muna sakawa a ciki ita kuma tass take shanyewa.. yau sati biyu ta shanye sachet biyu fa!.
Ragowar abubuwan ne dai da na toilet da na d’aki duk ba mu samu damar yi ba ai dama na gaya miki..saboda ya Yash ko k’afar benen sa bai bamu fuskar mu tab’a ba k’iri k’iri ma yace mana “ko ba ya nan kar mu shigar musu d’aki. Na abinci ita kuma ba ta yarda da mu ba! dan ko girkin mu ba ta ci kuma tana yawan addu’o’i so na san turaren shima ko ta shak’a ba lalle ace ya yi wani tasiri ba dukda dai na lura kwana biyu rikici suke yi but gaskiya ba lalle abubuwan namu bane dan ba ta cin duk wani abu da muka bata…maybe wata rigimar tasu ce daban.”
Ajiyar zuciya Baba larai ta sauk’e kafin tace”Allah ya shige mana gaba,tunda har suka fara rikici su kad’ai ai sun sauk’ak’a mana kinga….sannan ba komai dan ba ku samu kun yi waenchan d’in ba indai komai ya tafi yadda muke so,maganin da kuka saka da chatting d’in sun ishi komai.Yanzu Ya’isha ki kirawo Abbakar kice masa zai iya tunkarar Yashjub a yau!”

Shiruu Ya’isha ta yi kafin tace”amma bai yi wuri ba?”
Murmushi Baba larai ta yi tukunna tace”kina ji fa Yusra tace ta fara ciwon ciki!ai this is the perfect time,dan tunda ta fara ciwon cikin nan ba za ta kai jibi da shi a jikinta ba.”

“Tam shikenan,bari in kirasa…”
Daga haka ta d’au waya ta kirasa….a gaban su suka tattauna kafin daga baya suka yi sallama,zuciyar kowa fesss!!!.

Sosai Manubiya ta ji dad’in ganin Hajiya Mama haka itama Hajiya Maman…bayan gaishe gaishe Hajiya Mama ta bata tsarabar da ta yo musu ita da Yash ta karb’a tana ta murna da godiya.
Dai dai nan Ummi ta shigo dan haka suka zauna su uku gwanjn ban sha’awa bayan Ummi da Manubiya sun gaisa.
Hirarsu suke sosai,dukda Manu murmushi da eh ko a’a take ta cewa amma hirar tana yi mata dad’i.
A bakin Hajiya Maman take jin maganar Yadira da Junior ta inda take cewa”ta cewa Daddy kawai ya tsayar da date dan al’amarin Yaran gidan ya fara bata tsoro dan haka tunda har Junior ya nuna Yadira yake so gara kawai a saka rana a yi aure ragowar suma za ta bincika musu Miji a cikin jikikon k’awayenta na nan Nigeria da suke in contact with!ya zama dole a tashi a tsaya a kansu sun rik’a dayawa.”
Ita dai Manubiya murmushi ta yi tace”Allah ya tabbatar da alkhairi”
Dan zuwa yanzu ciwon cikin da ya addabeta sama sama tun d’azu ya k’ara k’arfi!
Tana ji Ummi tana cewa”ta ji suna cewa Yadiran fa ba ta son Junior d’in…!”
Ita kuma Hajiya Maman tace”Wallahi ko za ta mutu sai ta auresa!,Junior ba shi da wani mugun Hali dan haka dole da aure sa.”

“Washh!”
Manu tace sakamokon wani mahaukacin murd’awa da cikinta ya yi.
Da sauri duk suka kalleta sai kuma suka rufar mata sakamokon yadda suka ga ta rik’e ciki ta runtse idanuwa da mugun k’arfi.

Sannu suka shiga jera mata bayan Ummi ta rik’eta Hajiya Mama kuma ta fara k’ok’arin kiran Yashjub.

Yadda Manubiya ta fashe da wani irin kuka ta shiga kiran sunayen Allah ne ya sa Hajiya Mama ta ajjiye wayar ita da Ummi suka fara k’ok’arin kinkimarta dai dai nan Junior ya shigo.
Da sauri Hajiya Mama tace”ya fito da mota ga su nan sauk’owa zai kaisu asibiti.

Munirat da Ummi ne suka sauk’ar da ita suka sakata a mota suna ta faman jera mata sannu,Junior da Hajiya Mama da Manubiya sai Munirat da ta d’aura kan Manu akan cinyar ta,ne suka fara yin gaba suka nufi asibitin,Ummi kuma sai da ta koma ta sanarwa su Mommy tukunna ta bi bayansu a motarta,da taimakon kwatancen Munirat da suke waya ta Isa asibitin……

Yashjub yana zaune a office gaba d’aya tunani ya yi masa yawa dan sai yanzu ya ke ganin rashin kyautawar sa ga Manu…waya ya d’auko da niyyar kiranta amma sai shigowar Racheal ya katse masa hanzari…..

Cikin takunta ta k’araso tace”Sir,a guy named Abbakar is here to see you!he said he’s a friend of your wife.”
A take k’irjin Yashjub ya buga,
sai da ya d’an d’au lokaci kafin ya samu ya d’ago a hankali ya kalleta yace”send him away”.
Duk wani Abu da zai kawo matsala tsakaninsa da Manu ba ya so,gudan sa yake yi.
Ya san ya tsani Abbakar,yana kishinsa saboda Manubiya shiyasa ya zab’i k’in ganinsa.

Har ta juya za ta fita sai kuma ta juya tace”Sir he said it’s very important and urgent,he need to see you!..”

Wannan karon cikin d’an fushi yace”Racheal!send him awayyy!!!”

“Ok sir”
Ta ce,daga haka ta juya ta fita.

Dafe kansa wanda zuwa yanzu ya fara sara masa ya yi…ya d’an jima a zaune kafin ya gama deciding ya mik’e da niyyar zuwa gidan nasu ya samu Manubiya,shiruu da kyaliya bai kamata ace ya fara shiga tsakaninsu tun yanzu ba…abunda ya yi kwata kwata bai kyauta ba….

Yana wannan tunanin ya sauk’a ya shiga motarsa yana shirin kunnawa Abbakar ya k’araso wajen…tun da ya fito ya gansa dama dan haka ya sake tamke fuska tamau.

With full confidence Abbakar ya k’araso ya na zuwa ya d’an yi knocking glass d’in motar wajen mai zaman banza kafin ya bud’e ya shiga ya zauna.

Shiruu Yashjub ya yi sai kuma kawai ya kunna motar ya ja ya fice.

Sai da suka d’an yi nisa tukunna ya faka ya juya ya kallesa yace”I made myself pretty clear kuma na san Racheal ta gaya maka..”

Cikin tarar numfashinsa Abbakar yace”I have to see you,shiysa ka ga na yi hakan..”

Yashjub ji yake kamar ya bud’e motar ya hanakad’a Yaron dan ya yi tunanin idan ya yi masa hakan zai fita amma sam baiga alamun shakka ko shirin fita daga garesa ba ,shi kuma har ga Allah he can’t stand him.. ko sunan shi ba ya so ya ji an kira wallahi…ga kuma gudun zuciya..

“Am…Yashjub ban yi
Mamakin yadda kake treating d’ina ba, dan na san haushina kake ji kamar yadda nima nake jin haushinka!”
Muryar Abbakar ta katse masa tunani..
Juyawa kawai ya yi ya zuba masa jajayen idanunsa..wanda hakan ba k’aramin dad’i ya yiwa Abbakar ba dan ya hango trigger…

Cikin sauk’e numfashi yaci gaba da cewa”A da na so in b’oye maka kamar yadda Manu ta buk’ata amma kuma sai na ga rashin dacewar hakan dan bai kamata mu yi ta b’atawa kanmu lokaci ba shiysa na zab’i in tunkare ka…”

Cikin katsesa da tsananin fushi Yashjub yace”Kaii!dan ubanka na yi maka kama da Yaro???ni za ka zowa da wannan shirmen?fice mini a mota kafin na illataka!!!”

Murmushi ya ga Abbakar d’in ya yi kafin yace”idan ni ban maida kai Yaro ba ai Manubiya ta maida kai Yaro jariri ma kuwa..gashi kuma ina k’ok’arin wayar maka da kai amma kak’i ka saurare ni!.”

Kama sitiyarin motar Yash ya yi da mahaukacin k’arfi ya d’aura kansa a kai ya shiga karanto addu’o’i dan ya san tabbas tsaf zai iya kai Abbakar lahira muddin ya ce zai biye sa…

Tsabar b’acin rai zuwa yanzu sama sama yake iya jin Abbakar d’in yana cewa”Tun Yarinta muka taso ni da Manubiya..ba ta yi tunanin Ina sonta ba shiyasa ta karb’i soyayyarka…yanzu kuma ta fahimci Ina k’aunarta she’s ready to leave you for me Yash!saboda tace ko dan family d’inka ma ba za ta iya rayuwa da kai ba gashi ba ta son ka…kawai matsalar itace tace mini ba ta san ta yaya za ta gaya maka ba!tana jin kunyarka har gida ka siyawa iyayenta…ganin duk mu uku muna ta b’atawa kanmu lokacine ya sa na yanke shawarar tunkarar ka a yi ta ta k’are.”

A hankali Yashjub ya zare makullin motar ya d’ago kansa ko kallon Abbakar bai yi ba haka ya bud’e ya sa kai ya fita,dan tabbas shaid’an ya fara kad’a masa ganga maganganun Abbakar sun fara tasiri a kansa gashi zuciya
In banda tunzuroshi ya rufarwa Abbakar babu abunda yake yi shi kuma ya san muddin ya biye Yaron a halin nan da yake ciki to sai dai wani ba shi ba.

Bai san shima Abbakar d’in ya fito ba sai hannun sa da ya ji ya kamo ya saka masa wayar sa yace”idan baka yarda da ni ba ka duba wannan.”
Chapter 92 · 0% Book details