← Book details Munnubiya Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 62 OF 137

Sashe 62

Munnubiya Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Ita kam Manubiya ta yi laushi
shiyasa suna shiga motar da ya janyota ta gishingid’a a jikin sa sai bacci.
Sai da suka k’arasa tukunna ta ji ana tashin ta a hankali…cikin
kulawa kamar ya samu kwai haka yake lallab’ata yana tashin ta kamar baya so dan ba dan drivern na jiran su zai
koma ba da ba dalilin da zai
sanya ya tashe ta yadda yaga tana baccin ta peacefully ya san ba k’aramin dad’i baccin ya yi mata ba.

Tana bud’e ido suka yi ido biyu dan haka ta sakar masa wani lallausan murmushi kafin ta d’an gyara ta mik’e ta zauna
Cikin kulawa yace mata “mun iso bara in bud’e a rufe ne gate d’in.
“Tou” kawai ta ce.
Ta na jinsa da shi da drivern suka fita suna ta faman zuge gate sai da aka gama parking motar tukunna ya lek’o ya mik’o mata hannu yace “muje ko”
Jin jina kai ta yi a hankali kafin ta bi bayan sa suka fice daga bayan motar.dama tunda yace mata zai bud’e gate ta yi mamaki dan ita a tunanin ta za ta ga hotel ne amman sai ta ga gida flat mai d’ankaren kyau mai d’auke da d’an madaidaicin compound..
Murmushi ta yi suna fitowa dan gidan ba kad’an ba ya d’auki hankalin ta ya burgeta gashi dai d’an mitsitsi amman ya k’ayatu iya k’ayatuwa. Sai da driver d’in ya taya Yash suka gama kai kayan bakin k’ofar shiga drivern ya tafi ya rufe gate d’in tukunna ya dawo.
Yana zuwa ya sunkuya ya d’auke ta in a bridal style
Murmushin ta yi ta zagaye hannunta a wuyansa,a haka suka k’arasa bakin k’ofar..
Tumb d’in sa ya saka wata murya tayi welcomin d’in shi had’e da fad’ar sunan sa daga nan ya tura suka shige cikin k’ayataccen parlourn
Saida ya kai ta kan one seater tukunna ya zaunar da ita ya zauna a gefen ta kafin yace
“Do u like it ?The house!ya yi miki kyau?”
Sai da ta kuma k’arewa parlourn kallo tukunna tace “Sosai ma kuwa,ya yi kyau over”
Ta fad’i hakan tana kallon parlourn..
murmushi yayi ya sauk’e ajiyar zuciya kafin yace
“MashaaAllah na ji matuk’ar dad’i da kikace ya yi miki saboda dama Inata adduar Allah yasa yayi miki kyau…wannan shine Gida na farko da na fara siya a rayuwata,it’s so dear to me shiyasa na mallakawa the closest person to my heart and soul.Gidan ki ne…da na baki as a
gift halak malak”

Da sauri ta juyo ta kalle sa
sai kuma ta kalli parlourn kafin ta sake juyowa tace
“Bai yi yawa ba kuwa?…ba ma a Nigeria ba fa..
Cikin janyota jikin sa yace
‘’Gift da kyautar da kika yi mini Baby sun fi k’arfin wannan idan na ce zan biya ko zan kamanta to fa sai na baki komai nawa tass ba tare da na kamo k’afar biyan ki ba ma..to amma kinsan an ce yaba kyauta tukuici shiyasa na baki nawa tukuicin ki karb’a kawai ke dai ki yi min alk’awarin kasancewa a tare da ni a ko da yaushe..idan ki ka yi mini haka kin gama min komai Baby…”
“Already takardun are under your name tomb print d’in kawai za mu mayar ya koma na ki.”

Ahankali tana kallonsa tace”we are one remember?ba sai an chanja tombprint d’inba..we will always be together inshaaAllah”
Sai kuma ta sunkuyar da kanta ta d’ago ta kallesa dan Wallahi ita ba ma ta san ta Ina za ta fara yi masa godiya ba gaba d’aya ya saka ta a shock
Da kyar ta bud’e bakinta tace
“Nagode Sosai Allah ya saka da allhairi na s……”
Da sauri ya rufe mata baki yace “ni ne da godiya”
Bai sake ba ta damar yin magana ba sakamokon kissing dinta da ya fara yi da sauri da sauri yadda ta ji jikinsa har karkawa yake yi ne ya sanya ta hak’ura kawai dan ta san ba sarara mata zai yi ba……

Sai da gari ya fara haske tukunna ya samu kanshi..sai bayan kusan 2 minutes tukunna ya d’ago yana kallonta yana mayar da numfashi still yace”mu je mu yi sallah sai in nuna miki gidan naki,ke kika tsayar da mu ba mu yi tour ba”ya fad’i hakan yana murmushi.
Turo baki ta yi ta d’an kauda kai dan haka ya yi dariya ya fara yi mata cakulkuli duk yadda ta so dakewa sai ta gagara ta fara dariya itama a haka ya d’auke ta suka nufi d’aki tana cewa”dole ma ta yi kib’a ko dan yadda yake d’aukarta anyhow daganan sai ta ga yadda zai yi…..”

Wanka suka fara yi suka yi sallar Asubah suka ci abincin da ya yo musu order tukunna ya ce su je ya nuna mata gidan
D’akuna uku ne sai kitchen da store da tafkeken parlour.
Ta baya kuma pool ne da pool house sai garden ata gaban gidan mai d’ankaren kyau….

Suna gama zagayen ya kira masu gyaran gida aka zo aka gyara aka share aka goge koina tass tass.
Sun ci sa’a kusa da restaurant suke shiyasa order d’insu ba ya d’aukar lokaci…..sai la’asar tukunna komai ya kammala suka yi wanka sukai sallah.
Kwata kwata hutun awa uku ya bari suka yi daganan ya d’aura daga inda ya tsaya…ita kamar wanda ake yiwa ruwan energy ma haka take ganinsa dan sam ba ya gajiya…..

To dai kamar yadda Yashjub ya fad’a mata ashe da gaske shi bai ma fara cin amarcinnasa ba sai yanzu dan ita kanta ta tabbatar a Nigeria appetizer ya yi….Sai da suka shafe sati
d’aya da kwana uku ba ta lek’a waje ba shima haka dan da kyar ma aka samu ya d’an fita ya je ya sissiyo musu abubuwan da za su buk’ata daga nan sai da suka yi sati d’aya da kwana uku tukunna suka d’an fara fita suka fara zageye island d’in,ita Manubiya har ga Allah so take yi ta zauna a gidan ta yi barci sosai ta huta amman kuma ta san idan suka zauna a gidan ba barinta ta huta d’in zai yi ba shiyasa kawai take yarda tana biyosa suna fita yawon ba dan tana jin dad’in yawon ba gashi dai the view da duk wani abu about Cyprus is heaven amma ita sam ba ta enjoying tsabar gajiya…

A haka dai kafin su yi wata biyu ta samu ta d’an saba kuma ta yi accepting mijinta a yadda yake dan ta fahimci ba wai don ya takuramata bane hakanan halittarsa ta ke ga kuma gudummawar da soyayyarta da k’aunarta suke badawa..

Shi kansa Yashjub ya na mamakin yadda Manubiya ta taso masa da wani tsumin dake a jikinsa wanda a da sam bai san da shi…dan a da kwata kwata ko kallon mata ba ya son yi ballantana su basa sha’awa..yana jin sha’awa ba wai kwata kwata ba ya ji ba amman ko ta d’an taso masa to ba zai yi 10 minutes yana jin wannan feeling d’in ba dan tashi d’aya zai ji ya nemi feeling d’in ya rasa shiyasa a wannan lokacin wani zubin har tunani yake yi akan’Anya kuwa lafiyar sa k’alau!?’.

Kafin 2 months itama ta ware ta zama y’ar gari ta shiga faranta wa Mijinta rai yadda ya kamata Wanda hakan ba k’aramin dad’i ya yiwa Yashjub ba dan shi sai a wannan lokacin ne ma tukunna ya ke sake experiencing wasu ni’imomin da aure ya k’unsa…

Zaman lafiya kwanciyar hankali da asalin tattalin so da k’aunar juna shine definition d’in zaman Manubiya da Yashjub a Cyprus..wani zubin idan ya yi mata wani abun har kukan farin ciki takeyi ta yi sujjada ta yi ta godiya ga Allah S W A dan itakam in dai a fannin so da k’auna na tsakani da Allah ne to ba shakka za ta fito ta bugi k’irji tace “ta fi ko wacce mace sa’ar mijin aure…”

Hutun su kawai sukeyi gaba d’aya sun manta da matsalolin su sun yi fari sun yi k’iba abunsu….suna waya da video call da su Jidda haka shima Yashjub ya na waya da Mommy kuma ba yabo ba fallasa suke gaisawa ita da Manubiya itama Manubiyan da kanta takan kirata ta gaida ita ba yabo babu fallasa take amsawa.
Haka suna waya da chattin da su Ummi Yahanasu da Munirat sosai su Yasira kuwa ko ‘hi’ babu a tsakanin su da Manubiya amma suna kula d’an uwansu.
Yashjub ya lura kuma ya sani amma bai yi magana ba itama bata ce komai ba dan ko kiran sa sukayi basa cewa ya bata shima kuma baya bayarwa..Manubiya ba ta nuna masa text d’in da Ya’isha ta yi
mata ba 2 month ago kafin su taho amma shi ya gani..so yake kawai ya ga iyaka gudun ruwansu Daddy ya huce daganan zai san abunyi.

Watansu biyu da sati biyu Daddy ya kira Manubiya..ta yi mamakin ganin kiran amma sai ta d’auka da mutuntawa ta gaidashi
Da kulawa ya amsa ya tambaye ta ya Cyprus tace alhamdulilah daga haka yace”yaushe za su dawo?”
Diriricewa ta yi ta rasa bakin magana da kyar dai tace”Yash d’in bai gaya mata ba”
Jinjina kai Daddy ya yi kafin yace”ok shikenan daga haka ya kashe wayar.
Sarai Yashjub ya ji komai ya fahimci me Daddyn yake nufi da yin haka dan haka ya d’au waya ya fita ya kira sa…
Suna gaisawa Daddy yace”a lokacin da Manubiya ta mari Yadira na ji haushi sosai kuma yadda ka yi zato jiranku kawai nake yi ku dawo in had’a ka kai da ita Manubiyan in yi muku warning kuma in yi riga kafi saboda gaba amman tunda har za ka iya yi mana k’aura saboda hakan InshaaAllah maganar ta wuce kuma komai ya wuce amman a kiyaye gaba…come home..da ni da y’an uwanka da Mommynka muna buk’atarka a kusa da mu ba ka tashi tare da mu ba bai kamata yanzu ma ka sake barinmu ba”

Shiruu Yashjub ya yi kamar zai faiyyace wa Daddy halin su Yasira ya kare Manubiya amman kuma kawai sai ya bar maganar yace”ka yi hak’uri Daddy dama nan da 4 days ma za mu wuce Uk mu yi musu sati biyu daganan sai mu dawo inshaaAllah”.
Chapter 62 · 0% Book details