← Book details Munnubiya Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 87 OF 137

Sashe 87

Munnubiya Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Suna tsattsaye wasun su a zazzaune a kanta ta d’an fara motsi kafin a hankali ta dawo cikin haiyyacin ta!
Sai dai ba ta bud’e ido ba…
Ta san ta daku dan fuskarta in ba da kyar ba sai ta had’a da plastic surgery
amman kuma ba ta jin akwai ranar da ta tab’a tsintar kanta cikin tsananin farin ciki Irin wagga rana!…dan ta riga ta san nan da 10 days inshaaAllah burin ta zai cika
ko da balai ko ta wanne Hali!
Batajin alamun ciwo ko wani abun a mararta kuma dama ta san Yashjub bai sameta a wajen ba dan haka tana da yak’inin cikin ta yana nan daram!. Yo ai ko ya fita sai ta sake yin wani ta lik’awa Yash!yadda aka kamasu d’innan is the most amazing thing da za ta rik’e as weapon ta kowanne fanni.
Ta ji dad’i matuk’a gameda yadda plan d’insu ya tafi daidai babu targard’a.
Sannan bata wani damu da Manubiya ba dan ba Manubiya ba ko auren irinta uku ne da Yash wuyarta ta auresa Wallahi sai ta yi waje da ita!.

Mommy dake daff da kanta ce ta d’an matso tace “Kausar”.
Ahankali ta d’an fara k’ok’arin bud’e idanunta…
Duk matsowa sukayi sai da ta d’an bud’e idon guda d’aya saboda d’ayan ba zai bud’u ba!
Tukunna gaba d’ayansu suka ce
“Alhamdulillah”.

Da sauri Yassir ya je ta wajen kanta ya d’ago kanta ya d’aura a kan cinyar sa
Yace “Yasmeen d’an sake duba ta!idan babu emergency
Inaga yanzu za mu fara shirin wucewa kawai!na san dole flight d’inmu ta Abuja zai tashi”sam bai damu da yadda fuskarta ta kumbura kamannin ta suka sauya ba shi dai kawai ya san Kausar d’insa ce dan haka yanason ta a ko wanne irin yanayi.

Ajiyar zuciya Munirat ta sauk’e tanajin yadda zuciyarta take tafarfasa..a hankali
tace “Allah ya k’ara sauk’i”
Daga haka ta juya ta fita da sauri.
Ba wanda ma ya san ta fita ko ya jita dan tun d’azun ma ba wanda ya kula ta babu wanda
ya damu da existence d’inta a d’akin.

A b’angaren Munirat d’in itama ba wajen su ta zo ba dan in banda gaba harara da bak’ak’en maganganu babu abunda yake shiga tsakaninta da su Kausar d’in…Yassir ta biyo lokacin da taga sun kinkimo Kausar an kaita d’akinta ya fito ya fad’a d’akinsa shine ta tsaya akan idan ya fito su yi magana amma ko da ya fito sai ya d’auke kai kawai ya afka side d’in Kausar ya wani tamke fuska dan karma ta kula sa..itan ma ta yi alk’awarin fita daga harkarsa kwanakin baya amma babu yadda ta ita ne saboda yanzu haka maganar da take so su yi d’in is very important shiysa ta tsaya tayi ta jiran fitowarsa jin shiru shine itama ta shiga side d’in Kausar d’in….
A yadda taga yake d’innan ta san ba zai saurareta ba shine ta hak’ura ta tsara zata nemo numbersa kawai ta tura masa message ta san zai gani….
Sarai ya lura da ita!tana fita ya yi tsaki ya ci gaba da dudduba Kausar yana tambayarta Ina ne yake yi mata ciwo…

Ba abunda ya fi d’aurewa su Mommy Kai kamar yadda sam Yassir bai wani damu ko ya nuna jin haushi a kan abunda ya faru tsakanin Kausar da Yash ba shi ta lafiyar ta ma yake yi..
Ko da ya yi fushi ya fita d’azun suna zuwa suka tarar da shi a d’akin Kausar d’in yana safa da marwa…sun san dole zai tausaya mata amma
kuma sam babu alamun kishi ko wani jin haushi a tare da shi
ko irin kishin da ya nuna a d’akin Yashjub sam ba su ga alamarshi a tare da shi ba…dukda tace masa forcing d’inta Yashjub ya yi but ya kamata ya ci gaba da jin haushi ko da d’an k’ank’ani ne kamar yadda ya nuna a wajen dinner earlier da ta tafi side d’in Yash d’in da k’afarta.

Gyaran murya Mommy ta yi kafin tace”Yassir ka bar batun tafiya tukunna yanzu a ji da abunda ya faru..indai ba so kake Daddynku ya fusata da kai ba to ka ja bakinka ka yi shiru ka koma gefe tun kafin a huce a kanka.”
Zai yi magana Junior yace”kana fara batun fita da ita waje ma na san tsaf zai saka question mark akan yadda sam ba ka yi kishin komai ba!”
Ya fad’i hakan idanunwansa cikin na Yassir wanda ya juyo ya zuba masa su shima….lumshe idonta guda d’aya Kausar ta yi dama so take ta yiwa Yassir sign ya gane ya dena abubuwan da yake yi tun kafin ya tona musu asiri…Aikuwa gashi har an fara magana…
Shima Yassir d’in sai yanzu ya d’au haske dan haka ya ce “okay Mommy”kawai..daga haka ya mik’e sai da ya yiwa junior wani kallo tukunna ya sa kai ya fice saboda ya ji haushi da mamakin yadda d’an uwa kuma Abokin nasa ya so kunce masa zani a kasuwa! Ya san Junior ya sanshi ciki da waje duk abunda ya yi yana ganewa ya san wannan d’in ka ya gano da gashi har yana shirin yi masa b’aramb’atama a bainar Nasi amma ba komai za su had’u zai yi maganin sa dan ya lura ya fahimci komai kuma ya san yadda yake ji da yashjub dan haka dole ya yi silencing d’insa da wur wuri tun kafin ya janyo musu ruwa.

Washegari da sassafe Yahanasu ta tashi ta shirya tana shirin tana fargaba…if not Yash ya zab’eta ne kuma ta ji tausayinsa jiya wallahi da ba ta ga dalilin da zai sanya ta zamo itace wadda za ta gayawa Manubiya wanna mummunan al’amari ba.

Ummi ce ta yi breakfast suka shirya ita da Yahanasu suka nufi asibitin za su chanji Hajiya Mama da Siyama…

A d’akin suka tarar da Yashjub ga mamakinsu…lokacin Najeeb har ya je ya d’auki Siyama da Hajiya Mama zai maida su gida,ba k’aramin dad’i Hajiya Mama ta ji ba da ta ga Yashjub ya zo haka itama Siyama saboda dama tana ta addu’a Akan Allah ya sa ba fushi ya yi ko ya k’ullaci Manu ba.Ta san dole da zafi shiyasa ta d’aga masa k’afa ya d’an huce gudun kar ta jagula abun hakanan ta yi ta addu’a gashi kuwa yanzu ya zo…..
Shi ya tarar da su Hajiya Mama su Ummi kuwa ba su same su ba iyaka Yashjub d’in suka tarar.

Suna zaune Manubiya a kan gado shi kuma a gefenta ya rik’e hannunta ya sunkuyar da kansa k’asa ita kuma tana video call da Jiddah wadda Manubiya ta ji matuk’ar dad’in ganin yadda k’anwar tata ta yi k’iba ta yi fresh a cikin kwanaki k’alilan alamun Hankalinta a kwance yake.
Yadda su Ummi suka ga walwala da murmushi a kan fuskarta ya sa suka fahimci ba ta ji komai ba.

Gaisawa suka yi da Yash da ga haka ya mik’e ya k’arasa ya shiga had’a mata Breakfast Yayinda ita kuma suka yi sallama daJidda bayan sun gaisa da su Yaha ta ajjiye wayar suka shiga gaisawa da su Ummi.

Yana gamawa ya k’arasa ya ajjiye mata,ya fara k’ok’arin bata tace masa”ai Likita yace akwai allurar da zai yi mata kafin ta ci abinci”

“Okay”kawai yace ya d’an yi mata smiling kafin ya mik’e ya fita domin kiran Doctor d’in.

Yana fita yaha ta zauna a wajen da ya tashi tace”MashaaAllah Jidda ta yi fresh abunta,Al’ameen ya iya kiwo”
Dariya duk suka yi har Ummi kafin Manubiya ta kalli Yahanasu tace”Yaha akwai abunda yake damunsa ne bayaga al’amarin da ya faru da ni? Na ga yanayinsa gaba d’aya ya sauya.”

Shiruu ta yi ta d’an k’ura mata ido kafin tace”za mu yi magana anjima,ki kwantar da hankalinki”
Daga haka ta yi sauri ta mik’e ta fice, ba itace Yashjub ba amma yunk’urin sanar da Manu da ta yi kad’ai a yanzu tashi d’aya k’irjinta ya fara dukan uku uku.
Kusan karo suka yi da shi dan tana fita shi kuma yana shirin yin knocking.
“Ina Doctor?”
“Yace yana zuwa”
Ajiyar zuciya Yahanasu ta sauk’e kafin tace”Yash Ina ga gara mu bari ta warke garau kafin mu sanar da ita also har ga Allah bana so in yi tarnishin walwalar da na gani a kan fuskarta.”

Jinjina kai ya yi kafin yace”abunda nima nake tunani kenan,da na shigo d’azu she was soo happy to see me ta ma kasa b’oye murnar ta,I don’t think zan iya lalata farin cikin da nake gani a kan fuskarta ba zan iya fad’a ba Wallahi shiyasa kema dama na shirya akan zan ce miki ki yi shiru to Alhamdulillah tunanin mu ya zo d’aya.Mu bari mu koma gida sai a san abunyi dan tabbas kam ba zan b’oye mata har abada ba.”

Yahanasu ta bud’e baki za ta yi magana kenan suka jiyo k’arar fad’uwa sai kuma salatin Ummi…kafin ta fara cewa”Yashjub Yahanasu kuna Ina Ina likitan!!”dai dai ta bud’e k’ofa za ta fito a gigice suka yi kicib’is da su dan haka ta juya ta koma ita a tunaninta ma tare suke da likitan…
A rikice suma duk suka yi kan Manubiya da ta ke zube a k’asa yashe a tsakar d’akin…
Kasa tab’ata Yashjub ya yi tsabar tashin hankalin da tsoro
a mugun rikice ya rarumo gorar ruwa ya shiga yayyafa mata hannunsa yana wani irin karkarwa…ganin ta k’i motsi ne ya sa ya mik’e a gigice ya nufi k’ofar da niyyar sake kiran Likita suka yi karo,ba ma ya iya cewa kawai Manu yake nunawa Doctor d’in hankali a mugun tashe…da hanzari shima Doctor d’in ya k’arasa da taimakon Yahanasu suka kinkimeta suka d’aurata a kan gadon ya shiga bata taimakon gaggawa Yashjub kam ya ma kasa motsi ko magana hawayen ma sun k’afe in banda karkarwa babu abunda ilahirin jikinsa yake yi especially k’afafuwansa
dan har yanzun ba ta farfad’oba!luu haka ya tafi zai fad’i da kyar ya rik’e kansa ya samu ya zauna a kan kujerar bayansa yana ganin bibbiyu.
Chapter 87 · 0% Book details