← Book details Munnubiya Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 128 OF 137

Sashe 128

Munnubiya Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Kowa in banda dukan uku uku babu abunda k’irjinsa yake yi tsabar zullumi….da Ya Musbah suka fara had’uwa a bakin gate shi da Ya Nafi’u da Aisha waenda suma duk Gwaggo Suwaiba ce ta kirasu…Manubiya cikin zumud’i ta fara kokarin fita ta je ta sanar da su amma sai Yash yace mata ta tsaya tukunna surprises ne kar ta gayawa kowa…hakanan ta ja bakinta ya yi shiru farinciki kamar zai fasata haka
Suka nufi ciki gaba d’ayansu.

Daddy a waje ya tsaya shi da Yashjub sai da Baba ya zo ya shigar da su parlourn bak’i Yayinda su Ummi suka nufi ciki gaba d’ayansu….Hajiya mama ta na shiga sukayi ido biyu da Mama wanda hakan ya sanya duk su biyu suka k’ame a yadda suke kowacce ta kasa motsi.
Kuka Mama ta saka a take ta durkushe a wajen tana jin wani kalar nauyin Hajiya Mama yana lullub’eta…k’arasawa inda take Yahanasu ta yi ta durk’usa itama cikin kuka Mama tace”sai da kika yi abunda na hanaki ko?”
Dai dai nan Daddy Yashjub da Baba suka shigo dan suna ce masa Yahanasu ce ta kawosu gashi gashi yace to su shiga cikin suga menene surprise d’in…….
A hankali Yahanasu ta girgiza kai tace”kamar yadda na gaya miki basuyi tunanin kinada rai ba kuma Daddy bashi da wani burin da ya wuce ya had’u dake a halin yanzu..d’azun nan ya gama fad’in haka a gabana a gaban kowa shiyasa na kawo su…..”

Shi dai Daddy zuwa yanzu hatta tsokar datake a jikinsa karkarwa take yi…bai riga ya ga wadda Yahansu take magana da ba amma dukkan bayananta suna nuni ne da Khadijarsa ce……

Tashi d’aya numfashinsa ya d’auke jinsa ya d’auke a daidai lokacin da Hajiya Mama ta k’arasa ta mik’ar da ita tsaye tace”Khadija!!!”
Sai kuma ta rungumeta ta sa kuka…

Kallonsu Yashjub ya yi saboda Unlike Yahansu shi tun yana Yaro da aka ce ta rasu bai sake sakata a idanunsa ba shiyasa bai ganeta ba tashi d’aya ammafa kalar k’auna da son matar da yake ji suna shigar sa tashi d’aya a halin yanzu bana wasa baneba….
Yanaji Hajiya Mama tace”Khadija”
ya tabbatar tabbas ita d’ince dan haka ya taka izuwa gareta idanunsa suna zubar da kwallar….yana zuwa Hajiya mama ta matsa ya tsaya a gabanta yana hawaye…duk yadda ya so ya yi magana kasawa ya yi dan haka kawai sai ya rungumeta ya fashe da wani irin kuka wanda hakan ya sanya gaba d’aya suma su Manubiya suka saka kuka…..cikin k’ok’arin zaro sa daga jikinta take d’in tapping bayansa alamun rarrashi tana mamakin kalar so da tausayinsa da suke shigarta ga kuma da suka yi ido biyu ido d ido sai taga Yash d’in kamanninsa d’aya da ita…

Hajiya Mama ce ta share hawayenta tace”ki rungumi d’anki Khadija!
d’an da makircin mace ya sanya baki san kece mahaifiyarsa ba”

A rikice ta juya tana kallon Hajiya Mama!
Jinjina mata kai Hajiya Mama ta yi tace”tabbas!kece mahaifiyar Yashjub ta asali makirci rashin tsoron Allah da son zuciya ne ya sanya Larai da Khadija suka musanya miki shi..amma yanzu komai ya zo k’arshe,ranakun kuka bak’in ciki k’umbiya k’umbiya da munafurci sun k’are a zuri’ar Imam kura….”
gaba d’aya parlourn a tare sukace inshaaAllah kowa yana sheshek’ar kuka banda Mama da Daddy da suka yi mutuwar tsaye tun d’azu…
Ba kad’an ba Ammi ta shiga shock ba na wasa ba yanzu Yash d’in Manu shine asalin d’an Mama tabbas a duk yadda ka ga mutum kar ka rainasa…Bata ci zarafin mama ba bata wulak’antata ba tun bayan da ta fahimci ba ta da interest a kan Mijin ta amma duk da haka a take wata kalar kunya da nauyinta suka yi mata k’awanya.

Da kyar Hajiya Mama ta b’anb’are Yash daga jikin Mama ta kamo hannunta ta ja ta ta kaita gaban Daddy wanda ya yi mutuwar tsaye,ta kamo hannunsa ta saka hannun Mama a ciki tukunna ta juya ta shige cikin parlourn da su Daddyn suka fito a ciki yanzun…kowa wucewa ya yi banda Yashjub suka bi bayan Hajiya Maama suna shiga parlourn Baki’in dai dai nan kamar gwaggwo Suwaiba ta san suna nan itama ta shigo Inna a bayanta.

Suna shigewa Daddy ya fashe da wani irin kuka sai kuma ya durk’usa a gaban Mamaa yana kuka yama kasa yin magana

A hankali ta durk’usa itama tana hawaye da kyar ta iya cewa”sharri aka yi mi….”

Cikin tarar numfashi yace”you don’t have to explain anything to me Wallahi na dad’e da gane gaskiya na dad’e da fahimtar cewa sharri ne aka yi miki…ki yi hak’uri ki yafemini abunda na yi miki wallahi kunyar kallon kwayar idanunki nake yi,ban kyauta miki ba bai kamata ace na yarda da sharrin da aka k’ulla miki ba ki yi hak’uri ki yafe mini ki manta da komai ki yarda da ni a karo na biyu inshaaAllah ba zakiyi dana sani ba….”

Kuka duk su biyun sukeyi Mama tana mamaki da al’ajabin Mommy dan tunda Yahansu tace mata itace silar komai ta tsorata da lamarin d’an Adam matar da a ko da yaushe take yi mata kamar zata goyata ashe ba sonta take yi ba……

A hankali Yashjub ya k’araso ya had’e iyayen nasa su biyu waje guda ya rungumesu…tabbas inda ace a gida d’aya ya rayu da Mama da it won’t take long before ya fahimci itace asalin mahaifiyarsa ta gaskiya saboda so da k’aunar matar da yake ratsashi da yadda yake jinta a cikin jinin jikinsa kad’ai ya isa ya fahimtar da shi itace Mahaifiyar sa.

Sun jima a haka kafin Yash ya cikasu ya kalli Daddy yace”mun yafe maka Daddy zamu baka second chance…”
Duk murmushi suka yi daga nan suka tambayi Ina ta shige nan ta gaya musu komai tun barinta gidan Daddy har kawo yanzu….
Sosai suka sake girmama da Al’amarin Ubangiji
Ga ta dai tare da Manu amma kalli sai da Ubangiji ya k’addara saduwarsu tukunna suka had’u..dama shi Yash a ko da yaushe idan za su gaisa da ita ya kanji yanayinsa ya chanja itama Maman haka Ashe duk jini da asalin soyayyar tsakanin uwa da d’a ne dalilin abunda sukeji.

Sun jima kafin su shiga parlourn da suke ta jiyo koke koke da murna dama shi Yash da Daddy duk sun san menene Mama kuwa sai da ta kusan suma da suka yi idanu biyu ita da Inna dan haka ta tafi taje suka rungume juna cikin tsananin farin ciki nan murna ta zame musu biyu farinciki ba a magana musamman ma Yash wanda yake ta mak’ale da Mama duk inda ta zauna a nan shima zai zauna kamar wani d’an yaye……

Kabarin Ya’isha suka nufa anan k’auyen su Inna suka yi mata addu’a kowa yana kuka sai dare suka dawo dama already Yash ya yi magana da y’an sanda dan haka suna zuwa suka tarar da su a k’ofar gidan Mommy suna jiransu….Mama Manubiya Yahanasu da su Yadira k’in shiga suka yi Daddy Hajiya Mama da Yash ne suka shiga har cikin gidan sai da suka damk’a Mommy a hannun y’an sanda suka tabbata an tafi da ita tukunna suka wuce gida rayukansu fess!
Ba k’aramin dad’i Daddy ya ji ba da ya fahimci ba ta gani…ya san lokaci yayi da zata fara ganin masifu da bala’i reflection d’in abubuwan da ta shuka….

A Daren ranar aka sake d’aurawa Daddy da Mama aure…Daddy ya lura da yadda jikin Ummi ya yi sanyi matuk’a dan shi kansa ya san zumud’i da rawar kan da yake yi ba kad’an baneba Shiyasa ya sameta ya taushe ta yace mata ta kwantar da Hankalinta itama yana sonta kuma ta kasance tare da shi a worst times na rayuwarsu iinshaaAllah ba zai tab’a juya mata baya ba…”.
Ya san ba zai tab’a had’a son Ummi da Khadija ba amma in sha Allah zai kamanta adalci.

Sai a lokacin itama Ummi ta samu kwarin guiwa ta d’an sake Mama kuwa dama tunda ta ga Ummi ta san matsayinta sam bata ji haushi ko kishinta ba tunda dama ita hakan ba d’abiarta baceba.. nan ta rungumi Ummi itama Ummin haka suka rungumi juna zaman lafiya sai wanda ya gani!……

Sai bayan kwana uku tukunna y’an sanda suka tsinci gawar Kausar da Yassir! da taimakon wallet d’insa suka gano identity d’insa da gidansu…
Dama a lokacin da basu ga Kausar tare da Mommy ba tunaninsu basu ya yi tana tare da Yassir ai kuwa ilai…
Hannu bibbiyu su Daddy suka karb’i gawawwakin suka yi musu wanka aka yi musu sutura aka mik’asu gidansu na gaskiya.

Yasira ce taje ta sanar da Mommy rasuwar tasu…aikuwa nan ta haukace jininta ya hau..gashi ta so ta d’an karkato hankalin
Yasirar ta samu wani by her side amma tun daga ranar ko
mai irin muryaarta ba ta sake gani ba…ga ba ido ga rashin lafiya gashi ba ta da kowa shiyasa ta sake shiga cikin masifa.

Tun saura kwana uku appointment d’in Manu da Dr ya basu su cika suka wuce Berlin….da gaske mahaifarta ta tab’u kamar yadda Dr ya fad’a musu a Nigeria due to maganin da ta sha amma kuma za a iya treating d’inta ta samu ta haihu sai dai ba lalle ta iya haihuwar sama da Yara biyar ba….Manu ta ji dad’in good news d’in Alhamdulillah amma dukda haka sai da ta koka Astaghfirullah amma a k’aiyyade wa mutum haihuwa a ganinta hakan ma damuwa ce…..
Yash kuwa kamar ya zuba ruwa a k’asa ya sha hakanan ya yi ta jero hamdala ga Ubangiji subahanahu wata ala..Manu d’insa zata haihu kuma har morethan 4 kids ai Alhamdulillah,ya san dai babu dad’i ace mutum yanada matsala ga iya yaran da zai Haifa amma shi kam Alhamdulillah!!!Alhamdulillah!!!
….
Sosai ta samu cikakkiyar kulawa aka d’aurata a kan magani… watannnin uku suka yi a Berlin suka juyo da d’an cikinta cikin da su kansu basu san da shi ba sai da suka dawo Nigeria da sati d’aya tukunna ta fara ganin alamu aikuwa tana gwadawa ta ga positive.

Sai da ta yi kuka ta godewa Allah ta yi sujjada tukunna ta fad’a wanka ta yi ta fito ta chab’a kwalliya dan Yash ya kusan dawowa.
Chapter 128 · 0% Book details