← Book details Munnubiya Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 110 OF 137

Sashe 110

Munnubiya Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Jinjina kai Hajiya Mama ta yi,fuskarta har ta yi jaaa!
Ta kalli Ummi tace”ki kirawomin su Imam d’in ki ce na ce su zo yanzunnan!”

“Tam”Ummi tace daga haka ta mik’e ta sa kai ta fice.

Ba’a yi mintuna goma ba,Daddy ya shigo da shirin tafiya office Abhi kuma da jallabiya.
Ko gaisuwar su ba ta amsa ba ta kalli Daddy tace”ashe har kana iya tafiya office bayan masifar da ka k’ulla a gidanka jiya??”

A hankali ya sunkuyar da kansa k’asa yace”ki yi hkr Hajiya Mama da ma yanzu nake shirin shigowa mu tattauna kafin in wuce!”

Cikin fushi tace”Imam tattaunawa kuma ta nawa?
Sai da ka gama yanke decision da kai da munafuka!muguwa!!makirar matarka!!!!tukunna za ka zo ka ce mini za mu tattauna saboda ka raina ni??
Me za mu tattauna???
Ina sauraronka gaya mini menene ya rage wanda ba ka riga ka yanke hukunci ba?”

Shiruu ya yi ya gagara cewa komai.
Cikin tsananin b’acin rai ta kallesu su duka biyun tace”da ni da ku duk mun shirya a kan za a sakawa Khadija ido a bincike ta a gano ta a nunawa Yaranta illarta da illar d’abiar da ta d’aurasu a kai tukunna a sallameta a cikin gidan nan,amma saboda tsabar ku d’in ba jajurtattun maza bane ba a cikin awannin da basu wuce biyu ba Yarinya y’ar k’arama Kausar da Khadija sun juya muku tunani kun aurawa Kausar Yashjub!!!
Daga ta yi y’ar drama da shirmenta shikenan har kun kamu??”

Da kyar Abhi ya iya cewa”Hajiya mama cewa ta yi za ta tafi da Yaron shi kuma Yashjub ko
Maganar mu ba ya ji iyaka maganar Manubiya ya ke bi da farincikin ta..a jiyan fa cewa ya yi wai sai abunda ta yanke tukunna za a yi”

Sakar Baki kawai Hajiya mama ta yi ta na kallonsa har ya dasa aya tama kasa cewa komai.
Da kyar ta iya cewa”idan na fahimce ka, kishi kenan kuke yi da Manubiya kamar wasu mataa!!!shiysa kuka aura masa Kausar saboda kar Manubiya ta yi dominating d’insa ita kad’ai ko?”
“This is the dumbest thing da na tab’a ji tunda uwata ta kawo
ni duniya wallahi tallahi!
Ina tunaninku ya tafi ina hankalinku ya tafi??
Kausar faaa!!”

Cikin son yi mata bayani Daddy yace”ai Kausar d’in ba fa wai mun aura masa ita forever bane mun aura masa ita ne akan idan ta haihu sai su rabu”.

Mik’ewa kawai Hajiya mama ta yi ta nufi wajen kayanta ta fara fito dasu tana cewa”Bari
Ka ji in gaya maka,Indai Kausar ce to ba za ta tab’a rabuwa
da Yashjub ba ba za ta yarda ba!
Barr ganin wai da Yassir kuka santa,a yadda Khadija ta tsani Manubiya ba za ta bari Kausar ta bar Yashjub ba,
A tunani na auren ka da Khadija ya isheka ishara ya Isa ka gane idan aka auresa ba sa fita tunda tun yaushe kake so ka saki Khadija ta saku???”
Ta yiwa Daddy wanda ya matso ya rik’e trollyn hannunta tambayar.
Ba ta jira jin amsar shi ba tace”kuma saboda ku wawaye ne kuke tunanin Kausar za ta yarda a saketa?
Wai ma shin ina lissafin ku ya tafi da Kausar d’in tace za ta tafi kuka biye mata kuka yarda??
Khadija fa kad’ai sai Larai gareta a kaff fad’in duniyar nan,Wallahi ko ta tafi k’ark’ari ta yi wata biyu zuwa uku nasan ita da kanta za ta dawo ko su Larai d’in su nemota.Kuma indai Khadija ita ta haifi Yashjub ba zata bari Kausar ta b’ata masa suna ba,dan na san duk bakin su d’aya.

Abu simple very simple amma kuka gagara tsayawa ku yi lisssafi mai kyau sam saboda an had’a da asiri da wayo!!!
Saboda Allah kalli abunda kuka tafka!!ko
Shawara da ni bakuyi ba,kai da ake so a gyara gidanka a kub’utar da kai amma kalli yadda ka
sake damalmala komai!!!dan ba ka isa ka ce ka rabu da Khadija ba muddin Kausar ce matar Yash,ko ka kori Khadija a gidan nan indai Kausar tana a
matsayin Matar Yash wallahi ka yi ta banza ne…”

A hankali Abhi shima ya k’araso dan Daddy yana rik’e trolly ta sakar masa ta cigaba da zaro kayayyakinta rai a tsananin b’aci tana magana tana had’a kaya…cikin lallami yace”Hajiya mama ki yi hak’uri dan Allah mun yi laifi wallahi ni
kaina sai yanzu na ke ganin rashin dacewar hakan.”

Juyawa ta yi ta kallesa tace”kad’an daga aikin Khadija!ai ba za ku san lokacin da kuka d’aura ba dama…”
Cikin chanja topic d’in tace”ka
fara yi mini shirye shiryen tafiya meanwhile ka kama mini d’aki a hotel kafin komai ya kammala dan wallahi na gama zaman cikin gidan nan!”

“Innalilla wa Ina ilaihirrajiun”
Daddy yace kafin ya d’aura da cewa”Hajiya mama dan girman Allah ki yi hak’uri!!ina cikin garin nan da gidana amma ace kina hotel dan Allah ki rufa mini asiri,in dan har saboda Khadija ne to a yau za ta fita wallahi.”
Ya fad’i hakan kamar zai yi
kuka

Cikin b’acin rai tace”kar ka soma!!!ba zai you ka koreta saboda ni ba no matter what
sai dan halinta wanda na so in nuna maka ka runtse
Ido.
Ku zauna abunku kai da ita da surukarka Allah ya kareka daga sharrinsu zan dinga yi maka addu’a Ina daga chan…amma ba zan iya ci gaba da zaman a gidan nan ina tufka Khadija tana warware mini ba kai kuma kana biye mata!!ba zai yiu ba ba ni da wannan lokacin considering my age
yanzu lokacine da ya kamata ace na duk’ufa ibada da neman gafarar Ubangiji na.”

“Hajiya mama a yau Khadija za ta bar gid…”

Cikin fushi tace”wai
Ya ina magana ba ka ji nane??
Na ce maka ban yarda ba ko?
Ko shima taurin kai za ka yi mini ka nuna min iyaka ta?
A gaban yaranta za ka koreta saboda ni ko me??
Ka manta yadda muka yi ni da kai a asibiti ka manta abunda nace maka??

B’ata mini ran da ka yi ka k’i
jin maganata shiyasa zan tafi ka yi komai da kanka ni kam na tsame hannuna!ka bincika komai da kanka ka gyara gidanka ta hanyar da ta dace ba wai ka koreta haka kurum a gaban y’ay’anta saboda ni ba.”

Ya bud’e baki zai yi magana tace”Wallahi zan baka mamaki fa?da musu dakai kakeso
In ji ko da b’acin ran da kuka d’ura mini?”

A hankali Abhi ya d’an ruk’o hannusa alamun ya yi shiru dan ya san Hajiya mama yau kam ta riga ta gama kaiwa high!!!!

Daddy yana ji yana gani haka Hajiya Mama ta had’a kayanta tsaf tsaff ita da Junior suka tafi tsohon gidansa dan tace ko Abhi d’in ma kar ya biyo ta shima takaicinsa take ji idan kuma taga d’aya a cikinsu a inda take kafin ta wuce uk to sai dai ta k’arashe kwanakin ta a hotel har zuwa lokacin da za ta wuce uk.

Da Yamma Yashjub ya turo mata da message ta inda yake cewa”Jiya an d’aura masa aure da Kausar ba tare da yardarsaba a jiyan ya saki Kausar to kuma a jiyan Mommy ta zo ta sanyashi ya mayar da ita…yana da babban dalilin da ya sanya ba zai
Iya zama da Kausar ba sannan akwai abubuwa da dama a halin yanzu da suke damunsa waenda suka sanya ba zai iya ci gaba da zama a gari d’aya da su Mommy ba dan haka yana da buk’atar space da time dan Allah kar su nemeshi yanada buk’atar break daga fitinar family d’insa.”

Sai da Hajiya mama ta yi kuka da ta karanta message d’in Yashjub sosai ya tab’a mata zuciya,ace mutum shi da k’asar sa shi da gidan Ubansa amma fargaba da fitintinu sun hanasa ya sake ya rayu a wajen!!wannan wanne irin abu ne haka!!
Allah ya Isa tsakaninta da Mommy wallahi!…
Junior ta kira tace”ya je gidan ya duba mata idan sun riga sun tafi ko driver ne ya tambaya watak’il su gano inda suka nufa,ba wai binsa ko fad’an inda yake za ta yi ba kawai dai taana so ta san inda yake for her peace of mind..saboda itama ta goyi bayan tafiyar da zaiyi d’in d’ari bisa d’ari.

Har daren ranar Hajiya
Mama a fusace take ta k’i
ta kula kowa ta k’i ta saurari kowa kuma tace in banda Junior ba ta so ta ga kowa a inda take,hatta Yahanasu da ta je ba ta samu ganinta ba dan ta rufe d’akin ma da take ciki abubuwa da tunani sun yi mata yawa.
…….Tun ranar da su Mommy suka haifi Yashjub da Yahanasu ta kasa gane abu guda d’aya game da Mommy;kwata kwata ba ta d’aukarsa ya dad’e a hannunta kullum tana mak’ale da Yahanasu,a tunaninta kunyar Haihuwar fari ce takeyi amma sai ta lura kamar ma haushin Yaron take ji tun ba ma da ta ce a bashi madara ba wai ruwan nononta bai zo ba amma Likita yana zuwa da aka tilastata aka matso sai ga ruwan Nono fall yana zubowa…
Tun daga wannan lokacin ta saka mata ido dan tashi d’aya kwakwalwarta ta bata ko dai saboda maganar dukiya da Imam ya yi ne ya sanya Khadija ta musanya y’arta da d’an kishiyarta!!saboda a lokacin Yahanasu da take jaririya kamanninta sun yi shige da na Baba Larai da ta fara girma ne dai ta koma kamannin Daddy.
Shi kuma Yashjub da Daddy yake kama da yana jariri amma yana fara yin wayo har kawo yanzu da Khadija amaryar Daddy yake kama,sam ba ya kama da Mommy.
Chapter 110 · 0% Book details