Sashe 23
Munnubiya Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Basu bar muusu driver ko d’aya ba gashi Hajiya mama ta sanya su Yassira sun rarraba makullayen motocin su a drebobin da za su kaisu tun d’azu.
Dan tashi d’aya ta fahimci basa san zuwa da motocin su
shiyasa ta karb’e tun da wuri dan so take ayi convoy.
Haka su Hajiya mama suka jera convoy d’in nan kuwa dan kaff motocin gidan sai da suka kwashe iya na Daddy Yassir Yashjub ne kawai babu suma kuma dan sun fita a ciki ne.
Motar Ya’isha kuma ta samu matsala balle su Mommyn su fita a ciki,gasu da uban yawa…..
Suna fita Mommy ta fashe da kuka tace “Baba larai na ce miki dama ba zan iya tolerating matar nan ba kalli wulakanci da rashin tausayi da isa da mallaka a cikin gida na!”
Shiruu duk sukayi zuciyar kowa a wuya,da kyar Yassira ta share kwallar da ta zubo mata ta wuce ta nufi dak’in Kausar…da kyar kuwa ta ga makullin motar Kausar d’in dan haka ta d’auko ta fito aka samu aka tafi kaita Asibiti daga Mommy sai Yassira da Yasmeen wadda ta zauna da Kausar d’in a baya dan motar ba za ta ishe su su duka ba…..
Kaff layin su Manubiya har ma da makwaftan layin sai da aka san yau an kawo lefe,dan convoy d’insu Hajiya mama sai da ya cika layin taff.
Suna zuwa Yahanasu ta kira Manubiya tace mata ga su sunzo,ita kuma Manubiya ta sanar da Ya Musbah,dama sun ji zuwan nasu.
Aisha da Jidda aka tura suka yi musu iso zuwa parlourn su Siyama inda yake nan a gyare tsaf sai tashin k’amshi yake yi.
Manubiya tana zaune a d’akin su ta ji anata wucewa da kaya ana hada hada shiyasa tashi d’aya jikinta ya yi sanyiiI,hakanan ta koma gefe ta rakub’e ta yi shiruuu,tana jin yadda gabanta yake ta fad’uwa.
Sai da suka gama shigewa tsaff tukunna anty Umma ta zo kiran su inna da mama domin su gaisa da surukan nasu,inna ce ta samu ta je yayinda mama ta ce”sa had’u next time,bari ta zauna da amaryar”
Su anty umma sun so ta je amma tace “ba komai,”dan haka suka fita suka barta ita da Manubiya wadda ta fara hawaye kad’an kad’an…cikin rarrashi mama ta shiga lallab’ata had’e da nasihar zamantakewar aure mai ratsa jiki.
Ba mom ba hatta Ummi ta sha mamakin gidansu Manu dan a tunaninsu Yarinyar y’ar manya ce,ba wai reni ko wani abun ba,kawai dai sun yi tunanin Yash ba zai zo nan ba,amman tunda nan d’in ya zab’a to Allah ya basu zaman lafiya inshaaAllah su kuma za su so ta su rik’eta amana.
Hajiya mama ma ba ta ji komai ba,sai ma sake ganin hankalin Yash da ta yi dan ta san tabbas tun da ya zo nan tou tarbiyya da hankali ya bi ba wai kyalkyalin duniya ba!,ai kuwa inna tana zuwa ta tabbatar da hakan,dan ba kad’an ba kawaici da nutsuwar matar suka sake tabbatar mata da hankalin amaryar tasu.
Cikin mutunta juna da barkwanci suka bada lefe akwatuna goma sha biyu da su taburmi da kayan al’ada.
Su kuma su inna suka basu tukuicin naira dubu d’ari da hamsin suna ta jin kunya amman yadda Yahanasu ta sa hannu ta karb’a cikin mutunci da karamci da kamala ne ya sanya suka d’an ji sanyi dan su kansu sunsan d’ari da hamsin ya yi kad’an a wannan uban kayan da suka cika musu gida da shi.
Hajiya mama ta so a kira mata Manu su d’an gaisa,amman kuma yadda parlourn ya cika taff da jama’a ake jan numfashi da kyar ne ya sanya ta hak’ura,dan makwafta har sun fara shigowa,shiyasa suka yi musu sallama tare da fatan alkhairi bayan sunce”rana ita yau by this time inshaaAllah za su dawo su d’auki amarya su.
Hakanan aka rabu cikin mutunta juna,yayinda su Siyama Jidda da Aisha da Muhsin su ka yi musu rakiya da tray tray na pepper chicken daughnuts chin chin meatpie cakes da drinks…
Tunda suka zo ya yi parking ya kashe motar ya fara addu’a Allah ubangiji ya sa yau ma ya ganta….indai ya samu suka had’u yau to sai ya karb’i number ta,shi kad’ai ya san wahalar da ya sha a cikin watannni ukun nan,da tunanin ta yake kwana yake tashi. Kunyar Yashjub yake ji shiyasa ya gagara ce masa ya karb’a masa numberta a wajen Manubiya……
[17/09, 8:03 p.m.] Hauwajidda: MANNUBIYA
(Book 2)
Page 13
Na
Humayrah Bulama
Mikiya Writers Association.

Yana cikin wannan tunanin ya ga sun fito ita da Jidda ririk’e da trays na gifts,da sauri ya yi wuff ya fice gudun kar ma su nufi wata motar da ba ta shi ba,yana fita suka hangoshi kuma sun gane sa Abokin Yash ne shiyasa suka nefesa da niyyar gaidashi sannan su saka gifts d’in a motarsa.
Kafin su k’arasa su Hajiya mama suka fito kare da waya a kunnenta wadda kallo d’aya zaka yiwa fuskarta ka fahimci tana cikin tsananin tashin hankali,da sauri duk d’insu suka nufi Najeeb dai dai suma su Siyama sun iso kenan.
Da sauri mom tace”Najeeb!hurry up and call Yash ku fara nema mana flight za mu wuce,Na’ima ta yi accident!”
Ta fad’i hakan tana dialing number Abhi kafin ta kara wayar a kunnenta.
Da sauri duk suka ce”subahanallah!”a gigice
Da sauri Najeeb d’in ya zaro waya ya fara k’ok’arin kiran Yash tukunna ya juya ya bud’ewa su Siyama gidan baya suka ajjiye gifts d’in….
Cikin rashin jin dad’i su Aisha suka shiga yi musu jaje dukda ba su san wacecen Na’iman ba,tare da add’uar Allah ya kare gaba.
Sai da suka ga tashin motocin su tukunna suka juya suka nufi cikin gidan.
Already su Hajiya mama suna da visa d’insu a hannu shiyasa suka ci sa’ar samun flight dan a ranar suka samu na dare. K’arfe 3:00am daidai jirginsu ya d’aga gaba d’ayansu har da Abhi suka wuce uk.Su Yasira ba k’aramin dad’i suka ji ba dan atleast sun rage zafi,Ummi kuwa kamar za ta yi kuka…ta so ta bi su amman kuma in aka ce itama sai an nema mata visa tukunna za su tafi to za ta b’ata musu lokaci,shiyasa ta hak’ura akan inshaaAllah za ta je ta ga jikin Na’iman in an shirya mata komai.
Mommy ce ta zauna a asibiti tare da Kausar dan suna zuwa aka basu gado sakamokon jininta da suka ga ya yi mahaukacin hawa.
12:00am daidai Kausar d’in ta farka lokacin duk su Yassira sun tafi,tun da ta farka kuwa sam ta k’i yarda ko da had’a idanu ne ta yi da Mommyn,babu kalar lallashin da Mommy ba ta yi mata ba amma ta k’i kulata hakanan ta hak’ura ta mik’e ta fita ta je ta kira Dr aka zo aka shiga dubata.
Ko bayan fitar Dr d’in ma Mommy ci gaba da lallashin Kausar ta yi amman ko arzik’in kallo ba ta samu daga gareta ba.
Suna zaune a haka kira ya shigo wayar Mommy ganin sunan me kiran nata ne ya sanya ta saurin d’auka cike da
mamaki dan lokacin 2:00 ya wuce tace”Yasira har yanzu ba ku yi bacci ba?”
Cike da farin ciki Yasirar tace mata”Hajiya mama sun wuce,yanzun Yash ya tafi kai su airport gaba d’ayansu”.
Sai da Mommy ta tashi tsaye dan ba kad’an ba ta ji dad’in zancen Yassira tukunna tace”haka kurum suka tafi,Ina Larai?bata wayar….”
Sun jima sosai suna magana da Baba Larai….tukunna suka yi sallama,ta kashe wayar tana jin wani sanyi yana ratsata a ranta tace”inshaaAllah daga yanzu mun fara samun nasara akan duk wani mak’iyinmu kenan da izinin Allah.”
Ajiyar zuciya ta sauk’e tukunna ta koma kusa da Kausar ta zauna ta kamo hannunta kafin ta fara magana”Kausar a cikin kwana biyun nan da suka wuce kin b’ata min rai matuk’a dan ban tab’a tunanin zaki gaya min abunda kika fad’a ba…duba da yadda na rufe idanuna na ke bin bayanki a ko Ina sannan akan komai.Wallahi Allah Kausar yadda nake jin su Yassira haka nake jin ki a cikin zuciyata,kuma ko da ace su d’in ne a cikin situation d’in da kike ciki dole haka zan zuba idanu in hak’ura saboda babu yadda za mu yi.
Baba Larai ta yi iyakar bakin k’ok’arinta nima na yi amman abunda muke so d’in bai faru ba kuma tace ba ta da yadda zata yi no way out,ya kike so mu yi?”
Ba ta jira jin amsarta ba ta d’aura da cewa”na fad’a miki zan kuma sake fad’a miki cewa ki yi hak’uri a yi auren nan!
Bayan auren inshaAllah da ni da ke da su Yassira da baba larai za mu taru mu kwatar miki Yash,kuma na yi miki alk’awarin ba zan bari ki zauna da kishiya ba dan kafin ma ki shiga gidan na san ta dad’e da fita.
Amman fa idan kina so hakan ta faru dole sai kin kwantar da hankalinki kin nutsu kin yarda da mu an taru an yi abu d’aya tukunnan za mu taru mu taimaki juna.
Ban san me kike ji ba amman na san na fiki k’in auren nan,saboda ba ki san abunda auren ka iya janyomin ba shiyasa nake so ki yarda da ni saboda ko dan kai na ba zan tab’a barin Yarinyar nan ta yi lasting a gidan Yashjub ba dan zaman ta a tare da mu barazana ne ga duk wani farin ciki na da gata na.
Ahankali Kausar ta share hawayen ta tukunna tace”inshaaAllah Mommy zan yi yadda kike so.Sannan ki yi hak’uri da abunda na fad’a miki b’acin raine ya janyo hakan ba zan sake ba.”