← Book details Munnubiya Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 54 OF 137

Sashe 54

Munnubiya Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Da b’acin rai sosai ya juya ga Yashjub ya ce
“Yashjub’’
Ahankali Yash ya kalle sa ya ce
‘’Na’am Daddy’’
Cikin bada umarni da fahimtar wa Daddy ya fara magana
‘’kamar yadda na fad’a d’azu
ba zan bari giyar soyayyar da ka sha ta lalatamin zumuncin dake a tsakanin ku ba!ba zan bari wata mace ta shiga tsakanin ku ba dan bakasan yadda muka sha fama ni da mahaifiyar ka wajen ganin mun daidaita kanku ba!”

Ahankali Yash ya lumshe ido yana mamakin yadda su Daddy suka d’auki laifi gaba d’aya suka d’aura wa Manubiya…ta yaya Manubiya za ta shiga tsakanin sa da su Yasira shi kuma ya yarda..
Dan mai ya sa tun farko idan irin haka ta faru a tsakanin su ba’a d’abbak’a abun sai yanzu da yayi aure?
Kuma shi rainin da suka yi masa a gabanta ne ma ya sake harzuk’a sa ya koro su a
tunanin sa ya Isa da su.
Inda ace ci musu fuska ya so yi ai da a gaban Manubiyan zai fatattake su…Ita Manubiyan ma da suke ta cewa ‘za ta shiga tsakanin su’ bama ta san da case d’in korar sun da yayi ba.

Ahankali tunanin sa ya dawo cikin parlourn jin Daddy yana cewa “Inaso ka sanar da Manubiya idan kuma ba za ka iya ba ni zan sanar mata cewa
‘Ya’isha da Yusra za su gaida ita wannan dole ne!amma
tun daga kan Ya’isha har zuwa kan Yassir har Kausar ita ce zata gaida su tunda duk sun girme ta.’”

Da mugun sauri Yashjub ya d’ago sosai ya zubawa Daddy idanuwan sa.
“Kwarai kuwa”Daddy yace shima yana kallonsa kafin ya d’aura da cewa
“Ba wai nace dole in sun had’u sai ta gaida su ba,ruwanta ne idan taga dama ta kula su in bata ga dama ba karta kula su
amman kasancewarsu yayyu a gareta yasanya bazai yiu ace su su fara gaida ita ba.
Idan ta kula su ta gaida su su amsa
In kuma bata kula su ba
wannan alhakin yana a kanka
na ganin ka daidaita alak’ar dake a tsakaninta da su
kaine za ka nuna mata cewa yayun ta ne kuma ta dinga gaida su saboda a samu a zauna lafiya a raya zumunci.

Sai kuma magana ta biyu
‘Daga yau har gaban abada idan su Yasira za su je gidan ka a rana sau goma to baka da iko sannan baka Isa ka kore su ba!na san gidan ka ne nasan kai ka siya ka zuba furnitures ka yi komai da kanka amman ni kuma nine uban ka!
dan haka in dai ni na haife ka,to Yassira,Yahanasu,Ya’isha,Yadira,Yasmeen,Yusra,Yassir kai har ma da Kausar za su je gidan ka a duk lokacin da suke so
In ma hutu suke so su yi za su je su yi har sai sun gaji dan kansu tukunna su dawo amma kai dai baka da ikon koro su…in har kuma kace za ka yi taurin kai to zan sa ka had’omin spare key na kaff gidan naka in rabawa ko wanne a cikinsu….
Ban d’aura auren da zai tarwatsamin kan ya’ya na ba wallahi.!”
Yana gama fad’in haka ya mik’e ya ce
‘’a kiyaye” daga nan ya wuce sama.”

Shiruu Yashjub yayi ya ma kasa cewa komai

Har sai da Mommy tace
“Sai magana ta uku!Yadira ta had’a kayan ta tun d’azu
In kun zo tafiya ku wuce da ita
za ta zauna a gidan naka for sometimes.”

Saida ya lumshe idanunsa ya bud’e tukunna ya ce
“To Mommy ba damuwa,amma jiya na gaya miki za mu tafi Cyprus..y not a bari sai mun dawo t….”

Cikin tarar numfashinsa tace
“Ka wuce da ita,idan kun zo tafiya sai ka dawo da ita in kuka dawo sai ku koma tare da ita”
Ahankali yace”Mommy, jibi ne ai…”

Cikin fushi tace
“Ka san Allah Yashjub in ka gwada min taurin kai idan bance ku tafi honeymoon d’in tare da ita ba ka chanja min suna..”

Shiruu ya yi kafin ahankali ya ce “Shikenan Mommy..ki yi hak’uri”kafin ya kalli Yadira ya ce “Ki d’auko jakar ta ki yanzu zamu wuce.Bari in yi wa Daddy sallama”
Ya fad’i hakan yana mai hayewa sama.

Murna a wajen Yadira ba a magana…tashi d’aya itama ta yi wuff ta haye ta je d’auko kayanta.

Ko da Yashjub ya je wajen Daddy basa hak’uri yayi sosai
tukunna dakyar ya samu ya d’an sauk’k’o bayan zazzafan warning d’in da Daddyn ya zuba masa akan “indai har yanaso su zauna lafiya da shi tou ya ja k’annen sa a jiki…duk ranar da aka ce ya mutu shi ne Uba!…kar ya biyewa mace ta rabasu tun yanzu.”

“InshaaAllah”kawai Yashjub d’in ya ce daganan yayi masa sallama suka rabu lafiya
A ranshi yana mamakin yadda Daddyn yayi masa sannan yadda suka d’auki laifi kachokam suka d’aura akan Manubiya wadda bata ji ba bata gani ba
It’s like kamar ma Daddyn har ya fara jin haushinta ne tun kafin a je koina kawai dai bai nuna masa bane but ya fahimta dan tunda har Daddy yace “har Kausar sai Manubiya ta gaida ita ai abun babu sauk’i dan duk mutumin da Daddy zai yi favoring Kausar akan sa to yakamata ayi gaggawar gyara tsakanin su
Shiyasa kawai ya hak’ura yake ta basu hak’uri…ya san su iyaye ne fushin su garesa masifa ne sannan kuma yasan yanzu yana yin taurin kai ko ya yi wata maganar to Manubiya zai sake janyowa bak’in jini a wajensu.

A d’akin Yahanasu Yadira ta samesu dan haka suka fara shirin tafiya.

Manubiya ce tace “tana so ta je ta yiwa su Mommy da Ummi sallama”dan haka Yadira da Munirat suka tafi rakata.

Suna fita Yahanasu tace
‘Ayi hak’uri Yash
ayita hak’uri…d’azu Ina kitchen naji mommy tana waya da su
Yassira suna ajjiyewa na ji ta kiraka dama tun daga nan na san akwai matsala aikuwa da suka tashi shigowa kusan dukkansu da kuka suka shigo
wai ka kore su k’annenta kuma suna gidan yanzu haka.
Dama yadda na ji Mommy da su suna yiwa Daddy bayani shi kuma yana fad’a na san kawai ya riga ya hau shiyasa ban saka Baki ba.
Na yanzu ya faru sai a kiyaye gaba dan Allah Yash karka basu k’ofar da zaka janyowa baiwar Allah n nan bak’in jini a wajen Daddy…”

Ajiyar zuciya ya sauk’e daganan yace
“InshaaAllah’’

Ba a wani dad’e ba su Manubiya suka dawo
Sark’ar gold Ummi ta bata y’ar k’arama wadda ba za ta wuce 4OOK ba a cewarta ta ajjiye a tunanin ta za’ayi bud’ar kai ne sai ta bata tou kuma ashe su basa bud’ar kai…daga nan ta d’an yi mata nasiha.

Mommy kuwa sallama kawai sukayi daganna suka fito Manubiya tana mamakin yadda yanayin fuskarta ya chanja dan d’azu sam ba haka ta yi mata ba a gaban Yash.

Yash yaji dad’in gift d’in Ummi matuk’a kuma bai ji dad’in rashin ganin gift daga wajen Mommy ba yana sane ko a lefe ma ba ta basa komai ba Mom da Hajiya mama sai Yahanasu ne kawai suka bada…dukda ya san yau d’in ranta a b’ace yake
amman ai dama Uwa tana tanadan gift d’in amarya a irin wannan ranar ko da ace ta bayar da na lefe,ya san maybe za suce ai ya yi komai ya saka komai amman ai Ana bada gift ne saboda karramawa ba wai dan babu ba.

Har mota Yahansu da Munirat da Yassir suka rakasu da Yadira da akwatunan ta biyu.

Sai da suka ga ficewarsu tukunna suka nufi main door,
signal kawai Yassir ya yi wa Munirat daga nan Yahanasu bata san inda sukayi ba ita dai ta ganta ta shiga parlourn ita kad’ai.

Kausar tana ganin ficewarsu ta windown d’akinta ta koma ta kwanta ta fashe da wani irin kuka babu abunda yafi b’ata mata rai irin yadda yake wani rik’e mata jaka yake bud’e mata murfin mota.
Tana kwance tana ta faman kuka a haka ta ji an bud’e k’ofar d’akin an shigo.

Ta san Mommy ce dan haka tace ‘’I’m fine”
Murmushi Mommy tayi ta nemi guri ta zauna a kusa da ita kafin tace”Ki yi hak’uri Kausar
saura d’an k’an’kanin lokaci
nasan da ciwo amman ki k’ara hak’uri…
Ki duba kiga yanzu da ikon Allah Daddy ya fara karkatowa side d’inmu duk abunda muke so shi yakeyi.
Shima Yashjub d’in ki duba kiga ni ko b’acin raina ba ya son gani ai da ba haka yake ba.
Ki kwantar da hankalinki na yi miki alkawri indai kina da ni bazakiyi kuka ba…”

Ahankali ta tashi ta zauna tana kallon ta tace”thanks for everything Mommy,but na ga suntafi da Yadira kenan ba ranar dawowarta nan gidan kwana kusa kenan?idan fa ba ta dawo ba babu ta yadda za ayi mu…”
Cikin katse mata magana
Mommy tace
“Kar ki damu zata dawo
komai a hankali a keyi
ki kwantar da hankalin ki kinji”

Ahankali Kausar ta jin jina Kai daganan ta matsa ta kwanta a jikin Mommy tana mai sauk’e wata nannnauyar ajiyar zuciya.

Mommy tana so ta fad’a mata zancen tafiyar su Yash honeymoon amma kuma bata san ta Ina za ta fara rarrashinta ba dan ita kanta tun jiya da ya gaya mata ta rasa Ina za ta sa kanta…she just hope Yadira ta yi abunda ta tura yi a gidan…inshaaAllah in dai har ta yi to ita Manubiyan ce da kanta za ta tarwatsa batun tafiyar tasu.
Chapter 54 · 0% Book details