Sashe 7
Munnubiya Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Hakanan ta yi mishi ya jiki
harda d’an dessert d’inta ta had’o ta kawo masa.
Sam fuskarshi babu annuri haka ta yi ta tafi dukda kuwa ya ji dad’in zuwan da tayi amma ya kamata ya koya wa yaran nan hankali shiyasa d’azu yak’i sakarwa Yasmeen!ba zai yiu su yi fushi da shi a sanda sukaso ba tare da wani kwakkwaran daliliba sannan in sunga dama su kulashi a lokacin da suke so.Sam ba zai d’auki wannan iskancin ba,in the first place ma ba su Isa yin fushi da shi ba ko ma me ya yi ai shine Babba shine a matsayin ubansu ko da ace
shine bashi da gaskiya ba zai basu damar yi mishi wannan rashin ‘da’ar ba ballantana kuma shike da gaskiya,wannan tunanin ne ya sanya ciwon kan sa ya sake hauhauwa dan abun ya b’ata masa rai sosai especially ta b’angaren Mommy ya ji zafi kwarai a ganinsa bai kamata ta biyewa yara ta k’i zuwa duba sa ba,ya riga ya san halinta da
mugun tirjiya shiyasa kawai ya share ya yi k’ok’ari ya lallashi kansa da niyyar zuwa wajen ta anjima inshaaAllah ya bata hak’uri.
Daddy ya yi masa magana haka ma Manubiya sannan shima a karan kansa baya son irin zaman da suke yi da ita har cikin zuciyar sa amma ita take janyo komai,Mommy tanada wani hali sai wanda ya zauna da ita ne kad’ai zai iya sani
tanada shiru shiru tanada hak’uri amman kuma ba ta da dad’in zama kwata kwata
shiyasa duk wanda yaga irin zaman da sukeyi ita da shi sai ake ganin kmr shi ne ba ya kyauta mata bayan ita take tab’o sa.
Ahankali ya fesar da iska ya lumshe idanuwansa tashi d’aya tunanin dayake ta yi da rashin sanin abun da ya kamata ya yi game da rasuwar sa ya taso masa dan haka ya d’au waya ya kira Manubiya akaro na uku daga dawowarshi zuwa yanzu,dan tabbas yana buk’atar advice.
Bayan sun gaisa ne ya nemi ta bashi shawara akan ya yi bincike akan rasuwar driver d’insa ko kuma ya barshi,saboda ya san ba accident bane,dukda ya yi
alk’awarin d’aukar d’awainiyar family d’in mutumin daga nan har abada inshaaAllah to amma kuma yana gani kamar bai kyauta ba idan ya bari mutuwar sa ta tafi a banza saboda ya yi protecting kanshi
daga outcome d’in da binciken zai bayar wanda ka iya tarwatsa shi gaba d’aya.
Cikin son fahimtar da shi Manubiya ta yi masa nuni da yadda idan ya yi binciken kuma ya je outcome d’in ya yi destroying d’inshi to wa zai ci gaba da kula da family d’in mutumin??.the best thing da zai yi wa mutumin shine ya kular masa da family d’insa,shari’ah kuma su barwa Allah subahanahu wata’ala shi zai bi masa hakkinsa.
Ya ji dad’i kwarai kuma ya samu relief dan dama so yake a hanashi yin binciken.Sun d’an tab’a hira yau yaji dad’i dan babu mita babu complain haka suka sha soyayyarsu kafin su yi sallama ya katse kiran suna ji kamar kar su kashe wayar.
Suna gama waya ya mik’e ya nufi cikin gida.
Yana shiga side d’in Daddy ya wuce suka hau shirye shiryen gobe,ya dad’e sosai a wajen Daddy kafin su yi
sallama ya tafi,ba k’aramin dad’i Daddy yaji ba da ya ga hatta cokali Yashjub ya riga yayi order ya sayi komai
kuma gidan ma ya tsara komai
ya had’a komai ga lefe ma Yahanasu tana kan had’awa
ya san inda Yassir ne da zuba ido zai yi a yi masa komai….
Yashjub yana fita side d’in Mommy ya wuce sai dai yana zuwa k’ofar d’akinta ya ji a rufe ya so su tattauna ya bata hak’uri su fahimci juna amman yadda ya yi ta faman bugu ya ji shiru ne ya tabbatr masa da ta yi bacci,haka nan
ba dan ya so ba ya juya ya tafi ya barwa gobe.
A b’angaren Mommy kuwa a
lokacin da ya zo tana parlournta ta fara jiyo muryarshi yana magana da Yadira wadda take masa sai da safe
dan haka ta yi sauri ta afka d’akinta ta rufe da wuri dan ba za ta iya facing Yashjub a halin da take ciki ba ta san tsaf zata iya shak’e sa…tashi d’aya Yaro ya tsund’umata a cikin bal’ai da tashin hankali rabonta da ta yi bacci fiye da na awa biyu har ta manta,haka kurum yaje ya d’auko musu mayya!yo mayya mana idan ba mayya ba wacce irin yarinyace haka da za’a yi ta yin aiki a kanta amman a banza?.
Ba abun da yafi sake d’aga mata hankali kamar d’azu da ta lab’e ta ji Daddy yana waya da Abhi wai yana hanya ya taho,ta tabbata kenan gobe za a kai kaya a saka rana,dukda Baaba Larai ta ce ‘’ta jira taga goben tukunna in an kai shine sun yi failing’’
Amman ita a a yadda ta ga anata shirye shirye gadan gadan ta san an riga an kai ma an gama saidai su nema wani alternative d’in…and again ga maganar da Yasmeen ta gaya mata d’azu shiyasa duk take a gigice ta rasa inda za ta tsoma kanta ta d’an ji sa’ida.
Tun lokacin da Manubiya ta gama waya da Yash hankalinta yake a tashe bata nuna masa bane dan bata so ta sake assassa masa abun amma ba k’aramin firgita ta yi ba da ta ji yace’’ba accident bane wani ne ya so kashesa‘’.
Ganin ta a zaune tanata tunani ne yasanya Jidda matsowa ta shiga tambayarta….ai kuwa ita kanta Jiddan ba k’aramin firgita ta yi daga jin zancen ba amman sai ta da daure itama ta shiga kwantar wa da Manubiya hankali sannan ta d’aura da cewa’’kawai ta dage masa da addu’a Allah ya kare sa daga sharrin masharranta dama mutum kamar Yashjub dole yanada mak’iya.’’
Suna zaune suna d’an tattaunawa Baba ya shigo dan yau ya shiga busy shi da su Ya Musbah so suke su samu su gama shirye shiryen tarbar su Daddy da za su yi a gobe in Allah ya kaimu.
Sai da ya ci abinci ya d’an huta tukunna ya kira Manubiya ya zaunar da ita….nutsatstsiyar nasiha mai ratsa jiki ya yi mata,wanda sai da ta kai Manubiya ga yin kuka.
Murmushi kawai ya yi ya dafa kanta yace ‘’Allah ya miki albarka da ke da y’an uwanki Allah ya sa ki shiga gidan aurenki a sa’a.’’
Ahankali duk suka ce‘’Ameen.’’
Daganan Baba ya mik’e ya sake fita dan ba su gama ba ya shigo.
Murna a wajen su Jidda abun ba’a cewa komai dan yanzun kam maganar biki ta kankama tunda har suka ga Baba ya fara yiwa Manubiya nasiha .
Shiyasa suka yi ta murna suna cewa Allah ya sanya alkhairi’’kamar daga sama suka ji muryar inna tace’’Ameen’’cikin muryarta da suka jima suna mararin jin.Aikuwa duk d’insu rufar mata suka yi saida ta sake maimaitawa suka tabbatar tukunna Muhsin ya fita da gudu yaje ya kira su Baba a masallaci inda suke ta shirye shirye…..
A ranar murna wajen Manubiya da ahalinta ba’a magana dan har kuka sai da Baba yayi kukan farinciki da yaji muryar inna a zahiri,haka suma su Manu suka dinga kuka suna godewa ubangiji subahanahu wa ta ala.
Sun jima suna murna suna godewa ubangiji har da ya Nafi’u kafin su Baba suka fita domin zuwa su sanar da su kaka mallan maganar kawo kud’i da saka ranar Manubiya wanda za’ayi a gobe idan Allah ya kaimu……
[17/09, 8:03 p.m.] Hauwajidda: MANNUBIYA
(Book 2)
Page 03
Na
Humayrah Bulama
Mikiya Writers Association.
Yassir yana fita daga asibitin,direct gida ya nufa dan yana buk’atar ya ganewa idanunsa wanne hali
Kausar take ciki.
It’s either tana chan ta b’oye kanta tanata kuka ko kuma dai bata damu da Yashjub d’in ba shiyasa bai ganta a asibitin ba….
A b’angaren Kausar kuwa sai yanzu ta samu maganin baccin da ta sha ya sake ta.Dan haka ta mik’e ta nufi toilet,tana cikin wanke fuskarta ta fara jiyo muryar Baaba Larai a cikin d’akin nata tana cewa’’Kausar wai baccin uban me kike yi ne haka tun d’azu…’’
Dan haka ta yi maza ta k’arasa wanke fuskar tata ta fito.
‘’Lafiyarki kuwa??’’
Muryar Baba Larai ta katse mata tunanin da ta fito tana yi,ahankali ta d’an sauk’e ajiyar zuciya kafin tace’’na d’an sha maganin bacci over dose ne
shiyasa har yanzu kaina yake juya wa’’
Girgiza kai Baba Larai ta yi kafin tace’’Ni dai ince,na ga ban ga kin fito an tafi da ke ba’’
‘’ina?’’
Kausar tayi mata tambayar cikin katseta.
‘’Yashjub ne yayi hatsari shine aka tafi asibiti tun d…..’’
Da k’arfi Kausar d’in tace’’what!!!’’sai kuma ta tafi luuu za ta fad’i.
Dasauri Baba Larai ta tarota a rikice tace‘’relax,ba abunda ya same sa sai gocewar k’ashi kawai a hannu,amma Baba Iliya kam an amsa kira’’
Ajiyar zuciya Kausar ta sauk’e
da kyar ta k’arasa bakin gadonta ta zauna kafin tana haki da kyar ta samu ta iya cewa ‘’ba shi yake driving d’in ba kenan?’’sai kuma ta sake mik’ewa ganin tana shirin zubewa yasa tace’’Baaaba d’an rik’e ni jiri nakeyi,bari in je asibitin ki zo ki taya ni sauk’a’’.
Matsowa Baba Larai ta yi ta rik’eta sannan tace ‘’ki nutsu su Mommy sun kirani yanzu suma suna hanya,ki nutsu sosai mu jira ta dawo tukunna..’’
Cikin fushi ta hankad’e ta tace’’ Baaba kin san me kike fad’a kuwa ?
In nutsu kmr ya?Yashjub ne fa ba lafiya yana kwance ya yi hatsari shine kike ce min wani in nutsu??’’.
‘’Shikenan.Bismillah’’
Baba larai tace da ita da ga haka ta juya ta fita.
Yassira Kausar d’in ta kira dan ta tambayeta sunan asibitin amma kamar yadda Baba Larai tace mata itama Yasirar haka ta ce ta yi hak’uri ba sai ta je ba suna hanya suma akwai d’an case dan haka in aka ga ita ta je abun zai rinchab’e,and just so she should know yanzunnan suma Yasmeen take ce musu ta ji a bakin likitan yana cewa wa’enda suka kawo
su Yash d’in sun ce wai kamar kunce tayoyin motar tasa akayi.’’