Sashe 118
Munnubiya Part 2 Complete Hausa Novel · about 7 min read
Da kyar ta samu ta dake ta sanarwa Kausar d’in da su Yasira babu fa maganar aure dan tausayinta take ji gara kawai ta sani ta cire hope,aikuwa ranar duk dauriyar Kausar kasawa ta yi,sai da suka yi sati d’aya a asibiti tukunna ta dawo dai dai da kyar ta fara gane waye a kanta.
Dole ta sanya Mommy ta fito mata a mutum ta ce mata kawai ta hak’ura da Yashjub!!!
Ta yi trusting d’inta sannan ta taimaki kanta ta cire Yash a ranta zuwa yanzu ya kamata ace ta fahimci zuciyar Yash ta Manu ce,dan haka dan Allah ta hak’ura kawai!
Tana cikin masifa gashi babu Baba Larai dan haka dan Allah ta ajjiye komai a gefe ta tashi ta tsaya mata
she should stand by her side as her only realative ta tsaya mata ta taimaka mata akwai labarin da zata bata amma ba yanzu ba sai nan gaba.
Ta ajjiye batun soyayya haka ta taimaka mata ta rai da tsira ake yanzu dan duk abunda ya sameta to itama ya sameta farinciki da nasara ko kuma akasin hakan…sannan su Daddy sun ce har ta haihu a idanun duniya tana a matsayin matar Yashjub ne…InshaaAllah a tsakankanin nan Ubangiji ta san zai nuna musu hanyar da za su bi komai ya tafi musu dai dai.”
Ita dai Kausar tace mata “to” ne kawai amma bata gama fahimtar inda zancen nata ya nufa ba sakamokon bala’in da take a ciki,ita kanta yanzu kam ba ta san ta Ina za ta b’ullo ta sake zama mata ga Yashjub ba!!she can’t believe gaba d’aya hard work d’inta ya tafi a banza kenan???inaa da sake!.
Har yanzu babu Munirat babu labarinta Ummi ta kuma zama abun tausayin Hankalinta gaba d’aya a tashe!
Daddy ne yake dan tausar ta shi da su Hajiya mama wanda shima Hajiya Maman ce take tausar sa take tsayar da shi if not da tuni ya san na yi da Mommy…dukda ya san ba shi da wata hujja a kanta amma kawai shi he can’t tolerate her no more,ya tsaneta.
A bangaren Mama itama zuwa yanzu ba ta da wani burin da ya wuce ta saka Yahanasu da Yashjub a idanunta dukda tana tambayar Manubiya ya suke tana jin komai dan har gaisawa
sukeyi ma da Yashjub but tana buk’atar ta saka su a idanunta musamman ma da ta ji har yanzu Yahanasu ba ta yi aure ba!,ta san dole tana da buk’atar ta…..
Bayan watanni uku!!!
An yi auren Siyama da Najeeb gidansu yaana unguwar Badawa,haka shima Junior ya auri Yadira suna zaune a d’aya daga cikin gidajen Daddy dake a Unguwar Darmawa kafin ya kammala abunda ya zo yi ta karb’i transcript d’inta su wuce Uk.
Duk cikin aure biyun nan da aka yi su Manubiya ba su zo ko d’aya ba sun dai turo gudunmawa sun kuma yi addu’a.
Su Hajiya Mama ma da suka zo na su Junior ba su wani dad’e ba suka juya dan ita dama da kyar ma ta yarda ta zo.
Ya’isha tana nan yau lafiya gobe ba lafiya dan yadda ta kad’u ta damu da al’amari sai da ya girgiza su Mommy gashi har yanzu batama da shirin hak’ura da Najeeb.
Kausar ma tana nan tana fama kullum ba lafiya ga ciki ya tsufa..jira kawai take yi su Yashjub su dawo wllahi duk bala’i sai ta san yadda ta yi ta koma masa sai dai ta rasa ranta a hanyar raba sa da Manubiya da kasancewa tare da shi.
Ya Musbah ma ya kammala karatun da ya yi takardar tana fitowa ya fara shirye shirye successfully ya zana waec ya yi jamb yanzu haka neco ya ke yi kuma ya ci jamb d’in dan haka Najeeb ya sake zage damtse wajen nema masa gurbin karatu a fannin Business Administration a jami’ar Bayero uni,Kano.
Gwaggo Suwaiba ma ta zo,yanzu Mijinta shima Allah ya fara nuna masa k’arshensa kuma Itanma ta dage da addu’a sosai dan cikin ikon Allah tana cikin wnnan hali na ha’ula’i Allah ya kawo mata wasu makwabta jajirtattu wajen fanni addu’a har Al’k’urani suke rubuwata da littafai,sama sama suka fara gaisawa su kad’ai suke iya shiga gidan,sai da zama ya yi dad’i labari ya yi labari tukunna suka fahimci ashe ma Matar tana da relationship da Mahaifiyarsu Innar(very distant relative)amma.
Ita ta bata addu’o’i,kuma ta ce ta dage da Azkar da sallolin dare..Aikuwa da taimakon Ubangiji cikin ikonsa yanzu Mijinnata har islamiyya ya barta ta shiga sannan yanzu kam ana iya zuwa wajenta kuma wannan tsangwama ta kyarar duk babu,ba shi ma da lafiya ya kwanta jinya.
Ko da ta tambayesa zata zo ta ga Inna an yi auren su Jidda duk ba ta zo ba! Nan ma sam bai yi yunk’urin hanaawa ba dukda ba ya so amma shi kansa ya san yanzu kam surk’ullensa sun daina tasiri a kanta…hakanan ta taho kano ita da d’aya daga cikin y’ar mak’oftan nasu mai suna Hadiza bafulatanar Yarinya mai shekaru 17 kyakkyawar gaske siririya doguwa fara sol gashi har gadon baya.
Tunda suka zo da Ya Musbah ya kyalla ido ya ga Hadiza itama ta gansa suka kamu da k’aunar juna abun kamar had’in baki.
Satinsu biyu ya ga dai ba zai iya daurewa ba ya amayar da abunda ke zuciyarsa itama kuwa Hadiza ko irin d’an jan ajin nan na mata da kunyar fulani gagara kwatantawa ta yi tashi d’aya tace masa ‘Yes!!’
Dama su Inna sun fahimci take takensu ai kuwa Yarinyar tana gayawa Gwaggo Suwaiba suka hau murna itama kuma Inna Ya Musbah ya gaya mata,ba kad’an ba Inna ta ji dad’in had’in shiyasa Murna ta zame mata biyu,ga farin cikin ganin y’ar uwarta ga kuma farin cikin had’in Hadiza da Ya Musbah da Ubangiji ya had’a!
Hausawa sun ce ba ‘a yabon d’an kuturu sai ya shekara da yatsu amma tabbas ita kam za ta yabi Hadiza saboda Yarinyar tana da hankali ga ilimin addini ga son mutane da girmama na gaba da ita,sannan gwaggwo Suwaiba ma da suka yi watanni goma sha uku tare da su ta bada kyakkyawar shaida a kanta kuma itama ta ji dad’in had’in matuk’a.
Dama su Inna so suka yi a b’oye abun sai an saka rana komai ya kankama tukunna a fito da maganar ba dan komai ba sai dan Baraka amma Allah da ikonsa tun kafin kowa ya ji ma ita Barakar ce ta fara ji kamar wata mai duba…aikuwa nan da nan ta kunno masa wutar bala’i ta koina,ba ta tashi masifar ta sai dare ya yi ya zo bacci nan za ta hanasa bacci sai dai su kwana idanunsu biyu..amma har gobe shi nuna mata ma yake yi bai san a kan me yake take bala’in nata ba!!!shi inama ya ga lokacin yin wata budurwa???
Dukda hakan bai sa Baraka ra hak’ura ba hakanan itama Hadizar ba barinta ta yi ba dan yanzu tun safe har dare a wajen su Inna take wuni dukda fuskarta kullum kamar hadarn Kaji idan ta shiga wajen nasu amma kuma hakanan za ta zauna ta yi ta fad’an maganganu a Hadizan har ma da su Inna ko
a jikinta kuma zuwa yanzu hakanan ta hana Ya Musbahn keb’ewa ko da Innar ne wai duk dan gudun kar ya samu time da momment da Hadiza.
Kamar mai gadin sa haka ta koma ta kafa ta tsare,haka za ta yi ta zaman jiransa yana dawowa daga aiki zata fara hamma har sai sun tafi ko wajen Baba ya je haka za ta yi ta safa da marwa a bakin k’ofar parlourn nasa ta baya har da lab’e har sai ya fito sun wuce tukunna hankalinta zai kwanta.Tsabar bala’in da ta sakawa kanta ko girki ba ta iya zama ta yi ballantana gyaran gida koina ya yi datti gashi ba girki gida duk tsami kuma a da Baraka kam tanata tsafta gwanin ban sha’awa.
Sai dai kullum idan ta gama gadin nasa suka koma b’angaren su yace mata’ta d’an saka turaren wuta ta kimtsa gidan yana kyankyami’ shi kuma ya fita ya je ya siyo musu gurasa da nama…abunda Baraka ba ta sani ba shine idan ya yi fitar siyo gurasa da naman ne yake samun ganin Hadiza,dan sam ba shi ne yake zuwa siyowa ba almajirin su mai wanki da sharar gidan yake bawa shi kuwa ya dawo ciki ya wuce wajen Hadiza inda suke had’uwa kullum wajen wanke wanke ta baya.Yana lura da sa idon da Baraka take yi masa dan ko fitar zai yi sai ta lek’o ta tabbatar ya fita d’in tukunna take komawa ba ta san yana kallonta ba.
A yadda yake son Hadiza ba ya so a samu matsala a aurensu kuma zuwa yanzu ya fahimci Baraka ta hau Buzu,shiyasa ko su Inna da suke ta cewa ya fad’a mata idan auren ya rage saura sati biyu jin su kawai yake yi sai ya samu kansu zai nutsu ya zauna ya yi musu bayani sosai,domin shi kam inshaaAllah sai dai kawai Baraka ta ga Hadiza a d’akinsa matsayin matarsa ko kuma ta ji ana d’aura aure.